Showing 48001 words to 51000 words out of 78990 words
mata ba , Jaydeen tunda motar Huneed ta tsaya yaji ajikin sa Sanam na ciki , dan dama me gadi ya sheda masa ta fita ita da wani , kishine ya kamashi tuni ya nufo wajen motar Huneed d'in , b'angaren da Sanam ke ciki ya shiga bugawa , Huneed ransa ya b'aci shima ya bude murfin b'angaren sa ya fito , Duban juna sukayi dukan su sannan Huneed yace " Malam lafiya zaka zo kana bugamin glass d'in motar ? Jaydeen ya kalli Huneed cike da isa yace " wacce take cikin motar nakeson magana da ita Malam bakai ba , Huneed ransa ya sake b'aci yace " meye had'in ka da mata ta dazakayi magana da ita ? Jaydeen yace " matarka kuma ashe har ka aureta batare da sanin iyayen ta ba , inaso kasani Sanam bata dace da namiji irinka ba ka kalleka ka kalli motar da kake hawa , wannan kad'ai ya isheka kasan ita ba sa'ar auren ka bace , Huneed yayi murmushin takaici sannan ya kalli Jaydeen yace " sannu d'an gidan k'aruna rainon biskit da chocolate , inaso kasani tunkafin in canza maka kalar fatar jikinka , Jaydeen ya kalli Huneed yaga lallai inyace zasuyi fad'a to tabbas sai ya doku a gunsa , dan jikin sa ko ina a murd'e yake , amman duk da haka Jaydeen bai karaya ba ya ci gaba da gayawa Huneed magana ....
Tuni Huneed yayi kansa yafara kai masa naushi a fuska , dai dai lokacin hancin motar Hajiya Nafeesa ya sako kai cikin gidan , da sauri ta fito daga motar ko kashe ta bata tsaya yi ba , tana zuwa tafara fad'in " meye hakan zangani kai meyasa baka da hankaline kasan dan waye kake duka haka ? Huneed yanajin abinda tace kuma yasan dashi take , ko waiwayo ta baiyi ba yaci gaba da dukan Jaydeen ,
Sanam tana cikin motar tana kallon duk abinda yake faruwa , sai dai ko ajikinta tunda dama ita bawani k'aunar Jaydeen d'in take ba , dan dama yadameta da yawa ga uban kiran waya ga kuma turo mata test kullum, Marin da Hajiya Nafeesa ta d'auke Huneed dashi shine yasa Sanam katse tunanin ta tana mai bud'e murfin motar ta fito ...........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* π
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
_Wannan Page d'in gaba d'aya sadaukar wane gareki , Aysha Fulaniπ₯° Happy Anniversary One years, Allah yakaramuku zaman lafiya keda Oga ππ»ππ» Allah yakawo mana yara nagari masu Albarka Ameenππ»ππ»ππ»π₯°πΉπ_
Chapter 33.
Tana k'arasowa ta dubi Hajiya Nafeesa wacce ke uban sababi akan dukan da Huneed yayiwa Jaydeen , Sanam tace " amman Mumy meyasa zaki mari iya Huneed shi wannan sakaran bazaki maresa ba ? duban ta Hajiya Nafeesa tayi baki sake tana mai maita kalmar da Sanam d'in tafad'a , batare da Sanam tadamu da yanayin kallon da Hajiya Nafeesar keyi mata ba taci gaba da magana " Na ruga na zab'i wanda zanyi rayuwa dashi meye zaka dunga damuna , inaso kadaina zuwa wajena domin bazan tab'a saurarka ba , ta kalli Huneed wanda ransa yake a mutuk'ar b'ace tace " dan Allah My Dear kayi hak'uri da Hukuncin Mumy a gareka , Huneed jin abinda Sanam tace masa da kuma irin magan gun datayi yasa yaji zuciyar sa tayi sanyi , yasan ko iya haka ta nuna shine acikin zuciyar ta bawani ba , Huneed yace " Bakomi Baby indai akanki ne komai za'amin zan jure , abinda bazan iya jurewa ba shine wani banza yadunga kallemin ke ko kuma ya furta miki kalmar so , Jaydeen da hancin sa ya fashe da bakin sa tuni ya juya rai a b'ace ya shige motar sa yabar harabar gidan , shima Huneed sallama yayiwa Sanam sannan ya koma ciki motar yaja ya fice daga cikin gidan .....
