Showing 27001 words to 30000 words out of 78990 words

Chapter 10 - YAR KISHIYA BOOK COMPLETE BY Zee MD.txt

Zee MD   

19 Feb 2025

3689

Sanam d'in tace , Murmushi tayi na takaici batare da tace komai ba ta mik'e tabar wajen , shima kuma Alhajin bai wata nuna damuwa ba game da jin maganar Sanam d'in , Kashe wayar tayi sannan ta fara janyo kulolin da Hajiya Nafeesa ta jera mata su , tuni Hajiya Nafeesa tafara wani shu'umin murmushi , duban Fahad tayi suka had'a ido sannan suka murmusa....
[9/27, 09:52] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir Rahamanir Rahim*







Chapter 20.




Sanam tana bud'e kular taga sakwara sosai taji dad'in ganin nata , janyo d'aya kular tayi tabud'e miyar agusi da ta wadatu da naman rago sai k'amshi ke tashi , d'auko guda d'aya tayi tasa a filet tare da zuba miya tajanyo tana fad'in " Mumy tamkar kinshiga zuciya ta kinsan inason cin sakwara , tunda naje Turkey nake kewar cin ta amman bansamu ba , cike da kissa Hajiya Nafeesa tace " haba my luv kinsan komai da nasan zai faran ta miki ai shinakeso , yanzu dai bari nashiga d'aki na fito nasan lokacin kin gama ci sai kibani labarin Turkey , Sanam tayi murmushi tace " wanne labari Mumy ? sai dai ko labarin bikin da akayi zanbaki , Hajiya Nafeesa tace " ai daman shi nakeso kibani bari na fito....
Fahad shima tashi yayi yabi bayan Hajiya Nafeesa yana fad'in " Aunty ina key d'in motar ki zanfita ? ...


Sanam lomar ta d'aya taji muryar Diyana tana sallama , da gudu Diyana ta taho tana fad'in " Oyoyo my Besty ta , nayi missing d'inki sosai tunda kika tafi ko nemana bakyayi , murmushi Sanam tayi sannan tace "kinsan biki naje dole kimin uziri amman kina raina nima , zama tayi ta janyo filet d'in sakwarar dake gaban Sanam tace " kice nazo asa'a anyi best food d'inki , Sanam tace " wallahi kuwa Mumy ce tamin na murnar dawowata , lomata d'aya kika shigo zaki samin rani kawai , Murmushi Diyana tayi tana fad'in " naji d'in ai nima kinsan inason Sakwara sosai , Sanam tace " to gatanan ai sai kiyi ta fama , zata sake magana wayar ta tashiga ruri , d'auka tayi tana duba screen d'in wayar number Huneed tagani , da sauri ta mik'e tana cewa " Diyana ina zuwa , da kallo Diyana tabi bayan Sanam da kallo tana fad'in " a lallai Besty kinyi kamu wannan rawar jiki haka ,.....


Sanam can bayan gida ta fita sannan ta d'aga wayar , tana d'agawa tayi sallama tamkar ba ita ba , Huneed najin muryar Sanam ya lumshe ido yanajin saukar wani nishad'i , a hankali ya furta " My speacial ya kike ? Sanam sauke wayar tayi daga kunnen ta tana k'ara duban wayar , dagaske Huneed ne yakira ta da My Speacial ko dai kunnen tane ? maganar dataji ya kumayi ne yasa ta maida wayar kunnen nata , ci gaba yayi da magana yana cewa " andawo lafiya ? sai sannan mamaki ya kama Sanam taya yasan ta dawo ma ? murmushi yayi me sauti tana jiyowa yace " kina mamakin ta yadda akayi nasan kindawo ko ? to kibar mamaki kawai dai na tsoka ne kine , murmushi tayi itama sannan tace " yakake ? lafiya lau nake dafatan kindawo lafiya , Sanam tace " lafiya lau nadawo kaima ina fatan nasameka lafiya ? Huneed yace " lafiya lau nake sai dai kawai inason ganin kyakkyawar fuskar Mata ta , Sanam tace " ai sai ka koma gida ka kalleta ko zaka samu sauk'i , batajira yace wani abun ba ta kashe wayar sabo da wani kishi da yataso mata , kwata kwata idon Sanam ya rufe ko gaban ta bata gani ta nufi cikin gida da gudu ta haye sama d'akin ta......


