Showing 3001 words to 6000 words out of 78990 words

Chapter 2 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3670

duk lokacin dazata wuce kowa yake killace kansa saboda sanin halinta , Huneed jiyayi ransa yakuma b'aci tabbas saiya yi maganinta kuwa , dan tunda tashiga gonarsa wallahi saita raina kanta , mik'ewa yayi yace " inaso kafad'amin da wanne lokacin take wucewa dan tabbas saina saita mata hankalinta , Hisham yace " anjima ma zaka iya jinta sannan wajen sha biyun dare ma tana zuwa wucewa , amman inaso kabar wannan maganar ka shareta , dan wallahi bata da mutunci ko kad'an gashi Daddynta ko k'ararta bayaso ana kai masa , Huneed yace " wallahi daga ita har Daddyn nata dai dai nake dasu kuma tunda har ta tsokanoni wallahi saina koya mata hankali , yatasa tsaki yasa kai yafice daga d'akin nasu .......




Gudu Sanam take tamkar zata tashi sama har ta k'araso gidan gonar Daddyn su Zahra , tunda Diyana tagaya mata anan take Partyn nata , tana shigowa aka fara ihu ana fad'in " Oyoyo *'Yar kishiya rik'on me hak'uri* wannan sunan Sanam tana mugun sonshi , dan haka kawai hannu tasaka cikin jakar ta tafara zuba musu ruwan dollars , dan kwata kwata bata amfani da kud'in Nigeria mutuk'ar zasuyi wani party da k'awayenta , take gayu suka saka wawa suna ihun murna tare da zuba mata kirari , kanta ne yake k'ara fashewa tanajinta bakamar ta , Zahra tuni ranta yafara b'aci da abida gayun sukeyiwa Sanam , taya ita data shirya Party amman koda tazo basuyi mata kirari haka ba , daman tsakanin Sanam da Zahra akwai dabi sosai , kuma kowacce jitake da kanta tare da tak'ama da kud'i , sai dai duk kud'in Daddyn Zahra bai kai Daddyn Sanam ba , tuni Zahra ta d'auki speaker tayi wata tsawa tana fad'in "ya isheku haka malamai , in itace ta taraku zan iya tafiya inbaku guri , nan suka shiga bata hak'uri suna mata nata kirarin , Sanam ta tab'e baki tare da hawa step d'in da Zahra take , tana zuwa ta mik'awa Zahra hannu tana fad'in " Congrat k'awata rai yakashe , bandir d'in Dollars ta saka mata a hannu tare da cewa " gashi kyasha mai , tana gama fad'in hakan tayi sauri ta sauko tare da watsa kud'i sama sannan ta bar gun.....




Huneed tunda akayi sallar isha'i yaja ya zauna a k'ofar gate d'in Estate , dan yace yau bazai shiga gidaba har sai Yarinyar nan tazo tasamesa , kulle k'ofar gate d'in yayi yacewa megadi yaje ya huta zuwa anjima zai jire masa , wajen k'arfe goma na dare saiga Sanam ta nufo Estate da mugun gudunta data saba , koda Huneed yaji tahowar ta sai ya mik'e tare da nufar k'ofar gate d'in , aikuwa tuni Sanam tafara mahaukacin Hon d'in ta , cikin ransa yace zakiyi bayani wallahi nan ba k'ofar gate d'in gidan ku bane da kika saba iko , ganin ba'azo an bud'e mata ba yasa tafito a fusace , k'ofar ta nufo tana fad'in " wane mara mutuncinne wajen daya ruf'e gate d'in kuma yanaji ana hon bazai zo yabud'e ba ? buga k'ofar tafarayi amman taji shuru ba wanda yayi magana , ranta tuni ya k'ara b'aci sosai lallai masu gadin nan basu san ta bane shiyasa , tuni Huneed ya nemo ruwan sanyin s bokiti guda harda k'ank'ara sannan ya nufo k'ofar gate d'in , dama gashi anyi ruwan sama garin ya d'au wani sanyi me ratsa jiki , sakatun dayasa yashiga zarewa yana murmushin mugunta , lokacin Sanam ta kira wayar Mumy amman ba'ad'agaba , ranta yagama b'aci mutuk'a , tanajin anfara zare sakata ta dubi k'ofar tana k'issima irin rashin mutuncin dazatayiwa wanda ya bud'e .....
Bata ankara ba sai saukar ruwan sanyi taji ajikinta , tuni ta tsorata tana ja da baya jikinta yana tsuma , gashi ko kad'an Sanam bata shiri da ruwan sanyi , Huneed ya hasketa da touthlith yana fad'in " jiki wata k'azama dake sai rashin kunya da iya shege , inaso kisani ba'ayimin batare da na rama ba , kuma daga yau mun k'ullah nida ke , dan saina gyaraki a wannan Estate d'in namu , maza kizo ki wuce kibawa mutane guri mara kunyar banza , Sanam data daskare tamkar gunki a wajen ko motsi batayi saboda tsabar takaici.........








