Showing 3001 words to 6000 words out of 87659 words

Chapter 2 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf


abin bai dameta ba. Yes bai dameta ba ko ka’dan asalima wani murna take da farin ciki burinta ya cika
ranar da ta da’de tana jira ce tazo ranar da zata shafawa Amani black paint da mutane zasu tsaneta a
yanzu kam ta San Amani ba zata tab’a auruwa ba. Su Didin da suke matuk’ar sonta zasu tsaneta
musamman idan suka ji ita ta kai kanta d’akin Moddin. Akwai abubuwa da suka faru da yawa Wanda ba
zai bada k’ofar zarginta ba a matsayinta na kishiyar Uwarsu, tana da evidence da idan ta nuna sai zuciyar
kowa ta yi shock. Kallonsa kawai take idanunsa a lumshe tana hango yarda zuciyarsa take d’agawa da
sauri. “Ka tashi mu tafi, ba mu da lokacin b’atawa ka San yarinyar can da kafiya, kada tazo ta aikata
abinda za mu yi regretting.” Ya mik’e jikinsa a sanyaye yana d’iban phones d’insa. Bai canja daga jallabiyar
da take jikinsa ba, ko hula Babu a kansa hakan ya bawa sumarsa mai kyan gaske damar fitowa sai shek’i
take. Suka fita securities da body guards na ganinsu suka yi saurin mik’ewa zuwa inda suke. Da sauri
Moddi ya dakatar da su duk da Sun so turjewa amma ya sanar da su ba inda zai fita da su. Ya shiga
zafaffiyar motar sa shi da Safna suka fice daga gidan. Still wani irin zafi yake ji a zuciyarsa kamar ma ciwo
zuciyar take masa tun sanda abin ya faru har yau bai huta ba, ba zai kuma ce ga lokaci guda da ya yi barci
nutsatstse ba, ba ya iya barci yana jin takaicin kansa da kallon da yarinyarsa take masa. Kallo ne mai
bayyana tsanarsa sosai a ranta. Ta raina shi bata ganin girmansa. Yes ya cancanta ta aikata fiye da haka
shi da kansa ya san He deserves more than that…. Sam zuciyarsa ba nutsuwa yake driving d’in. Ya san
dai yau dole asirinsa zai tonu. Yau Didi zata tsaneshi don yau Adda Tee zata bayyana abinda ta sani itama,
Wanda ta sha garga’din sa Amma Safna ta rusa komai ta saka shi aikata abinda yake nadamar zamowarsa
d’an Adam ba dabba ba. Yana jin a yanzu ba ya buk’atar ku’din, mulkin da komai ma yafi buk’atar
mutuncinsa, yana son ya koma
Malaminsa na Jami’a ko ma’aikacin company kamar yarda yake a baya. Amma ta yaya? Duk wancan
labarin ya shu’de yanzu wani shafin labari zai bu’de Wanda ya tabbatar ba zai rubutu a wajensa ba. Bak’in
ciki da takaici ne zasu kashe shi. Amani ba zata tab’a rufa masa asiri ba…. A cikin irin wannan tunanin
yake driving d’in. Ya saba fitar sirri da wannan motar shi yasa ba Wanda ya kawo shi ne.