Sanam ko takan Hajiya Nafeesa bata bi ba tashige cikin gida abinta ........
*Bayan kwana biyu*
Kwata kwata Hajiya Nafeesa ta d'aukewa Sanam wuta , ko hanyar bata bari su had'a ko da yaushe sai wasan b'uya take , in Sanam taje ganin ta sai ta tadda me aikin ta ta shaida mata batajin dad'i , ahaka tagaji da zuwa itama tashiga sabgogin gananta , ....
Soyayyar Huneed da Sanam sai k'ara yawa take , kwata kwata yanzu Huneed nema yake yakasa tafiya aikin sa , koda yaushe suna tare a waya kuma ko yaushe indai zasuyi waya sai ya mata maganar Mumyn twins , yana kuma nuna mata matsayin ta a gunta da kuma cusa mata soyayyar ta , yauma kamar kullum suna cikin waya da ita ya shiga tambayar ta wasu littattafai tasani na addini ? shuru Sanam tayi batare da tace masa kanzil ba , jin hakan ya tabbatar masa ko kad'an Sanam batayi islamiyya ba , murmushi yayi sannan yace " sai nemo mata malamin da zai dunga koya mata karatun alk'ur'ani da wasu littattafan na addini , batare da musu ba Sanam ta yadda dan itama tanaso tasan wasu abubuwan ,.....
Bayan kwana biyu da maganar su Huneed yasamo mata malamin kamar yadda yayi mata alk'awari , a sati zai dunga zuwa sau uku kuma Huneed ya gaya masa sunayen littattafan da zai koyar da ita , tuni Malam yafara zuwa kuma ba laifi Sanam tana bashi had'in kai......
Hajiya Nafeesa da Fahad zaun suna tsara yadda shirin su zai kasance , Maryam wacce itace cikon ta ukun su tuni tasamu ciki wanda bazaka ce ga namijin da yayi mata shi ba , mazan da take bi Ita kanta baza ta tantance ba , tuni Hajiya Nafessa tasa mata 2milloins a account , Maryam sai murna take dan itama zata faso gari kwana nan , Duban Hajiya Nafeesa tayi sannan tace "Hajiya inaso in badamuwa zan dawo gidan nan da zama , Hajiya Nafeesa tace " babu damuwa amman inaso kibari me gidan nan yatafi dan jibi zai bar k'asar nan , kuma zaiyi kamar wata tara ko goma bai dawo ba , dan akwai wani aiki dazaije koyowa , Maryam tace " nagode sosai Allah yanuna mana lokacin , Hajiya Nafeesa ta tashi ta haye sama abinta tabar Fahad da Maryam zaune , suna ganin Hajiya Nafeesa ta mik'e suka matso jikin juna suka fara tab'a juna da shafe shafe , Fahad yace " Babyna kisamun 1m. A account d'ina tunda kinga nine nasamo wannan aikin , Maryam ta d'an turesa tana fad'in " gaskiya bazai yuwuba Dear , kaifa Auntynka ce koda yaushe ka tambaye ta zata baka , nikuwa iya rabona zanci kafin inyi gaba , dan haka kayi hak'uri zan baka 200 Hundrend in sunyi maka , Fahad sosai yaji haushin abinda Maryam d'in tace , sai dai ba yadda zaiyi tunda nema yake kuma shi bawani kud'i Hajiya Nafeesa ke bashi ba , .....
