Showing 84001 words to 87000 words out of 87659 words

Chapter 29 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf

Advertisement

mu
bamu da wani sauran business da kai… yarinya kuma tana hannun mu.” Moddibo ya waro ido yana sake
kallon message ‘din mai hakan yake nufi? Alwan ya yaudare shi kenan? Har Abuja ya je Amma an sanar
masa Alwan baya nan. Bai dawo daga wancan firgicin ba wani message ‘din ya shigo masa…. “Amani
bata Nigeria Imam, kada ka yi wahalar nemanta zamu dawo da ita da zarar mun samu abinda muke so,
Nima kuma ba zaka sake samu na ba…..” da k’arfi Moddi ya ce “Don’t Alwan, Don’t ba haka muka yi da
kai ba…” ya fa’da a zafafe kamar Alwan ‘din yana gabansa. Ya tura masa message amma bai tafi ba, da
alama da gaske Alwan ya daina aiki da layin. Me kenan ya aikata me ya shiga Kansa da ya aikata komai ba
shaidu? Me zai ce da Didi wani bayani zai yi musu? Dole ne ya yi shiru kawai da bakinsa… ya dinga cijen
leb’ensa yana Jin kwanyar Kansa kamar ta tarwatse… ba kowa ya jawo masa wannan matsalar ba sai
Safna… ta ina zai fara? Kiran numberr Alwan yake amma still wayar bata shiga. Ya kifa kansa kawai a
saman sitiyarin motar yana sakin huci a hankali. A haka ne yake pretending kamar bakomai, kamar ba ya
Jin komai a zuciyarsa Amma shi ya San abinda yake zuciyar tasa… kamar an tsikare shi, ya sake fincikar
motar da mugun speed. Allah ne ya kiyaye, Allah ne kuma ya kai shi gida lafiya… ko motar bai rufe ba ya
fito ya nufi cikin gidan…. A bedroom ‘dinta ya dinga jiyo hirarsu da dariyarsu basu San da zuwansa ba shi
yasa suka cigaba da hirar cikin ‘daga murya. Boss lady ta ce “Kice dai gida ya zama naki, kai Safna kin iya
tsiya, ya aka yi wai aikin ya ci har haka?” Ba za ki gane ba Na’ima, bafa k’aramar tsanar yarinyar nan na yi
ba, duk wani aiki da na yi a kanta baya tafiya min successfully. Ba k’aramin asarar ku’di take saka ni ba,
yarinya sai ka ce aljanna. Alwan shine tsani na na cikar buri na, da abinda ya bani na yi amfani, na saka
mata a furar da na san tana sha duk dare, na san Didi bata Shan sugar don haka mazubin da ake zuba
mata daban ne, a cikin na Didin na saka maganin barci, shi kuma Imaam a kettle ‘din shayinsa da yake sha

duk dare kamar ibada anan na zuba maganin da na karb’o wajen bokan, Wanda ya tabbatar min in dai
suka sha a tare sai sun kusanci juna, koda ba’a cikin hayyacinsu ba ne, na kirkirarwa kaina ciwon k’arya
don kawai na cika buri na… sai gashi komai successfully, ai ina ta jira ki dawo daga South Africa ki sha
labari. Zancen da nake miki suna can har tsohuwar zube a asibiti sakamakon bayyanuwar ciki a jikin
yarinyar, cikin da na tabbatar koda tsiya koda tsiya tsiya sai na zubar da shi….” Da sauri Dada ya ja baya,
yana k’ok’arin controlling zuciyarsa… Ashe Safna ce da wannan mugun aikin, yaransa suke zargin shi ya
saka musu magani suka kusanci juna. Ya dinga jin jiri a Kansa fisgar leb’ensa kawai yake, yana k’ok’arin
danne b’acin ransa, bai kamata ya nunawa Safna ya ji komai ba, zai yi maganinta a lokacin da bata
tsammani ba, shi yanzu burinsa ganin inda Amani take. Don haka ya shige part ‘d’insa hankalinsa a tashe,
duk wani layin Alwan da na Boss ‘d’insa ba Wanda bai kira ba sun k’i shiga…