*Comment* plss



*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_ 🌹😍
[9/27, 09:37] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*







Chapter 3.


Tanaji tana gani Huneed ya juya yashige cikin Estate d'in , da kallo Sanam tabi bayan sa tare da mamakin irin Zarrarsa dayayi mata wannan wulak'ancin , komawa tayi cikin motar ta taja ta da gudu tashiga Estate d'in itama........


Sanam tana zuwa tayi wani mahaukacin Hon. Da gudu megadinsu yatafi tamkar zai kifa ya bud'e gate d'in , da gudu ta shigo tayi parking ta fita kana ganinta kasan a fusace take , tana shiga cikin Falor ko kallon kowa batayi ba tahaye sama da gudu.....
Hajiya Nafeesa lokacin suna zaune ita da Alhaji Abba suna hira , yana ganin wucewar Sanam a haka ya mik'e yana cewa " Anya lafiya kuwa naga My luv tashigo gida a haka ? Hajiya Nafeesa cike da kissa tace " nima naga kamar ranta a b'ace inajin dai akwai abinda akayi mata , da sauri Alhaji Abba ya nufi sama d'akin Sanam , Hajiya Nafeesa tabishi da wata uwar Harara tana fad'in " aikin banza yarinya ta dunga garaka kamar wani k'wallo , wannan soyayya taku gab nake da datseta , tsaki taja tare da nufar saman itama ........


Sanam tana shiga d'akinta tanufi toilet tasakarwa kanta ruwan d'umi , tanayin wanka tana tunanin irin rashin mutuncin da guy d'innan yayi mata , tabbas tunda aka haifeta batajin akwai wanda yatab'a yimata irin wannan wulak'ancin ba ,
Shigowar Daddyn ta taji cikin d'akin nata yana kiran sunan ta , dasauri tayi maza ta fito daga toilet d'in d'aure da tawul, Daddyn ta yace " meyafaru dake kika shigo a wani yanayi ? murmushi tayi sannan tace " babu komai Daddy wlh gajiya nayi kuma gashi inajin fitsari shiyasa , wata ajiyar zuciya yayi tare da cewa " kin tsoratani My luvly Dauther , dai dai nan Hajiya Nafeesa tashigo tana fad'in " meye yafaru my Happiness duk kin tsorata mu , murmushi tayi tace " babu komai fa Mumy kawai fitsari nakeji shiyasa , nan Hajiya Nafeesa ta rik'e mata kunne cikin wasa tana fad'in " zanyi maganinki agidan nan , naga kullum sabuwar rigima kike k'arayi , dariya suka saka dukansu sannan Daddy yace " in kinshirya kifito zamuyi magana , Sanam tace " to Daddy bari nasa kaya ganinan zuwa.......




Huneed baki har kunne saboda Abinda yayiwa Sanam ko banza zata shiga taitayinta , duk dayaji da gudu ta wuce amman zai gyara mata zama kwanan nan ,
Tunowa yayi lokacin daya watsa mata ruwan tayi tsamo tsamo da ita , dariya ya tuntsire da ita yana cewa " ni ko fuskar ta ban tsaya gani ba saboda wulak'ancinta , cikin zuciyar sa yace " amman gaskiya tana kama da Aljanu , dan yaga farinta har yaso yayi yawa duk da bawani tsayawa yayi ya k'are mata kallo ba ......




