Showing 57001 words to 60000 words out of 78990 words
baki yana fad'in " ina sauraron ki hajjaju , Maryam ta kalli gefe da gefen Unguwar tasu taga babu kowa sannan tace masa " Diyana tana siyayya agurin kane ? Deeni yayi d'an dum sannan yace " Diyana kullum tana siyayyan Fresh yo guda biyu , wani lokacin ma in bata zo ba da kaina nakan aika mata , wani murmushi Maryam tayi sannan tace " dan Allah inaso kamin wani aiki kafad'i nawa zan biyaka , Deeni yace " wanne irin aiki kenan Hajjaju ? nan Maryam ta d'auko wata k'waya ta bawa Deeni tace " wannan kawai nakeso ka sawa Diyana a cikin lemon datake siya , Deeni ya zare ido kad'a yana fad'in " kinaso nayi kisan kai fa kenan ? Maryam tace " bawani kisan kai da zakayi kawai dai zata d'an bugu na wani lokacin kai kuma zan baka dubu hamsin , Deeni mayen kud'ine shiyasa Maryam tazo wajen sa , dan tasha wucewa tagansa shi da Diyana suna hira ko kuma taga Diyana ta siyo lemo a wajen sa , da wannan tayi amfani da kuma son kud'in Deeni , take ta curo Dubu Hamsin tabawa Deeni sannan sukayi sallama akan anjima zata dawo inyayi mata aikin , .......
Acan gidan su Sanam itama ansa mata k'wayar bacci a cikin lemon ta , kuma tana dawo wa daga sch taci abinci tasha lemon ba 'ajima ba bacci yayi awon gaba da ita , tuni Hajiya Nafeesa tazo ta kashe wayar Sanam d'in tare da ajiye ta a k'asan filow......
Diyana kamar kullum ta nufo wajen Deeni domin ansar Fresh Yo d'in ta , tana zuwa sukayi wasa da dariya sannan ya d'auko ya mik'a mata , nan tace masa " yanzu kud'in ka sun kai nawa kenan ? yayi murmushi yana fad'in " zan duba list hajjaju ai baki ansa dayawa ba , daga haka Diyana ta ansa ta nufi cikin gida.....
Nan Deeni ya kira Maryam a waya ya sheda mata aiki ya kammalu , Maryam tayi murmushi sannan ta d'au waya takira Hajiya Nafeesa tace " ina fatan Sanam taui baccin da mukeso tayi yanzu ? Hajiya Nafeesa tace " tuni tayi bacci kawai ke nake jira kifara aiwatar danaki aikin , nan Maryam takashe waya tashiga neman number Huneed , sai da ta kira kusan sau uku sannan ta ya d'aga yana fad'in waye ? Maryam ta gyara murya tamkar me kuka tace " K'awar Sanam ce dama Sanam ce tazo gidan mu kuma naganta bata cikin hayyacin ta , sai wani sambatu take dan Allah kataimaka kazo ka maida ta gida , cike da tashin hankali Huneed yace " wacce unguwa gidan naku yake ? nan tashiga yi masa kwatance tiryan tiryan , ...
Yana kashe waya Maryam ta fito daga gidan su ta nufi motar da suka zo da ita , take ta shedawa Fahad abinda ake ciki nan ya shedawa me d'aukar hoto ya fito dan yafara aikin sa , bayan kamar minty 13 sai ga Motar Huneed ta shigo cikin unguwar su Diyana , take Maryam ta lab'e tana kiran number Diyana , tana d'agawa Maryam tagane kwayar da tasha tafara aiki dan wata iriyar magana ta shiga yi , Maryam tace " kifito k'ofar gidan ku Sanam ce inaso muyi magana yanzu , Diyana tana cikin maye tace ganinan zuwa shegiyar Besty ta ashe kina gari , Maryam tuni ta kashe shikuma Huneed yashiga kiran wayar Maryam d'in dan ya sheda mata ya iso.........
[9/27, 10:08] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 38.
