Showing 75001 words to 78000 words out of 78990 words
yaranta Fara rene itama kuma Fara ce wannan yaro kuwa bak'ir k'irin haka yake , take cikin Asibitin ya d'auka akan anyiwa wata Mata musayar Jariri , Nurse d'in da aka had'a baki da ita sai Uwar zufa take tana faman zare idanuwa , Nan take 'yan jarida suka iso Asibitin suka Fara neman labarai .....
Huneed ya iso asibiti yasamu wannan labarin na musanyan yaro , wucewa yayi yafara duba inda yake tunanin samun Maryam ,...
Maryam kuwa taci kuka ta k'oshi tarasa ta yadda zata fita daga cikin d'akin , duk wannan Abu da akeyi na batun musayar yaro batasan anayi ba, jefe jefe tana d'an lek'awa ta window Dan ganin wannan mutanen suna Nan. ....
Wasa wasa k'aramar magana tazama gaske , Dan tuni Asibitin ya cika da mutane anata fad'in " dole likitoci sunsan inda d'an wannan Matar yake , Take Babban likitan ya had'a taro na gaggawa daga kan likitoci har Nurse a Babban office d'insa .,....
Har dare Huneed baiga d'akin da aka kwantar da Maryam ba , Kiran wayar Sanam yayi yace " My Wifey nayi neman duniya Amman bansamu Maryam ba , ko Zaki tuntub'a Mana kiji tana Asibitin ko tana gidan ? Sanam tace " yanzu nazo gidan kuma duk inda na duba Banga Maryama ba , Amman Dana zagaya baya ta wajen tagar palor naji K'awar Hajiya Nafeesa wato Hajiya Harira tana waya , Koda na kasa kunne naji tana cewa kusan duk yadda zakuyi ku d'auketa daga cikin Asibitin sai kutafi da ita , sannan naji tace " in sun kashe ta su jefar da gawar a wajen gari , tabbas nasan ba kowa za'ayiwa haka ba face Maryam Dan haka tana Nan cikin Asibitin Nima ganinan zuwa , tana gama cewa haka ta fito daga gidan ta hau motar ta ta nufi Asibitin......
Alhaji Abba tuni ya taho tare da tarin siyayyar da yayiwa yaro da me jego , farin ciki yake tamkar ba atab'a Masa haihuwa , tunda yataho ya shedawa Hajiya Nafeesa Nan tashiga gyara jiki da kuma k'ara maida kanta kalar masu jego ka rantse itace ta haihu , ...
Acan Asibiti Sanam na shiga itama ta tadda wannan hatsaniya ta musanyan yaro da akayi , sosai tashiga mamaki tare da ayyanawa a ranta watak'ila ma Hajiya Nafeesa ce suka aikata hakan , haka tashiga cikin Asibitin sanye da face mark tana dube dube , baya ta zagayo aikuwa ta hango wannan k'artin masu kama da arnan daji itama , tana ganin su tayi saurin komawa da baya batare da sun ganta ba , wayar Huneed tashiga Kira tana magana a hankali , Nan ta sheda Masa tana cikin Asibitin daga baya , yazo taga wasu mutane kuma i tadai Bata yadda dasu ba , Nan ya tambaye ta daga wajen Ina kenan ? Nan tashiga Gaya Masa tiryan tiryan har ya k'araso , Yana zuwa shima ya lek'a ya hangosu Nan ya tabbatar da duk yanda akayi sune wad'an da zasu kashe Maryam , Nan take ya Kira yaransa ya sheda musu maza suzo Asibitin Royal hospital su same shi yanzu , Nan yashiga kaiwa da komawa Yana jiran zuwan su , Sanam tace " My Sojana ina shigo naji wata Hayaniya Wai anyiwa wata Mata musanyan yaron data Haifa , Huneed yace " Nima naji wannan Asibitin ai komai akace zasuyi Babu musu zasuyi shi , Sanam tace " wallahi jikina yabani Hajiya Nafeesa ce tayi wannan aikin , Huneed ya dubeta da sauri ta d'aga Masa Kai alamar ea ,. duban ta yasakeyi Yana nazari sannan yace " bazan yi Miki musu ba Dan wanda yasa akashe wani babu abinda bazai iya ba , Kiran yaransa ne ya katseshi suka sheda Masa sun iso , Nan yashiga kwatanta musu ta b'angaren da yake , Nan take suka zagawo suna k'amewa tare da Sara Masa , Dan dukansu shine ogan su cike da girma mawa suke bashi girman sa , Nan Huneed yabasu Umarnin kamo Masa wannan mutanen da aka saka sukashe Maryam , tare suka nufesu har dashi suka kamasu batare da sun ankare dasu ba , Sanam ta lek'a window Nan ta hango Maryam zaune sai sharar hawaye take , Kiran sunan ta tayi da sauri ta jiyo tare da mik'ewa tana jin wani dad'i ya ziyarce ta , zagayowa Sanam tayi suka bud'e k'ofar tare da shigowa d'akin da Maryam d'in take , Sanam ce ta rik'o Hannun Maryam suka fito daga cikin d'akin , Nan taga wannan mugayen mutanen ansaita su da bindugu kowanne Yana durk'ushe akan gwuiwarsa ,.....
