Showing 30001 words to 33000 words out of 87659 words
Chapter 11 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf
yara ba…
Safna tana ganin ya fita ta juya tana kallon Mama Talatu da Laraba. Ta k’unduma wani zagi kamar ba za
su yi sa’a da uwarta ba. “Ni kuke son ku kashewa aure ko? Wallahil azeem k’arshen zamanku a gidan nan
ya zo…” Haka ta dinga zaginsu tana ci musu mutunci ba su ce mata komai ba. Sai dai zuciyarsu fal take da
murnar tonuwar asirinta yau. Don kam Safna muguwa ce ta bugawa a jarida ba irin azabar da bata bawa
yaran Allah ne ka’dai ya yi da kwanansu a gaba. Sau tari daga su har yaran ba sa sake cin wani abinci
bayan wanda Zata basu da rana sai kuma garin Allah ya waye. Haka suna ji suna gani za su yi ta jin
k’amshin abu amma haramiyarsu. Ko idan Babansu ya kawo abu zai sa ta d’iba ta bi su k’aramin parlorn
da suke zama a tsakar gida da daddare ta shiga da kayan da’din ta ajiye ta ce kuma duk wanda ya ci sai ya
ha’du da fushinta. Wani lokacin Amani ce duk hanata da zasu yi sai ta ci tun bata iya k’unk’uni har ta fara
sakarwa Mommyn k’unk’uni kuma duk abinda zata mata ba zata yi kuka ba, sai dai ta yi ta cizon leb’enta
tana huci kamar yarda ta ga Dahdansu yana yi. Har tsarki da ruwan borkono ta tab’a yiwa Amani ranar ba
su yi barciba kuma duk kukan yarinyar ta hanasu su gayawa Ubanta… kai muguntar Safna garesu ba zata
k’irgu ba.. idan suka yi nufin gayawa Hajja sai su ji kamar an k’ulle musu baki sun kasa…
Suna kallonta ta shiga d’aki ta saka Hijab ta fito rik’e da jaka. Bata ko kallesu ba ta fice daga gidan. Suma
ba su damu ba don sun san ta saba fita idan baya nan don haka ba wani sabon abu bane a wajensu suka
saki ajiyar zuciya a fili suka fara tsine mata da son Allah ya tona mata asiri komai daren da’dewa….
★✍️
Yana fita ya biya super market ya siya musu kayayyakin da’di da yawa sannan ya sauke su a makarantar
da suke zuwa. Irin private school d’innan ce mai sauk’in ku’di.. Suna sauka a machine d’in Amani da bata
shiru da bakinta ta kalleshi “Dahda kullum zaka dinga bamu k’wai da shayi mai madara… ka siyo mana
kayan da’di mu je da su makaranta?y’an ajinmu duka da kayan da’di suke zuwa, ba da tuwo da kwaki ba.”
Imaam sai da ya yi da gaske sannan ya amsa mata saboda yarda wata k’walla ta fara zubo masa “Zan
muku duk abinda kuke so Ama…” ya fa’da yana sumbatar gefen kumatunsu. Ya rungume su sannan suka
shiga aji. Yau zuciyarsu fal nisha’di ba rashin walwalar nan da suke zuwa da shi makaranta. Imaam ya bi
bayansu da kallo yana share k’wallar da take zuba a idonsa, ya furta “Allah ka yafe min…” cikin raunin
murya don sai ya tattara laifin gaba d’aya ya d’ora a kansa yana ganin koma me ya faru laifinsa ne da baya
bincika halin da yaran suke ciki musamman sanin da ya yi basu da mahaifiya. Kai tsaye zuciyarsa ta ba shi
shawarar ya mayar da yaran nasa gidan Hajja hankalinsa zai fi kwanciya.
ℯ★✍️HADARIN GABAS……
ℯℯ ℯ★✍️
08033748387.
★★★★★ 1️⃣3️⃣
_*BRIGHT PENS...*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huɗu a sabuwar tafiyar ta second batch.
