Showing 39001 words to 42000 words out of 78990 words

Chapter 14 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3685

k'arewa palor kallo , Fahad ya mik'e yana ce mata " bari naje nayiwa Hajiya Magana kinji , Maryam tace " to batare da ta dube saba , sama ya haye abin sa ya nufi d'akin Hajiya Nafeesa.......


Sanam tunda tagama waya da Huneed takejin wani dad'i na ratsa duk ilahirin jikin ta , mik'ewa tayi tafad'a toilet dan yace mata gashinan zuwa , samun kan ta tayi da murnar son ganin sa dan haka dole tayi masa kwalliya ta musamman ......


Hajiya Nafeesa na zaune suna waya da Hajiya Harira Fahad yashigo d'akin , sallama tayi wa Hajiya Harira tana fad'in " sai mun sake waya ta katse wayar , duban Fahad tayi sannan tace " lafiya kuwa ? Fahad ya zauna a hannun kujerar dake bedroom d'in nata yace " Yarinyar nan da zamu sa aikin itace ta k'araso , Hajiya Nafeesa tace " har tazo kenan , kaje kufara magana ganinan zuwa ka gaya mata komai da muke so tayi kafin nazo , Fahad ya mik'e yana fad'in " to shikenan sai kin sakko , har yaje bakin k'ofah zai fita Hajiya Nafeesa tace " Fahad inaso kaduba ko 'inah na palor nan ka tabbatar ba kowa dan banaso muyi magana wani yaji , Fahad yace " angama Hajjaju yasa kai yafice daga palor......




Koda Sanam ta fito daga wanka zama tayi a gaban Mirror tayi kwalliya ta musamman , bayan tagama tabi jikin ta da wata had'add'iyar Khumra , bud'e dirowar kayan ta tayi tafara duba wanda zata saka , idanun tane suka sauka kan wata atamfar ta sabuwa d'inkin riga da siket strike gown , tsagar dake bayan siket d'in abud'e take ko kad'an ba'arufe taba , sosai kayan suka kama jikin ta , hips d'in ta tamkar an dasa mata shi haka yayi , d'an kwalin ta ta d'aura dan Sanam sosai ta iya d'aurikan d'an kwali kala kala , fesa turatuka daya kawo mata tayi sai mur mushi take , mayafi kalar atamfar ta d'auko k'arami tare da wani hill d'in takalmi tasa , kana ganin ta sai kazata wani gagarumin biki zataje irin had'uwar datayi , tana cikin saka takalmi kiran wayar Huneed ya shigo wayar ta , sai da takusa yankewa sannan ta d'aga yace mata ya iso , nan tace masa ya k'arasa d'akin saukar bak'i gatan zuwa , dama tuni tasa angyara d'akin tare da turareshi da turaruka masu k'amshi , sai da tabari minty 10 tayi sannan ta fito daga d'akin nata tanufo k'asa ...


Fahad tuni ya wassafawa Maryam abubuwan da suke so zatayi , duk shaid'an cin Maryam sai da ta girgiza da batun su , amman yadda Fahad ya shiga kwad'ai ta mata yadda zata samu kud'i da irin yadda zata huta tuni taji ai abun ma bakomai bane , ita da tasaba yin ciki ta zubar so d'aya ne ma ta haihu ta yarda jaririn tun randa yazo duniyar , bare wannan da gata zai samu itama ta samu ai ta warke zata amince da wannan abun ko dan son datakewa Fahad d'in , tana cikin zancen zuci suka hango sakkowar Sanam daga sama cikin takun ta na isa da izzah , tuni Maryam tasaki baki tana kallon Sanam cikin ranta fad'i take " tsarki ya tabbata ga Mahaliccin wannan sura me kyau , tabbas wannan yarinyar ta had'u tamkar ita tayi kanta , lallai 'Yayan masu kud'in nan suna hutawa ga kyau ga kud'i kamar su sukafi kowa a gun Allah , da sauri tace " Astagafirlah Allah muma kabamu kud'in nan muhuta , Sanam nagama sakkowa ko kallon wajen da suke batayi ba bare tasan Allah yayi ruwan su agun , haka ta fice daga palor tabarsu da shak'ar k'amshin ta , Fahad har wani lumshe ido yake yana bin Mazaunan ta da kallo har ta fice , cikin ransa yake kissima yadda zai sarrafa Sanam duk randa ya damk'eta a hannun sa , Maryam ta dubesa tace " Dear wannan kyakkyawar Babyn fa Yarinyar Auntyn naka ce ? Fahad yace "ea yarinyar tace Maryam tace " gaskiya ta had'u sosai tamkar ita tayi kanta , zata sake magana tahango Hajiya Nafeesa tana sakkowa itama , Acikin second biyu Maryam ta k'arewa Hajiya Nafeesa kallo taga yadda suke kama da Fahad , cikin ranta tace "inajin ita yarinyar da Babanta take kama dan ta nunka Hajiya Nafeesa kyau sosai , ....