Take cikin Asibitin yakuma d'auka ankama wasu 'yan fashi sun shigo zasu kashe wata , nanfa 'Yan jarida suka samu abinda sukeso sukayo caa.. dason jin labari , sai dai kwata kwata Huneed ya Hana ayi magana dasu dan basaso a haska a social media har Hajiya Nafeesa tagani , Koda suka zo wucewa ta wajen Matar dake kuka akan canza Mata yaron da akayi Maryam ta hangi yaron ana ta kallonsa , da sauri ta anshe hannun ta daga na Sanam ta nufi wajen jaririn , tana zuwa ta anshe shi a hannun wata Mata tana fad'in " wannan ai shine d'ana Wanda na Haifa , aikuwa kallo yadawo kanta yayin da Uwar waccan yaron ta mik'e tana fad'in " to Ina kika kaimin yarona ? Sanam tace ki kwantar da hankalin ki yaron ki nanan kizo muje daga ciki zamuyi magana , take suka shiga wani d'aki suka keb'e Nan Sanam tashiga bawa Matar labarin komai game da Hajiya Nafeesa , takuma shada Mata yanzu zasu d'auki hanya su nufi gidan Hajiya Nafeesa Nan zata anso d'anta , ba'ayi wata wata ba Sanam da Huneed da Maryam tare da wannan Mata suka nufi gidan Hajiya Nafeesa......
Akan Hanyar su ta zuwa suka Kira Mummyn Twins suka sheda Mata komai , Nan itama ta sheda musu Alhaji yadawo dan tund'azu ya sauka kuma yanzu haka Yana gidan Hajiya Nafeesa shima , itama gatana zuwa zasu taho da Hajiya Babba wato Mahaifiyar ta. .....
Diyana tuni ta bayyana itama a gidan Hajiya Nafeesa , tunda suka taho daga asibiti 'yan sandan da mijin Bahijja ya d'auko suma suke biye dasu har suka shigo cikin estate d'in area 11 ......
Hajiya Nafeesa ana zaune a palor sai wani yauk'i take ita ala dole ga me jego , Alhaji Abba na rungume da yaro sai kallonsa yake Yana Murmushi , duban ta yayi sannan yace " nifa haryanzu narasa da wa wannan yaron yake kama , Hajiya Nafeesa jitayi gabanta ya fad'i Amman sai ta dake tace " haba Alhajina wannan yaron ai kana ganin sa anganka , Murmushi kawai yayi Dan bai ga ta inda suke kama da yaron ba , duk yadda yataho Yana d'okin yaron Yana ganin sa yaji bai kwanta Masa Rai ba sab'anin sauran yaran sa , Hajiya Harira ce ta sauko daga sama tana fad'in" kaga iyayen yaro kunsa shi agaba tamkar za'a k'wace muku shi , zama tayi kusa da Hajiya Nafeesa tana fad'in " sonake nazo na wuce gida tunda na kammala Miki komai , Hajiya Nafeesa ta dubi Hajiya Harira tana yi Mata alama da ido ya sukayi da su Goga ? Ta bud'e baki zatayi magana sai ga su Sanam da Mummyn ta da Hajiya Babba da Diyana sun shigo , Bayan su kuma Maryam ce da Bahijja da kuma Mahaifiyar Bahijjar , a zabure Hajiya Nafeesa ta mik'e ita da Hajiya Harira suna kallon juna .........
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Alhamdulillah ! Alhamdulillah !! Alhamdulillah !!!
Chapter 50.
