Showing 72001 words to 75000 words out of 78990 words
a yanzu zaizo k'arshe , Sanam tayi wani shu'umin Murmushi tare da mik'ewa tsaye itama tana fad'in " banason Shirin ta ya rushe a yanzu , kamar yadda ta shirya hakan ne zai tafi Amman inaso daga k'arshe wasan ya canza salo ,. .
Huneed ya dubi Sanam da mamakin abinda tace , Sanam itama tana duban sa sannan taci gaba da magana " Maryam inaso kifad'amin nawa ta biyaki kike Mata aiki ? Maryam datayi tsuru tana kallon su duk jiki na Mata ciwo tace " lokacin da zanyi mata aiki munyi da ita zata bani " 2 million Amman Bata bani ba kawai dubu d'ari biyu tabani shima dan kawai zan Mata aikin rabaku da juna , Sanam tace " inaso kituromin account number ki zansa Miki 3 million kiyi min nawa aikin , Maryam sosai ta girgiza dajin hakan to itakuma wane aiki zatayi Mata hakan? Huneed da Diyana su kansu kallon Sanam suke suna son jin wane aiki zata saka Maryam , Sanam tace " inaso kici gaba da zama a gidan mu , sannan karki kuskura ki nunawa Hajiya Nafeesa nasan komai data ke shiryawa , Abu na k'arshe kuma kiyi yadda zakiyi kishiga jikinta sosai Dan ki jiyomin duk wani shiri da take akaina , kuma ban yadda ko Fahad yasan da wannan maganar ba , yanzu za'a sakeki kitafi sai ki nuna musu accident kikayi tunjiya shiyasa baki kwana a gidan ba ,
Diyana ta kalli Sanam sannan tace " Besty meyasa kikeson yin hakan ? Sanam tayi Murmushi sannan tace " inaso Daddy yazo yakamata da hannun sa , tunda yanzu Daddy ta had'ani dashi komai zance bazai yadda ba , kuma yanzu bamu da hujjar tunkarar ta da wannan maganar , zata iya k'arya tawa tare da sake sabon shiri Wanda ba lallai musan irin Shirin da zatayi Nan gaba ba , dukansu sukayi Na'am da maganar da Sanam tayi , Huneed ya kalli Maryam sannan yace " kinji abinda tace Miki ko ? Maryam da sauri ta d'aga kai Dan tana mugun tsoron Huneed , Huneed ya durk'uso wajen fuskar Maryam yace " inaso kisani mutuk'ar kika sake wannan Shirin namu ya lalace to tabbas saina kashe ki da hannuna kafin ita Uwar d'akin naki takashe ki , Maryam cike da tsoro tace " bazan karya alk'awariba , Nan Huneed ya fito suma dukan su suka fito har Maryam datake d'ingishi ,
A jikin motar suka samu Huneed Yana jiransu , kullo gidan yaje yayi sannan yazo ya bud'ewa Sanam murfin motar , shiga tayi itama Diyana tashiga sai Maryam a tsaye sai muzurai take , wata tsawa Huneed ya daka Mata Yana cewa" ko bazaki tafi ba ne in maidake cikin gidan ? Da sauri tashige motar Dan Bata fatan sake taka k'afarta a k'ofar gidan ......
Huneed sai da suka Kai Diyana har cikin makaranta sannan suka taho , tsayawa sukayi nesa da gidan Hajiya Nafeesa suka sauke Maryam tare dayi Mata Manyan worning akan maganar da sukayi , jikinta na rawa ta amsa da to tayi saurin barin gurin......
Huneed da Sanam tunda suka sauke Maryam kowanne yayi shuru , a haka har suka k'araso gidan Mummy twins , suna shiga suka sameta a palor tana kallo twins duk sunyi bacci , sallama sukayi Mata ta amsa tana cewa " sannun ku da dawowa , Huneed yace " sannu da gida Mummy , yauwa sannu Huneed kungaji da yawa daga ganin ku , Sanam tana k'arasowa ta durk'usa wajen k'afar Mummyn Twins tasaka wani kuka me tsuma zuciya .........
