Showing 42001 words to 45000 words out of 78990 words
abunda ya tsaya mata a zuciya zai wuce........
[9/27, 10:02] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATIN* π
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Raheem*
Chapter 29.
Sama Alhaji Abba ya haye yana fad'in " yaufa ciki na babu komai ataimako da ruwan lipto kafin asamar min abinda zanci , Hajiya Nafeesa tabishi da harara amman a fili ta furta " Angama Angon k'arni , murmushi Alhaji Abba yayi cikin zuciyar sa yana jin dad'in sunan da takirashi dashi , .....
Hajiya Nafeesa tana shiga cikin kitchen tasa kuka mara sauti , yanzu ta k'ara tabbatar da cewa Hajiya Maimuna tayi mata zarrah ta ko ina , dana sani tashiga yi na irin abubuwan datayi a baya , dan danan Abubuwan dasu faru a baya suka shiga dawo mata cikin kwakwalwar ta.......
*Wacece Hajiya Nafeesa*
Malam Umar shine asalin Mahaifin Hajiya Nafeesa , haifaffiyar garin Maiduguri ce asalin Bare bari , Mahaifin ta Malam Umar Da Mahaifiyar ta Falmata , su Uku iyayen su suka Haifa Tahir Nafeesa da Fahad , Mahaifin su bawani me k'arfi bane amman yana da wadatar zuci , Mahaifiyar su tana sana'ar ta ta hannu a cikin gida , da haka suke rufawa juna asiri suke zaune lafiya , tun tasowar Nafeesa take da buri sosai , ko cikin k'awayen ta tana da nuna itad'in me aji ce da kuma nuna itad'in yar wani ce , Ba laifi Nafeesa kyakkyawa ce sai dai Bak'a ce ita ko kuma ince chocolate colour , tana da tsayi me tafe da dirin jiki shiyasa take rud'a maza sosai da wannan surar ta ta , Nafeesa tana da son abin duniya shiyasa duk saurayin da yazo gunta in taga babu mamora atare dashi take yagashi , hakan yasa duk samarinta suka kasance attajirai masu kud'i sosai , sai dai duk cikin samarin nata ba wanda ke sonta da aure sai dai su shek'e ayar su.....
Tuntana b'oye b'oye kar iyayen ta sugane har suka fahimci halin data ke dashi , Nan Mahaifinta Malam Umar yayi ta fad'a yana cewa sai ta fito da miji yayi mata aure ko kuma ya bata wanda yayi masa , akwai wani Alhaji da sukafi shek'ewar su tare , sosai takejin dad'in Mu'amala dashi dan haka tasamesa da maganar itafa agida andame ta akan tayi aure , dan haka kawai ya turo gidan su suyi aure tunda suna son juna , Alhaji Dauda yanason Nafeesa sai dai shi ba soyayyar aure yake mata ba , Amman ko dan ya huta da ita dole ya aureta na wucin gadi tun da tana sonsa , batare da b'ata lokaci ba yaturo akayi bikin su shida ita....
Bayan tarewar ta a gidan sa tagane Matan sa Uku Yayan sa goma sha takwas , haka ya had'asu gida d'aya tashiga takurar gaske , dan kwata kwata matan sa basu da mutunci haka ma 'Yayan nasa , dan ma itama bata da mutuncin shiyasa suke shakkar ta kad'an.....
Tana shiga tasamu ciki Alhaji Dauda naganin haka yasa ta agaba akan saita zubar , shifa bai aurota dan tayi ciki yanzu ba kawai yanaso su huta ne shida ita , Nafeesa tace itafa bazata zubar da ciki har sai ta haifesa , nan Alhaji Dauda yafita sabgar ta ko kallo bata ishe shiba , a hankali tagane duk matan gidan sune suke d'aukar nauyin yaran su wajen karatu da maka mancin su , ganin haka yasa taje ta samu Alhajin Akan ta shirya aje a zubar da cikin , dan itakam bazata iya wahala da yara ba haka kawai wanda azubar ta huta , haka kuwa akayi Alhaji Dauda baki har kunne ya d'auketa sukaje aka zubar da cikin , tunda ga lokacin Alhaji Dauda yashiga bawa Nafeesa kwayoyin hana d'aukar ciki , itama batare da damuwa ba ta dunga d'ibgawa cikin ta dan son faran ta masa rai , ana haka ta wayi gari Mahaifar ta tasamu matsala ko ciki bazata iya d'auka ba , anan kuma Alhaji Dauda ya fara tsiyacewa ko Abinci ba'aci A gidan sa , tuni Nafeesa tashiga yi masa iskan ci kala kala har sai da yagaji yasaketa , yana sakin ta tadawo ruwa ta goge tamkar batayi aure ba taci gaba da iskancin ta , tun Malam Umar nayi mata fad'an takuma wani auren har yagaji ya k'yaleta .....