*HADARIN GABAS*
Nazeefah Sabo Nashe
*ƘARFE A WUTA*
Ayushercool
*ZAYTOON*
Zee kumurya
*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.
Yawaitar kiran da Muhammad Alwan Yake masa ne, ya saka shi bai k’arasa gidan Hajja ba sai kawai ya tafi
direct wajen Muhd d’in, bayan ya yi waya office ya bada uzirin gaibu. Don bai ji a ransa zai iya barin aikin
sa ba. Madadin ya fito Muhd d’in cewa ya yi ya shiga d’aki ya same shi. Bai masa musu ba ya shiga in da
ya ce masa.
Tsaf d’akin sai zabga azababben k’amshi yake. Muhd ya nuna masa wajen zama “Please sit mana Imaam,
me yasa kake yin kamar bak’o.” Murmushi Imam ya saki karo na farko tun bayan ha’duwarsu ya zauna a
kujerar. Alwan ya cigaba da shiryawa cikin ha’daddiyar suit d’insa ya yi combing kansa mai kama da
gashin larabawa. Sai da ya gama ya kalli Juice d’in da ya ajiye masa da snacks ya mayar da kallonsa kan
Imaam d’in da alamar tambaya ya furta “Me yasa baka ci komai ba? Ko baka yarda da ni ba ne?” Girgiza
kai Imaam ya yi kafin ya tsiyayi lemon mai sanyin gaske ya kai bakinsa. Idanunsa akan Alwan da yake
sakin murmushi. “Nagode da ka sha, da baka sha ba akwai matsala….” Ya furta yana saka glass d’insa da
ya kasance bak’i wuluk. “Matsala kuma?” Alwan ba wani damuwa a fuskarsa ya d’aga kai yana furta
“Babba ma kuwa…” ya d’an ja fasali sai kuma
Ya furta “Ka san mu larabawa bama son mu yiwa mutum kyauta ya k’i amsa, sai mu ji ba da’di a
zuciyarmu.” Ya sake fa’da yana d’an sakin murmushi. dafa shi ya yi ya furta “Rashin shan da zaka yi zai
saka na ji a zuciyata baka amince da ni ba.” Sai sannan Imam ya saki ajiyar zuciya, amma sai ya samu
kansa da jin wani irin nauyi a kansa take ya d’an lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya bai kawo komai a
ransa ba sai tunanin ko don yana cikin b’acin ran Safna ne.
“Ka tashi mu je.” Ya furta yana dafa kafa’darsa Imaam ya mik’e a hankali ya bi bayansa.
Motarsa ya ce su shiga ya ajiye machine d’in nasa. Hakan kuwa aka yi. Direct cikin abinda bai fi mintuna
ba Imaam ya gan su a cikin Government House. Da mamaki yake kallon Alwan d’in. D’aga masa kai kawai
ya yi ya furta “Mu je, zan ga Governor na kai masa sak’o.” Jikin Imaam a sanyaye ya fito ya bi bayansa
yana mamakin wai yau shine zai ga Governor lallai ha’duwarsa da Alwan alheri ne.
A babban parlorn gwamnati aka saukesu inda gwamna yake gaisawa da manyan bak’insa. Mamaki bai
gama cika zuciyar Imaam ba, sai da Gwamna ya shigo madadin yaga Alwan ya mik’e ya kai gaisuwa sai
yaga ma Gwamnan ne yake daraja Alwan d’in. “Barka da sauka Doctor Alwan…” Murmushi Alwan ya
sakar masa yana firta “Nice to meet you excellency…” Gwamna ya d’aga kai yana sake sakin murmushi
sai kuma ya kai dubansa kan Imaam yana masa kallon rashin sani ko kafin ya yi magana Alwan ya yi
gyaran murya ya furta “A best friend of mine…” Gwamna ya saki murmushi yana mik’awa Imaam hannu.
Imaam ya d’an ji wani banbarakwai sai kuma ya dake ya mik’a masa nasa hannun shima.