Tunda Sanam tayi sallama palor bak'i Huneed ya shak'i k'amshin ta , tana shigowa yayi mutuwar zaune saboda tsabar had'uwad dayaga tayi masa , tasbihi yashiga yiwa Allah tare da addu'ar Allah ya mallaka masa Sanam a matsayin mata yasan yagama dacewa , haka ta k'araso har kusa dashi tana murmushi tashiga gaidashi , yaji dad'in yadda Sanam ta gaidashi tare da nuna masa ashe itama tana da tarbiya ba laifi , duk yadda yake tunanin Sanam sai yake ganin ashe tana da dad'in zama , yasan da sannu zata dawo yadda yake buk'ata insha Allah , nan Huneed yashiga tambayar ta ya Mumy da Daddy , tace" Mumy lfylau take Daddy kuma yana d'aya gidan bangan saba amman nasan lfylau yake , Huneed ya d'an dubeta da mamaki a fuskarsa yace " dama Daddy matan sa biyu kenan ? Sanam tace ea su biyune amman nidai guda d'aya nasani Mumyna bansan wata ba bayan ita , Murmushi Huneed yayi yana duban Sanam yace " wato kishi kike taya Mumyn ki ko ? canza fuska Sanam tayi tana fad'in " plss Sojana mubar wannan maganar muyi hirar mu kaji , ganin batason maganar yasa Huneed yayi shuru tare da d'auko wata hirar daban.......


Hajiya Nafeesa tana zuwa Maryam ta gaida ta cike da girmamawa , Hajiya Nafeesa ta kalleta cike da kulawa ta amsa , tambayar Fahad tayi akan yafad'awa Maryam komai da suke buk'ata tayi ? Fahad ya amsa da nafada mata kuma ta amince , Hajiya Nafeesa tadubi Maryam tace " kinji komai ina fatan bazamu samu matsala ba ? kuma inason wannan Abun yazamo sirri tsakanin mu , daga ke sai Fahad saini banason surutu dan kinsan koni wace duk abinda naga zai ban matsala zan kaudashi , Maryam tayi kasa da kai tana fad'in " Insha Allah bazan gayawa kowa ba komai kikeso nayi Alk'awarin yi miki shi , Hajiya Nafeesa tace " yauwa kiturawa Fahad account Number dinki zaisa miki kud'i sai najiki , tana kaiwa nan ta mik'e ta ta haye sama abinta..........






*Tabbas in banga Comment ba bazan cigaba da Typing ba*😡😡😡
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*






*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/










*Bisimillahir Rahamanir Rahim*










Chapter 28.


Maryam bin Bayan Hajiya Nafeesa tayi da kallo tana k'issima ina ma itace a wannan matsayin , Fahad ne ya katse mata tunanin ta yace " to My Baby kinji komai kuma ina fatan zaki bamu had'in kai ? Murmushi Maryam tayi sannan tace " angama Oga na ai farin cikin ka kai da Auntyn mu nima shine nawa , Fahad ya dubeta yace " kizo mushiga daga cikin d'akina tun yau nafara aikin samo Baby Boy , Maryam tawani kashe masa ido tana mik'o hannu alamar ya d'auketa , murmushi Fahad yayi sannan yace " Baby ai kinyi nauyi dayawa kawai ki mik'e mutafi , turo baki Maryam tayi har sai da Fahad ya d'auke ta ya nufi bed room d'in sa da ita......


Sosai Sanam tasaki jikinta da Huneed suka sha hirar su , sai wajen goma da rabi yayi mata sallama ta rakoshi har jikin motar sa yatafi , juyowa tayi d'auke farin ciki akan fuskar ta , batasan meyasa in suna tare da Huneed kwata kwata bataso yayi nesa da ita ba , dai dai da zata shiga k'ofar palor Fahad da Maryam suka fito suma hannu cikin hannu , tsayawa Maryam tayi cak tana kafe Sanam da idanu , Sanam mamakine ya kamata naganin Fahad tare da mace sun jero daga cikin gidan hannu cikin hannu , koda yake bazatayi mamakin ganin hakan ba tunda tasan waye Fahad farin sani , kallo d'aya tayiwa Maryam ta d'auke kai tare da bi ta gefen su ta shige abinta......