Hawaye ne ke zuba a idon ta ta fad'a kan gadon ta , cikin ranta tace " me yake nufi dani ne ? daga munfara magana sai yadunga min maganar matar sa ina ruwana da ita , sosai Sanam keyin hawaye saboda wani mugun *Kishi* dataji yana taso mata......
[9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*




*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*






Chapter 21.



Huneed tunda yaji yadda Sanam ke magana k'arshe ma ta kashe waya yake mamaki , to shifa yasan har yanzu bai furta mata yana sonta ba , amman taya take da wannan kishi haka ? to kodai itama kamar yadda yakamu da sonta haka itama ta kamu da nasa ne ? idan kuwa hakane to tabbas zai yi rawa ya juya dan daman fargabar sa ita , kuma abinda yasa yasan ta dawo shine ' Diyana ce tazo wucewa d'azu suna tsaye da Hisham , tana ganin su ta k'araso tazo suka gaisa anan take shedawa Hisham ai Sanam tadawo , murmushi yayi sannan a hankali ya furta ai dole na shirya zuwa lallashi , tashi yayi ya nufi toilet dan watsa ruwa.......


Kwata kwata Diyana bataga shigowar Sanam ba , hankalin ta na kan cin sakwara da miyar agusi ta , dama Diyana akwai shegen kwad'ayi gashi gidan su basu da wani k'arfi sosai , sanadin k'awancen su da Sanam ma a sch suka had'u , Yayan Baban Diyana yana da kud'i shine ya d'auki nauyin karatun ta shiyasa tasamu tayi sch d'aya dasu Sanam , ga Diyana akwai gayu da gwalli dakuma shish shigi , ta duk'ufa tana ta cin Sakwarar ta taji muryar Hajiya Nafeesa tana fad'in " Diyana ina kuma Sanam d'in ? sai sannan ta saita kanta dan gudun yarfi , dan tasan halin Hajiya Nafeesa akwai wulak'anci da jin kai , gaishe ta tayi tace " Mumy barka da yamma dafatan kin wuni lafiya , Hajiya Nafeesa a tak'aice ta amsa da cewa " lafiya ina Sanam ? Diyana tace " naga ankira wayar ta tafita waje ta d'aga shine bata dawo ba , Hajiya Nafeesa da sauri ta dubi Diyana tace " taci Abincin nan kuwa ? Diyana tace " e nashigo nasameta tana ci daga nan muka fara magana sai kuma aka kira wayar tata , wata ajiyar Zuciya Hajiya Nafeesa tayi idon ta ya rufe kwata kwata tace " Alhamdulillah , sannan ta kuma kallon Diyana tace " kin tabbata dai taci ko ? Diyana cike da mamaki tace " ea na tabbata Mumy , cikin ranta tace " meyasa Mumyn Sanam takeso taci Abincin nan haka ? kodai akwai abinda takeso tayi mata ? ganin Diyana ta tafi Nazari yasa Hajiya Nafeesa ta saita kanta tace " kinsan k'awar taki batason cin Abinci shiyasa nadamu , kuma kinga daga tafiya tadawo yakamata ace taci abinci kar Daddyn tq yayi fad'a , dayake Hajiya Nafeesa ta k'ware wajen kissa da kisisina tuni ta shigar da Diyana.......




Sanam tuni bacci yayi awon gaba da ita , daman agajiye take ga kuma kuka da tasha ai tuni tayi nisa a bacci....




Diyana ganin shuru shuru Sanam bata dawo ba yasa ta mik'e dan ta lek'a , dai dai lokacin Daddyn Sanam ya bud'e k'ofar palor ya shigo shima , sunayin karo da Diyana yaji ya tsani ganinta ya had'e fuska sosai , Diyana ta rissina tana gaidashi , wata harara ya wurga mata yatsa tsaki batare da ya amsa ba yayi gaba , duk abinda yafaru akan idon Hajiya Nafeesa ba k'aramin dad'i taji ba ganin maganin yafara aiki , cikin ranta tace maganinki ai kwad'ayayyi yar banza da wofi , Diyana tunda taga kallon da Daddyn Sanam yayi mata da kuma k'in kula ta dayayi jikinta yayi sanyi , Daddyn da inya ganta har tsokanar ta yake tare da wasa da dariya , amman yau ko kallo bata ishe shiba sai ma harara da tsaki , tabbas inajin akwai abinda yafaru dole tasamu Sanam suyi magana , sai dai tana fitowa harabar gidan bataga Sanam ba , ba inda bata duba ba amman babu Sanam babu dalilinta , cikin ranta tace " to ita kuma ina tayi haka ? gashi duk motocin gidan suna ajiye bare tace fita tayi , har zata koma cikin gidan wata zuciyar tace " karki shiga kuma yanzu Daddy yasa miki duka , tuni ta fice daga cikin gidan batare da ta kuma bi takan neman Sanam ba ....