Zai Mik’e ya fita ganin kamar tattaunawar tasu ta sirri ce Alwan ya saka baki ya kira shi. “Just sit, ba sai ka
fita ba.” Ya koma ya zauna. Yana kallon wani kallo da Gwamna ya masa sai kuma ya d’auke kai ya cigaba
da kallon Alwan da yake mik’o masa papers. “Zaka yi signing anan kamar yarda na fa’da maka, mun kuma
amince da buk’atarka ta ka sanya hannun jari a companyn da zamu bu’de anan, mun yarda zamu bu’de
babban companyn don cigaban arewa…” Murmushi da ya bayyana tsananin murnarsa gwamna ya saki
yana furta “Alhamdulillah… Nagode sosai ka mik’a min godiyata wajen Boss…” murmushi Alwan ya saki
yana furta “No problem Excellency..” ya mik’e yana mik’a masa hannu suka gaisa da tafawa sannan ya fice
a hanzarce bayan ya kalli Imaam da duk yabi ya zama kamr wani gunki a wajen. Murmushi ya saki ka’dan.
Ya dafa shi yana furta “Shall we?” Imaam ya d’Aga kai ya mik’e shima ya bi bayansa da d’an hanzari.
A mota kasa shiru Imaam ya yi sai da ya kalli Alwan ya furta “Dama ka tab’a zuwa Nigeria?” Murmushi
kawai Alwan ya sakar masa kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya furta “Rabin
rayuwa ta na yi ne a Nigeria Abuja, shi yasa zaka ji na iya Hausa sosai, amma all my family suna Turkey, ni
na zauna anan ne saboda issue na business…” Imaam ya girgiza kai. “Ka san Turkish companies da suke
cikin k’asar nan?” Imaam ya yi saurin d’aga kai “Shi kuwa ya san Turkish group of companies duk wanda
yake K’asar nan Ai ba zai ce bai san wa’dannan companies d’in da k’asar nan take alfahari da su ba.
Kamfaninnika ne da suke sarrafa kayan masarufi iri iri na abubuwan amfani da furniture’s masu kyau da
tsadar gaske, a kwanan nan suke shirin bu’de companyn ha’da motoci. “Na familyn mu ne…” Ya ji muryar
Alwan a sama “Ni nake monitoring na Nigeria.” Da sauri Imaam ya juya yana kallonsa idan kuwa har ta
tabbata da gaske ne tabbas Alwan ba shi da girman kai kuma ya tsinci dami a kala. “Kana son ka yi
business da mu?” Imaam ya d’aga kai da sauri don ba zai bar kansa ya k’ulle ba. Murmushi Alwan ya saki
a zuciyarsa ya furta “Nice, hakan ya yi…” a fili kuwa cewa ya yi “Akwai shara’di… idan ka amince sai nace
maka ka godewa Allah ka kusa shiga sahun billionaires na Arewa…” Imaam ya ha’diye yawu yana d’aga
kai “Sharad’in me?” Sai da Alwan ya juyo kamar ba driving yake ba sai kuma ya juya yana cigaba da tuk’in
ya furta “I will tell you, but not now.”
A wurin siyar da motoci ya yi parking yana kallon Imaam ya furta “Mu je ka min rakiya, Allah yasa ka iya
mota ka ja min ita.” Imaam ya d’aga kai yana furta “Na iya..” ya jijjiga kai yana murmushi suka isa wajen
wata Honda accord mai masifar kyau bak’a wuluk. Ya yi ciniki ya biya ku’din ya mik’awa Imaam key d’in.
Imaam yana kallonsa ya furta na menene? “Na taimako na da ka yi, kuma kada ka ce min ba zaka amsa
ba ka san hukuncin hakan islamically..” Imaam ya saki ajiyar zuciya ya kuma kasa yi masa musu yana kallo
ya fita ya bar shi a wajen yana furta “Zan kiraka anjima zan je Abuja but zan dawo morning.” Ya lakace
hancin Imaam ya fita daga wajen yana murmushi ko bakomai burinsa ya cika. Imaam kasa motsa wa ya yi
daga wajen ya dinga kallon Motar da aka ce tasa ce ya lumshe ido yana mamakin Alwan da dukkan
alherensa daga ha’duwa jiya kawai? Ko da yake a arziki irin na danginsu ya san wannan bakomai ba ne.
