Showing 9001 words to 12000 words out of 78990 words
Bayan kwana biyu Sanam kwata kwata bata canza ba , gudu a motar sai abunda yayi gaba dan so uku tana jiwa mutane ciwo , Duk abinda takeyi Huneed nasane da ita kawai jira yakeyi yagama abinda yakeyi yadawo , dan ya fuskanci lallai saiya koya mata hankali sannan za'asamu sauk'in ta .......
Yau Alhaji Abba na gidan Hajiya Nafeesa suna zaune suna hira sai ga Sanam , tana shigowa ta dubesu tace " Hi Daddy Hi Mumy , Alhaji Abba yace " Hy my luv your wel come , K'arasowa tayi tana taunar cingum ta zauna sannan ta dubi Daddyn nata tace " Daddy inason zuwa Turkey za'ayi bikin wata k'awata da mukayi karatu tare kuma acan suke , murmushi Alhaji Abba yayi sannan yace " bakomai My luv zantura miki kud'i ta Account d'inki saikiyi yadda kikeso , wani tsalle Sanam tayi tana rungume Daddyn nata sannan tace " thanks my sweetheart Allah yakare mana kai , Ameen my luv Allah yayi miki albarka , Da sauri Sanam ta mik'e tayi sama tana murna , dan kwata kwata bata zata Daddyn ta zai barta taje Turkey ba........
Hajiya Nafeesa wani kishine ya turnik'e ta ko magana ta kasayi , cikin ranta take fad'in " wannan farin cikin naku da kukeyi duk lokacin da kuka kasance da juna kun kusa dainashi , dan saina saka muguwar k'iyayya a tsakanin ku ta yadda in d'aya yaga d'aya sai yabar guri , Alhaji Abba ne ya katse ta da cewa " lafiya kuwa Matar kirki ? murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " jinayi banason Sanam tayi tafiyar nan , dan kasan banajin dad'in na wayi gari bansata a idanuna ba , wani dad'i Alhaji Abba yaji murmushi yayi yana janyo Hajiya Nafeesa cikin jikinsa sannan yace " kiyi hak'uri kibarta taje ai nasan baza ta dad'e ba zata dawo , wannan soyayyar da kike nunawa My luv itace tasa nake k'ara sonki , ina Alfahari dasamunki a matsayin mata , kin d'auki Sanam tamkar kece kika haifeta kin nuna mata gata da soyayya wacce ko wacce ta haifeta batayi mata ita , nagode sosai matar Kirki kema Allah ya nuna min randa zanga d'anki a duniya , Hajiya Nafeesa cike da kissa tace " inbanso Jininka ba Alhaji wazanso ? Sanam kuma 'Yace a guna na raineta tuntana tsumma inbanso ta ba wazan so , inajin kewar ranar da zatazo wacce Sanam zatayi min nisa , Alhaji Abba yace " ai babu wanna ranar da My luv satayi miki nisa , Hajiya Nafeesa tace " Akwai mana Alhaji ko kamanta da ranar aurenta , kasan nan gaba kad'an gidan wani zataje dole zamu rabu , Alhaji Abba yace " duk wanda zai kasance miji a wajen Sanam tabbas zai kasance a k'arkashina yake , dan nafison ta auri wanda zandunga bashi umarni yana bi wanda yarinya ta zatayi yadda takeso , wani murmushi Hajiya Nafeesa tayi cikin ranta tace " lokaci yafara , zansa Fahad yashigo rayuwar Sanam yadda zamu tafiyar da komai a dai dai , a fili kuwa tace " Allah dai yabata miji nagari wanda zai dunga yi mata duk abinda takeso , Alhaji Abba yace Ameen......