'Dagawa Maryam tayi tana fad'in ganinan fitowa , Huneed ya fito daga motar yana gyara tsayuwar sa a jikin motar , baifi minty 2 da tsayuwa ba sai ga Diyana ta fito rik'e da gyale a hannu ta tana had'a hanya , kana ganin ta kasan ba a hayyacin ta take ba saboda yanayin yadda take , Huneed ya tsallako batare da ya kula da yanayin da Diyana take ba , tambayar ta yashiga yi yana cewa "ina Sanam d'in take plss ? tuni su Fahad sunfara aikin d'aukar hoto batare da Huneed ya lura ba , Maryam wayar ta ta d'auko tashiga yin video tana murmushi , Diyana kallon Huneed take tana dafe kanta tare da nazarin tambayar da yayi mata akan ina Sanam , duban sa tayi sannan tace " wace Sanam kuma kaima waye ? mamakine ya cika Huneed to ba itace takirasa tagaya masa cewa Sanam na cikin wani hali ba yazo , gashi yanzu kuma tana ce masa wace ce Sanam , kafin Huneed ya dawo daga tunanin dayake yaji Diyana a jikin sa ta fad'o , da sauri ya rik'e ta tare da fad'in " subhanallah yana dube dube ko zai ga wani a shigar da ita gida , hango su Fahad yayi a tsaye duk da Fahad d'in yasa face mark ya rufe fuskar sa , sannan yasa Glass suna ganin ya kallesu suka yi saurin waske wa suna juyar da fuskokin su d'aya gefen , Huneed jiyayi kawai gaban sa ya fad'i kawai yaji yana zargin wad'an da yagani , Da sauri su Fahad suka shige motar suka gudu dan yadda suka fahimta Huneed yaganesu , Maryam ta maida Nikaf d'in ta tare da nufar wajen da Huneed yake rike da Diyana , da saurin ta take fad'in " Subhanallah meyafaru haka Malam ? Huneed yace " yauwa dan Allah shigar da ita cikin gidan nan wlh bansan meyafaru da itaba take hakan , Maryam na rik'e Diyana tana fad'in " wayyo Allah sannu Diyana muje ciki , Huneed tuni ya tsallaka ya shiga motar sa dan so yake ya gano meyasa mutanan nan suka gudu da suka gansa ? sosai yake gudu amman yarasa hanyar da sukayi , tuni zuciyar sa ta yanke masa akan yaje gidan su Sanam dan ya tabbatar da lafiyar ta , .
Maryam tana ganin tafiyar Huneed tayi saurin kiran Fahad a waya , yana d'agawa tace " ku canza hanya wallahi daga ganin Guy d'in nan ku ya biyo , kuma tabbas yakama ku to shirin mu zai lalace nima yanzu zantaho , tana kashe wayar ta shigar da Diyana cikin gidan su tare dace musu ganin ta tayi zata fad'i a waje , Maryam ba b'oyayyiya bace a gidan su Diyana nan suka mata godiya tafito tabarsu........
Huneed yana zuwa gidan su Sanam me gadi ya bud'e masa ya shigo , tambayar me gadin yayi Sanam na cikin gidan kuwa ? me gadi yace " tabbas Hajjaju tunda ta shiga gida haryanzu bata sake fitowa ba , Huneed yace " taje Sch ne yau ? Me gadi yace " taje shine tunda tadawo bata sake fita ba , nan Huneed ya shige tare da yin parking d'in motar sa ya fito , kiran wayar ta yashiga yi sai dai haryanzu a kashe yake jin ta , yana tsaye yana ta kai kawo tare da tunanin meyasa Sanam ta kashe waya yasan dai ba rashin caji ne yasa wayar taje a kashe ba , me yi musu aiki yagani ta fito da alamar aiken ta akayi , kiran ta yayi ya ce mata ta kira masa Sanam , jim tayi sannan tace " Bacci take tund'azu , yanzu ma haka daga d'akin ta nake naje shigar mata da kaya , Huneed yayi hamdala jin Sanam na gida tana bacci ya tabbatar da lafiya take , nan ya shiga motar sa yafara nazarin lallai akwai wata a k'asa , tabbas wani abu ake shirya masa wanda akeso a saka shi a rud'ani , amman dole zai bibiyi number da aka kirasa dan gano ko wacece tayi masa hakan ........
