Showing 63001 words to 66000 words out of 78990 words

Chapter 22 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3682

sauk'i ? Sosai Mumyn taji dad'in yadda Sanam d'in ta tambayi jikin Hajiyar ta , cike da fara'a tace " jikin ta da sauk'i sosai tace tana gaidake kuma yaushe zakije kugaisa ? Sanam tace " zanje insha Allah inkwanar mata biyu , nan Mummy ta mik'e tana fad'in " bari nayi wanka nadawo sai muyi magana , ta mik'e ta hau sama tabar su Sanam tana wasa da Twins abinta tamkar babu abinda ke damunta.......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️






*NA*
*Zee MD*





*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/










*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 42.



Mummy wanka tayi sannan ta tada sallar magriba , tana cikin yin addu'a taji wayar ta nayin ring. Bayan ta shafa ta duba Dan ganin me kiran nata Huneed tagani , lokacin wani Kiran yakuma shigowa ta d'aga tare da yin sallama , amsawa yayi cike da bata girma tamkar tana ganin sa , gaisheta tare da tambayar ta twins , Nan tace lafiya lau suke tashiga tambayar sa aikin da yakaisu katsina , Huneed yace"Mummy nifa nataho gida Dan yanzu haka ma ina hanyar zuwa wajenki , Mummy bazan iya aikata komai ba mutuk'ar bana sanin halin da Sanam ke ciki , nakira ta Amman kwata kwata bata d'agamin waya duk nadamu dayawa ,. Hajiya Maimuna tayi murmushi sannan tace "haba Soja kana Captain guda kana wasa da aikin ka , yakamata kacire damuwar Sanam aranka katsaya kabawa k'asar mu tsaro , Huneed yace " Mummy nidai ganinan zuwa sai muyi magana , Allah yakawo ka lafiya ta furta tare da kashe wayar......


Saukowa tayi k'asa tasamu Sanam har lokacin tana wasa da twins, zama tayi tana duban ta sannan tace " kinyi sallah kuwa ? Sanam tace " nayi tunkafin kushigo , Mummy ta gyara zama sannan ta dubi Sanam tace " inason inji abinda yake damunki dan haryanzu hankalina ya kasa kwanciya da yadda Naga yanayinki , Sanam tuni idanun ta suka Fara hawaye , batace komai ba illah kunnawa Mummyn nata videon Huneed da Diyana datayi , tana kunna Mata ta tashi da sauri ta hau sama jin kuka na niyar k'wace Mata......



A can b'angaren su Hajiya Nafeesa kuwa , duniya tayi musu sabuwa kowanne sai nishad'i yake , Maryam ta kalli Hajiya Nafeesa tace " Aunty yakamata infara zuwa awo tunda cikin yayi wata biyu , Hajiya Nafeesa tace " kibari nayi magana da likitana komai yace sai kifara zuwa , Maryam ba haka tasoba sotake kawai Hajiya Nafeesa tadunga bata kud'i tana fantamawar ta , bata rasa ci ba Bata rasa sha ba sai dai gaskiya Hajiya Nafeesa bata sakin kud'i shine babban matsalar ta , suna zaune Kiran Alhaji Abba yashigo wayar Hajiya Nafeesa d'agawa tayi tana wani murmushi , Alhaji Abba yace " uwar biyu yakike ya daren ? Hajiya Nafeesa tawani lumshe ido tana shafa cikin tamkar me cikin gasken tace " habadai Alhajina guda d'aya ma ai ya isa tunda Babbar Yaya tayi mana twins , murmushi Alhaji Abba yayi sannan yace " kikasani ko kema ki haifo Mana Twins d'in , Kinga shikenan nahad'a garke babba , Murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " to Allah yakawo Mana masu albarka , da Ameen ya amsa sannan yace " Ina shalelena take kwana biyu bamuyi waya ba saboda bana samun lokaci , kuma yau nakirata Amman wayar ta akashe take ,. Hajiya Nafeesa ta tab'e baki tamkar Yana ganin ta tace " Sanam Ni kaina yau kwana d'aya bansata a idanuwana ba , da sauri Alhaji Abba yace " kwana d'aya kuma to Bata gidan ne ko Yaya ? Cike da k'osawa da maganar Sanam d'in dayake Mata tace " kasan yanzu kullum sai sunfita yawo da wannan yaron Huneed , Dan nayi Mata magana shine take fushi Dani , kuma bawanda ya lalata Sanam yanzu inba wannan yaron ba , kwata kwata batajin magana duk ta canza halinta ,. Alhaji Abba shiru yayi Yana nazarin maganganun Hajiya Nafeesar ,. Amman meyasa Huneed zaiyi Masa haka ? Ya d'auki amanar 'yarsa yabashi saboda yaga tana k'aunar sa shine zai lalata Masa ita , A hankali Alhaji Abba yace " idan Kinga tashigo cikin gidan ki kirani a waya ki had'ani da ita , Hajiya Nafeesa da sauri tace " karka kuma had'ani da ita kasan in kayi Mata magana zata tsaneni sosai tunda tafara yimin rashin kunya , kawai idan tashigo zance Mata takiraka kaga daganan sai kasan yadda zaka b'illo Mata da maganar , sosai ran Alhaji Abba ya b'aci yakashe wayar batare da yakuma cewa komai ba , ....


