Showing 12001 words to 15000 words out of 78990 words

Chapter 5 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3672

banzo na bud'e ba , kuma banji k'arar motar ki ba shiyasa tuba nake , wuce wa tayi batare da tace masa kanzil ba har ta shige k'ofar falor su , binta yayi da kallo yana mamakin yanayin ta , cikin ransa yana addu'ar Allah yasa dai lafiya .......




Sanam na shiga cikin falor sukayi ido biyu da Fahad , da sauri ya mik'e yana fad'in " Oyoyo my Special ina kikaje haka ? tunda nazo nake cigiyar ki banji kiba , daurewa kawai Sanam take dan kanta ne yake ciwo sosai , murmushi tayi sannan a hankali ta furta " na d'an je gidan su k'awata ne dafatan kazo lafiya , Fahad ya rik'o hannun ta yana fad'in " lafiya lau nazo My Special me yasa me kine naganki haka ? Sanam ta zame hannun ta a hankali tana fad'in kaina namin ciwo bari na hau sama , bata jira amsar da zai bata ba ta haye sama abinta......


Da ido Fahad yabi bayan ta ana had'iyar wani mugun miyau , cikin ransa yake yaba tsarin halittar da Allah yayi wa Sanam , dan duk iya yawon dayayi k'asa she baiga mace me dirin jikin Sanam ba , dan haka ko tak'i ko taso dole yasha romonta .......




Huneed yana shiga gida ya fad'a toilet yayi wanka tare da d'auro arwala , yana fitowa ya nufi masallaci lokacin har sun tada sallah , bayan an idar yayi lazimin sa da yasa ba sannan ya taso ya shigo cikin gida abinsa , samun Hajiyar su yayi ita da Hisham suna hira abinsu cike da so da k'auna , shima zama yayi suka ci gaba da hirar abinsu , sai bayan sallar isha'i sannan suka ci abinci ya fito , Hisham ne ya biyosa yana cewa " wai Ya Huneed yaya ta kasance kai da Sanam ? murmushi Huneed yayi sannan yace " nakuma saka mata doka ta biyu inaso naga yadda zata kuma karya ta , murmushi Hisham yayi yana fad'in " Wannan yarinyar kuwa zata iya bin doka ? amman bari dai mugani nan da gobe ko zata iya , Huneed yace " inaso ka d'auki motar ta ka kaimata gidan su ga wayar ta nan ka had'a mata da ita , Hisham yace " to shikenan bari na kai mata na dawo , Huneed ya shiga motar ya fice dan akwai wasu aiki da xaije dubawa........


Koda Hisham yakai motar gidan me gadi yabawa yace ya shigar mata dasu , me gadi ya ansa da mukullin da wayar ya nufi cikin gidan dasu .......




Tunda Sanam ta hau sama wanka taje tayi ko sallah batayi ba ta haye gado ta kwanta , sai dai me tana rufe idon ta hoton Huneed ne ke yawa a cikin idanun ta lokacin da ya ke fincikar ta yana shiga da ita cikin gidan , hawaye ne taji yana bin kuncin ta tabbas Huneed ya karya mata record d'in ta , itace harda yin fitsari itace har dayin wanki , ga uwa uba kukan data sha tamkar ranta zai fita , tabbas batason dame zata rama abinda Huneed yayi mata ba , tunani tatafi akan yadda zata rama abinda yayi mata har bacci yayi gaba da ita......




Fahad ne ya hawo sama dan kawo mata wayar ta da mukullin motar , yana shigowa d'akin nata yaganta tana bacci duk ilahirin cinyoyin ta a waje , gashi saman k'irjin ta ya bayyana duk da gashin kanta ya rufe wani wajen , wani miyau ya had'iya tare da nufo gadon yana jin D d'insa na mik'ewa , Hawowa yayi cikin sand'a tare da nufar ta dan yadda yakejin kansa bazai iya rik'e sha'awar saba , turo k'ofaf da akayi shine ya dakatar dashi yana wai wayen yaga waye wanda yashigo..........








*Bana ganin Comment fa*






*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*






*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨






*Bisimillahir Rahamanir Rahim*








Chapter 10.