Tuni su Maryam da Fahad sun dawo gidan sun samu Hajiya Nafeesa tare da hotunan da Video , wata shewa suka shigayi suna dariyar mugunta, Hajiya Nafeesa tace " yau zanyi bacci harda minshari dan nasan k'arshen Halak'ar su tazo , babban burina shine naga shegu biyun nan basa tare da Sanam , wannan kad'ai zaisa komai mukayi mata yakama ta , yanzu wannan sabon sim d'in zaki d'auko ki saita whaspp dashi ki turawa Sanam Videon nan da hotunan , tana ganin su komai zai rikice dan nasan Sanam farin sani tana da kishin masifa , musamman aka abinda takeso dan tasha cemin zata iya rabuwa da kowa akan abinda takeso , dariya sukayi su dukan su suna fad'in kice muna da ganin game , Hajiya Nafeesa tace " Babban game kuwa , dukan su suka tuntsire da dariya sunajin dad'in muguntar da suka k'ullah ........
*Kundaina Comment Ko*😒🤒🤒
_Kushirya amsa tambayoyi a wajen D.P.O_😎😎 *nagaji da halinku🤨🤨*
[9/27, 10:09] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Riƙon Me Haƙuri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 39.
Sanam sai wajen sallar Magriba ta farka daga baccin datake , wanka ta fad'a sannan tana fitowa tayi arwala dan yanzu sallah bata wuce ta , tana idar da sallah ta shirya cikin wasu kaya marasa nauyi sannan ta sauko ƙasa ....
Bawanda da tasu a cikin palor dan haka ta wuce kitchen , tana shiga ta kunna gas ta ɗora indomie tasa kifin gwangwani sannan ta koma palor ta zauna , tunowa tayi da wayar ta dan tasan yanzu haka Huneed ya kira ta , da sauri ta hau sama tanufi ɗakin ta dan ɗauko wayar , tana ɗaukowa taga wayar akashe take mamaki yaka mata cikin zuciyar ta take tunanin yaushe ta kashe waya ? ko bacci zatayi bata kashe waya sai dai tasa ta a silet , kawai taɓe baki tayi sannan ta sauko ta koma kitchen....
tana zuwa tasamu indomie sa ta ɗora ta dahu , sauke wa tayi ta juye a filet sannan ta kashe gas ɗin tafito ,..
zama tayi kan dinning tafara ci tana danna wayar ta , data ta buɗe take saƙonni suka fara tururuwar shigowa , koda tashiga duba saƙonni rabi duk numbobi ne baƙi da bata san dasu ba , wasu maza ne masu nuna suna sonta wasu kuma mata ne ƴan sch ɗin su , wasu tabasu amsa wasu kuma tayi tsaki abinta , a haka tana tafiya har tazo kan number da su Hajiya Nafeesa suka turo mata saƙo , da har zata wuce sai taga ai kamar pic aka turo mata da kuma video take tashiga tafara buɗewa , suna gama buɗuwa Sanam tayi tozali da hotunan masoyinta abin ƙaunar ta wanda take burin yin rayuwa dashi ta har abada tare da ƙawar ta kuma bestyn ta , wata iriyar zabura tayi tana miƙewa tare dayin zoom ɗin pic dan ta tabbatar , tabbas sune Diyana ce rungume a jikin Huneed kuma a ƙofar gidan su , hannun ta har rawa yake wajen buɗe video dan taga me yake ciki shima , nan ma dai sune a rungume da juna , dama da yake su Fahad sunsa me hoton yayi musu edityn har wata murya yasa musu tamkar sune , Huneed na cewa " Diyana kinji yadda jikin ki yake da laushi tamkar auduga , ita kuma Diyana tace " Allah Babyna dani da Sanam wace kafi jin daɗin jikin ta ? Huneed yace " ina da haɗi ai kinfita komai Baby , tamkar da gaske suke maganar amman duk sharrin edityn ne , dan lokacin Huneed salati yake yadda yaga Diyanan nayi , shine suka saka musu murya tamkar sune suke maganar , Sanam jiri taji yana ɗibar ta take ta zauna daɓas a ƙasan tayel , duk ac. dake aiki a cikin palor bai hana Sanam yin zufa ba , tuno hawaye suka fara mata zarya akan kuncin ta , cikin zuciyar ta tanajin wani irin ɗaci meyasa Huneed zai mata haka ? duk san