Showing 21001 words to 24000 words out of 78990 words
ya shige abinsa tamkar bai ganta ba .....
Taxi ta tsaida tagaya masa inda zai kaita , sai da ta shiga ta zauna sannan tafara zancen zuci " to yanzu innaje mezan ce masa nazo yi ? wata zuciyar tace " kawai kice kin yarda abinki ne shine kika dawo d'auka , tana wannan tunane tunanen nata har suka zo dai dai k'ofar Hotel d'in , fitowa tayi sannan tabiya me taxi kud'in sa yayi gaba , ta dad'e a k'ofar wajen tana kaiwa da komowa , da shawarar da zuciyar ta ta yanke nacewa wani abun ta yardar tashiga ciki......
Tunda gari ya waye Huneed ya had'a kayan sa cikin jakar sa , wajen goma na safe a can k'asar ya fita yashiga gari zaiyiwa Hajiyar sa siyayya , daga can ya biya airpot yagama komai jirgin su zai tashi k'arfe uku na rana , yana gama komai ya nufi gidan su Rauda ya tsaya daga wajen daya saba tsayawa yana lek'en harabar gidan ko Allah zai sa Sanam ta fito , yafi minty 30 amman baiga kowa ba sai yara suna ta wasan su abinsu , ganin yana k'ara b'ata lokaci yasa ya juya zai tafi , wata zuciyar tace " to inta fito mai zai ce mata ? kawai ya juya ya hau taxi yakoma Hotel d'in , a lokacin Sanam na zaune a reception dan sun sheda mata me number da ta tambaya ya fita , tana xaune ta had'a kai da gwiwa taji wani k'amshi ya doki hancin ta , tana d'agowa taga wucewar Huneed batare da ya kula da ita ba , sai da tabari ya jima da wucewa sanna ta nufi d'akin nasa......
Tana zuwa ta k'wank'wasa k'ofa daga ciki yace " yes coming , tura k'ofar tayi tashiga cikin d'akin lokacin dagashi sai tawul zai shiga wanka , tana ganin da haka ta juya da baya zata koma waje , da sauri yace " karki fita bati nashiga toilet wanka zanyi , da sauri ya fad'a cikin toilet d'in yanajin wani farin ciki da ganinta dayayi , Sanam kuwa yadda tagansa ba k'aramin tsoro taji ba , tunda take bata tab'a ganin jikin namiji haka ba sai yau , samun waje tayi ta zauna tana tunanin meyake shirin faruwa da itane.......
*Comment* plss
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ ππΉ
[9/27, 09:46] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir* *Rahamanir Rahim*
Chapter 15.
Bayan minty 7. saiga Huneed ya fito sanye da kayansa , har lokacin Sanam tana duniyar tunani batasan ma ya fito ba sai da yayi mata gyaran murya , da sauri ta dawo daga tunanin tana d'ago kai a hankali tana dubn sa , wani kyau yayi mata cikin k'anan nun kaya , Huneed yana da k'ira me kyau dayake jan hankalin 'Yan mata da ita , kana kallon da kaga cikakken namiji jarumi wanda baya shayin komai , yana kama da wannan sabon jarumin na indi'a Allu Arjun , sosai Sanam ta shagala a kallon sa tamkar wacce ta warke daga makanta , ganin ta kafeshi da idanu yasa yace mata " Hy 'yan mata wannan kallo haka kuma ? wata kunya ce ta rufe Sanam tayi saurin yin k'asa da kanta , a hankali ya furta " ya kike ya gajiyar ki ta dukan ruwa , ina fatan bakiyi zazzab'i ba dai ? Sanam tace " lafiya lau babu abinda nayi , kaima dafatan kadawo lafiya ? Huneed yace " yes nrml nake dan yanzu haka ma shirye shiryen barin k'asar nake , wani abu Sanam taji ya tsaya mata a k'irji wanda ta shiga tambayar ko meye oho , cikin zuciyar ta dai taji rashin dad'in maganar tasa dayayi , tambaya ta shiga yiwa kanta meyasa dayace zai tafi taji rashin dad'i haka ? maganar sa ce ta katse ta da yace mata " ko akwai wani abun da kike buk'ata ne ? da sauri Sanam ta girgiza kai alamar babu abinda takeso , Huneed ya tab'e baki irin ko ajikinsa ya juya gaban mirror yana gyara