Alhaji Abba yana k'arasowa Hajiya Nafeesa tafara murmushin kissa tana fad'in " wato anji shalele ta dawo shine aka taho a ganta ko , murmushi yayi yana mejin dad'in yadda Hajiya Nafeesar ke nunawa 'Yar tasa tilo soyayya , ko ba komai hakan yana sawa yaji yakuma santa sosai , zama yayi a d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falor yana fad'in " wai ina take ne ? Hajiya Nafeesa cike da murmushi tace " inajin tana d'akin ta , amman bari naduba nagani ko bataji shigowar kaba , da sauri ta nufi sama dan ganin Sanam d'in ko tana nan , dan ta matsu taga sun had'u yayi mata yadda yayiwa Diyana , wata dariya tayi tare da furta " Sanam ki shirya yau kinzo hannu , sai na rusa miki farin cikin ki saina saka kinzama abar tausayi kuma mak'ask'anciya , haka ta k'arasa cikin d'akin Sanam d'in .....


Tana tura k'ofar tasamu Sanam kwance a gado tana bacci , gashin kanta ya rufe mata duk ilahirin fuskar ta , tsayawa rayi tana mamakin meyasa Sanam d'in bacci a irin wannan lokacin ? tunowa da tayi in Sanam na bacci ba'a tashin ta yasa ta tsaya , dan tabbas in ta tashe ta to rarrashin ta ma sai yazama aiki kafin tayi shuru , har ta juya zata fita taga Sanam d'in ta motsa , da sauri tace " My luv kin tashine ? Sanam ta bud'e idon ta a hankali tana duban Hajiya Nafeesa , a hankali ta furta " natashi Mumyna akwai wani abin ne ? Hajiya Nafeesa tace " Daddyn ki ne yazo yakeson ganinki shine nazo kiranki naga kamar bacci kike , Sanam jin ance Daddy yasa ta mik'e zaune tana fad'in " ganinan zuw Bari nayi wanka dan jikina ciwo yake min , Hajiya Nafeesa tayi murmushin yak'e tace " to shalele inkin fito kisamemu a k'asa , Sanam tace " to tana mik'ewa ta nufi toilet.......




Bayan Minty 10 saiga Sanam ta sauko sanye da riga da siket na wata babbar atamfa , sosai kayan suka amshi jikinta suka mata kyau , kanta babu d'an kwali sai wani k'aramin gyale da ta yafa kalar jikin atamfar , sai kuma filet shoe d'in ta datasa , sosai tayi kyau sai k'amshi ke tashi ajikinta ta ko' inah , tana k'arasowa Daddyn ta yafara murmushi yana fad'in " your welcome my love , a hankali Sanam ta k'araso jikinsa tana murmushi tare da murnar ganin Mahaifin nata , tabbas 'Da da Mahaifi sai Allah wata k'auna ce a tsakanin su me zafi , Alhaji Abba yana mutuk'ar ji da tilo d'in 'Yar sa , dan haka a koda yaushe bayason yin nisa da ita , sundad'e a manne da juna suna murnar ganin juna kafin Sanam tasamu guri kusa da Daddyn nata ta zauna , gaishe shi tayi cike da girmamawa dan Sanam duk iskancin ta tasan darajar gaida iyaye , amsawa yayi cike da so da k'auna yana cewa " kinga yadda kika rame kuwa ? nasan ba lallai kina cin Abinci ba acan , shiyasa nafison muyi tafiya tare saboda baki kulawa , Hajiya Nafeesa tamkar gunki haka ta koma tunda Sanam ta fito da yadda taga Daddyn nata ya tare ta , cikin ranta take fad'in " wato da alamar Sanam bataci maganin nan ba kenan ? tabbas bata ci ba tunda gashi Diyana taci kuma taga Yadda Daddyn Sanam d'in yayi mata , tayi nisa cikin tunani taji muryar Alhaji Abba yana fad'in " Hajiya Nafeesa ko bakyaji ne ? firgigit tace " inaji Alhaji kasan in muna tare da Sanam bana iya sauaran komai sai sautin ta , murmushi yayi sannan tace " ai gatanan ta dawo sai kitajin sautin muryar ta ta , nan suka saka dariya wacce a b'angaren Hajiya Nafeesa yak'e ceb, dan ji take kamar ta mik' e ta shak'e uba da yar saboda takaici , sukuwa ko ajikin su sai hira suke cike da nishad'i , tuni Hajiya Nafeesa ta mik'e tace " zataje d'aki tadawo ...
Tana shiga d'aki ta d'auko wayar ta ta shiga kiran Hajiya Harira.......