Sanam cikin kayan bacci ta fito Falor tasamu guri kusa da Daddyn ta ta zauna , cike da Shagwab'a tace " Daddy gani mezaka gayamin ne ? murmushi yayi yadubi Hajiya Nafeesa yace " ki gaya mata da kanki , murmushi Hajiya Nafeesa tayi tace " kagaya mata da kanka kaidai , Sanam tafara turo baki tana cewa " wai Daddy mene dan Allah kugayamin plss , Daddy cike da murna yace " zaki samu k'anwa ko k'ani kwanan nan , wani tsalle ta daka tana rungume Hajiya Nafeesa tace " Mumy da gaske cikine dake wayyo dad'i zansamu k'ani , murmushin yak'e Hajiya Nafeesa tayi tare da cewa " banice nake da cikiba my Baby , Mumy Maimuna itace take da ciki , tsayawa tayi cak murnar ta ta koma ciki tana fad'in " toni ina ruwana da cikinta tunda ba Mumyna bace , Daddy ya dubeta yace " haba My luv yakamata kitayani da murna koda bazakiyi murna saboda itaba , karki manta inaso naga kinsamu k'anne wanda zakina wasa dasu , shuru tayi nawasu mintyna sanna tace " Daddy kayi addu'ar Allah yabawa Mumyna sainayi duk yadda nakeso dasu , amman a yanzu bana murna dan nasan soyayyar dakakemin ce zata ragu , murmushi yayi yace "haba my luv kinsan duk yawan Yaran da zansamu a duniya babu abinda zai ragu game da soyayyarki , ked'in kece wacce Allah yafara bani a duniya kinga kuwa dole zansoki tamkar raina , Hajiya Nafeesa dauriya kawai takeyi saboda wani abu dake tokare da k'irjinta , mik'ewa Sanam tayi sannan tace " saida safe Daddy nagaji bacci nakejin , to my luv Allah yatashemu lafiya kiyi bacci me dad'i , matsawa tayi ta sumbaceshi a kunci , shima ya sunbace ta a goshi sannan ta juya wajen Mumy itama hakan tayi mata Ta juya tahaye sama d'akinta.....




Zahra tunda Sanam tabata wannan kud'in takejin haushi , ita Sanam zatazo har wajen Party d'in ta ta tozar tata , tabbas saita rama ai lokacin Birthday d'in Sanam yakusa anan zata rama abinda tayi mata ...
.
Washe gari Sanam sai sha d'aya ta farka tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa , d'inkin sosai yakamata ko ina najikinta a d'ame , sakkowa k'asa tayi sai faman zabga k'amshi take tamkar wata sabuwar Amarya , zama tayi kan dinnig tafara had'a break fast , Soyayyiyar plantain ta xuba tare da had'a tea , sai da tagama zubawa cikinta sannan ta mik'e tafita........


Harabar gidan tafito tafara tunani wanne mataki zata d'auka akan wanda yayi mata wanka da ruwan sanyi , tabbas saita nemosa ta nuna masa da banbanci tsakanin matsiyaci dakuma me kud'i , dan daga ganinsa talaka fak'iri dan tasan duk cikin estate d'in su babu wanda yakai Daddyn ta kud'i , ita kuwa duk wanda bai kai Daddynta ba to tabbas ba me kud'i bane a wajenta , a hankali take tafiya har ta k'araso k'ofar gate , da gudu me gadi yataho yanayi mata kirari tare da cewa " hajjaju aikene kikawo ayi miki ? bud'emin gate kawai tace tana kuma d'aure fuska , da sauri ya bud'e mata tare dayi mata fatan dawowa lafiya.......




*Kuyi hak'uri da wannan*




*Comment plss*




*'Yar* *Mutan* *Kanawa* _Ce_🌹😍
[9/27, 09:37] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR* *KISHIYA*
_Rik'on_ _Me_ _Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*






*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*






Chapter 4.