kansa , ganin shuru Sanam tak'i yin magana yasa ya juyo yace " Babbar direba ko dai akwai abinda kika manta ne shine kika zo d'auka ? Sanam tace " Ae daman ina tunanin ko nabar d'an kunne na anan ne , Huneed yayi murmushi sannan yace " baki bar d'an kunne ba sai agogo nagani gashican , nuna mata inda A gogon ta yake na gold. Sosai Sanam ta shiga mamakin halin Huneed , kwata kwata ma ita ta manta da Agogon ta d'an kunnen ma ta fad'esa ne kawai , dan tasan bata bar d'an kunne ba ashe tabar a gogo , Agogon ta yana da mutuk'ar tsada dan Daddyn tane ya siyo mata shi a America , ba yadda Mumy Nafeesa batayi ba akan ya siyo mata irin sa amman yak'i , akan hakan har matsala suka samu da Daddyn lokacin , d'auko Agogon tayi ta saka a hannun ta tana cewa " nagode sosai bari nazo natafi Allah ya sauke ka lafiya , Huneed yace " Ameen nagode da addu'a , amman ke sai yaushe zaki koma gida ne ? Sanam tana saka takalmi tana fad'in " bazan dad'e ba nima zantaho , da kallo Huneed yabi yatsun k'afar ta ta wanda yayi bala'in had'uwa cikin takalmin filet , a hankali ya furta " komai naki yayu yadda akeso , halinki ne kawai mara kyau duk da naga kin fara rage wani Abun........
Har Sanam ta bud'e k'ofa zata fita Huneed yace " inaso ki kula da kanki har kidawo gida , sannan karki k'ara yin direbin a cikin wannan k'asar saboda nan ba Nageria bace , Banda saka k'ananun kaya plss ki kula sosai kinji k'anwata , Sanam wani dad'i takeji mutuk'ar Huneed nayin magana , musamman maganar sa ta k'arshe da yakira ta da sunan k'anwar sa , a hankali tace " zan kiyaye insha Allah , amman inason card d'inka saboda wani lokacin , murmushi Huneed yayi sannan yace " ni da ba ma'aikaci ba me yahad'ani da card , kawo phone d'inki insa miki number ta sai mudunga gaisawa tunda yanzu munzama abokai mundaina fad'a ko ? murmushi Sanam tayi tana d'aga kai alamar Ae , mik'a masa wayar tayi yasa mata number sa ta Nageria sannan ya bata wayar ta ta , tana ansa ta dube sa tace " Allah ya sauke ka lafiya ta juya ta fita bata jira cewar saba , har ta fice daga d'akin kwata kwata ya kasa motsi , wata k'aunar ta ce ta shige sa lokaci d'aya , sai sannan ya kuma jin dadin yadda ta fara canza halayen ta , wani dad'i yaji ya kamashi ganin yadda tasa doguwar rigar daya ce ta dunga sawa , haka ya gama shiri cikin farin ciki tare da kewar Sanam d'in , sosai yakejin k'aunar ta na ratsa cikin duk wasu k'ofofi na jikin sa .........
Sanam na fitowa ta sauko k'asa tasamu waje guda ta zauna , kuka ta shiga yi tana share hawayen da ke zubo wa akan kuncin ta , cikin zuciyar ta take fad'in " meyasa nakejin wani iri a game da kai ? tabbas najin tamkar inbishi mutafi iya jiya kawai nakejin wani abu game dashi , wata zuciyar ta ta kuma tace " Son shi kike Sanam wannan shine So , da sauri tace " a'a ba soyayya bace kawai kulawar da yayi danine lokacin da Asuk yaso ketamin haddi , ta dad'e tana sak'e sak'e akan Huneed sannan ta mik'e tafita daga cikin Hotel d'in .......
Huneed tuni ya janyo trolly d'insa yafito daga Hotel d'in , yana tafe yana murmushi shi kad'ai wanda yakejin wani shauk'i , Sanam har lokacin ta kasa barin k'ofar Hotel d'in saboda son tasake ganin Huneed , tana hangoshi tayi saurin lab'ewa bayan wata bishiya tana lek'oshi , wani kyau taga ya kuma yi mata ga glass daya sa tamkar ba indiye , Taxi ya tsaida ya hau suka tafi sannan Sanam ta fito daga wajen data b'uya , da kallo tabi bayan motar har ta k'ulewa ganin ta sannan itama ta tsaida Taxi tayi gidan su Rauda........