Ana haka suka taho kawo Amarya Abuja wata k'awarta , Anan Allah ya had'ata da Alhaji Abba ya nuna yana sonta , tuni ta amince duba da yanayin data gansa Alhajin burni ga kud'i ga kuma Kyau , ya sheda mata yana Mata kuma shekarsu hud'u da aure amman bata haihuba , Sosai Nafeesa taji kishi akan matar tasa , dan tasan tabbas matar sa tana hutawa ina ma bashida mata ita kad'ai zai aura , amman jin dad'in ta guda d'aya jin ance matar tasa bata tab'a haihuwa ba , tana komawa Alhaji Abba yaje gar Maid neman auren ta , bawani jan lokaci aka d'aura musu aure Amarya Nafeesa ta tare gidan mijinta dake Abuja.....
Bata dad'e da tarewa ba Allah yabawa Hajiya Maimuna ciki , kar kaso kaga murna wajen Alhaji Abba , Hajiya Nafeesa tayi bak'in ciki sosai amman saboda kissa sai take nuna tamkar tafi kowa murnar samun cikin , saboda wannan ciki da Hajiya Maimuna tasamu sai da Alhaji Abba ya biyawa mutum arba'in Hajji , ciki harda iyayen Hajiya Nafeesa da ita kanta da kuma Yayan ta Tahir , .....
Ciki na shiga wata tara Alhaji Abba yadaina zuwa ko'inah , kullum yana tare da Hajiya Maimuna yana bata kulawa , wata ranar Alhamis ta tashi da nak'uda akayi asibiti da ita , cikin sauk'i batare da tasha wuya sosai ba Allah yabata 'Yar ta kyakkyawa me kama da ita , 'Yan Uwa da Abokan Arzik'i sosai suka tayasu murnar Samun K'aruwa , Hajiya Nafeesa cike da kissa tashiga hidima kullum tana gidan Hajiya Maimuna tana rungume da Da Jaririya , kayan barka akwati set goma ta had'awa Jaririya duk saboda iya kissa , sosai Alhaji Abba yaji dad'i na irin yadda take nunawa gudan jinin sa Soyayya , itama Hajiya Maimuna sosai taji dad'in irin hidimar da Hajiya Nafeesar keyi , Ranar suna yarinya taci Suna Hafsat sunan Mahaifiyar Alhaji Abba suke kiran ta da Sanam , sun sha hidima sosai sannan kowa ya watse aka bar me jego da Baby Sanam , tundaga nan Hajiya Nafeesa ta shiga yin Magiyar abata Sanam in antashi Yayeta , lokacin da aka Yayeta Alhaji Abba da kansa yad'aukota batare da Hajiya Maimuna tace kanzil ba , dan dama ita macece me hak'uri basawa ba fitar wa , tunda ganan rik'on Sanam yadawo k'ark'ashin Hajiya Nafeesa , kuma tunda ganan tashiga horor da Sanam da tusa mata ak'idar tsanar Mahaifiyar ta , ....
Wannan shine tarihin Hajiya Nafeesa a tak'aice ...... .......
*kuyi Manegi*βπ»
[9/27, 10:04] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
π€¦π»ββοΈπ€¦π»ββοΈ
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* π
( Domin Marubuta Mata )
β¨ (W.W.A) β¨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 30.