★★

A karo na biyu ta sake Jin motsi a bakin k’ofar d’akin… da sauri ta gyara zamanta don wannan karan kam
ta shirya fita daga gidan koda hakan yana nufin sai ta sumar da mai kawo mata abincin ne. A lissafin ta
kwananta biyu a gidan ko wanka bata yi ba, ba kuma ta damu ta yi ba duk da nacin matar da take kula da
ita. Ta d’auki k’ullin yajin data b’oye a hannunta ta tsaya da shirin ko ta kwana. Ana bu’de k’ofar ta nufi
kan Wanda ya bu’de k’ofar da niyyar ba’da masa yajin sai dai da sauri ta ja baya tana Ware ido ha’de da
nuna Wanda yake tsaye a bakin k’ofar murya a sark’afe ta furta “You?”



JIKAR NASHE✍HADARIN GABAS…….




34.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️


08033748387.


BRIGHT PENS SECOND BATCH.



Lumshe ido Alwan ya yi yana d’aga mata Kai ya furta “Yes Me…” Sai ta zauna jikinta na rawa ta furta
“Uncle kai ka kawo ni nan?” Ya ‘d’aga mata kai yana cigaba da fa’din “To save your life from danger ba.”
Sai ya zauna idanunsa a kanta yana kewayeta da wani irin kallo da ta kasa fassara shi. “Akwai dalili babba
na kawo ki nan, dole zan nesantaki da jama’a gudun idon mutane a kanki, zaki haihu anan ba tare da
kowa ya san abinda ya faru ba, Boss zata karb’i Babyn ta rik’e ke kuma sai a samar miki admission ki tafi
karatu bayan kin je kin yi sallama da su Didi. Abu guda da zan gaya Miki ki aikata duk abinda aka umarceki
bana son musu, idan ba haka ba komai zai iya faruwa, bana son tsiwa bana son rashin kunya kin ji ko?”
Da k’yar ta tattaro nutsuwa ta saka a fuskarta tana Jin yawun bakinta na son d’aukewa. Ta furta “Ni dai
Uncle ka mayar da ni, na San Didi da Imaan suna can hankalinsu a tashe…” “Da kuma Dada ba.” Ya furta
yana kallon cikin k’wayar idonsa with a smile kwance a fuskarsa. Ta turo bakinta tana Jin wani b’acin rai a
zuciyarta bata son zancen Dada da duk abinda ya dangance shi. “Ni Ban ce maka Dada ba..” ya sake
fad’ada dariyarsa murya a k’asa y’a furta “But Why? Dada kuma ya damu dake fiye da zaton ki, banda ma
damuwar da yayi da ke ‘din da tuni wani zancen ake ba wannan ba…. Tun jiya yake kirana don ma na yi
blocking line d’insa, amma me Dadan ya Miki ba kya son zancensa?” Ta lumshe idonta tana Jin zuciyarta
na sake nauyi da k’yar take fusgar numfashinta ta furta “I hate him…” sai ta danne lips D’in kalar yarda
Dadan yake yi.
Alwan ya tuntsire da dariya yana furta “Like daughter like father, so duk kin ‘debe wannan halin cije
leb’en nasa…” Ta sake turo Baki tana furta “Ni bana Kama da shi…” “Ni ban ce kina Kama da shi ba…”
ya fa’da yana kwaikwayon muryarta with happiness in his voice. Sai ya kalli kwanonin abincin ya ‘d’ago
kuma yana kallonta “Me yasa ba kya son cin abinci? Idan kina son fa kina son kullum na dinga zuwa,