IMAAN

★★



Jikinta a sanyaye ta yi parking tata motar. Tana bin motar Amani da take parking space na asibitin da
kallo. Haka kawai sai ta samu kanta da tashin hankali ta ji bugun zuciyarta yana k’ruwa. Kife kanta ta yi a
saman steering motar idanunta a lumshe sam bata son ta ji ta shiga irin wannan yanayin, don a duk
sanda ta ji ta a arin wannan yanayin kamar alerting d’inta ake something bad is going to happen….
Addu’a ta yi sosai a ranta kafin ta bu’de motat jikinta a sanyaye ta fito. Tana tafiya bugun zuciyarta na
sake k’ruwa. A sanyaye ta yiwa receptionist d’in magana. Receptionist d’in ta d’ago tana kallonta kafin ta
furta “She is Inside.” Ta fa’da tana nuna mata consultation room d’in da Amanin ke ciki. Duk Wanda yake
asibitin ya san su, ya kuma san matsayin su asibitin Mahaifinsu ne Moddibo kuma bayan da ya ci mulki
bai fasa zuwa asibitin ba. Asibiti ne da aka yi shi kamar kana k’asar waje idan kana cikinsa. Imaan ta wuce
jikinta sai rawa yake k’afafunta ma kamar ba zasu iya k’arasawa da ita d’akin ba…. Tana mur’da handle
d’in zata shiga a lokacin ne ta ji Amani ta yi wata irin k’ara tana furta “I won’t abort it… ina son ciki na…”
wannan karan ji da ganin Iman sai da ya d’auke na wuncin gadi. Ta dafa bango tana Jin wani irin bugu da
zuciyarta take tun ma bata ji waye ya yiwa y’ar uwarta ciki ba, ta shuga wannan tashin hankalin ina ga ta
ji? Ina ga ta ji mahaifin da ya kawota duniya ne? Blindly ta tura k’ofar ba tare da ita kanta ta San ta tura
d’in ba. Idanunta a zube cikin na Amani da take kwance a sume. Hannunta na rawa ta isa wajenta da
sauri tana kallon Doctor d’in ta ce “Hope she isn’t…. I hope she is Okay?…” Doctorn ya d’aga kai
hankalinsa tashi ganin yarda hawaye yake screaming a idanun Imaan d’in. Rungume Amani ta yi a jikinta
tana furta “Save her life Doctor pls! Ita ka’dai nake da a duniyar nan, mahaifiyarmu tunda ta haife mu ta
mutu. Ba zan iya cigaba da rayuwa ba idan babu twin sister d’ina.” Ta fa’da cikin tashin hankali tana kai
bakinta kan na Amani kyakykyawar sumbata ta bata sai kuma ta sake sakin kuka. Hawayen ne ya dawo da
Amani duniyar da Iman take ciki. Amani met Iman and she knew her twin sensed her turmoil. Bata da
Wanda yafi Imaan a duniya they shared a silent, understanding a connection that transcended words. Ta
kama hannun Imaan d’in ta rungume a jikinta kafin ta saki kuka da k’arfin gaske. Iman ta rungumeta tana
hura mata iska a kunne. Tun yarintar su haka take rarrashin Amanin idan tana rigima, tun bayan Didi
kakarsu ta tabbatar mata ita aka fara Haifa kafin Amanin sai ya zama na ta d’au girman dole ta sakawa
kanta, kamar wadda ta bawa Amanin shekaru ba mintuna ba. Ita kuma Amanin kasancewarta
shagwagwgwab’iya mai son jiki sai ta mayar da Iman wata elder sister d’in ta. Bata da inda take kai
damuwarta sai wajen Iman ita ce uwarta ita ce Yayatta K’awarta and komai ma. Amani ta janye idonta
daga na Imaan da ta hango damuwa b’aro-b’aro a cikinsu. A yanzu kam ba zata gayawa Iman ba bata son
ta saka zuciyarta ta buga, amma dole ta sanar da ita tana da ciki. Ta San dai zata yi breaking heart d’inta
ba mamaki ma Iman daga ranar ta tsaneta ta tsani a kirata twin sister d’inta. Ba mamaki daga ranar ba
zata sake mata kallon tausayi ba don ta sha warning d’inta Akan abinda ba ita ta d’orawa kanta ba.

Lunshe idanunta ta yi her heart racing kamar yarda ta Iman ma take yi. Murya a raunane Iman ta ce
“Amani cikin waye a jikin ki? Am afraid ina tsoron tabbatuwar zargi na, Amani don’t tell me….” Sai ta cije
bakinta tana kallon Doctorn ba zata so ta yi magana a gabansa don haka hawaye ya cigaba da saukar
mata tana Jin zafin saukar su har cikin zuciyarta…. Lura da kamar suna son magana da junansu yasa
Hisham fita daga d’akin. Hakan yasa Iman ta saki ajiyar zuciya ta juya tana kallon Amanin with curious
Eyes ta furta “Don’t tell me kina d’auke da cikin Dada? Amani talk to me bana son zargina ya tabbata…”
Iman emphatetic geze encouraged Amani to Open Up” runtse idonta Amanin ta yi kafin ta ja deep breath
and revealed her secret, hawaye yana screaming down her face. Da d’aci take furucin tana Jin zafin
bayyana wa Imani gaskiya Amma ya zama dole ta gaya mata bata da wata bayan ita.