Hajiya Nafeesa yagani tsaye a bakin k'ofa , sauko wa yayi daga gadon yana sosa k'eya , duban sa tayi tace " me zakayi mata ? k'asa yayi da kansa yana fad'in " sorry My Aunty babu komai kawai yarinyar ce tahad'u sosai , Hajiya Nafeesa tace " amman karka manta yau fa kazo kabari aikin da zamuyi yafara tafiya , yanzu in ka haike mata sai ka b'ata komai na shirin namu , Fahad yace Shikenan za'a kiyaye hakan insha Allah , fitowa sukayi daga d'akin tare da janyo mata k'ofah suka sakko.....


Washe gari .
Sai wajen k'arfe sha d'aya Sanam ta sauko cikin kwalliya tare da trolly ta matafiya , lokacin Hajiya Nafeesa da Fahad suna zaune a falor suna hira , suna ganin ta suka tsaya suna kallon ta , dan iya had'uwa Sanam ta had'u tamkar itace ta tsara kanta , sai da ta k'araso sannan suka d'auke kansu da ga kallon ta , Sanam ta k'araso jikin Hajiya Nafeesa ta rungume ta sannan tace " Mumy yau zanbar k'asar nan inaso tafiya Turkey saboda zuwa na da wuri yana da amfani , Hajiya Nafeesa jitayi kamar ta shak'e Sanam d'in kowa ya huta , a fili kuma tace " haba My Dauther kibari mana bikin yataho basai ki tafi ba , kodai wani abun akayi miki da kikeson guduwa kibar mu ? Sanam a cikin ranta take fad'in " tabbas ina buk'atar yin tafiyar kwana biyu ko dan wannan azzalumin mutumin , mutuk'ar tana gari to tabbas zata biya ko nawa ne aje a kashe mata shi , tunda take a rayuwa ba'a tab'a yi mata abinda yayi mata ba , shurun da tayi ne yasa Hajiya Nafeesa fad'uwar gaba , cikin ranta take ayyana kodai Sanam tajisu jiya da daddare ne ? da sauri ta dubi Fahad tayi masa wata inkiya da idanu , shima hakan yayi mata sannan Hajiya Nafeesar ta katse shurun da cewa " Haba My Dauther na d'auka ina da muhimman cin da zansan dukkan damuwar ki ? ashe ba haka bane ! idan wani ne ya shigar miki rayuwa yana da kyau ki fad'amin mud'au mataki akansa , Sanam tace " babu komai fa Mumy kawai inaso in tafi da wuri dan Rauda tace sainaje zatayi komai , wata a jiyar zuciya tayi sannan tace " to shikenan hakan ma yayi kyau , yanzu yadda za'ayi ki kira Daddyn ki ki sheda masa kin janyo tafiyar yau kikeso , in kina buk'atar rakiya ga Uncle d'in kinan sai yaraka ki , Murmushi Sanam tayi sannan tace " munyi waya da Daddy tunda asuba kuma ya amince intafi yau , Fahad yace " to bari na had'o kayana mutafi tare nima naga gari , murmushi Sanam tayi sannan tace " Uncle ai dama kayi zamanka tunda nima ba wani dad'ewa zanyi ba , kuma kai daka zo hutawa ai baka kuma shan tafiya ba , Sanam kwata kwata jininta bai had'u da Fahad ba , tun tana k'arama in yazo gidan bashi da aiki sai rungumar ta da yi mata wasanni wad'an da bata so , dan haka bata shiri dashi ko yaushe ta gansa sai ta tsiri fita kullum.....


Ganin Sanam bata son tafiya da Fahad yasa Hajiya Nafeesa tace " to shikenan amman yana da kyau kije gidan Hajiya Maimuna kiyi mata sallama , Sanam tace " sauri nake Mumy kuma yanxu haka saura minty sha biyar jirgin mu yatashi , tana fad'ar hakan ta mik'e daga jikin Hajiya Nafeesa tana fad'in " Miss u so much my Mumyna , bye sai munyi waya ki kula min da kanki Mumyna , Hajiya Nafeesa cike da kissa tace " Miss u so much my luvly Allah yatsare min ke , Fahad ya mik'e yana fad'in " kawo trolly d'in naki na rakaki airpot d'in tunda ba'ason nayi rakiyar can d'in , murmushi Sanam tayi sannan tace " haba Uncle kana Abbana zan baka rik'on Trolly ? kabar shi kawai ai ina fita zansa a bayan mota , haka suka fito dukan su har jikin mota sannan Fahad ya shiga wajen direba ya zauna tare da cewa ta shigo ya kaita airpot d'in , sake rungume ta Hajiya Nafeesa tayi sanna tayi mata adawo lafiya ta shiga motar Fahad yaja suka tafi.......