Don haka sai ya ji ya samu nutsuwar zuciya ya shiga motar cikin matuk’ar farin ciki ya ja zuwa gidan Hajja
don ita ya kamata ya fara sanarwa….
★★✍️
Safna kuwa tun bayan fitar ta gida hankalinta tashe bata tsaya ko ina ba sai a gaban Malaminta. Yanayinta
da ya gani ya tabbatar masa ba lafiya ba. Ya san Safna ba tun yau ba ta amince da cewa shi ke samar
Mata da duk wani farin ciki.
Sun gaisa hankalinta a tashe ta sanar da shi dalilin zuwanta. Idanu ya zuba mata bayan duk ya gama jin
abinda ta ce ya furta “Akwai matsala Safna, dole ki tashi tsaye akan Mijinki don idan baki wasa ba kina ji
kina gani zai fi k’arfinki…” Tashin hankali ya bayyana k’arara akan fuskarta idan da abinda ta tsana a
sanar mata da Imaam zai rabu da ita. Ta yarda da aikin Malamin nan tun farkon ha’duwarsu da Imaam shi
ya mallake mata zuciyarsa da tunaninsa. “Akwai alheri ma da yake matso shi nan kusa, sai dai idan ba ki yi
da gaske ba zai ture Alherin akan wani dalili…” Ta waro ido “Malam hakane wallahi, don jiya ya ha’du da
wani mutum mai ku’di sai dai da dukkan alamu baya son tarayyarsu da mutumin Malam ina son ka kulle
bakinsa ya zama duk abinda mutumin ya umarceshi kawai ya aikata ba musu, ni in dai Imaam zai yi ku’di
kawai koma ta wani hali ne ya yi, ko na huta da gorin dangina na auri wanda ba shi da ku’di…” Malam ya
saki murmushi “An gama Safna, arziki kam Mijinki zai yi shi, amma a k’arshe fa naga wani duhu…..” “In
dai a k’arshe ne Malam duk daga baya ne, kawai a min aikin da zai yi abinda suke so ko baya so. Sannan
ka rufe min bakinsa tsaf kada ya dinga gayawa kowa sirrinsa sai ni ka’dai don kada ya je ya gayawa Hajja
ta hana shi ta cucemu.” Ta fa’da ba tare da ta bari bokan ya gaya mata duhun me ya gani ba.Malam ya
jijjiga kai ya cigaba da dube duben k’asarsa ya d’ago yana kallonta ya furta “Zaki iya birne bunsuru da
rai?” “Ba abinda ba zan iya ba Malam kai kanka shaida ne don na yi wanda ya fi wannan in dai akan
Moddibo ne….” Tabbas kin yi Safna ni kaina ina jinjinawa jarumtarki da rashin tsoro, don ma dai mijin
naki tsohuwar sa a tsaye take a kansa da wallahi sai yarda kika yi da shi tsabar Mallaka… amma yanzu
ma ki sha kuruminki za mu yi masa aikin da ba zai gaya musu komai ba daga cigaban da ya sameshi
gudun kada su hana ruwa gudu….” Ta saki ajiyar zuciya ta fara kallon Malam tana godiya. Ya ha’da mata
duk abinda ya dace saura kuma ya ce ta dawo kashegari. “Yanzu Malam idan na aikata haka d’in, ba zai
min maganar abinda ya faru da safe ba?” “Ko zancen ba zai d’aga ba, ki je kuma zaki bani labari.” Bata ji
ko d’ar a ranta ba don ta yarda da Aikin Malamin. Ta zura takalminta jikinta na rawa ta fice direct gida ta
koma hankalinta kwance ta fara aiwatar da surkullenta da k’ulle k’ullenta… Tana yi tana sakin murmushi
a ranta tana k’addara cin zalin yaran da bata son ganinsu ko ka’dan yanzu ta fara….