Hajiya Nafeesa tayi wani shu'umin murmushi najin dad'in nasarar data Fara samu , take ta yanke shawarar bama sai ta kashe kud'inta a banza ba gurin malamai , kawai wannan kissar zatayi batare da ta kashe kud'i ba cikin ruwan sanyi taraba Sanam da Mahaifin nata ,. ....




Mummyn Twins tana cikin kallon videon da Sanam ta kunna Mata taji sallamar Huneed , ajiye wayar tayi tana Masa lale da zuwa , ko a fuska bata canza Masa ba ko kuma ta nuna Masa tasan abinda yake faruwa , Dan zuciyar ta bata gamsu da cewa Huneed zai aikata abinda tagani ba , durk'usawa Huneed yayi Yana gaidata ta amsa cike da kulawa da sakin fuska , bayan sungama gaisawa ya zauna kan kujera Yana d'aukar abokin sa , wasa yashiga yi dasu Nan Mummy tasa Murja ta had'o Masa abin motsa baki....


Bayan murja ta kawo masa tace Mata ta d'auki su Twins su hau sama gurin Auntyn su ,. Kwata kwata Huneed bai kawo Sanam bace tunda baiyi tunanin tazo gidan ba ,
Bayan Murja ta bargun Huneed ya kalli Mummy yace "Mummy Dan Allah ki kiramin Sanam wallahi ni inna kirata Bata amsamin waya ,. Mummy wallahi bazan iya komai ba mutuk'ar Banga Sanam nasan laifin danayi Mata ba , Mummy tace " inaso ka kwantar da hankalinka indai Sanam ce tana cikin gidan Nan , wata irin zabura Huneed yayi Yana mik'ewa tare da cewa " Mummy Ina take plss inason ganin ta ,. Hajiya Maimuna tabbas ta yarda da irin son da Huneed d'in keyiwa 'Yar ta , kuma batajin zai aikata abinda tagani , kallon sa tayi sannan tace inaso ka nutsu ka zauna bara naje nataho da ita Dan inaso ku dukan ku naji abinda yake damunku dan samun mafita , Huneed zama yayi yana maida numfashi tamkar wanda yayi gasar tsere , mik'ewa Mummy tayi ta nufi sama Dan tahowa da Sanam....


Sanam na kwance kan gadon Mummyn sai kuka takeyi , da sallama Mummy tashiga ta zauna bakin gadon , a hankali ta furta " Sanam inaso kitashi kije ki wanko fuskar ki kisameni a k'asa muyi magana , Bata k'ara magana ba tamik'e tabar cikin d'akin....


Bayan kamar minty 5 da dawowar Mummy sai ga Sanam ta sauko daga sama , kwata kwata bata kula da Huneed ba saboda kanta na k'asa saboda kukan datasha , tunda ta taho Huneed yake kallon ta saboda ganin yadda ta koma duk ta rame kana ganin ta kasan tana cikin damuwa kamar yadda shima yake , .


Tana k'arasowa zata zauna idanun ta suka dira kan Huneed dake zaune ya zuba Mata idanuwan sa , k'irjin tane ya buga take taji ranta ya b'aci tamkar ta juya ta koma Amman hakan tasan bazai samu ba , d'auke kanta tayi daga kallon sa tasamu waje ta zauna tafara wasa da yatsun hannun ta , Mummy tayi gyaran Murya sannan tace " Huneed gaka ga Sanam inaso kufad'amin abinda ya had'aku ku dukan ku , shuru sukayi aka rasa me magana daga ciki , Mummy tace " to shikenan tunda bawanda zaiyi magana Bari intashi in baku guri , yunk'urawa tayi zata mik'e da sauri Huneed yace " Mummy karki tafi zanyi magana , komowa tayi ta zauna batare da tace komai ba ,
Huneed yace " Mummy nidai haryanzu bansan laifin danayiwa Sanam ba , tun Randa nataka naje k'ofar gidan k'awar ta wannan abun yafaru , Nan Huneed ya laburtawa Mummy komai Sanam na zaune tanaji , Mummy tace " tabbas wannan shirine aka shirya muku , kuma gashi anyi nassara akan Sanam d'in sosai , Mummy Nan ta kunnawa Huneed videon da aka turowa Sanam a waya tabashi tace yagani ,....