Mummyn Twins Bata hanata ba illah zuba Mata idanuwa datayi tana kallonta , cikin muryar kuka Sanam tace " Mummyna Dan Allah kiyafemin duk iri Abubuwan da nayi Miki , tabbas na aikata kuskure Wanda bansan illar hakan ba sai yanzu , na d'auka duk duniya Hajiya Nafeesa tafi kowa Sona saboda yadda take nuna min gata da kuma yadda take barina inayin yadda nakeso , Ashe duk ba haka bane duk duniya ba Wanda yakaiki Sona Mummyna kece kikasan ciwona kece kika fi kowa k'aunata , nayi nadama akan duk abinda na aikata Miki Dan Allah ki yafemin Mummy ko nasamu sauk'i a zuciyata ,Hajiya Maimuna cike da so da k'auna ta rungumo 'Yar ta jikinta tana bubbuga Mata baya tare da cewa " kiyi shuru kidaina kuka Ni bantab'a rik'eki araina ba , a Koda yaushe Ina Miki addu'a akan Allah yashirya minke , kuma Koda yaushe kina cikin raina bantab'a ganin laifin kiba akan abinda kikeyimin , nasan komai da kikeyi bayin kanki bane irin tarbiyar da aka baki ce tunfarko ,yanzu Alhmdllh tunda Allah ya amshi addu'ata ya shiryamin ke kindawo hanyar danake son kihau , Allah yayi Miki albarka Sanam Allah yakuma tsaremun ke daga sharrin dukkan abin k'i , Huneed ya amsa da Ameen cike da so da k'aunar Mummyn Sanam , cikin zuciyar sa Yana hamdalar samun sirika ta gari abar alfahari , ......
Nan Huneed ya kwashe komai da Maryam tafad'a musu yagayawa Mummyn Twins ,. Sosai ta girgiza dajin maganar Bata tab'a zatar abin Nafeesar zaikai hakaba , lallai Allah yanason su tunda gashi ba'aje ko'inah ba Allah yatoni asirin ta........
[9/27, 14:29] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 48.
Har irin Shirin da Hajiya Nafeesar take akan raba Sanam da Daddyn ta sai da Huneed ya gaya Mata , Mummyn Twins tace " insha Allah bazatayi nasarar hakan ba , inaso ki kwantar da hankalin ki k'arshen makircin tane yazo shiyasa tashirya muku wannan Shirin nata , gashi kuma ta dalilin hakan nata Shirin duk zai wargaje , Nan sukaita tattauna akan irin abubuwan da Hajiya Nafeesar ta ke k'ullawa ,
Sai bayan sallar la'asar sannan Huneed ya yiwa su Mummy sallama tare da sheda musu gobe da Asuba zai koma kan aikinsa , Nan Mummy tayi Masa addu'a tare dayi Masa godiya akan yadda ya jajurce akan lamarin Sanam ,. ..
Sanam har jikin Motar ta rako Huneed Nan suka tsaya , duban ta yayi yace " My wifey zan koma kan aikina Ina buk'atar addu'ar ki , Sanam ta dubesa tana kashe idanu cike da kissa tace " My Soja shigowar ka cikin rayuwata Babban Alkairine , Kai d'in agareni Babban jigone Dan haka addu'ata a Koda yaushe na zama mallakin ka , Ina yi maka fatan Alkairi Allah ya tsaremin Kai a duk inda kake , sannan Allah yarabaka da sharrin Matan zamani , Murmushi yayi ya amsa da Ameen Mata ta Allah ya dawo Mana da Daddy lafiya in turo iyayena a mallakamin ke , rufe idanuwa Sanam tayi tana dariya Nan suka rabu tamkar sutafi tare saboda tsananin k'aunar juna .......
Haka akaci gaba da tafiya kwanaki na shud'ewa , watanni na wucewa har Cikin Maryam ya shiga watan haihuwa , duk wani k'ulli da Hajiya Nafeesa take Maryam na Kiran Sanam ta sanar Mata , har Asirin da tazo gidan Mummyn Twins ta barbad'a da niyar zuwa ganin Sanam , Nan ma Maryam ta sanar da Sanam Dan haka Hajiya Nafeesa na tafiya akasa masu gadi suka wanke gidan tass.....
Daddyn Sanam sai turowa Hajiya Nafeesa kud'i yake tana Masa k'aryar siyan kayan barka , shi ason sa ma soyake ta taho inda yake ta haihu , Amman tashiga tsarashi akan dole ya hak'ura , sai dai yace da zarar ta haihu zai taho gida ayi hidimar suna da shi , ....
Wani magani likitan Hajiya Nafeesa yashiga bata duk jikinta yafara kumbura tamkar me cikin gaske , a cikin satin Maryam tafara nak'uda tamkar batayi , asibiti suka kaita da k'yar aka samu ta haihu Amman tasha wuya sosai , cikin ikon Allah ta haifi d'anta bak'ir k'irin dashi , tamkar Hajiya Nafeesa tasa ihu saboda munin d'an data gani , haka suka ja gefe ita da Harira suka shiga magana , Hajiya Nafeesa tace " yanzu wannan jaririn ta inah yake kama da Fahad ? Shegiyar yarinyar bin mazan ta yayi yawa wallahi , wannan yaron duk Wanda yagansa yasan ba d'ana bane , Babu ta inda zance Yana kama dani bare kuma Alhaji , Hajiya Harira tace " a can d'akin Naga wata mata itama ta haihu Amman kamar naji an cewa Bata motsi , me zai Hana muje muga wanne kalar d'a ta Haifa sai musan abinyi , kinga inyaso sai ki jik'a likitocin Asibitin da kud'i suyi Mana musanye , take Hajiya Nafeesa tayi na'am da shawarar Hajiya Harira suka nufi d'akin da Matar take .....