Iman fita hankalinta ta yi, sanda Amani ta fara sharing secret d’inta da ita. Imam’s expression mirror her
emotions- shock, sadness and determination… a hankali cikin whispering voice d’inta sosai ta ce “We’ll
face This together Ama.” Ta fa’da idanunta suna wani kalar juyewa. Zafin da zuciyarta take ciki ya bayyana
a saman idanunta. “Dole time ya yi da zamu gayawa duniya irin rayuwar da muka taso a cikinta. Time Yayi
da Mahaifiyar Dada zata San wa ta haifa. Time ya yi da za mu bayyana tozarcin da aka Miki duka a silar
rashin Uwa. Maraici ne ya jawo mana Amani….” Iman ta fa’da tana rushewa da kuka ta rungume.
Amanin suna sakin kukan tare gefe guda kuma wayarta take dannanwa Didi take kira tazo asibitin ita da
kanta zata gaya mata Moddinta shi ya yiwa Amani y’ar da ya haifa da Kansa ciki saboda Neman duniya.
Ba zata kira Umma T ba don ita take hanata tonawa Moddibo asiri.


DIDI
____


Wayarta da take ringing a gefenta ta zubawa ido. Kafin ta saka hannu ta d’auka idonta Akan hoton Emojin
da ta sakawa Imani. Da haka take banbance su tunda ita ba wani boko ta yi ba. A raunane ta d’aga kiran
don haka kawai yau take samun kanta da fa’duwar gaba. Iman daga can b’angaren ta furta “Didi, kizo
asibiti Magajiyarki ba lafiya Likita yana buk’atar ganin ki.” Didi muryarta na rawa ta zabga salati hankalinta
tashe ta ce “Me ya sameta?” Iman ta ce “Ki zo dai kawai idan kin zo zaki gani. Muna Moddibo special
hospital.” Didi ta sauke wayar da sauri ta mik’e mayafin ta ta sake Gyarawa kawai ta fice waje tana
k’walawa D’an LAMI driver kira. Sam bata da nutsuwa don a duniya bayan Moddi ba Wanda take so take
ji a ranta fiye da y’ay’anta kamar y’an biyun da Moddibo ya haifa mata.

Iman ta dafa kan Amani tana karanta mata addu’oi tana tofa mata. Wani irin zafi take ji a ranta Wanda ko
cikin a jikinta yake iya zafi da tafasar zuciyar da zata ji kenan. Amani ji ta yi ta samu relief ganin Imaan
bata juya mata baya ba. Duk da ta San dama ba lallai ta juya mata d’in ba. She grew up together, sharing
secrets and laughter. Ka fa’dar Iman da Didi nan ne wajen kukanta wajen sangartar ta. She recalled how
Iman Supported her a komai da zata zo mata da shi ko da ita bata so… idanunsu a lumshe suke kowa da
abinda yake sak’awa a ransa. Suka bu’de idon a tare Jin lokacin da aka turo k’ofar. Mommy Safna ce ta
fara shigowa sai ga k’amshin Dada yabi ya cika hancinsu. K’amshin da Amani ba abinda ta fi son ji sama
da shi a da. A yanzu ya riki’de ya zama k’amshi mafi Muni da bata so. Gaba d’ayansu suka zubawa juna
ido. Iman da Amani kallonsu suke zuciyarsu cike da tsanarsu. Dadan ya d’an ja fuska ya tsuke yana kallon
Iman gabansa na fa’duwa ganin irin kallon da take jifansa da shi. Sai dai ya maze yana furta “Ba kwa amsa
sallama ne? How is she feeling?” Iman ta zuba masa wani kallo kafin ta ha’diye wani Abu da ya tsaya
mata a rai ta furta “Ta Yaya zata samu sauk’i alhali tana d’auke da cikin mahaifinta a mararta, me kake so
ta yi feeling bayan bak’in ciki da ciwon zuciya. Ciki fa Dada kai ka yiwa Amani ciki saboda son mulki da
ku’di Dada ka tozarta mu?” Yif suka ji an zube a k’asa da sauri idanunsu suka koma kan Didi da take zube
ba alamar numfashi a tare da ita…..





JIKAR NASHE★✍️HADARIN GABAS…..



‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/HBqR4GFrqIMH7TjAy8IYgj

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️


08033748387.