*Hmm wallahi nagaji da rashin Comment dinku*
[9/27, 09:47] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* πͺ
https://www.facebook.com/111403834371046
β¨β¨ *{{* *H.W.A* *}}*β¨β¨
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 16.
Har aka gama shagalin bikin Rauda Sanam bata cikin sukuni , tunda Huneed yatafi tamkar yatafi da duk kan wani sukuni nata , gashi shuru sai jiran kiran wayar sa take amman bai kira taba , haka suka kai Rauda gidan ta sosai anyi shagali tamkar baza adaina ba , haka aka mik'a Amarya gidan ta kowa ya kama gabansa...
Sanam tuni tunanin Huneed yafara damunta , tuni tabi shafin sa na Face book tana neman number sa , akuwa tayi sa'a tasamu ranar murna sosai tamkar tayi tsalle , kiran wayar tasa tashiga yi har ta katse bai d'aga ba , haka ta kuma bin number tasake kira amman yanzu ma baid'aga ba , sai da tayi kira biyar ba a d'agawa har tagaji ta ajiye wayar tana jin babu dad'i , ring din wayar ne yasa da sauri ta d'auki wayar tana tunani ko shine ya biyo ta , number Hajiya Nafeesa tagani wanda tasa Mummyna , d'an guntun tsaki taja sannan ta d'aga wayar tana fad'in " Mummyna barka da wannan lokaci , Hajiya Nafeesa cike da kissa irin ta ta ta manyan mata tace " Barka kadai My Luv yakike ya Turkey ? Sanam tace " lafiya lau Mummy ya gida ya kowa da kowa ? lafiya lau Luv kunsha biki nasan kin gaji sosai amman yaushe zaki dawo? Sanam tace " ban fara shirin taho ba amman inaso intaho gida dan ina da abubuwan da zanyi , Hajiya Nafeesa cikin ranta tace " nima nafiso kiyi kidawo dan insamu infara gabatar da aikina , a fili kuma tace " yaka mata kidawo dan ina missing d'inki sosai , gashi Fahad ma kullum cikin zance ki yake wai gidan babu dad'i tunda bakyanan , Sanam ta tab'e baki tamkar tana ganin Fahad d'in tace " ina nan tafe Mummyna kice ina gaida Uncle d'in , daga nan tace " Byee Mum zan fita yanzu sai nadawo mayi waya , kafin Hajiya Nafeesa tace wani abu tuni Sanam ta kashe wayar .....
Tunda Huneed yadawo Nageria aiki yasa shi gaba , dan yana dawowa aka turasu Zamfara dan maganin ' Yan ta'addar dasuka dami garin , tunda yatafi baya samun wani lokaci gashi wajen babu network bare yayi waya , kullum zuciyar sa tana tunanin Sanam dan yasan dole zatai ta zaman jiran kiran sa , wata zuciyar tace masa " wannan mara kirkin ai farin ciki zatayi da baro k'asar dakayi , wata zuciyar tace " aikuma alamun ta kamar tadaina komai datakeyi , haka yashiga tunani akan Sanam yana lissafo kyan dirinta da kuma uwa uba kyan fuskar ta baki d'aya .....