Huneed Yana Fara kallah ya zabura Yana fad'in " tabbas wannan shirine aka shirya Mana , wallahi Mummy yadda nafad'a muku haka abin yafaru , Mummy tace " basai ka rantse ba Huneed wallahi duk me hankali yaga wannan abun yasan shirine , kuma kowaye yayi muku hakan to tabbas na cikin gidane ,. Sanam shuru tayi tana nazari meyasa zasuce shirine wannan ? Wata zuciyar tace Mata " tabbas shirine ki yarda Sanam taya Huneed da Diyana zasu miki haka ? Kinajin duk abinda Huneed yace ankirasa anfad'a Masa a waya , sai kuma tashiga tunanin tabbas da ta tashi daga bacci tayi mamakin ganin wayar ta a kashe , kenan hakan na nufin ankashe Mata wayar ne saboda Kar Huneed ya kirata , tabbas itama ta yadda shirine to waye yake Shirin ganin sun rabu ? Huneed ne ya katse mata tunani da cewa " Mummy zanyi bincike sosai akan wannan al'amarin kubani kwana daya rak , Mummy tace " kayi komai a nutse Dan kasan shi mak'iyi Koda yaushe shima cikin shiri yake , sannan inaso kununawa mak'iyan sunci galaba akan ku , Kar ku yadda ku nuna musu kunshirya kuci gaba da takun sak'a , gefe d'aya kuma kuci gaba da soyayyar ku , Nan taci gaba dayi musu nasiha me ratsa zuciya har kowannen su ya gamsu da lallai shirine akai musu Dan anaso arabasu, Sanam sosai tayi Nadama akan abinda taje gidan su Diyana tayi , .....
Mummy tunda taga Sanam tasaki jiki ta mik'e tabasu waje Dan su zanta....


Huneed tamkar me jiran tashin Mummyn yayi saurin dawowa kusa da Sanam , jikin sa har Yana gugar nata yace " Haba Bbyna kin wahalar Dani dayawa fa , kinsa naje yak'i Amman nakasa tab'uka komai saboda tunaninki , Sanam ta d'ago da idanuwan ta da suka sha kuka tana hararar sa , Huneed ya kama kunnen sa Yana fad'in "ayimin afuwa Dan bazan iya jurewa fushin My Wifey na ba ,. Sanam ta turo baki tana cewa " bawani Matarka meyasa ka saka Diyana a jikin da Ni kad'ai nakeson mallakar sa ? Huneed yace " taimakonta nayi ganin tana neman fad'uwa , Amman da nasan hakan zai ruguzamin farin cikin mata ta Dana barta tafad'i , sosai Sanam ta yadda da Huneed Dan dama sharrin zuciyane yasa ta yadda da abinda tagani batare da tayi bincike ba, Nan Huneed yaci gaba da lallab'a Sanam tare da yi Mata kalaman soyayya masu kwantar da hankali ,


Sai wajen sha d'aya na dare sannan Huneed yace " zanzo natafi gida Naga dare yafarayi , kuma kiksan yau nadawo kuma inaso gobe tunda safe nafara binciken masu son shiga tsakanina da My Wifey d'ina ,. Sanam tace " Yana da kyau Dan Nima zanso sanin suwaye suka saka ayi Mana hakan , Mummy ce ta sakko Dan haka Huneed ya mik'e Yana cewa Sanam " zantafi Amman Dan Allah karki koma can gidan yanzu kibari sai bayan kwana biyu , Sanam tace " band'auko kayana ba da sauran abubuwan buk'ata ta , sai dai ko gobe naje nad'auko inyaso sai nadawo , Nima kaina Ina bukatar yin nesa da gidan na kwana biyu , sosai Mummy taji dad'in kalaman Yarinyar tata , a zuciyar ta tayi Mata addu'a akan Allah yakuma tsareta yasa daga haka yarinyar ta tadawo gareta,......