Maryam ta dubi Fahad tace " gaskiya wannan yarinyar Auntyn naka ta had'u sosai , duk da naga kamar zatayi rashin Mutunci amman tashiga raina sosai tayimin , dama zaka had'amu k'awance wallahi dana ji dad'i , Fahad ya dubi Maryam yace " mutuk'ar kina son zaman lafiya koda kinzo gidan nan to karki shiga shirgin Sanam , bata da mutunci ko kad'an batak'i ta tsinkaki a cikin taron mutane ba , Maryam tace "wow My Dear sunan nata ma wallahi ya had'u gaskiya tahad'u shiyasa sunan ta ma yake had'add'e , Fahad ya rik'o hannun ta yana muje kar Sanam ta zautaki tun d'azu sai yaba kyanta kike , Maryam tayi murmushi tana fad'in " ai dole na yabi kyanta amman da alama ita da Mahaifinta take kama ko ? Fahad kawai ea yace tare da d'auko wata hirar , dan shi yafara gajiya da tambayoyin Maryam d'in tamkar 'Yar jarida......


Jaydeen tunda suka koma gida da Hajiyar sa yake faman kiran wayar Sanam , sai dai ko sau d'aya bata tab'a d'agawa ba , har a whaspp yayi mata magana nan ma bata dawo masa da reply ba , gashi kullum soyayyar ta k'ara ninkuwa take cikin ransa , tunyana hak'uri har yagaji Hajiyar sa tasan halin dayake ciki , d'aukar waya tayi ta kira Number Hajiya Nafeesa , bayan sun gaisa takeyi mata bayani akan k'in d'aga wayar Jaydeen da Sanam keyi , sannan ta k'ara da cewa shine dalilin kiran nata taji ko lafiya kuwa ? Hajiya Nafeesa tasan halin Sanam sarai bata da mutunci , musamman indai batason Abu to bataso ko kad'an ya rab'e ta , cikin iya siyasa da kissa tace " kinsan Halin yaran yanzu tunda ga ranar da kukazo na gaya mata muka shiga wasan b'uya da ita , kuma inajin ba lallai in tana da number tasa ba , amman insha Allah zan mata magana zata d'aga , sannan A bawa My Son d'ina hak'uri Sanam tamkar tazama tashi angama , Hajiya Halima akayi dariyar jin dad'i ta shiga godiya tare da addu'ar Allah ya daidai tasu , Nan suka tab'a hira kafin suyi sallama da juna......




*Bayan kwana biyu*


Tuni Soyayyar Huneed da Sanam tayi k'arfi sosai , koda yaushe suna mak'ale da juna a waya suna shan luv , saboda Huneed Sanam taji bazata iya fita wata k'asar karatu ba , dan haka ta zab'i tayi karatun ta a nan , Daddyn Sanam sai shirye shiryen tafiya yake zuwa Jamus , sosai yake jin dad'in had'uwar Tilon 'Yar tasa da Huneed , yagama yabawa da hankalinsa da kuma irin yadda yake ja jurtacce , cikin satin da Alhaji Abba zai tafi Jamus Allah ya sauki Hajiya Maimuna wato Mahaifiyar Sanam , ansamu Twins mace da Namiji cike da k'oshin lafiya , karkiso kiga Murna wajen Alhaji Abba tun A asibiti yake kiran wayar Sanam , sai dai kwata kwata bata d'aga ba saboda lokacin tana tare da Huneed , itama Hajiya Nafeesa tana wanka tabar wayar a palor k'asa shiyasa batasan yakira ba , ganin haka yasa Alhaji nufo gidan Bayan an sallamesu daga asibitin yakawo su gida , yana shigowa gidan yasamu Huneed da Sanam a farfajiyar gidan suna hirar su cike da nishad'i , tana ganin sa ta mik'e tana murnar ganin sa , shima baki bud'e ya nufosu yana murmushi tamkar wanda akayiwa Albishir da gidan Aljannah , kafin ya k'araso tuni Huneed shima ya mik'e ya nufesa yana rissinawa yana gaidashi , cike da sakin fuska ya amsa yana tambayar sa 'yan gidan , Huneed yace " lafiya lau suke Daddy duk suna gaidaka , ina amsawa sosai nima in ka koma ka gaidamin da Hajiyar taka , ..... Zataji insha Allah inji Huneed...
Alhaji Abba ya dube su yace " Abin farin cikine yasameni tare daku baki d'aya , Sanam tayi murmushi tace " ai tunda kataho nagane hakan Daddy meyasamu ? murmushi yayi sannan yace Mumyn ki ce ta haifa miki k'anne Twins , Suna nan kamar su d'aya dake har sun so ma sufiki kyau , Nan danan fuskar Sanam ta canza daga murmushi zuwa b'ata fuska , shikuwa Huneed tuni ya saki murmushi yana fad'in " Masha Allah Allah yarayasu yayi musu albarka , Lallai munyi k'anne har naji d'okin nagansu , duban Sanam yayi yaga canzawar datayi lokaci guda duk wata walwala ta tafi daga fuskar ta , Alhaji Abba inda sabo yasaba da halin Sanam na rashin jituwar da batayi da Mahaifiyar tata , duk da tunfarko yana da laifi dan ko kad'an bayaso ayiwa Sanam fad'a , duk rashin kunyar da zatayi wa Hajiya Maimuna baya tsawatar mata , amman ya d'auka in taji anyi mata k'anne zatayi murna sai yaga sab'anin hakan , duban ta yayi yace " My luv bazaki tayani murnar samun Yara ba kenan ? kin manta koda yaushe kina fad'in yaushe za'a haifa miki k'anne wanda zaki dunga wasa dasu kina jin dad'i , amman yau gashi nazo miki da albishir kinyi shuru ko murna bakyayi da hakan , Sanam ta turo baki tana fad'in " Daddy nifa nafison ace Mumyna ce tanan gidan ta haifamin k'anne , ni kasan ba zuwa nake gidan waccan Mumyn ba kaga baruwana da yaran data haifa , kuma Daddy har kafara cewa sunfini kyau wato zaka koma Sonsu kenan nikuma kadaina sona , Alhaji Abba yayi murmushi yana duban Sanam wato kishi zata fara dasu kenan , Huneed shima murmushi yayi duk da cikin zuciyar sa yana tunanin meyasa Sanam kwata kwata batason Matar Daddyn nata , tabbas yana ganin tsantsar kiyayyar matar a idon ta duk da baisan me tayi mata ba , haka Daddy yashige ciki yana fad'in " bari naje nayiwa Hajiya Nafeesa Albishir , ....