Ajiyar Zuciya Hajiya Nafeesa tayi tare da yin wani murmushin mugunta , tabbas Lokaci yayi da zata fara yak'i da Hajiya Maimuna , a haka ta gama had'a masa ruwan lipton d'in ta fito daga kitchen ta nufi sama , karo taci da Sanam zata sakko itakuma , Hajiya Nafeesa cike da kissa tace " Baby ashe munsamu k'aruwa Mumyn ki tacan gidan ta haihu , ya mutsa fuska Sanam tayi sannan tace " nifa ba ruwana da haihuwar ta , gashi daga haihuwar ta har Daddy yafara cewa wai yaran sunfini kyau , aikuwa Hajiya Nafeesa cikin zuciyar ta wani dad'i taji ya ratsa ta , dan tasan Halin Sanam da son yara da kusan kullum sai tasa ta gaba da tambayar yaushe zata haifo mata Baby , ko kuma ta dunga rigimar itama sai an haifo mata k'anne tunda taje gidan su k'awayen ta taga suna da k'anne , a haka har ta girma tana k'ulaficin ganin tana da k'anne , sai gashi k'annen sun samu amman bata murna da samun su , wani dad'i Hajiya Nafeesa taji sannan ta dubi Sanam tace " kwantar da hankalin ki Babyna , kinsan Daddyn ki da tsokana amman nasan ko rabinki bazasu kamo a kyau ba , wani murmushin jin dad'i Sanam tayi sannan tace "shiyasa nake k'aunar ki Mumyna , nasan kece kad'ai bazaki juya min baya ba , Daddy kuwa nasan yanzu batani yake ba ta sababbin Babys d'in sa yake , Hajiya Nafeesa tace " Rabu dashi ai da tsohuwar zuma ake magani , kece dai tagaban goshi ko ank'i ko anso , Sanam tayi murmushin jin dad'i tare juyawa zata sauka daga benen ......
Har ta kusa sauka Hajiya Nafeesa ta d'aga murya da cewa " yaushe zakije kiyi mata barka tare da gano jariran ? Sanam ta juyo tana fad'in " Mumy nifa wallahi banson zuwa amman Huneed yace dole na shirya gobe muje tare , wata fad'uwar gaba Hajiya Nafeesa taji dan ko kad'an ita dai wannan Huneed d'in bai yi mata ba , tunda tafara ganin sa taji ta tsanesa gashi kuma yadda ta fahimta Sanam tafad'a soyayyar sa ko daga ganin yadda take rawar k'afa dashi , cike da kissa tace " yauwa nagode wa Huneed da ya miki hakan , in ba haka ba nasan ba zuwa zakiyi ba lallai yayi min maganinki , turo baki Sanam tayi cike da Shagwab'a tana cewa " au Mumy haka zaki ce ma kenan ? kawai dai zanje ne shima badan shi ba sai dan ra'ayin kaina sannan kuma inason inga yaran da Daddy yace sunfini kyau , Murmushi Hajiya Nafeesa tayi tana nufar d'akin ta tana fad'in " baki da dama Baby kedai akwai rigima , cikin ranta kuma tashiga tunanin yadda zata raba Sanam da wannan shegen Huneed d'in .....
*Washe gari*
Tuni Sanam tabawa Diyana labarin Mumyn Asokoro ta haihu , Diyana tashiga murna tare da cewa Besty yaushe zamuje barka inga 'yan biyu ? nasan yaran sun had'u sosai koda bangan su ba , kinsan Allah Sanam inason Mumyn Asokoro saboda tana da mutunci gata me kyau har ta fiki kyau , Sanam cike da jin haushin Diyana tace " sai ki koma gidan ta da zama ki ta kallon ta , tunda kinason ta saboda tana da kyau ko to madallah sai anjima , kit ta kashe wayar batare da Diyana tayi magana ba , Diyana rik'e da waya a hannu tana mamakin irin tsanar da Sanam tayiwa Mahaifiyar ta ta , wannan wacce irin rayuwa ce ace mutum da uwar sa amman ko zan cen ta bayaso anayi masa , ina ma itace tasamu uwa irin Hajiya Maimuna wallahi da duniya sai tasan wace Uwar ta , mata gata me mutunci ga kyau tamkar ita tayi kanta , duk kyan Sanam inta tsaya gaban Hajiya Maimuna wallahi sai ta dusashe , tab'e baki Diyana tayi sannan ta furta " duk wannan makirar matar itace tasa kika tsani Mumyn ki Sanam , amman insha Allah watara na zaki so ta kuma zaki k'aunace ta , ......
