Showing 36001 words to 39000 words out of 78990 words
fad'in " haba sarauniyar mata abin kuma 'yar haka ce ? Sanam ta ya mutsa fuska batare da tace dashi kanzil ba , gyara tsayuwar sa yayi sannan yace " wajenki fa nazo amman naga kina neman fita batare da munyi magana ba , Sanam tadube sa a wani shek'ek'e sannan tace " wajena kamar yaya ? dan Allah Malam inason kabarni ina sauri zanfita ne , Jaydeen sosai yaji rashin dad'i abinda Sanam d'in tayi , amman sai ya shanye tare da k'ak'alo murmushi yace " haba Gimbiyata , amman kinsan yadda nadamu dake kuwa ? dan Allah kibani aron minty 5 zamuyi magana plss , dafe kai Sanam tayi sannan tace " Inajinka fad'i abinda zaka fad'a dan sauri nake , Jaydeen yace " Ina Sonki Sanam kuma ina son muyi aure dan Allah kisoni , zanbaki duk wata kulawa plss kisoni My Sanam , Samun kanta tayi da kallon sa kafin tayi murmushi tace " inaso nan da sati biyu kadawo zanfad'a ma duk abinda na yanke , bata jira cewar sa ba ta shige motar ta taja tana zuba hon.Da sauri me gadi ya bud'e mata gate ta fice da mugun gudun nata data saba.......
Jaydeen binta yayi da kallo har ta fice daga gidan , cikin zuciyar sa yake tunanin " meyasa komai takeyi burgesa take , duk irin yadda ta raina masa hankali amman ko kad'an baiji yana jin haushin taba sai ma k'ara shiga ransa datayi , tunowa yayi da yadda 'yan mata ke binsa suna mutuk'ar son sa , har da masu bashi jikin su saboda yayi amfani dasu , tabbas Sanam ta dabance ita kuma tashiga zuciyar sa kuma bayajin zai iya rqbuwa da ita , juyawa yayi yashiga cikin gidan dan yanaso yasamu Number ta wajen Mumyn ta .......
Huneed shida Hisham suna zaune a k'ofar gate d'in gidan su , wannan al'adar Huneed ce indai yana gari , koda yaushe zaka samesa a k'ofar gida shida d'an uwansa suna hira , Sanam ce tazo ta wuce da mugun gudun nan nata da tasabayi , Hisham ya d'ago yana kallon motar wacce har ta k'ule yace " gaskiya wannan yarinyar bataji wato haryanzu bata daina gudun ba kenan , Huneed sosai yaji ransa ya b'aci wato Sanam zata dawo da halinta kenan , wayar sa ya lalubo ya danna kiran ta , har ta katse bata d'aga ba haka ya jera mata kira sau uku amman bata d'agawa, test ya tura mata sannan ya ajiye wayar tasa.....
Tana zuwa unguwar su Diyana tasamu Diyana a tsaye a k'ofar gida tana jiran ta , shigowa motar tayi sannan suka nufi Garden na cikin Asokoro .......
Hajiya Halima tuni sukayi sallama da Hajiya Nafeesa , nan suka kuma musayar contac tare da alk'awarin zuwan da Hajiya Nafeesar tace zatayi , Jaydeen yadubi Hajiya Nafeesa yace " Mumy dan Allah kibani Number Sanam dan inaso muyi waya , Hajiya Nafeesa cike da fara'a tabashi phone d'in ta tare da gaya masa sunan da zaigani akan number Sanam d'in , Bayan ya d'auka sukayi mata sallama tare da fitowa harabar cikin gidan , siyayyar da Hajiya Halima tayiwa Sanam tabawa megadi ya shigar mata da ita sannan suka tafi......