Tunda ga ranar Hajiya Nafeesa ta tsiri cutar k'arya , haka ta k'i zuwa tayi barkar Twins har Akayi suna , koda Alhaji Abba yayi mata magana sai tace bata da lfy yanzu daga ta mik'e jiri take gani , amman da zarar taji sauk'i zata shirya taje taga yaran , ganin lokacin da take maganar ma tana kwance yasa yarda da ita kuma yace dole ta shirya taje taga likita , dama tuni ta biya likitan ta kud'i akan in sunzo ita da Alhaji lallai yace ciki gareta , aikuwa suna zuwa akayi gwaje gwaje likita ya sheda musu tana da ciki , sosai Alhaji Abba ya shiga murna yana mata addu'ar Allah ya sauketa lafiya , bakin sa ko rufuwa bayayi dan murna da baiwar da yake ganin yasamu , haka suka taho gida sai lallab'a ta yakeyi yana wani ririta ta , ita kuwa sai wani langab'ewa take tamkar me cikin gaske , Alhaji Abba yana shigowa palor yafara k'walawa Sanam kira , dan yasan zata fi kowa farin ciki da wannan ciki tunda kullum burinta Mumyn ta ta haifa mata k'anne , Sanam ta sauko daga sama tana fad'in " Daddy lafiya kuwa naji kana k'walamin kira ? Alhaji Abba yace " bani goron Albishir kafin infad'a miki , hannu ya mik'o mata yana murmushi , kallon Hajiya Nafeesa tayi sai wani ya mutsa fuska take ita ala dole me ciki , sake duban Mahaifin nata tayi sannan tace " Daddy nidai kafad'amin inji sai nabaka ko me kakeso , Murmushi ya sake yi sannan yace " Mumyn ki zata haifo miki k'ani ko k'anwa nan da 8Month , wani tsalle Sanam ta doka tana matsawa kusa da Hajiya Nafeesa "Mumy dagaske zaki haifo yaro daga cikin ki kema ? Murmushi Hajiya Nafeesa tayi sanna tace " Ea My luv zan haifo miki k'ani me kama dake wanda zaki dunga d'auka kina yawo dashi kema , nan Sanam ta shiga murna sosai , da sauri ta hau sama tana d'aukar wayar ta ta shiga kiran Huneed , yana d'agawa tafara cewa " My Husbee Katayani murna Mumyna tasamu ciki itama , Huneed yayi murmushi sannan yace " congrat My Baby kice dai yanzu zaku k'ara yawa kinzama Babba tunda gashi kina ta samun k'anne , Allah yarabata dashi lfy yasa watarana Albishir zakimin gashi kina d'auke da cikina , Sanam najin haka ta kashe wayar tana mejin kunyar maganar tashi......
Diyana ta kira tashiga gaya mata itama , murna ta taya ta tare da cewa " nace inzakije gidan Mumyn Twins kifad'an amman naji ki shuru , Sanam tace " bantashi zuwa bare in fad'a mikin amman kijira sai randa zani zan miki magana , tana kaiwa nan ta katse wayar tayi jifa da ita tana me fad'awa kan gadon ta .......
Da Alhaji Abba cewa yayi dole sai dai Hajiya Nafeesa ta shirya su tafi tare saboda ya dunga kulawa da ita , amman sam tak'i yarda ta lallab'ashi aka ai nan da wata biyu zata ware taji sauk'i , sannan ta k'ara da cewa zata kira waya can Gidan su a turo mata wata k'anwar ta , da haka ya barta tare da cewa ba lallai yayi wad'an nan watannin ba , nan yatafi yana kewar iyalin sa su duka suma suna kewar sa , musamman Sanam wacce itace ta rakashi air pot har kuka tayi lokacin da jirgin nasu zai tashi ....
Bayan kwana biyu tuni Sanam tafara zuwa Universaty ta abuja dan kammala digree d'in ta , duk kwana uku kuma Malamin Islamiyya nazuwa yana koya mata karatun alkur'ani , sosai tana maida hankalin ta a karatun duka , lokacin Huneed yayi tafiya zuwa Lagos wani aiki , sai dai ko yaushe suna manne da junan su a waya tamkar su janyo junan su , ......
Tuni Hajiya Nafeesa ta ware tadawo yadda take abinta , Maryam ma tuni ta dawo gidan da zama dan haka jin kanta da k'aryar ta sai suka k'aru , tana so ta shigewa Sanam amman ko kad'an ba fuskar daza ta tunkare ta , Koda Sanam taga Maryam a gidan sai Hajiya Nafeesa ta shara mata k'aryar wai 'yar gidan k'anin Mahaifin ta ce , Sanam da yake bata da damuwa da sabgar su shiyasa ko ajikinta.....
Yau takama asabar Su Sanam suna hutu dan haka tana gida abinta tana shan barci , wayar tace tashiga ruri cikin barci ta janyo ta ta danna ta kara a kunne , jin muryar Muradyn ta yasa ta wartsake tafara rikitashi da shagwab'ar ta , aikuwa Huneed ya kuma narkewa harji yake kamar ya bud'e ido yagan sa a gaban Sanam d'in sa , nan ya sheda mata gobe Sunday yana hanyar dawowa dan shima yakasa komai yanzu in ba zuwa yayi yaganta ba murna sosai Sanam ta shiga yi tana fad'a masa yadda tayi missing d'in sa , haka sukaita misayar kalamai har suka yi sallama da juna zuwa anjima .....