*Rashin Comment* *shine yake sani typing kad'an*🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️




_Indai zanga Comment to kuwa zan muku typing me yawa_






*Dan Allah kugyara kudunga Comment*






*'Yar Mutan Kanawa* _Ce_✍🏻🌹😍
[9/27, 09:54] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻‍♀️🤦🏻‍♀️




*NA*
*Zee* *MD*






*Hamdala* *Writer's* *Association* 💪
https://www.facebook.com/111403834371046


✨✨ *{{* *H.W.A* *}}*✨✨




*Bisimillahir* *Rahamanir* *Rahim*








⚜️ *BU'DA'D'DIYAR SOYAYYA*




Jameey yar' mutan kankia




*Promo* *Promo* *Promo*






Daga yau 21/5/2022 promo dinmu zai fara , har zuwa 30/5/2022 inshaa Allah , ga yanda promo din yake.




#300-sau biyu a rana
#500-sau ukku a rana
#700-sau hudu a rana






kiyi man wannan number magana danjin yanda zaki biya 08160508316







Chapter 22.




Kuka Hajiya Nafeesa ta fashewa da Hajiya Harira , da sauri Hajiya Harira tashiga tambayar ta " lafiya kike irin wannan kuka haka ? waye ya mutu kuma ? Hajiya Nafeesa tace " wallahi wanda ayi mutuwa da abinda yafaru , dasauri Hajiya Harira tace " sakin ki Alhaji Abban yayi ne ? da sauri Hajiya Nafeesa ta dakatar da kukan tace " ki rufamin asiri ba sakina yayi ba shirin mune dai ya lalace , wani guntun tsaki Hajiya Harira tayi saboda takaici , taso ace ma sakin Hajiya Nafeesan akayi tasamu tayi wuff da Alhajin , a fili kuma tace " garin yaya akayi hakan kuma ? kinfi kowa sanin irin wahalar da mukaci kafin musamu wajen wannan bokan , ga mak'udan kud'in da kika kashe , Hajiya Nafeesa ta goge Hawayen ta tace " duk tarin kud'in dana kashe bashine yada meni ba , kawai ina tunanin yadda zamu kuma komawa wannan dajin me nisan tsiya , gashi bokan nan kwata kwata bashi da imani wajen cewa sai ya kwanta dani , Hajiya Harira tace " wannan ma me sauk'i ce mutuk'ar buk'ata zata biya , sai dai kar mukoma kizo kisake yin sakaci wani abun yafaru kuma , wai garin yaya hakan tafaru shirin namu ya lalace , nan Hajiya Nafeesa tashiga gayawa Hajiya Harira duk yadda abin yakasan ce , wata ashar Hajiya Harira tayi tana fad'in " shegiyar k'awar tata ce me kwad'ayi munafika , wanda ma da Alhajin ya tsaneta kinga zata rage zuwa gidan sai muyi yadda mukeso , nan Hajiya Harira tashiga kwantar wa da Hajiya Nafeesa hankali har da k'ara tinzura ta akan lallai sukoma wajen bokan , abinka da wacce tayi nisa zuciyar ta ta k'e k'ashe tuni takuma jin wani k'arfi yazo mata , take suka shirya randa zasu koma wajen boka me doki.....


Sanam sai hira suke da Daddyn nata cike da so da k'auna , anan yashigo mata da maganar taje ta gaida mumyn ta Hajiya Maimuna , Sanam take fara'ar dake fuskar ta ta dakushe , cike da shagwab'a tace " Daddy nifa kasan matar nan taka ba sona take ba , koda yaushe naje gidan nan bata da aiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login