sai kin dinga yarda ana miki duk abinda ake so, ki dinga musu biyayya idan ba haka ba….” Sai ya girgiza
kansa. Da sauri Amani ta ce “Idan ba haka ba me?” Ya ja hancinta yana furta “Idan ba haka Boss zata yi
fushi, kuma fushinta means a lot.. don haka ki kiyaye, bana son wani Abu ya samu Babyn Dada, nafi son
yarda muka d’auko ki mu mayar da ke, ba tare da ko kwarzane ya same ki ba, Boss Babyn jikinki take so
kawai sai a sallame ki, kin ga ba Wanda zai San kin haihu ko?” Ta wani irin waro ido, tana kallonsa ta furta
“Me zata yi da shi?” Ya bu’de hannunsa ya wara su alamar he don’t know. Sai ta turo bakinta tana furta
“You meant zan yi five months anan kenan?” Ya ‘daga mata Kai yana furta “Sure, after kin haifi Babyn za’a
mayar da ke wajen Dadan ki…” Sai ta saki kuka da k’arfin gaske. Alwan ya yi saurin kallonta yana furta
“Oh sorry, Ban sani ba Nima ban sani ba, idan kika yi musu biyayya zasu bari ki tafi, kin San ina nan ko?
Zan dinga zuwa kuma, ba zan bari a cutar da ke ba…” ta ji wani relief a ranta. Ta San Alwan kam yana son
su, Don idan suka yi tafiya da shi ba abinda ba ya siyar musu, yana kula da su sosai. “Anan ka ke?” Ya
d’aga mata kai “Aiki nake ma Boss…” “Wai wacece Boss ‘din nan?” Alwan ya yi dariya yana furta Zaki
ganta as soon ta dawo daga tafiyar da ta yi… kina so ki ganta ne?” Amani ta ‘daga Kai tana amsar plate
‘din da ya cika mata da abinci. Sai ta samu kanta da cin abincin sosai ko don yana ta janta da hira ne. At
last ta saka hannu zata ‘debi abincin sai taji wayam. Ta yi saurin kallon plate ‘din tana waro ido. Shima
Alwan waro idon ya yi ya ce “Duka kika cinye?” Kunya ta kamata ta yi saurin sunkuyar da kai. Alwan ya yi
dariya yana janyo leda ya tura mata a gabanta. Chocolates ne da Ice cream masu mugun tsada. Farin ciki
ya bayyana a fuskarta sosai don ta yi missing ‘dinsu. Da sauri ta ja robar Icecream ‘din mai flavor ‘din
chocolate ta fara sha. Tana furta “Thank you Uncle…” Alwan ya saki ajiyar zuciya yana mayar da fuskarsa
serious face ya furta “Kina so na cigaba da zuwa?” Ta d’aga Kai. “To ki dinga yin duk abinda aka saki, kin
ji? Bana son musu kuma ko me aka baki ki ci, a yanzu dai ba zasu cutar da ke ba, don ba su d’auko ki don
haka ba, but idan kika musu taurin Kai zasu iya cutar da ke.” Hawaye ne yazo idonta ta yi saurin Kama
hannunsa tana girgiza kai. Don’t live here Uncle, ka zauna please…” ya duba watch d’in hannunsa yana
girgiza kai “I have a meeting, but bari na kunna Miki kallo akwai Korean movies da Indian movies ki kalla
zasu dinga d’auke miki kewa…” ta bi babbar Wall Tv ‘din da kallo ita ta manta ma da wani zancen kallo
saboda tashin hankalin da take ciki. Sai ta ji wani relief ganin Uncle Alwan yasa ta ji ta samu nutsuwa
sosai, a yarda ta ‘d’auke shi kuma a inda yake mu’amalantar su sai taga kamar ba zai cutar da ita ba. Ya
kunna mata kallon sannan ya fita bayan ya ce mata ta yi wanka. Bata yi musu ba kuwa yana fita ta mik’e
ta shiga wankan, don ita da kanta ta san tana buk’atar wankan a yanayin yarda take Jin jikinta. Wanka ta
yi sosai a ha’dadden toilet ‘din. Kuma ta samu Skin routine masu kyau sosai. Ta wanke gashin kanta. A
mirror ta tsaya tana kallon cikinta da ya fara tasawa ka’dan. Sai ta dinga Jin tausayin cikin tana mamakin
dalilin da yasa Alwan ya ce cikin kawai suke so, amma ta San ya yi haka ne don ya taimaketa, don da
kansa ya furta shi yasa aka ‘d’auko ta don baya son a San ta haihu. Hankalinta ya kwanta ta ji bata da
wata damuwa tabbas hakan shine rufin asirinta…..