Tana kashewa ta kira Diyana tace mata lallai ta shiryo yanzu zata raka shopping , dan turarikanta sun kusa k'arewa gashi My Husbee d'in ta zai dawo , Diyana tace gatan dan tasan itama zata d'ibi abin datake so .....
Ba'afi minty Goma ba sai ga Diyana lokacin itama Sanam ta shirya cikin shigar ta me kyau sai k'amshi take , tana zuwa suka fito tare suna hira abinsu , dai dai wajen da zasu shiga mota Maryam da Fahad suka taho hannu cikin hannu , turus Diyana tayi tana kallon su tare da cewa " wanake gani Kamar Maryam Harka ? Sanam ta kalli Diyana tare da kallon su Maryam d'in , itama Maryam Diyana take kallo duk jikinta na rawa kada asirin su ya tonu...........
[9/27, 10:05] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*π
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 34.
Ganin za'a ranfota yasa Fahad yayi saurin zungurar ta , da sauri ta saita kanta tana duban Diyana tare da cewa " Baiwar Allah banganeki ba ni sunana Maryam amman bansan d'aya sunan da kika kira ba , Diyana ta dube ta sosai sannan tayi murmushi tace " Haba Harka ko bacci nake naga me kama dake ai saina ganeta bare kuma ido biyu , Fahad a k'ufule ya kalli Diyana yana fad'in " ke dallah Malama ki iya bakin ki , wanne irin sunan banza ne haka kike kiranta dashi tunda tace bata sonki ba ana dole ne ? aikin banza kawai sai wani shishshigi kike da cusa kai , sosai maganar ta tab'a zuciyar Sanam , tsawa ta dakawa Fahad d'in tana cewa " to kai ina ruwanka tunda ba kai take tambaya ba , juyawa tayi ta kalli Diyana tace "kema gashinan kinjawa kanki ai , koda yaushe ina gaya miki ki rage cusa kai a irin wannan wajen , tsaki taja sannan ta wuce motar tabar su Fahad baki bud'e , Diyana itama motar ta nufa tana mamakin yadda Maryam Harka ke neman raina mata wayo...
Sai da suka fita daga harabar gidan sannan ta dubi Sanam wacce har lokacin ranta yake had'e , a hankali ta furta " Besty wannan Maryam d'in kodai 'yar uwar kuce ? nifah abin mamaki yake bani ganin yadda ta raina min wayo , Sanam tana tuk'in Motar ta kalli Diyana tace " to ke a inah kika santa ? Diyana tace " wallahi A k'asan Unguwar mu take , duk cikin fad'in Unguwar nan bawanda bai san Maryam Harka ba , amman k'iri k'iri tana neman ta maidani wata bugun shaho , Murmushi Sanam tayi sannan tace " Maganin ki ai tunda kin iya saka ido ai dole ayi miki haka , dama basu rufeki da duka ba kuma kinsan ba kwatar ki zanyi ba , Diyana tace hmm " nifah dole sai nabi duddugin abinda yakawo Harka gidan ku , dan duk inda taje to tabbas ba Alkairi akwai wani k'ullin ak'asa , Murmushi Sanam tayi sannan tace " aiki ne yasameki wallahi , Ni Mumy cemin tayi 'yar kanin Baban tace , kinsan bawani sanin Family d'in ta nayi ba , tunda duk rabin su suna can Borno state acan suke da zama , tunda tazo gidan naga take taken ta tanaso tasamu fuska a gurina nikuma tuni ba fara had'e girar sama da k'asa , dan kwata kwata banji ko kad'an zan bata fuska ba , Diyana ci gaba tayi da Maimaita kalmar 'Yar K'anin Baban ta , to itadai tun tasowar ta a layin su bata tab'ajin su Maryam harka suna da 'Yan uwa masu kud'i ba ,
Asalima Baban ta harya mutu sana'ar sa Baduku ne , ko zaman makoki ba'ayi masa ba saboda basu da halin yin abincin masu zaman makoki ,