Tunda Sanam ta fito daga cikin gidan su tafara zagaye a Estate d'insu duk akan idon Huneed , dan shima tunda gari ya waye yafito yake gadin wucewar ta , dan yanaso ya tabbatar da cewa taji kashedinsa ko kuwa , tana tafe tana duba k'ofofin gidajen dan sotake ta tabbatar da a wanne gida yake , kamar daga sama taji muryar sa yana fad'in " sokike kiganni ko ? da sauri taja da baya tana dubansa cikin zuciyar ta take fad'in " anya wannan mutumin mutum ne kuwa ? zarrarsa da kuma yadda yake nuna wata izza dajin kansa , katseta yayi da cewa " kind'auka ni Aljanine ko ? k'iris yarage Sanam bata zura da gudu ba , wata zufa ce ta tsatstsafo daga jikinta duk irin sanyin da akeyi , amman ta dake ta dubesa tace " Hmm nasan kai mutum ne kamar kowa , sannan ba kowa bane kai face talaka fak'iri wanda bai wuce kazo a meyimin wankin takalmi ba , Wani Shu'umin murmushi Huneed yayi yana dubanta sannan ya matso gab da ita Numfashin su na dukan juna yace " inaso kisani duk wani d'agawarki da ji da kanki da kuma dukiyar dakike tak'ama da ita duk abanza suke a wajena , kuma kamar yadda kikace ni bakowa bane yes ni bakowa bane kuma ba d'an kowa bane , amman inaso kisani ni ba k'ask'astance bane bakuma mara zuciya bane , ni d'in da kike gani Namiji acikin mazaje me zuciyar Nema , kuma mutuk'ar muna numfashi dani dake a duniya to watarana sai kin gogemin takalmin da zansa , kuma kin wankemin kayan jikina tare da gogemin motar dazan hau , yana gama gaya mata hakan yajuya zai tafi tuni tayi saurin shan gabansa tare da rik'e k'ugu tace " wai kai dame kake tak'ama da har kakemin irin wannan maganganu ? Huneed ya dubeta yace " bana tak'ama da komai sai dai innuna miki Namiji Namijine a ko'inah kuma duk irin girman kan mace to tabbas Namiji ne gatan ta , nasan duk wanna d'agawar taki da jin kan naki dole watarana gidan wani zakije kuma dole ya juyaki mutuk'ar ba maza yarako duniya ba , kuma ina fatan kina sane da sharud'an da na gindaya miki akan gudu da motar , in kunne yaji to jiki ya tsira yashige yafara tafiya abinsa , a fusace Sanam tace waye kai d'in kuma acikin Estate d'in inaso isan waye Mahaifinka da har kake kafamin doka haka ? batare da Huneed ya juyoba yace " Sunana Huneed Abdallah Kiyi tambaya cikin Estate d'in zakiji tarihina in kina buk'ata , Nabarki lafiya Bera a cikin Mata.........
Sanam tsayawa tayi tana kallon sa har ya k'ulewa ganinta , Sunan daya kirata dashi tashiga maimaitawa Bera a cikin Mata , tabbas wannan yaraina mata hankali wato yana nufin ita ba mace bace ba , lallai zata nuna masa kalar halinta sai yagane lallai ita ba Bera bace mace ce data amsa sunan ta , a fusace ta juya ta nufi Hanyar gida.......


Huneed yana dawowa yasamu kira a wajen ogan su , tuni aka turasu aiki wani gari a jihar Calaba dan ko 'Yan ta'adda , had'a kayansa yayi kafin yafito har anzo d'aukar sa , yana fito wa yaron sa ya fito ya sara masa tare da bud'e masa murfin mota , Hisham yadubi Huneed yace " Soja wuta soja harbi Soja gatan daji inbaku gari baza ya kwana k'alau ba , inayi maka fatan samun Nasara a wannan fitar taku Allah yadawo mana dakai lafiya , Murmushi Huneed yayi tare da duban Hisham yace " Ameen d'an uwa ka kulamin da Hajiyar mu kadunga bata magungunan ta akan lokaci , sannan inaso kasa idonka akan Berar yarinyar nan kaga zata gyara halin nata ko saina fito mata a kalar ta , tuni Hisham yasa dariya yace " Anya wannan yarinyar zata canza kuwa ? amman zandunga saka ido naga yadda wasan naku zai k'are , Huneed yayi Murmushi yace " ai haryanzu yarinya ce batasan komai na duniya ba , gata da kud'i shine tasani amman da sannu saina saita ta tadawo dai dai , tarbiyar da iyayenta sukayi mata saina gogeta na d'ora mata tawa , Hisham yace " Allah yasa hakan dan gaskiya basu d'orata adai dai ba , Huneed yace " zata dawo dai dai tunda har ta shiga gonata , juyawa yayi ya shiga motar tare dacewa Hisham sai sunyi waya....


Koda Sanam tadawo gida Sama tahaye cikin d'akinta , wayar ta ta d'auko tare da kiran Number Diyana , bugu d'aya tayi ta d'aga tare da fara yiwa Sanam kirari " Babbar Yarinya gidan kud'i sarauniyar kyauta , duk wanda yaga kiranki to yafara washe baki dan yasan Alkairine , Sanam cike da jin kai da wata Izza tace " Diyana kina inah yanzu ? Diyana tace " ina gida a zaune inah zaman banza ko da aikine inzo ? Sanam tace " tabbas akwai Aiki akan wani Mutum dayake neman zama matsala arayuwa ta , Diyana tace " waye shi dazai shiga sabgar Uwar d'akina baya goya marayu ? Sanam tace " shine nakeso kizo yanzu kiyimin bincike cikin Estate d'in nan namu akan labarin sa kaf , Diyana tace " karki damu *Rik'on Me Hak'uri* ganina zuwa kibani minty 10 kacal , Sanam ta kashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login