Ranar da suka dawo gida da nasarar da suka samu a zamfara , ranar Sanam tayi masa wanna kiran ya shigo sai dai yana kallo yak'i d'agawa , dan basosai yake d'aga kiran number da baisani ba , duk da yaga number ba ta k'asar bace amman kwata kwata bai kawo Sanam ce ke kiran saba ,
Acan b'angaren Sanam kuwa tunda ta fice yawo bata dawo ba sai dare , koda ta dawo wanka tayi tasa kayan bacci ta kwanta abinta , dan kwata kwata Sanam bata damu da ibada ba , karatun addinin ma ba damunta yayi ba bare , dan haka tana kwanta tawa ta d'auko wayar ta tafara chat da k'awayen ta , sai ta duba number Huneed taga yana kan online , da sauri tafara murna tana shirin yi masa magana , wata zuciyar tace mata " kina mace me Daraja da Aji amman kiyi masa magana , inajin ma yana ganin kiranki d'azu amman yak'i d'agawa , sannan ai tunda yana da number ki yakamata ace ko sau d'ayane ya kiraki kun gaisa , haka Sanam tabi shawarar zuciyar ta ta fasa yiwa Huneed magana , hirar su suka ci gaba dayi ita da Diyana tana ta basu labari akan k'awayen su na Nageria , sai wajen k'arfe d'aya sannan Sanam ta sauka daga online tayi kwanciyar ta , sai dai me ? tana kwanciya hoton Huneed yafara yi mata yawo a idanun ta , musamman lokacin data gansa d'aure da Tawul da kuma lokacin data fad'a jikin sa a k'ofar gidan su Rauda , haka tai ta juyi ta kasa bacci tamkar mara lafiya , tashi tayi ta kuma d'aukar wayar ta tashiga Face book shafin sa , aikuwa tana shiga taga bai dad'e dayin posting ba da shigar sa ta cikakken Army , zoom d'in pic d'in tayi tana k'are masa kallo , murmushi tayi tana shafa fuskar sa tana fad'in " tabbas ka cika cikakken namiji wanda yaka mata a jinjinawa , babu Namijin da Sanam ta tab'a so a duniya sai kai , har wani lumshe ido take tana shafa masa fuska tare da tuno yadda yake komai nasa irin na isassun maza , tuni ta danna kiran number sa dan tana buk'atar jin wanna daddad'ar muryar tasa , addu'a tashiga yi aka Allah yasa ya d'aga mata kira wanna karan , ring take har ta yanke ba'a d'aga ba , sake kira tayi karo na biyu sai da takusa yankewa sannan ya d'aga yana fad'in " Assalamu Alaikum , cike da tsoro Da rawar Murya Sanam tace " wa'alaikas salam barka da dare , da sauri Huneed ya watstsake daga baccin da yasoma kamashi , cikin ransa yafara fad'in " tabbas wannan muryar ta Sanam ce , duba number yayi yaga number ta k'asar waje ce , da sauri yace " wanakeji kamar K'awata Sanam ? Murmushi Sanam tayi har sautin na fito tace " nice nakira dafatan ban shiga hak'k'in ka ba kana bacci ? Murmushi Huneed yayi yace " kin shiga hak'k'ina kuwa dan ina tare da mata ta kika kirani , yanzu haka gashican ta turoni waje ta kulle d'akin ta , Sanam jitayi wani abu ya tokare k'irjin ta wata zufa ta karyo mata , cikin ranta tace " dama mutum nan yana da mata bata sani ba ? kamar yasan abinda take tunani kenan yace " kinsan mantawa nayi kwata kwata ban sheda miki ina da mata ba har da yara guda biyu , yanzu gashi kinjawomin kwanan k'ofar waje , cikin murya me sanyi Sanam tace " kayi hak'uri wallahi bansan kana da mata ba da bazan kira ka a wannan daren ba , kabata hak'uri kaji sai da safe , kafin ta kashe wayar yayi sauri yace " lah babu komai muci gaba da magana kinji , yakike yana baroku dafatn komai nrml ? Sanam da kishi yake taso mata kawai tace masa " lafiya nake komai yana nan yadda kabarshi amman kayi hak'uri sai da safe , bata jira cewar saba ta kashe wayar dukan ta tana jifa da ita , kafin kuka ya biyo baya tare da jin haushin kanta na kiran datayi masa , tabbas da tasan yana da aure da baza ta saka shi a cikin ranta har haka ba , yanzu yazatayi da Soyayyar sa wacce tashiga zuciyar ta lokaci d'aya ? kuka take sosai tana jin babu dadi , gashi ita tun tasowar ta batason kishiya koda ta sittira ne bare ya kai ga had'a miji , kuka takeyi tare da addu'ar cire son Huneed daya kamata batare da ta gama shirya hakan ba.......
Huneed tunda ya fahimci Sanam kishi ne yasa takashe waya , dariya yashiga yi sosai yana murna yadda ta fad'a son sa , dan tabbas wanna kad'ai zai tabbar masa da ta fad'a soyayyar sa , kwanciya yayi yana tuno yadda komai nata yake , murmushi yake in ya tuna yadda take gudu sosai a titi ranar da yaje k'asar Turkey , a hankali ya furta " Iluv u my Baby Sanam I really luv u more ,