Huneed koda yaje bacci kasa bacci yayi saboda tunanin Sanam , tabbas yarinyar tafara shiga ransa , sai dai gaskiya yanayin tarbiyar ta baya burgesa ko kad'an , inda zai ga iyayen ta tabbas sai yayi musu gyara sosai a cikin rayuwar su , dan yakamata ace sun bata tarbiyar da za'ayi alfahari da ita a matsayin ta na 'Ya mace , a haka bacci yayi awon gaba da shi me cike da mafarkin Sanam kala kala......




Washe gari wajen sha d'aya na safe ya fito waje yana zaga Estete d'in nasu , can ya hango motar Sanam tataho a hankali batare da wannan gudun na hauka ba , mamaki ne ya kamashi na ganin tabbas ta fara d'aukar horonsa , bai gama tunani ba motar tazo giftawa ta kusa dashi , anan ya hangi wanda yake tuk'in ashe ba Sanam d'in bace , sai dai itama ya hango ta tana cikin motar tana danna wayar ta , cikin ransa yake fad'in " wannan d'in shikuma waye ? take wani kishi ya ziyarce shi wanda bai tab'a jinsa ba ko akan Fateema wacce zai aura , da sauri ya nufi cikin gidan su dan d'auko motar yabi bayan su dan kwata kwata bai yadda da guy d'in ba .......


Fahad suna tafe yanajin music ya dubi Sanam yace " Baby yanzu kuma sai yau she zaki dawo ? Batare da ta dube sa ba tace " inason inyi 2 weeks kawai , in kuma na zarta to babu laifi dan can ma gidane , Fahad yace " gaskiya bazan iya jure rashinki har 2 weeks ba , ki taimaka min kiyi 1 weeks kidawo kinji Baby , murmushi Sanam tayi tare da mamakin maganar Fahad d'in , a cikin ranta tace kaji mun Uncle sai kace wata budurwar sa wai zai yi missing d'ina , a fili kuma tace " kamar yaune ai Uncle kuma ai zamuyi waya , Fahad yawani shagwab'e baki tamkar yaro yana fad'in " My BBy ki kulamin da kanki karki kula kowa kinji , Sanam tace " zan kula . Daga haka tayi shuru bata sake magana ba har suka k'araso air pot......


suna zuwa dai lokacin aka fara kiran sunayen matafiya , Daddyn ta ta hango yana murmushi ya nufo ta bayan sa body quart suna biye dashi , da sauri ta nufi wajen daya ke itama tana murmushi , tana zuwa ta fad'a jikin sa ya rungume ta sanna yace " bazan iya zama banzo munyi sallama da My One and Only d'ina ba , Murmushi Sanam tayi tana fad'in " nasan hakan Daddyna Abin k'auna ta , jin ankira sunan ta yasa ta saki Daddy tana fad'in " Miss u my Daddy so much , ta sumbace shi a kunci sannan ta nufi hanyar wajen hawa jirgin , tanayi tana wai wayen su tana d'aga musu hannu har ta k'ule......


Duk abinda akeyi Huneed na tsaye yana kallon Sanam har ta k'ule , cikin ransa ya furta " wato zaki bar k'asar kenan kije ki k'ara koyo wasu banzayen halayyar , duban wajen dasu Daddyn nata suke yayi suna tsaye har lokacin suna magana da Fahad , takawa Huneed yayi har wajen da suke yayi musu sallama tare da gaisar da Daddy , amsawa yayi cike da kulawa yana fad'in " kamar Canal Huneed Abdallah ko ? Huneed yayi murmushi sannan yace " nine , Daddy yace " masha Allah ya fama da gwagwar maya ? kuna k'ok'ari sosai Allah yabiya ku , Huneed yace " Ameen ya Allah nagode da addu'a , nan suka wuce shikuma ya tsaya yana dube dube , Huneed ya tsaya ne yana son sanin wacce k'asa Sanam tatafi ? yanaso yasan k'asar da zataje da kuma dalilin ta na tafiya , cikin wajen ya shiga ya nufi office d'in ma'aikatan jirgin , yana zuwa dayake dayawa sun san shi bai sha wata wahala ba suka sanar dashi garin da jirgin ya nufa , take Huneed yasamu kansa da biyan kud'in visar k'asar Turkey shima zaije......