Huneed yau ya dira garin Abuja da tarin Nasarorin da suka samu , sosai Hajiyar sa tayi murna da ganinsa ita da Hisham , wanka kawai yayi yaci abinci yafito daga gidan , dan yanaso yau sai Sanam tashiga tai tayinta , bai mi minty 15 da zama ba saiga motar ta nan ta taho da mugun gudu , aikuwa shima ya shiga cikin tasa ya take mata baya , kwata kwata Sanam bata kula dashi ba dan cikin murna take sosai sai faman jin kid'a take abinta , sai da yabari tashiga wani layi mara yalwar Jama'a yayi sauri yasha gabanta , wani wawan birki taja har tana bige bakinta a jikin sitiyari , cike da masifa ta fito tana fad'in " wanne mahaukaci ne wannan d'in haka ? motar Huneed ta nufo sai zage zage takeyi tana fad'in " banza talakan wofi kawai , taya zaka zo kasa mutane su kusa jin ciwo taja wani tsaki mtsss, Huneed tuni yasa bak'in glass ya rufe k'wayar idanunsa , sannan yasa face mark ya rufe bakinsa da hancinsa , tuni ya bud'e murfin motar ya fito , baiyi wata wata ba yajanyota ya wurga ta cikin motar tare da zagaya wa ya shige wajen tuk'i ya figi motar da mugun gudu , tuni yayi waya da Hisham akan yazo ya d'auke motar Sanam d'in ya maida mata da ita gidan su.......
Ihu Sanam take tana nan agaji tare da k'ok'arin bud'e motar ta fice , sai dai ko 'inah a rufe yake gam takasa bud'e komai , shikuwa ko kallonta baiyi ba kawai gudu yakeyi sosai tamkar zasu tashi sama ........
*Kuyi maneji*
*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_ 😍🌹
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪🏻
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 8.
Dai dai k'ofar wani gida Huneed ya tsayar da motar sa , fitowa yayi daga ciki yana huci tamkar zaki , zaga yawa yayi b'an garen da Sanam take ya bud'e ta , janyo ta yayi waje da k'arfin tsiya tamkar zai b'alla ta , k'ofar gidan ya nufa rik'e da hannun ta , yana zuwa ya saka mukulli ya bud'e gidan yashiga da ita , sosai Sanam ke ihu amman babu mejin ta saboda unguwar babu gidaje.......
Huneed maida k'ofar yayi ya rufe kuma har lokacin yana rik'e da hannun Sanam , sai da ya tura wata k'ofar falor sannan ya tura ta ciki ya janyo k'ofar , Sanam ihu tasaka tana fad'in " menayi maka ne bawan Allah ? plss dan Allah kazo kafitar dani kabarni natafi gida , Huneed yana jinta ya fito daga gidan yana huci , cikin motar ya koma ya zauna ya fara tunanin yadda zai hora Sanam ,......
Hisham tunda Huneed yamasa waya akan yazo ya d'auki motar Sanam , yana zuwa daya d'auketa gidan su ya nufa yaje ya ajiyeta wajen parking space , yana fitowa ya shiga cikin gida abinsa yana dariyar koya hankalin da Hauneed zai wa Sanam d'in ......
Diyana ce tashiga kiran wayar Sanam , lokacin Huneed yayi nisa a tunanin yadda zai fara horata yaji ring d'in waya , dubawa yayi yaga ansa My D katse wayar yayi sannan ya kashe ta gaba d'aya yayi jifa da ita bayan motar , fitowa yayi daga cikin motar yana nufar cikin gidan......
Yana shiga gidan ya bud'e k'ofar falon yashiga , lokacin ya cire face mark d'in sa da kuma glass d'in , Sanam ta zauna a k'asan cafet ta had'e kanta da gwiwa lokacin tana shan kukan ta , a lokacin taji shigowar sa da sauri ta d'ago kanta , aikuwa ido biyu tayi da Huneed ya had'e girar sama da k'asa yana tsaye yana kallon ta , da sauri ta mik'e tana dubansa kafin ta fara magana " me na tare maka a cikin rayuwa daka takura min haka ? menayi maka kake shiga cikin Rayuwa ta , kuka ne ya k'wace mata tana yi tana fad'in " wallahi bazan tab'a k'yaleka ba azzalumi kawai , wata tsawa Huneed ya daka mata wacce tasa Sanam yin shuru jikinta har rawa yake , Huneed ya k'araso gaban ta yace " keda kike mara kunya wacce bata san darajar mutane ba , sau nawa ina fad'a miki kigyara halinki amman kika yi min kunnar uwar shegu ? saboda kin samu sake har taka mutane kikeyi batare da and'au mataki akan ki ba , to kisani nine zan d'auki mataki yau akanki dan saina gyaraki tunda iyayenki sun kasa baki tarbiya , wani tsaki yaja tare da dubanta yace " Komai kikeyi aganinki dai dai ne ko ? shuru tayi batare da tabashi amsa ba , tsawa ya daka mata sannan yace " ina tambayarki kinyi min shuru wallahi yanzu jikinki zai gaya miki , kuka take k'asa k'asa yaci gaba da fad'in " meyasa bakyajin magana ? nan ma shuru Sanam tayi ba tare da ta Bashi amsa ba , fusata yayi yayi kanta ya d'agota da gashin kanta da ya baje a bayanta , wata k'ara ta saki tare da sakin fitsari .......