Da sauri Bahijja ta nufi wajen da Alhaji Abba ke zaune rik'e da jariri a hannu , tana zuwa tace " bani d'ana mugaye azzalumai , Alhaji Abba cike da mamaki ya dubi Bahijja sannan ya Kai duban sa ga Hajiya Nafeesa wacce zufa ke tsatstsafo Mata , duk irin yadda na'urar ac. Ke aiki Amman Hajiya Nafeesa gumi take, kafin yayi magana 'yar sanda mace ta shigo tare da nufo Hajiya Nafeesa da ankwa tana fad'in your onder arrest , sai a lokacin bakin Alhaji Abba ya bud'e yafara magana " Wai meye yake faruwa zaku shigo min cikin gida batare da izini na ba kuma kuna neman tafiya da iyalina , 'yar sanda ta dubi Alhaji Abba tace " kabiyomu office duk sai kasamu wannan amsar tambayoyin naka , take suka ingiza Hajiya Nafeesa a gaba zuka nufi fita da ita , Hajiya Harira na k'ok'arin guduwa Huneed ya rik'eta tare da mik'awa 'Yan sanda ita yace itama suje da ita , ...
Koda Hajiya Nafeesa tazo wucewa ta gefen da Maryam da sauri Maryam ta tare ta tace " Allah ya tsareni daga sharrin ki tun lokacin da kika shirya kasheni nake harkance dake , duk wani motsin ki akan idanuwa na kike shiyasa Nima na shirya Miki nawa Shirin , inaso kuma inyi Miki albishir akan duk wani Shirin ki da kikeyi akan Sanam tasan komai , zare idanu Hajiya Nafeesa tayi Maryam tayi wani murmushin takaici sannan tace " ki k'arewa gidan Nan kallo Dan da alama ba lallai ki dawo ba , tuni akayi gaba da Hajiya Nafeesa wacce tuni tafara zubar da hawaye.....
Alhaji Abba har yanzu ganin abin yake kamar al 'amara , Nan su Huneed suka zaunar dashi sannan Huneed ya umarci Maryam data fad'i duk irin Shirin Hajiya Nafeesa da yadda ta kawo ta gidan , Nan Maryam tashiga karantawa Alhaji Abba komai da dukkan irin makircin da Hajiya Nafeesa ta shirya Masa , Banda kalmar Innalillahi Babu abinda Alhaji Abba ke Mai maitawa , Nan aka Kira Fahad a waya akan anasan ganin , dayake baisan komai ba haka ya nufo gidan kansa tsaye...
Sai da ya shigo sannan yaga abinda yake faruwa agidan , Nan Alhaji Abba yasa shi agaba akan shima yanaso yaji komai daga bakinsa , Fahad ba yadda ya iya tunda akan kamasu da laifi dumu dumu haka ya gayawa Alhaji komai da Yayar tashi take k'ullawa , wani abun da Maryam d'in ma Bata fad'a ba shi Fahad sai daya fad'awa Alhaji Abba , wani jiri Alhaji Abba yaji Yana d'ibarsa daga zaune , da sauri Sanam ta k'arasa tana rik'eshi da sauri , duban ta yayi cike da so da k'auna ya rungumeta Yana kuka , cikin zuciyar sa Yana tirr da halin Hajiya Nafeesa wacce yaji yanzu a duniya ba wanda ya tsana sama da ita , ....
Kukan Maryam ne yadawo dasu daga shurun da akayi , rok'on Alhaji Abba gafara tashiga yi tare da Sanam da kuma Huneed shima ,. Jaririn ta na hannun ta tana rik'e dashi , Alhaji Abba yace " ta tashi taje ya yafe Mata , Nan ta mik'e ta fice Fahad shima yabi bayanta , ....
Suna fita Fahad yadubi Maryam yace " yanzu shikenan haka zamu tafi Babu komai da muka samu ? Maryam ta kallesa cike da tsana tace " Dan kaga ka Sha shine kake wannan maganar , wallahi nayi danasanin had'uwar mu dakai , gakuma d'anka Nan kasan yadda zakayi dashi , Fahad ya kalleta shek'e k'e yace " wannan shegen d'an zan karb'a Abu mummuna dashi , Maryam tace " koma dai meye ai jinin kane kuma dole ka anshe shi , wani mari ya sakar Mata tare da Fara zaginta , Huneed Wanda tun fitowar su ya biyo bayan su Yana jin komai da suke fad'a take ya kama Fahad , dama Yana so ya hukuntashi shima akan abinda sukayi Masa shida Sanam , take yasa aka tafi da Fahad Dan shima abashi horo me tsanani .....
Maryam kuma ta nufi gidan su tare da jaririn ta a hannu.....
*Bayan kwana biyu*
Alhaji Abba yanzu ya d'an samu sauk'in abinda Hajiya Nafeesa tayi Masa , ya tattara komai nata da yasani yayi sadarsu , komai na cikin gidan tuni yasa aka kwashe su dan ko kad'an baya k'aunar abinda zai sa yasake tunawa da Hajiya Nafeesa a rayuwar sa , tuni ya rubuta Mata takardar sakin ta kawai so yake yaje police station yakai Mata ,. ...