Duk inda tashin hankali yake to Familyn Lami’do suna cikinsa. Ba inda basu duba Amani ba sai dai ba ita
ba labarinta. Didi kam ciwo ya sake rikicewa, ga Umma D data saka su a gaba da tijara iri iri, tana furta
“Ashe citata aka so a yi, shi yasa aka dinga cusawa ‘dana ita, to yanzu kam Asiri ya tonu, ai na San za’a kai
ga haka, wannan dukiya ta Moddi ai abin a binciki hanyar da ya samu ne, ga abinda sangarcin da kuka
masa ya janyo, sannan ake tunanin na rufa masa asiri bayan Allah ya tona masa….” Didi ta dinga kallonta
tana tuno sanda ta haifeta da kanta a cikin d’aki, bada haka da sai ta ce canja mata Dijatu aka yi. Hawaye
take fitarwa cikin karyayyen harshenta ta furta “Dijatu, kika furta labarin nan ga kowa Allah ya isa ban
yafe Miki ba, d’anki dai Amani ba zata aure shi ba, ba shikkenan ba…” “Bas kuwa.” Fateemah ta furta
zuciyatta cike da jin haushin y’ar uwarta. Dijatu ta watsa mata wani kallo ta furta “Eh Mahmud ba zai
aureta ba, ke ki aura mata wani cikin y’ay’anki, kinibabbiya kawai.” Fateemah ta sauke wani murmushi
tana furta “In dai ni na haifi yara na kuwa kuma na isa da su zaki sha mamaki…” fa’da fa ya kaure a
tsakanin su. Moddi yana ji ya lumshe idonsa kawai ya yi shiru. Sai yamutsa sumar kansa yake zuciyarsa na
fitar da wani irin hucin turiri. Idan har ya ce zai bu’de bakinsa ya yi magana abinda zai fa’da ba zai zama
mai sauk’i ba, zai kuma iya yiwa Dijatu mugun duka idan ya bu’de idonsa ya ganta. Shi yasa ya rufe idon
ruf. Shi duk ba wannan ne a gabansa ba ina Amani ta shiga shine tambayar da yake wa kansa. Ina Alwan
ya kai ta. Furucin Didi shi ya togace Dijatu daga yama’di’di da zancen, sai dai an ce zancen duniya baya
b’uya don labari sai ya fara baza gari da ka’dan ka’dan.



★★★★


Ita ka’dai take juyi a saman gadon. Bayan shigar Dada toilet ya kuma gaya mata ta shirya zasu Paris.
“Duniya sabuwa!” Ta furta cikin wata irin murya mai nuna zallar farin cikin da take ciki. Komai yazo mata
a sauk’i burinta ya cika. Amani ta bi duniya. Dama yarinyar ce take togace ta da komai. Don ba k’aramin
shakkar yarinyar take ba. “Y’ar banza mai kafaffar zuciya, yau kema kin bi Uwarki…” ta furta tana sakin
dariya. Imaam kuma shi da aure har abada. Sai ta sake jin wani relief a zuciyarta. Fitowar Moddi ce yasa
ta ta yi shiru ta dawo cikin hankalinta ta dinga binsa da kallo tana son furta abinda ke k’asan ranta, ta
wani gefen tana shakkarsa. Mik’ewa ta yi ta isa wajensa tana karb’ar lotion ‘din da yake shafawa cikin
yaudara ta dinga Shafa masa. Murya a k’asa ta furta “Amma idan mun je, this time zaka