Sanam da Diyana zaune akan wani had'add'en cafet suna hira , Duk rabin hirar akan Zuwan Huneed ne sannan kuma tashiga bata labarin Jaydeen , Diyana tayi murmushi sannan tace " besty kawai haka zakice min kinyi samari jarumai , zan so ingansu dukan su dan jinjina musu ta yadda suka tunkareki , Sanam tayi murmushi tace " kefa Diya akwai ki da iskanci , nifa kwata kwata ban shirya soyayya yanzu ba dan kinsan yadda nakeson in koma inyi degree dina , in nace zan had'a karatu da soyayya bazan nutsu yadda nakeso ba , sannan shifa Huneed Soja ne kuma kinsan yadda natsani soja da d'an sanda , dariya Diyana ta tuntsire da ita har da rik'e ciki , Sanam ranta yafara b'aci saboda iskancin Diyana , duban ta tayi rai a b'ace tace " meye hakan kuma wannan dariya saikace mahaukaciya , Diyana ta dubeta kuma har lokacin dariya take tace " wallahi dariya kika ban wai bakyason Soja da 'Dan sanda , to dan Allah besty meye aibun su ? ni wallahi inason auren Soja kodan inzai tafi yak'i inrakoshi ina kuka , sannan kuma wallahi sojojin nan akwai iya soyayya sosai , Sanam ta tab'e baki sannan tace " wasu kuma akwai iya duka kuma ina ganin tamkar yanayin sa me dukan ne shi , Diyana tace " taya zai doki wacce yake so ? dan Allah kidaina wannan tunanin kawai ki zab'i wanda zuciyarki ta kwanta dashi , kinsan dai dole zakiyi aure tunda baza asakaki agaba ana kallo ba , Diyana tace " ke kanki kinsan ina da samari 'Yayan manya wadan da suka amsa sunan su , amman ban tab'a jin inason wani ba sai akan wannan Sojan , dan gaskiya tun ina turkey nafara sonsa , kuma a kullum son sa k'aruwa yake a cikin raina , Diyana tace " to ai tunda kina sonsa komai yazo da sauk'i , kawai ki anshi soyayyar sa nasan bazakiyi dana sani ba , nan suka ci gaba da hirar su tsakanin su na kawaye kuma aminan juna...........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION* 📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 26.
Sai yamma lik'is su Sanam suka baro cikin Garden , gidan su Diyana tafara zuwa ta sauke ta sannan ta jiyo da motar ta tayo gida.....
Huneed sau kusan takwas yana kiran Sanam amman bata d'agawa , tunani ya shiga yi anya lafiya kuwa ? tun sanda ta fita da gudun nan daga Estate d'in yake dakon dawowar ta , yana zaune a wajen har ogan sa ya kira sa akan yana son ganin sa , haka ya shiga gida ya shirya sannan ya fito da motar ya nufi kiran Ogan nasa.....
Koda Sanam ta dawo gida tana shigowa palor tasamu Hajiya Nafeesa da Fahad zaune suna hira , sallama tayi k'asa k'asa sannan ta nufi hawa sama , da sauri Hajiya Nafeesa tace " Sanam zonan mana , kwata kwata Sanam batasan ganin Fahad shiyasa ta canza fuska da tashigo , k'arasawa tayi kusa da Hajiya Nafeesa tace " gani Mumy , Duban ta Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " waye ya tab'amin ke naga fuskar ki haka babu walwala ? Sanam ta d'an saki fuska kad'an tace " babu komai Mumy kawai nagaji sosai ina buk'atar hutawa , Hajiya Nafeesa tace " kuma gashi inason yin magana dake amman in kin huta sai ki sauko kici abinci sai muyi magana , Sanam tace " to Mumy tana fad'in haka ta juya dan dama a k'age take ....