*Tofah Sanam kinsamu cingum*


Tunda Sanam ta isa garin Turkey takejin wani nishad'i na ratsa ta , ba komai take tunawa ba sai rayuwar datayi a garin , tuni Rauda sunzo airpot d'aukar Sanam dan ta sanar mata da zuwan ta , ai suna ganin juna Sanam suka fara murna tare da tahowa da gudu suka rungumi junan su ......



*Comment plss*




*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[9/27, 09:42] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*






*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*






Chapter 11.




Rauda ta dubi Sanam tace " kinga yadda kika koma kuwa ? murmushi Sanam tayi sannan tace " haba my R ke bakiga yadda kika koma ba saini , Rauda ta rik'e mata hannu tana fad'in " aini dole na canza tunda nasha gyara haryanzu ina shan gyaran , haka suka k'arasa wajen motar cike da so da k'auna suna tafe suna hirar yaushe gamo .......


Rauda k'awar Sanam ce tare sukayi karatu tun datazo turkey , sun shak'u sosai har takai iyayen su sun san da wannan shak'uwa tasu , Iyayen Rauda 'yan asalin Nageria ne amman suna zaune a Turkey anan suke aikin su , da Ammin ta da Abeeh duk likitocine shiyasa suke zaune a Turkey suna aiki , Yaran su biyu suka haifa Asuk' da Rauda suna bala'in k'aunar 'yayansu...


Suna k'arasawa gidan su Rauda aka fara murna da zuwan Sanam , duk wanda yake Family d'in su Rauda sai yasan Sanam saboda shak'uwar su , Ammi tana murmushi tace " oyoyo my dauther , Sanam tafad'a jikin Ammi tana fad'in " nayi kewarki Ammi dakuma kewar daddad'an girkin ki , dariya suka saka baki d'aya Ammi " tana fad'in " kwantar da hankalin ki indai girki nane gashi can a dinning yana jiranki tund'azu , da sauri Sanam ta nufi dinning tana fad'in "dama yunwa nakeji banci komai a cikin jirgi , tana zuwa ta janyo kujera ta zauna tana cewa Rauda " zokiyi serving d'ina yunwa nakeji , Rauda ta nufo wajen tana fad'in " girman kine ai dole nazo nayi .......




Huneed yana zuwa gida yafara shirin tafiya , Hajiyar su yaje yiwa sallama yana fad'in " tafiya ce tazomi zuwa k'asar Turkey amman ba jimawa zanyi ba , Hajiya tayi masa addu'ar Allah yatsare shi yayi mata sallama ya fito , wayar Hisham ya shiga kira yana sheda masa tafiya tazo masa zai tafi Turkey amman ba jimawa zaiyi ba , zai saka masa kud'i a Account saboda ko zasu buk'ata shi da Hajiya , Hisham yayi masa fatan Allah yatsareshi sannan sukayi sallama , Huneed yashiga motar sa yabata wuta ya nufu airpot , yana zuwa visar sa na fitowa aka ce masa zuwa yamma jirgin su zai iya tashi ..........


Bayan Sanam taci abinci tanufi d'akin Rauda ta fad'a toilet tayi wanka , tana fitowa Rauda ta shigo tana fad'in " kinsan mungama shiryawa ke kad'ai muke jira , Ammi cewa tayi wai mutafi mubarki ki huta tunda yanzu kika zo ya kikagani , Sanam tana shafa mai tadubi Rauda tace " ai babu gajiya atare dani kawai kujirani insa kaya sai nafito mu wuce dan inaso inzaga gari tunda nadad'e banga garin ba , Rauda tajuya tanufi fita tana fad'in " muna jiranki cikin motar sai kin fito , Sanam tana gama shafa mai tasa kwalli daman bawata kwalliya tacika yiba , kayan ta ta bud'e ta d'auko wasu riga da wando bata tab'a sasu tasaka abinta , ta d'auko filet shoe da hand bag

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login