datake masa wannan shine tukucin da zai bata kenan ? tabbas tayi nadamar da yadda ta saki jiki take nuna masa soyayya , komai yace da ita batayin musu haka zatayi masa , amman sakamakon da zai mata shine soyayya da ƙawar ta wacce tafi yarda da ita akan sauran ƙawayen ta , Lallai Diyana taci amanar ta amman suje dan kansu daga yau babu ita basu har abada , kuka sosai tashiga yi me ratsa zuciya tamkar zatayi ihu , duk abinda ke faruwa da Sanam su Hajiya Nafeesa suna laɓe suna kallon ta , wata dariya suke ƙasa ƙasa gudun kar taji , sai da sukayi me isar su sannan Hajiya Nafeesa ta nufo wajen Sanam ɗin tana faɗin " Innalillahi My luv meyasa meki haka kike kuka ? Sanam tamkar an tunzura ta takuma sakin kukan batare da tace komai ba , da sauri ta ɗauki wayar tana faɗin " me aka turomiki yasamin ke kuka , tana ganin wannan hotunan tafara salati tare da cewa " wannan ba saurayin nan naki bane Huneed shida Diyana ? kai Sanam kawai ta iya ɗagawa tana sharar ƙwallah , Hajiya Nafeesa tace " wato dama haka suke shiyasa tun farkon zuwan sa banyi na'am dashi ba , to tunda naga kina sonsa shiyasa nima nafara son sa dan inason farin cikin ki , amman ko ranar nan sai da Fahad ya gayamin yagansa a wani hotel shi da Diyana , gudun ɓacin ranki yasa nace yabar maganar banaso kiji , to gashinan kingani da idanunki wallahi sunji kunya azzalumai , tuni Sanam ta miƙe ta haye sama tana kuma fashewa da kuka......
tana hayewa sama su Maryam da Fahad suka fito daga inda suka ɓuya suna dariya , nan suka shiga murna na nassarar da suka samu na raba Sanam da Huneed , kuma da wannan damar zasuyi amfani komai suyiwa Sanam tunda me bata kariyar su musu farraƙu , duk makircin da suke ƙullawa Rabi me musu aiki tanaji , kawai sai dai ta gyaɗa kai tana jimami tare dayin Allah wadai da halin Hajiya Nafeesa.....
A ɓangaren Huneed tunda yasamu kira akan zasu tafi jihar Katsina domin kamo ƴan ta'adda , kwata kwata ji yayi bayason zuwa saboda Sanam , tabbas yanason sanin halin da take ciki , kuma zuciyar sa na gaya masa lallai akwai abinda ake shirya masa shida ita , amman bashi da yadda zaiyi dole zai tafi tunda aikin sane haka , kiran wayar ta yayi har lokacin bata buɗe ba , sosai yake mamakin rufe wayar ta datayi yauɗin , dan ma dai yaje gidan kuma ya samu tabbacin lafiyar ta ƙalau bacci kawai takeyi....
Haka ya shirya tsaf yayiwa Hajiyar sa sallama tare da Hisham , su duka fatan Alkairi suka yi masa sannan ya shige ya tafi cike da kewar gida......
Sai Bayan sallar Magriba ya kira wayar Sanam ta shiga , sai dai har tagama ring ɗin ta ba'a ɗaga masa ba , sosai hankalin sa ya tashi dan yayi mata miss call shida amman bata ɗaga ba , tuni zuciyar sa tankarye tabbas akwai abinda ke damun Sanam , jiyayi tamkar ya dawo gida yafasa aikin saboda fargaba da kuma son sanin halin da Sanam ke ciki , tuni ya kira Hisham yace masa yaje gidan su Sanam dan yagano masa lafiyar ta , Hisham yashiga tsokanar sa sannan yace masa yana gama cin abinci zaije yaga lafiyar ta.....
Koda Hisham yaje bai samu ganin Sanam ba saboda ance masa baza ta samu damar fitowa ba , kiran Huneed yayi ya sheda masa abinda akace masa a gidan su Sanam , sosai hankalin Huneed ya tashi yakira Mummyn Twins wato Hajiya Maimuna , nan ya gaya mata abinda yake faruwa tun farkon kiran da akayi masa har yaje gidan su Diyana dakuma zargin da yake akan akwai shirin da ake yi akan su , nan tayi shuru tana nazari sannan tace " tabbas akwai abinda za'a ƙulla muku , amman ka kwantar da hankalin ka ka