Huneed tunda sukayi waya da Sanam yace " ta shirya k'arfe biyar na yamma zai zo suje barkar , tana sama tunda garin Allah ya waye bata sakko ba , ko kayan break a kitchen d'in ta na cikin d'aki ta had'a komai ta karya , Hajiya Nafeesa ce ta turo k'ofar d'auke da sallama a bakin ta , Sanam ta amsa mata tare da cewa "Sorry Mumy yau banzo na gaidaki ba keda Daddy ko ? Hajiya Nafeesa tayi murmushi tare da cewa " nasan baki tashi da wuri bane Daddyn ki kuma ya tafi gidan masu jego tun k'arfe goman safe , Sanam taji rashin dad'i yanzu har Daddyn ta yafara fita batare da yagan ta ba ? wani haushin jariran taji ya kama ta , duk yanayin data shiga Hajiya Nafeesa na kallon ta , kuma dama abinda takeso kenan ace Sanam tafara jin haushin Mahaifin nata , shima kuma zata san yadda zata fara tura masa tsanar Sanam d'in shikenan tayi musu farraqu , lokacin da Alhaji Abba zai fita sai da ya shigo d'akin Sanam yasamu tana bacci , har shafa mata kai yayi yana fad'in " Rigimammiya ta haryanzu bata motsa ba , Hajiya Nafeesar ce cike da kissa tace masa yabar mata 'yar ta tana bacci karya tashe ta , murmushi yayi yafice yana nima bazan so ta tashi yanzu ba kar tashiga yimin rigima , amman yanzu sai ta nunawa Sanam cewa wai d'okin Yaran sa sababbi yake dan haka ya manta da ita , aikuwa tayi nasarar zuga Sanam dan sosai tashiga jin zafin Mahaifin nata tare da Twins d'in da Hajiya Maimuna ta haifa ........
Wajen K'arfe hud'u da rabi Huneed yakira wayar Sanam , d'agawa tayi lokacin tana zaune akan gadon ta tana shan chocolate , dan Sanam akwai shan zak'i tamkar sha zuma ma , d'aga wayar tayi a hankali ta furta Sojanaπ , har cikin jikin sa yaji muryar ta ta tare da jinsa a wani yanayi da yakasa bam ban cewa , cikin kasalalliyar Murya yace " Babyna ina fatan kin shirya dan banajin zan kai har k'arfe biyar d'in nan batare da nayi tozali da idanun ki ba , Sanam cikin murya me sanyi tace " ni dai bazani ba gaskiya dan banason inje inga sunfini kyau , gashi a saboda su yau Daddy ko damuwa baiyi dani ba harya fice baiga lafiya ta ba , kuma haryan zu Daddy bai kirani ba dan haka naji banason ganin su kawai mubarshi , Huneed ji yayi Dariya ta kamasa a hankali ya furta " haba Babyna taya zasu fiki kyau kinsan yadda kike da kyau kuwa ? kwantar da hankalin ki kizo muje mugansu kinga sai kiga kaman nin su , ni ajikina naji basu da wani kyau Babyna tafi su komai da komai , ked'in fa sarauniya ce acikin matan duniya kinga kuwa taya za'afiki kyau , nan Huneed ya shiga lallab'a Sanam da kalamai masu ratsa zuciya , aikuwa yayi nasarar shawo kanta tace zataje bari ta shirya yabata Minty 20 .......
Huneed sosai yayi dariya bayan ya kashe wayar , tabbas ya lura da Sanam k'uriciya nadamun ta , daga haifar yara tafara takun sak'a dasu tabbas yasan akwai me zuga Sanam , wannan kishin datakeyi da Maman yaran gaskiya yayi yawa , murmushi yayi tare da cewa " Zan yi k'ok'arin yadda zanyi naga nasa miki soyayyar k'annen ki koda ba uwa d'aya ce ta haifeku ba .....
Bayan minty 20 tuni Sanam ta shirya cikin wani had'adden less , d'inkin riga da siket ya kamata sosai d'in ki , less d'in kalar pink yaji duwatsu a jiki sosai , ta d'auki blue d'in gyale k'arami ta yafa tare da saka wani blue d'in takalmi me tsini , fesa turarukan ta tashiga yi masu k'amshi da tsadar gaske , tana gamawa ta kira wayar Huneed tana fad'in " Sojanaπ na shirya kai nake jira kawai , Huneed yayi murmushi yace " My angel kifito harabar gidan ku tun d'azu nake jiran sarauniya ta , murmushi tayi tare da kashe wayar sannan ta fito , koda tazo palor bata samu kowa ba haka tafice abinta ....
Tunda ta fito idanun da yake kanta yana yaba