*Dan Allah kuyi hak'uri an hanani kallon hasken waya zuwa lokacin da zanji sauk'i sosai*
[9/27, 09:40] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*Hamdala* *Writer's* *Association*💪
https://www.facebook.com/111403834371046
✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨
*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*
Chapter 9.
Huneed ko ajikin sa yace " za kiyi magana ko ba zakiyi ba ? da sauri Sanam tace " zanyi wallahi zanyi , sakin ta yayi sannan yace " to ina jinki meyasa ba kyajin magana kuma Alhalin ke ba yarin ya bace ? Sanam tana kuka tana fad'in " kayi hak'uri duk abinda kake so nayi wallahi zanyi , dan Allah ka maidani gida plss , Huneed ya kalle ta fuskar ta jage jage da hawaye tamkar ba itace Sanam 'Yar gayun nan ba , jiyayi dariya na neman kamashi amman sai ya maze yace " daga yau inaso inga shedar kin fara jin magana ta , a ko yaushe ki kasan ce kina jan Motar cikin Nutsuwa , sannan ki girma ma duk wanda yakasan ce ya girmeki , sannan inaso ki daina irin wannan shigar mutuk'ar zaki fito yawan ki na gari , kuma inaso duk wad'an da kika buge su da Motar kije kine mesu ki basu hak'uri , nabaki nan da kwana biyu zanga in kinji magana ta , sosai Sanam take kuka har Huneed yaga ma magan ganunsa , jiyawa yayi ya kwaso mata wasu uniform d'in sa na Sojoji yace ta shiga toilet maza ta wanke masa sannan tazo ya maida ta gida , Sanam ba musu ta anshi kayan ta nufi cikin toilet tana share hawayen ta , tunda take a duniya bata tab'a wanki ba ko sau d'aya , komai sai dai tasa ayi mata amman yanzu lokaci d'aya ace wani yasa ta wanki , tana shiga toilet d'in tasa ka wani kukan tare da zuba kayan a cikin wani bawool na wanki , saka kayan tayi a gaba tana kallo tare da tunanin taya zata fara , gashi intace masa bata iya ba nan ma zaiyi mata wani rashin mituncinne , sabulu tagani a gefe a ajiye nan ta d'auka tafara wankin tana kuka.......
Tuni Hajiya Nafeesa ta kira K'anin ta a waya wato Fahad , suna waye take sheda masa duk abinda yake yabaro k'asar Cameroon yadawo gidan ta , tanaso tasaka shi aiki akan Sanam , tuni Fahad yafara shirin tahowa dan dama babu abinda yake sai bin mata kamar bunsuru , kud'i ta tura masa ya hawo jirgi ya sauka a garin Abuja......