Amince naga Doctor Akan maganar rashin haihuwar nan…” D’auke kansa ya yi kafin ya furta “No
need…” da sauri ta kalleshi cikin harzik’a ta furta “Wai me yasa Moddi? Me yasa duk sanda na maka
magana akan matsalar rashin haihuwarta sai ka ce wani No need? So kake sai na wuce haihuwar? Ya
‘d’ago ya kalli cikin idanunta. Sai Ya saki murmushi yana furta “Ba zaki tab’a haihuwa ba…” Da sauri ta
saki lotion ‘din a k’asa jikinta na rawa ta furta “Saboda me?” Ya lumshe idonsa yana fusgar lips ‘d’insa ya
furta “Saboda na bada mahaifarki Safna, na bayar da mahaifarki a lokacin da kika umarce ni komai su
Alwan suke so na amince ciki har da ran Uwata, y’an uwana, da yara na, sai abin yazo min da sauk’i don
basu nemi komai ba sai mahaifarki ni kuma take na basu, saboda kince ana yin komai saboda ku’di…..”
Ya fa’da yana ‘dage mata gira guda. Wani irin tashin hankali ta shiga, tashin hankalin da har ganinta ya
‘d’auke na wuncin gadi, ga wani irin zufa da take zubarwa zuciyarta sai fisga take. Bata San sanda ta
cakumo Moddi ba tana furta “Muguntar da ka min kenan?” Ya ‘dan waro ido yana furta “Na miki ko kika
ma kanki? Ku’di kike so kuma kin samu, ina da ku’din da har ki Mutu ba zaki gama cin su ba. Kwanciyar
hankali dai kika saka muka rasa…. Don’t blame, blame yourself…” ya fisge rigarsa ya fice ya bar mata
masifaffen k’amshin turarensa “6;00 pm… jirginmu zai tashi.” Ya furta yana rufo d’akin da k’arfin gaske.
Buguwar k’ofar ya yi daidai da sake buguwar zuciyarta da k’arfin gaske bata San sanda ta dafe zuciyar ba
tana sakin kuka. Me take shirin ji? Abinda Moddi ya yi mata kenan, tana ta sak’ar yarda zata samu
haihuwa sai yazo mata da wannan banzan zancen, har tunani ta fara yi ko cikin k’arya zata k’irk’ira ta siyo
jariri a asibiti, Ashe shi ya Riga ya siyar da mahaifarta ba zata tab’a ganin gudan jininta ba har abada!





★★★


Amani ta samu nutsuwa sosai ta daina fargabar komai, don ba taga alamar cutarwa daga ahalin gidan ba.
Ta sake wani irin kyau saboda komai aka kawo mata tana ci tana gyara jikinta da kayan gyaran jiki da suke
zube a toilet ‘din. Fatarta ta sake fresh kuma Alwan kullum yana tafe wajen ta yana kula da ita sosai. Kyau
fa kam iya kyau ta yi sha ga na ciki ga na zama waje ‘daya. Akwai abubuwa da yawa da idan suka bata
kawai sha take ba tare da ta tambayesu na menene ba. Kyau kuma ta sake yinsa sosai. Boss ce dai bata
tab’a ganinta ba don an sanar da ita bata gari tana Paris. Yau ma tana zaune Sadiya mai kula da ita ta
shigo. Waya a kunnenta tana sakin dariya k’asa-k’asa ta furta “Ma’am ga ajiyarki, tana nan lafiya sai ma
kyau da ta k’ara…” ta sakawa Amani wayar a kunnenta. Sannan ta juya ta fita daga d’akin. Amani ta yi
shiru bata ce komai ba a cikin wayar kamar yarda Boss itama ta yi shirun… sai can Amanin ta ji ta saki
ajiyar zuciya tana furta “Ama… tana kan line?” Aman ta ‘d’an cije bakinta tana jin Voice ‘din matar ya cika

kunnenta muryar y’an gayu sosai. “Kina ji na?” A hankali Amani ta furta “Yes Ma’am.” Matar ta saki dariya
tana furta “Ke ma Ma’am ‘din zaki kira ni? Whatever dai ki shirya gobe za’a kawo ki waje na. Zamu ga juna
gobe, hope Baby na ya lafiya?” Amani ta saka hannu ta Shafa cikinta, sai dai bata ce komai ba. “Ki shirya
Sosai Sadiya zata baki kaya masu kyau ki saka, don gobe zaki San dalilin da yasa nake bibiyar cikin ki, zaki
ha’du da mutane ki yi shiga mai kyau, bana son Gardama…” Amani haka kawai ta ji gabanta ya fa’di kafin
ta yi wani furuci an katse kiran. Tabi wayar da kallo tana kallon rututun Numbers ‘D’in da aka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login