Bayan tafiyar Huneed Sanam da Mummy suka ci gaba da tattauna maganar akan abinda yafaru , Kiran wayar Hajiya Nafeesa ne yashigo wayar Sanam , sai da ta kalli Mummyn ta kafin ta d'aga Kiran , Hajiya Nafeesa tace " My luvly Wai Ina kika shigane yau ? Tund'azu nake nemanki a waya Bata shigowa , kuma na Kira wayar k'awarki itama Bata shiga Daddyn ki ma yakiraki yace min Bata shigowa Anya lafiya kuwa ? Sanam tace " lafiyalau Mummy Ina gidan Mummyna shiyasa , kuma wayata akashe take shiyasa Bata shigowa sai yanzu na bud'e , Hajiya Nafeesa cike da son jin abinda Sanam d'in tace tace " wacce Mummyn naki kenan ? Sanam tace "Mummyn Twins Aman zan kwana , yanzu zankira Daddyn sai muyi magana dashi sai da safe Mummy , Bata jira me Hajiya Nafeesar zatace Mata ba takatse wayar ,. Hajiya Nafeesa rik'e da waya a hannu tayi saroro tana mamakin canzawar Sanam d'in haka........






*Comment* plss


*'Yar Mutan Kanawa*
_Ce_✍🏻
[9/27, 14:27] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️






*NA*
*Zee MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/










*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 43.



Hajiya Nafeesa rik'e da waya a hannu sai mamakin irin canzawar da Sanam tayi , tabbas akwai wata a k'asa lallai Hajiya Maimuna ta tashi tsaye , gashi lokaci d'aya Sanam na neman komawa wajen mahaifiyarta , Hajiya Nafeesa ji tayi wani Abu ya tsaya Mata aranta Wanda tarasa gane meye , shin murna zatayi da komawar Sanam haka ko kuma bak'in ciki ? Duk irin yadda ta tsani Sanam da kuma yadda takeson rabata da Mahaifin ta sai data samu kanta da jin kewar Sanam d'in , .....



*Washe gari*


Tun asuba Mummyn Twins ta tashi Sanam tayi sallah , bayan sun idar da sallah Mummy ta d'auko Hisnun Muslum tafara koyawa Sanam yadda zata dunga yin azkar ,. Sannan ta Gaya Mata fa'idar yin Azkar saboda neman kariya daga sharrin Mutum da Aljan , bayan sun kammala Sanam takoma bacci saboda ba saba tashi tayi a wannan lokacin ba.,.....




Huneed bayan ya idar da sallar asuba Yana fitowa daga masallaci ya nufi unguwar su Diyana Dan Fara bincike ,.
Yana zuwa yasamu wajen me saida Drinks ya zauna akan banci , Yana zaune har gari ya k'arasa wayewa mutane suka Fara wucewa , sai wajen takwas me shagon yazo ya bud'e , sallama yayiwa Huneed sannan ya shiga Yana aikin gyare gyare , Huneed wayar sa ya d'auko yafara danne danne a haka har yagama gyara shagon ya fito ya zauna kan Bencin da Huneed yake ,. Tunda Huneed ya k'arewa Isma'il kallo yasan lallai Yana da mugun son kud'i , Dan haka yayi amfani da wannan Yanayin nasa yace " Malam inason kamin aiki kuma kafad'i ko nawa kakeso zanbaka ,.
Isma'il ya kalli Huneed da sauri sannan yace " Oga wanne irin aiki kenan ? Sannan taya zanyi maka aiki bansan kaba kawai daga ganinka yau sai inyi maka aiki , Huneed yace " sanina bashida amfani kawai aiki nakeso kamin na Rana d'aya , Amman in bazakayi ba zantafi innemi wani , Huneed na Gama magana ya mik'e Yana shirin barin wajen ,. Da sauri Isma'il yace " Oga kadawo muyi magana zanyi maka kafad'amin wanne irin aiki zanyi ?
Huneed yayi wani murmushi Wanda shi kad'ai yasan ma'anar yinsa yadawo ya zauna ,.
Duban Isma'il yayi yace " inaso kafad'amin ranar Asabar d'in data wuce wasu masu motar k'irar Vibe fantia sunzo wajen nan suntsaya, kalar motar Blue ce misalin k'arfe hud'u da minty 40 na yamma me suka zo yi unguwar Nan ? Isma'il take yagano su Maryam mutumin Nan yake nufi , Nan Isma'il yace " Oga gaskiya bangane me kake Nufi ba ,kuma Ni ranar ma banbud'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login