Koda Daddy yatafi Huneed ya dubi Sanam yace " Baby meyasa abin farin ciki yasamu Daddy amman ke bazaki taya shi ba ? karki manta in ita mahaifiyar yaran ta kasance me laifi a gunki to ai su yaran basuyi miki komai ba , asalima su basusan komai ba a yanzu sai Mahaifiyar su , dan haka karki k'ullacesu a cikin zuciya kijasu ajikin ki tunda sud'in jininki ne kuma 'Yan uwanki ne , inaso ki shirya gobe In Allah ya kaimu zaki rakani muje tare mugan su , Sanam duk jikin ta yayi sanyi game da maganganun da Huneed yayi mata , kuma ko kad'an bata yi masa musu indai yace mata Abu , haka ta amsa masa da Allah ya kaimu suka ci gaba da hirar su...


Lokacin da Alhaji Abba ya shigo palor dai dai lokacin Hajiya Nafeesa ke saukowa daga sama , yana ganinta yasaki murmushi yana kallon ta , itama martanin murmushin ta maida masa tare da kashe masa ido , tana k'arasowa tashige cikin jikin sa , shima rungumeta yayi yana fad'in " d'awisu sarkin ado sannu da fitowa gimbiya ta , Hajiya Nafeesa takuma lafewa a jikin sa tana fad'in " Alhajina kadawo lafiya ina kewarka sosai , Alhaji Abba yace " ai nayita kiran Wayar ki keda Babyn ki baku d'aga ba , dama sonake inyi muku Albishir munsamu k'aruwa , tuni Hajiya Nafeesa gaban ta ya fad'i ta d'ago tana duban Alhaji Abba sannan tace " waye ya haihu ? Alhaji Abba cike da murmushi yace " Hajiya Maimuna ce ta haifo mana Twins mace da namiji , ai jitayi tamkar an soka mata wuk'a wani abu ya tsaya mata a k'irji yakasa wucewa , sai a hankali ta saita kanta gudun karya gane sannan tace " Alhamdulillah kace munyi yara Masha Allah , Allah yaraya su yayi musu Albarka , nan tashiga nuna masa murnar ta wacce a iya bakice batakai zuci ba....


Alhaji Abba sosai yaji dad'in yadda Hajiya Nafeesa ta nuna farin cikinta , har addu'a yake mata akan Allah yabata itama saboda kyan halinta , baisan nan cikin zuciyar ta cike take da tsanar gudan jinin nasa ba , dayasan yadda takeji a yanzu da ya gaggauta tashi ya fita dan tasamu tayi kuka ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login