Tuni anbawa Bahijja d'an ta tare da tsare Hajiya Nafeesa da Hajiya Harira a gurin 'yan sanda , nurse d'in da suka had'a baki da ita aka canza Yaron itama ankamota tare da tufe Asibitin gaba d'ayanshi , ...
A can b'angaren su Sanam ransu fess sun rabu da annoba , Mummyn Twins sai k'ara kwantar wa da Alhaji Abba hankali take , ranar da zai kaiwa Hajiya Nafeesa takardar sakin ta Sanam tace zata bishi , aikuwa tare suka taho dashi da Sanam da Twins wad'an da sukayi wayo , suna zuwa aka fito da Hajiya Nafeesa wacce saboda dukan datasha har ta canza kamanni , Alhaji Yana ganin ta ya kauda kansa cike da wata iriyar tsanar ta , Hajiya Nafeesa tana k'arasowa ta zube kan gwuiwo winta tana fad'in " Alhaji dan Allah ka yafemin wallahi na tuba nadaina komai , Alhaji Abba ya mik'o Mata takardar ta Yana rungume da da Twins , kasa ansa tayi jikinta sai rawa yake tana fad'uwar gaba , tana dubawa kuwa taga dakinta yayi saki kuma har uku Babu batun komowa , rushewa tayi da kuka tana fad'in kayimin Rai Alhaji natuba , ta juya wajen Sanam tana fad'in " Dan Allah kisa baki Daddyn ki ya yafemin , Sanam tayi Murmushi sannan tace " Nafeesa kenan , ke aganin ki Yana da kyau a zauna da wacce zuciyar ta Babu Allah acikin ta ? Har kisan Kai fa kikasa ayi Allah yasa asirin ki ya tonu , duk irin abinda kikayi Daddyna ya yafe Miki sai dai bamason ki k'ara dawowa cikin rayuwar mu , mik'ewa sukayi Alhaji ya dubeta yace " Ina son in Gaya Miki daga yau ko me kama dake bana son k'ara gani acikin rayuwar mu nida iyalina , nagode wa Allah da baisa na had'a zuri'a dake ba , Yana fad'in haka yashige ya tafi shida 'Yayan sa suka bar Hajiya Nafeesa da tarin Dana sani..........
Tuni Aka tura su Hajiya Nafeesa da Hajiya Harira da Nurse virson zaman shekara uku da horo me tsanani ,.....
*Bayan shekara d'aya*
Tuni an saka ranar Huneed da Sanam wata Uku masu zuwa , Diyana itama lokacin aka saka Ranar ta da wani saurayin ta Umar , Soyayya ake zabgawa tsakanin Huneed da Sanam tamkar sukai junan d'aki , lokacin saura wata biyu da sati biyu su Sanam su kammala digree d'in su , kuma a lokacin Huneed yasamu k'arin girma yazama Babban Major ,
Mummyn Twins sai aikin gyara 'yar ta take da kayan Mata , duk wata kunya yanzu ta cire ta janyo 'yar ta jikinta tamkar k'awaye.....
Mummyn Twins yanzu ta ko'inah kulawa take bawa mijinta , dan Bata son Koda minty d'aya tabada k'ofar dazai yi tunanin wata mace bare kuma ya Kai ga aurowa , ...
Alhaji Abba kuwa kwata kwata baya tunanin k'ara wani aure ma , Dan duk wata kula Yana samu a wajen Hajiya Maimunar sa , ....
Koda Sanam tabawa Maryam kud'in da tayi Mata alk'awari k'in karb'a Maryam d'in tayi , sai da Sanam ta takurawa Maryam sannan ta nuna Mata ai ba komai ko jari taja dan ta rik'e kanta , Dan tunda Maryam ta haihu tasamu lalura saboda irin wuyar da taci , tuni Maryam ta tuba tasamu waje d'aya ta zauna tana kula da yaron ta ....
Akwana atashi yau saura kwana biyar bikin Sanam da Huneed Diyana da Umar , tun ranar talata aka fara biki domin biki ne na 'yar gata gaba da baya , Sosai kayi b'arin kud'i Amarya Sanam tasha kyau tamkar ita ta tsara kanta.
Duk Wanda ya d'ora idanuwa akan Sanam bazai so ya d'auke ba , gyara iya gyara tasha shi duk inda ta gifta sai dai kaji k'amshi na tashi