Da ido Fahad ya bita kafin yace " gaskiya hak'uri na yana k'ok'arin k'arewa , wannan sura me kyau kana tare da ita amman ace har yanzu bakayi test d'in ta kaji yadda take ba , Hajiya Nafeesa ta galla masa harara tana fad'in "kaifa baka da kunya Fahad har yanzu halin nan naka yana nan nabin matan banza , sosa kai yayi yana fad'in " to ai Aunty kinsan abun ne sai da dabaru yanzu , kinsan dai bani da kud'in da zan yi aure yanzu kuma ke kin ki min auren , Hajiya Nafeesa ta kallesa tace " wai dama nice zanyi maka aure Fahad ? wai aikin da kace kanayi a libiya dama k'arya kake , Fahad yace " haba Aunty nawa ne duka kud'in da nake samu da zan yi aure , nifa nafiso nayi kud'i tamkar mijinki in gina gida me kyau wanda yafi nakin nan , dan Allah Aunty ki taimaka kisa baki Sanam ta soni nasan Mahaifinta zai mallakamin kud'ad'e , Hajiya Nafeesa taja Numfashi tace " Sanam bazata Amince da kai ba Fahad , dan ko idanuwan ta ka duba zakaga tsanar ka a ciki , inajin ka gwada mata halin naka shiyasa , amman tabbas naso ace kuna shiri da ita da ko ta b'angaren ta masamu kud'in da mukeso mu samu , Fahad yace " nifah bawani hali dana nuna mata , kinsan halin shegiyar yarinyar da girman kai tare da wulak'anci , kuma fa duk lefin kine Aunty yarinya k'arama ta dunga wahalar dake , kawai sawa zakiyi a kashe ta sannan akashe uban nata ki mallaki kud'a d'enki mukama gaban mu , duban sa Hajiya Nafeesa tayi sannan tace " baka da hankali Fahad inason mijina fa kawai dai Sanam d'in ce na tsaneta , kuma inajin rashin dadi yadda Alhaji yake fifita ta akan komai , duk wasu Companoni da Alhaji ya mallaka gida da waje sunan Sanam ne akai , cewa yake ya mallaka mata komai to yanzu ko mutuwa Alhaji yayi me zan tsira dashi tunda banice na haifeta ba , maganar da nake maka yanzun haka Uwar ta wani cikin gareta itama , Fahad da sauri ya furta " kutt kawai kice ke zaman banza kike a gidan nan , Hajiya Nafeesa tace " zaman asara dai dan wannan yafi zaman banza , Fahad yace " in zaki yadda tunda kince Alhajin yakusa yin tafiya ta wata goma me zai hana inyatafi kice masa kina da ciki , da sauri Hajiya Nafeesa ta dubi k'anin nata , d'aga mata kai yayi alamar ae cike da rashin fahimta tace " kamin bayani yadda zan fahimta , Fahad ya gyara zama yace " akwai wata budurwa ta da muke chat kuma anan garin take , to yarinyar iyayen ta talakawa ne shiyasa take fita yawon ta , gata da kula kulen maza kuma tana da saurin d'aukar ciki , zan d'auko ta in kawota gidan nan muyi tarayya da ni da ita har tasamu ciki , kinga da wannan cikin nata zamuyi amfani muce kece me cikin har Allah yasa ta haifesa , ke kuma zaki samu wani likitan da zai miki alllurar da zaki kumbura kidinga canzawa a yadda da cewar kina da cikin , sosai Hajiya tashiga nazarin magangun k'anin nata , tabbas indai hakane Fahad yana da basira sosai kuma ta jinjina masa da irin wannan aider tasa , nan yashiga bata labarin irin hajiyoyin da yake kulawa suma sunsha aikata hakan in suka ga basu haihu ba , take Hajiya Nafeesa tayi na'am da shawarar Fahad sannan tace yakawo mata yarinyar tagani , ......
Sanam na shiga d'akin ta wanka tashiga tayi sannan ta fito , sai a lokacin ta d'auko wayar ta dan ta duba tagani , Miss call 20 tagani ga kuma test kala kala anyi mata , dubawa tayi taga kiran Huneed wajen goma tare da test d'in sa , dafe kai tayi tana fad'in ohh my god na manta kwata kwata da wayar ma , Test d'in dayayi mata ta karanta wanda fad'a yayi mata akan gudun data fita d'azu tanayi , murmushi Sanam tayi sannan a hankali ta furta " shauk'in soyayyarka itace tamin yawa har nake wannan gudun , amman daga yau nadaina dan banaso mu kuma wani fad'an , kiran wayar tashi tashiga yi har ta katse wayar bai d'aga ba , Sanam ta furta wato fushi kayi kaima bazaka d'aga ba kenan , haka ta dudduba sauran kiran wanda duk number d'aya ce kuma batasan number ba , tsaki taja ta ajiye wayar tare da hayewa gado ta kwanta , ..