Har k’ofar gidan Hajjan ya je da motar, sai dai yana fitowa ya samu k’aton kwa’do a k’ofar gidan. Rik’e
kansa ya yi kawai don bai ji da’din rashin ganin Hajjan ba. Don haka ya sake komawa motar ya nufi
gidansa duk da yaso zuwa gidan Fateema sai ya ji zuciyarsa ta kasa aminta gida kawai yake so ya je ya
nunawa Safna.
Gidan fes ta saka su Mama Talatu sun share sai k’amshin turaren wuta yake. Ita Kuma ta fece wanka da
wani Ubansu Riga da wando ta yi kyau sosai don kam k’irjinta a cike yake sosai har yana rinjayarta daga
k’asa ne dai bata da shape ko ka’dan. Jikinta gaba d’aya ta balbaleshi da turarukan sihirin Malam. Ta d’au
Layar ta saka a k’asan harshenta idonta akwai sihirtaccen kwalli.
Tunda ya yi sallama ya ji kansa ya sara da k’arfin gaske. Matsalar Moddibo kenan rashin addu’a ya kama
kan yana zama a saman kujera kafin ya yi aune Safna ta shiga jikinsa ta yi amfani da wannan damar wajen
ribartasa ya kusanceta a take a wajen cikin fitar hayyaci saboda turarenn da yake jikinta ya sabbaba masa
son kusantarta a k’asanta kuwa dama ta shafa rubutun da Malam ya bata. Tuni Moddi ya manta da duk
abinda ya faru. So da k’aunar Safna sai sake ruruwa suke a ransa. Ya kama hannunta yana janta waje. “Zo
mu je kiga kyautar da aka ba ni?”
Cikin farin ciki ta dinga zagaye motar tana jifansa da wani kalar murmushi ta furta “Alwan d’in ne ya
baka?” Ya ‘d’aga mata kai yana murmushi. Cikin son sanin ko aikinta ya kama shi ta furta “To kada na ji
kada na gani bana son ka gayawa kowa cigaban da zai sameka……” Imaam Ya d’aga mata kai, fuskarsa na
bayyana da gaske ya bi umarninta. Ta d’an saki murmushi tana lakace masa hanci ta furta duniya sabuwa!
Daga ranar an d’au tsawon sati biyu Alwan bai neme shi ba. Bai kawo komai a ransa ba don shi sam bai
saka son duniya a gabansa kamar yarda Safna ta saka ba. Itace dai shiga d’ari fita d’ari idan zai yi, she will
keep asking Alwan D’in Ya kira ka?” Idan ya girgiza mata kai. Sai ta yi kamar zata yi kuka ta furta “Kai
kuma ba sai ka nemeshi ba, ni wallahi Ban tab’a ganin Wanda arziki ke bi ba sai kai, ko da yake ba abin
mamaki ba ne dama kun yi gadon talauci duk Wanda Ya Saba da arziki ai ba zai guje shi ba…” Ranar da ta
fara fa’da masa haka zuba mata ido ya yi ransa a b’ace yana fitar da hucin numfashi Amma kuma ya kasa
d’aukan mataki. A kashegari kamar wasa sai ga kiran Muhammad Alwan nan wajen sha biyun dare… Da
wani irin sauri Safna ta finciki wayar ta saka ta a handsfree tana masa nuni da Ya amsa… murya a hankali
suka gaisa da Muhammad Alwan d’in. Sai daga can Alwan D’in Ya ce “Friend, sai ka ji ni shiru kuma?
Amma baka nemeni ba, haka ake abota?” Da sauri Safna ta ce “Eeeh wallahi, yana ta son kiranka to ba ya
so ya damekane kana aiki, amma kana ransa wallahi…” ta furta tana hararar Imaam da ya yi shiru kawai
ya kasa furta komai. Alwan daga can ya d’an yi murmushi kawai kafin ya furta “Haba Aboki, ai an zama
d’aya you can call me at what ever time you want… yanzu forget wannan, abinda yasa na kiraka I want to
meet with you at Abuja that’s why na maka booking flight na 7:30 am zaka same ni gobe a can.” Moddi
ya d’an waro ido. Safna ta zabga masa