Sukayi sa'a kuwa d'akin Babu kowa Nan suka ga jaririn ta fari kyakkyawa dashi , Nan suka rik'e baki suna duban juna kafin su fito da sauri suna Hamdala , wata nurse ce tazo zata shiga cikin d'akin , da sauri Hajiya Nafeesa ta tare ta tana fad'in " kece wacce kika amshi haihuwar wannan Matar ? Nurse tace " nice lafiya kuwa Hajiya ? Nan suka ja ta gefe suka shiga kora Mata bayani akan aikin da suke so su sata , tare dayi Mata tayin kud'ad'e masu tsoka inhar tayi musu aikin , tanajin irin kud'in da suka fad'a take ta amince Nan Hajiya Nafeesa tayi Mata transfer na dubu d'ari biyar akan zata ciko Mata sauran , Nan suka koma d'akin Maryam suka d'auko d'anta batare da sun yi karo da kowa ba suka kawoshi d'akin Matar Nan , sannan suka d'auki na Matar suka dawo dashi d'akin Maryam , Nan Hajiya Nafeesa ta kwanta a gadon mara lafiya likitan ta har lokacin bai k'araso ba , Yana zuwa yayi Mata wata allura wacce ta maida jikin ta tamkar namasu jegon gaske , dayake likitan shima ba Mai kula bane gashi da son kud'in tsiya shiyasa bai San kalar d'an da Maryam d'in ta Haifa ba ......
Tuni aka shiga gayawa 'yan uwa da abokan arzik'i haihuwar Hajiya Nafeesa , Alhaji Abba baki har kunne yakira waya tare da cewa Yana Nan akan hanya , ..
Koda su Sanam da Mummyn ta suka samu labari take suka shiga dariya Dan wasan yazo k'arshe ,. Mummy Twins Koda tayi waya da mijinta tayi Masa murna na samun k'aruwar da akayi batare da ta nuna komai ba , Nan yake sheda Mata gobe Yana hanya shima dan dole yadawo gida dan taya Hajiya Nafeesa murnar samun haihuwa ,Mummyn Twins tace " gaskiya dai yakamata kadawo Dan kuwa wannan abin murna ne sosai yasamu, abinda ake nema shekara da shekaru Allah bai kawo ba sai yanzu ai dole azo ataya murna , Nan sukayi sallama tana duban Sanam suna dariya , lokacin tuni Sanam da Mummyn ta sunzama tamkar k'awaye , duk dangin Hajiya Maimuna babu inda Sanam yanzu Bata shiga , gidan Hajiya kuwa Kakar ta kusan kullum tana hanya saboda akwai sa'anin ta a Family d'insu kusan kullum suna tare.,...
Sanam tuni ta shedawa Huneed Maryam fa ta haihu , kuma dole yadawo dan a yanzu Maryam tana buk'atar kulawarsu sosai , tunda kaga ta haihu nasan a Koda yaushe zata iya sakawa akasheta , Huneed tuni ya had'o kayansa shima ya nufo Abuja Dan wannan wasan k'arshen dole yadawo agama wasan dashi ...........
[9/27, 14:29] Muhammad Karim: [9/26, 21:04] Muhammad Karim: *'YAR KISHIYA*
_Rik'on Me Hak'uri_
🤦🏻♀️🤦🏻♀️
*NA*
*Zee MD*
*WOMEN WRITERS ASSOCIATION*📚
( Domin Marubuta Mata )
✨ (W.W.A) ✨
https://www.facebook.com/106752595253176/posts/107924965135939/
*Bisimillahir Rahamanir Rahim*
Chapter 49.
Hajiya Nafeesa tuni tabiya kud'i akan a kashe Maryam batare da Fahad yasani ba , Maryam tasha wuya sosai shiyasa ake bata kulawa a Asibitin , ita kuwa Hajiya Nafeesa tuni ta d'auki jaririn da sukayi musanye sunyi gida , Koda Maryam ta farka bataga jaririn data Haifa ba sannan Babu Hajiya Nafeesa , take maganar Hajiya Nafeesa ta fad'o Mata na cewa tana haihuwa zasu kashe ta , da sauri tafara yunk'urin tashi sai dai jitayi jikinta duk ciwo yake Mata takasa motsin kirki ,.