Jaydeen da Hajiyar sa tunda suka taho daga gidan su Sanam suke hirar ta , Hajiya Halima tace " gaskiya yarinyar tahad'u sosai dole tasace zuciyar Jarumin d'ana , murmushi Jaydeen yayi sannan yace " Mumy yarinyar fa ta had'u sosai ba inda bazan shiga da ita ba , daman Abokaina na cewa saga irin yarinyar da zan aura , aikuwa zasu ganta wacce zatafi duk nasu matan cewar Hajiya Halima , dan tana son duk abinda zai kankarowa Tilon d'anta mutunci , kuma ta shirya tsaf dan bin duk wata hanya da Jaydeen zai samu Sanam , Abinda ya tsaya mata arai shine ganin kwata kwata Sanam bata kama da Hajiya Nafeesa , Sanam Farace Sol har wani jaja takeyi tsabar farinta , gata da wani sirtaccen kyau mara misaltuwa , ga gashi tamkar 'Yar india ga dirin jiki tamkar dai ita tazab'i halittar ta , ita kuma Hajiya Nafeesa ba fara bace kuma ba bak'a bace , kawai dai tana da kyau itama ga kuma dirin jiki , kawar da zancen tayi daga zuciyar ta tana fad'in " inajin ita ko da Mahaifin ta take kama.....
Bayan Huneed yagama ganawa da Ogan sa ya fito yaga kiran Sanam , zama yayi cikin motar sannan yashiga kiran number ta ta , sai da ta kusa yankewa sannan Sanam ta d'aga , Huneed yace " barka da wannan lokacin My wifey , Sanam wani lumshe ido tayi tare da janyo filo tana k'ank'amewa dan jin dad'in sunan daya kira ta dashi , murya k'asa k'asa tace " Barka kadai dafatan kayini lafiya , Kashe murya yayi yana fad'in " ban yini cikin sukuni ba tunda banji muryar wacce zata sakani inyini cikin sukuni ba , Murmushi Sanam tayi sannan tace " ayya sorry yau busy nayi dayawa ban samu d'aukar waya ba , Huneed yace " shiyasa naga kinfita da wannan gudun naki da kikamin alk'awari kindaina , Sanam batasan sanda tasa dariya ba tana fad'in " sorry Sojana nadaina daga yau , wani dad'ine ya rufe Huneed dajin sunan da Sanam ta kirashi dashi , a hankali ya furta My Wifey d'an mai maita sunan da kika kirani dashi plss , sai sannan Sanam taji kunya ta rufeta da sauri ta kashe wayar , Huneed murmushi yashiga yi nasamun Nasarar mallakar zuciyar Sanam d'in , wani nishad'i yajishi aciki nan da nan ya tada motar ya nufi gida dan bazai iya jurewa ba dole yaje yaga sanyin idaniyar sa , .......
Tuni Fahad yakira Maryam a waya ya sheda mata yana son ganin ta , Maryam dayake Allah yasa mata k'aunar Fahad jitayi tamkar tayi tsalle saboda murna , nan ya kwatanta mata gidan Hajiya Nafeesa sukayi sallama , ........
[9/27, 10:00] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee* *MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 27.
Tuni Maryam ta shirya tsaf ta nufo gidan Hajiya Nafeesa , dan cike take da d'okin sanin dalilin kiran nata da Fahad yayi , tana zuwa k'ofar gate ta kira Fahad ta sheda masa gata nan a k'ofar gate d'in gidan ......
ba ad'auki lokaci ba Fahad yak'araso suka shigo gidan tare , tunda Maryam ke shige shige bata tab'a shiga gidan daya had'u kamar wannan ba , tuni tasaki baki sai kallon ko'inah take na gidan tamkar 'Yar k'auye , Fahad yajanyo ta jikin sa yana fad'in " wannan irin kallon gida tamkar wacce tazo daga Ruga ? Murmushi Maryam tayi sannan tace " ai gidan ne yayi mugun had'uwa tamkar a turai , gaskiya banga laifinka ba Dear daka dawo wannan gidan da zama , dan ko nice Yaya ta take irin wannan gidan wallahi da gudu zan had'o kayana nadawo , dariya Fahad ya shiga yiwa Maryam yana fad'in " ai yanzu ma zaki dunga shigowa duk sanda kike so idan har kin amincewa me gidan da buk'atar ta , Maryam ta dubi Fahad alamar tambaya ? ya d'aga mata kai yace " muje daga ciki sai muyi magana ,.....
Tana shigowa cikin Palor gidan sai kawai taga ashe harabar gidan ba komai bace duba da irin had'uwar da palor yayi , sakin baki tayi tana kallon palor wanda yagaji da had'uwa tamkar a turai , ba kowa a palor shiyasa Maryam tasaki jiki tana