Yana isowa ta tareshi da murna tare da nuna masa masaukin da zai dunga kwana , bayan Fahad yayi wanka ya shirya ya fito dan cin abinci , Hajiya Nafeesa tana zaune ta kame tasha wanka da kwalliya tamkar zataje gidan biki , zama Fahad yayi yana duban ta yace " gaskiya Aunty kin samu duniya sosai , dubi yadda kika koma tamkar wata shuwa arab , murmushi Hajiya Nafeesa tayi sannan ta dubesa tace " zaka fara rashin mutuncin naka ko ? yanzu dai kaci abinci sai muyi magana , Fahad yace " inacin abinci kina gayamin abinda duk kiso ayi miki , Hajiya Nafeesa ta gyara zama tace " inaso ka bud'e kunnen ka kaji sosai , kasan dai duk duniya banida kamarka ko ? to inaso kasan cewa duk wannan daular danake ciki da zarar Alhaji Abba ya rasu bani da wani kaso me yawa aciki , kasan ba haihuwa nayi dashi ba dan ni likita ya tabbatar min da bazan haihuba saboda yawan zubar da cikin dana ringa yi ina budurwa , duk wannan dukiyar ta Alhaji a yanzu inya mutu duk rabinta ta zama ta Sanam , sai kuma uwar ta wacce take da wani cikin a yanzu , kaga ni zan tashi a tutar babu kenan , abinda yasa na kira ka dan ka tainaka min nima insamu kaso na me tsoka acikin dukiyar Alhaji , gashi tun yanzu babu abinda nake k'aruwa dashi , wannan shegiyar 'Yar tasa itace komai akan dukiyar yanzu , komai na dukiyar sa sunan tane ajiki kuma duk abinda takeso to tabbas sai ya mallaka mata shi duk tsadar sa , inaso kashiga jikinta ka k'ullah soyayya da ita yadda zaka dunga kwaso mana rabon mu , ta wannan hanyar kawai zamu samu kud'i yadda mukeso , wani murmushi Fahad yayi sannan yace " ina yinki Auntyna tabbas kin yi kyan kai , nikuma bazan baki kunya ba duk yadda zanyi nashiga rayuwar Sanam sai nayi , daman ina masifar sha'awar yarinyar , dan naga tana da Albarkatun ruwa atare da ita , wata harara Hajiya Nafeesa ta watsa masa tana fad'in " kana nan da halin naka kenan ? sosa k'eya yayi yana fad'in " to mezan fasa Aunty ai mata duniya ce dole sai dasu rayuwar zata tafi.......
Sanam sosai tasha wuya a wajen wankin sannan ta fito tace ta gama , duban ta Huneed yayi sannan ya kauda kai yana fad'in " kishiga kiyi wanka sai nazo na maidaki dan bazaki shigar min motar a haka ba , wani takaici ne ya kuma kama Sanam batare da tace komai ba ta juya cikin toilet d'in.....
Tana fitowa tasame sa a tsaye yace " taho mu wuce , yana fad'in haka ya juya ya fita daga cikin falor , binsa tayi a baya har ta fito daga gidan tasame sa a k'ofar gidan yana tsaye jikin motar , tana zuwa ta bud'e baya zata shiga Huneed yace " ni direban ki ne da zaki zauna min abayan motar ? maza ki dawo gaba ko ranki ya b'aci , da sauri Sanam ta dawo gidan gaba ta zauna shikuma ya zagaya yaja su suka tafi....
tunda suka fara tafiya yake waya yana musayar kalmomin soyayya shida budur warsa , wani ta kaici ne ya kama Sanam wato ita yagama horata shikuma gashi nan sai wani farin ciki yake abinsa , wani murmushi yasaki yana fad'in " kinsan Allah na matsu sosai na ganki , gaskiya kiyi ki tattaro ki dawo Nageria , ko mai akace masa daga can b'angaren yace " habawa ai ba wacce ta isa ta kwace miki ni , kinsan matan Abujan yawancin su duk garorine , gasu da rashin tarbiya uwa uba kuma akwai su da iya bin saurayi , Sanam ji tayi tamkar ta rufesa da duka dan tasan wannan magan ganun da ita yake , haka ta k'yalesa tanaji yana ta zubawa Budurwar sa luv , har wata shagwab'a yake yi mata tamkar k'aramin yaro , a haka har suka k'araso cikin Estate d'in su , lokacin har ankira sallar magriba haka ya ajiye Sanam tare da cewa " daga yau nake so naga kinfara aiki da abinda nace miki , rashin hakan zai tabbatar min da cewa bakiji magana ta ba , rashin jin magana ta kuma tamkar kin k'ara ansar hukunci na ne , kuma inaso kisani in ma kin fad'awa Iyayenki babu abinda aka isa ai min sai dai ma ki saka kanki a wata babbar matsalar , in kunne yaji to jiki ya tsira zaki iya fita sai wani lokacin , A hankali Sanam ta bud'e motar ta fice batare da tayi magana ba , tana fita ya ja motar sa da gudu ya nufi gidan su dan sauri yake yaje yayi sallah tunda ankira........
Lokacin da Sanam ta zo k'ofar gate bugawa tayi da hannun ta , megadi yana sallah lokacin haka ta ci gaba da bugu har ya idar yazo ya bud'e mata , yana ganinta ya zube yana fad'in " kiyimin rai hajjaju wallahi sallah nake shiyasa