Wani zogi taji a k'asanta Wanda ya tabbatar Mata a wajen haihuwa ta k'aru ,. Nan tashiga neman wayar ta Dan ta Kira Sanam akan ta taimaka Mata , sai dai wayam Babu wayar sai sannan ta tuna tunjiya data Fara cin wuya tayi jifa da wayar , a hankali Maryam ta shiga saukowa daga kan gado tana d'ingisawa , a haka har ta k'araso k'ofar fita wacce tazo bud'e k'yaure tajishi arufe gam , gaban ta ne yafad'i Kar dai ace sun rufeta ne ? Da sauri ta nufi window tana k'ok'arin lek'awa , wasu maza tagani masu zubin arnan daji a tsaye jikin window suna Mata muzurai , da sauri tasaki labule tafara zubar da hawayen ta , tabbas Bata da mafita anan dan basai anfad'a Mata ba tasan wannan Shirin nasu Hajiya Nafeesa ne , jingina tayi da jikin gado tafara kuka tana addu'ar Allah yakawo Mata mafita,.....
Huneed tuni ya iso Abuja cikin shigarsa ta babban Captain , Koda ya k'arasa gida wanka yayi sannan yaci abinci ya fito , Kiran Sanam yayi a waya ya sheda Mata isowar sa sannan yace tafad'a Masa Asibitin da Hajiya Nafeesa take zuwa , Nan Sanam ta gaya Masa yakashe waya ya nufi Asibitin ,...
Tuni gidan Hajiya Nafeesa ya cika da 'yan uwa da Abokan arzik'i , kowa Yana zuwa yi Mata barka da murnar samun haihuwa , Jariri kwata kwata tak'i badashi Wai bayason jagwal gwalo , Yana kan gadon sa na jarirai sai dai a lak'a aga fuskar sa kowa sai fad'in " tubarkallah yaro Yana da kyau , ....
Me jego sai washe baki take tana farin ciki tamkar itace ta haihun , Madara ake bashi saboda itadai ba ruwan nono gareta ba bare tabashi , kuma Koda aka fad'a Mata magungunan da zata Sha Dan tasamu ruwan Nono k'i tayi , bataji aranta zata iya shayar da d'an da ba nata ba bare kuma d'an shege , Kullum cikin bashi Madara take tana fad'awa mutane ruwan nonon har yanzu baizoba......
Acan asibiti kuwa Wannan Matar da su Hajiya Nafeesa suka musanya d'an Maryam da nata itace ta farko , tunda ta farko ta had'a ido da jaririn da ke kusa da ita tasan ba jinin ta bane wannan , da sauri ta mik'e zaune tana k'walawa likita Kira , da sauri Nurse dake kula da ita ta shigo tana tambayar ta lafiya ? Kallon Nurse d'in tayi sannan tace " Ina Babban likita yake ? Nurse tace " Yana office kina buk'atar wani abune ? Tuni ta sakko daga kan gadon ta ta fito daga d'akin , Nurse sai binta take tana fad'in " kiyi a hankali baki Gama jin sauk'i ba fa , Likita Yana cikin office d'insa Yana Zaune Yana waya ta banko k'ofar da k'arfin gaske , da sauri ya kalli k'ofar Dan ganin Wanda ya shigo haka , batayi wata wata ba ta shak'o wuyansa tana fad'in " Ina kukai min yarona ? Wallahi wancan bak'in d'an bashi na Haifa , ko ku fitomin da d'ana konayi k'arar ku , take kuma tashiga kuka tana fad'in " wallahi bazan yadda ba d'ana ko d'umin jikina baiji ba ace arrabani dashi , likitan jikinsa tuni yashiga rawa Yana fad'in " waye ya d'auke miki d'an naki muje aduba cikin Asibitin sai aga ku nawa kuka haihu yau , Fitowa sukayi kuma a dai dai lokacin mijin Matar da 'yan uwan ta sukazo , dama mijin nata da yakawo ta Asibitin sai ya manta wayar sa a gida shine ya koma Dan ya d'auko ya Kira 'yan uwan ta ,...
Suna iso ta tare su da maganar musanya Mata d'an ta da akayi , da sauri suka nufi d'akin da take ciki aikuwa suna tozali da wannan d'a kowanne sai yayi baya Yana salati , tabbas wannan ba d'an Bahijja bane , wannan ce haihuwar ta ta uku kuma duk yaranta kamar su d'aya da Babansu , kuma