3️⃣



(My dear fans, I've received many messages asking if I've stopped posting updates about Hadarin Gabas.
I'm sorry to say that I won't be posting this weekend. We haven't even reached the midpoint of the story
yet, and I'm already feeling anxious about how it will unfold. Just be patient, all will be revealed soon.
Stay tuned, fans! This is just the beginning of the story.)



Da sauri Amani ta ware idonta, Iman ma a firgicen take. Dada kuwa bai wani jira komai ba ya isa gaban
mahaifiyarsa Didi da take yashe a k’asa jikinta sai rawa yake cikin matuk’ar tashin hankali Ya d’Agata yana
kallon yarda jikinta ke kakkarwa “Iman Go and call the Doctor she is unconscious…” Iman ta janye Amani
daga jikinta ta fita da sauri. Safna kuwa wani farin ciki ne ya shiga zuciyarta a take ta fara addu’ar Allah
yasa Didin ta mutu ta huta. Dama sosai matar ta tsaya mata a Rai ta hanata rawar gaban hantsi… Don
haka a ranta ta dinga furta “Margaya Didi, Allah ka amshi ran baiwarka.” A zahiri kuwa sai ta isa wajen
Didin da sauri itama tana furta “Imaam tofa mata addu’a, Allah yasa ba ajalinta ba ne yazo.” Wani irin
kallo Imaam Ya jefa mata yana sake jin wata muguwar tsanarta a ransa. Ji yake kamar ya mata saki Uku,
sai dai Ya san bai isa ba he is not authorizedto do that..” Ya rungume Didin a jikinsa hankalinsa a tashe
yana furta “Ya Allah, kada ka saka Didi ta mutu ta sanadiyyar bak’in cikin da na k’unsa mata, ba zan iya
rayuwa ba babu ita ba, Ya rabbi ka bata lafiya…” Ya fa’da manyan idanunsa masu hasken gaske tuni suka
riki’de suka koma wasu kalar Brown kamar yarda suke zama a duk sanda yake cikin b’acin rai. Leb’ensa
kawai yake fisga da k’arfin gaske bai damu ba koda zasu fashe. Zafin da yake ji na zuciyarsa yafi masa
kowane irin ciwo da zai ji ra’da’di.


Amani dai tana zaune her heart filled with pain and sorrow. Tana ta addu’a Allah kada ya amshi ran Didi,
don Didi ita ce kwanciyar hankalinsu sai Umma T.

A da kama tana son Dada kamar ta Mutu ganin yarda yake nuna musu kulawa sai dai tun bayan abinda ya
faru take jin wata muguwar tsanarsa. She feels intense anger.

Shigowar Doctor ne yasa ta tsagaita daga kukan da take. Tana sauraran bayanin Doctorn da yake bawa
Nurses Umarnin su kawo masa wasu allurai. Yana kallon Moddibo Ya ce “Kada ka damu, she will survived
In sha Allah, firgita ta yi normally kuma mutum yana shiga irin wannan yanayin a lokacin da Ya shiga
firgita ko damuwa ko razana, so that ba wani abu ne she will be there zuwa nan da two days muga
abinda Allah zai yi.” Imam ya lumshe ido a hankali yarda leb’ensa ne kawai Ya d’aga ya ce “Allahu Ya
sha…” Shi kansa sai ya ji kunyar saka Allah a Lamarinsa. Anya Allah zai amsa addu’arsa bayan wannan abin kunyar da Ya aikata. Ya sake runtse idonsa
yana jin yarda zuciyarsa ke wani irin bugu. He wished ya mutu kawai a lokacin Ya daina kallon Amani yana
jin kunyarta. Didi da idanunta ke zubar da hawaye ta saka hannunta da yake rawa ta yafito Imaan. Da
sauri Imaan ta isa wajenta a hankali ta kara kunnenta a kusa da bakin Didi. Didin cikin rawar murya ta
furta “Ki…..ra….min…Tee…” Sai kuma bakin ya datse. Imaan tsaf ta gane nufinta don haka da sauri ta
d’au wayarta zata kira Umma T D’in, da sauri Imaam Ya kalleta cikin dakiyar murya ya furta “Give me your
phone Imaan…” Irin Tsawar da Ya daka ne yasa Imaan bata san sanda ta mik’a masa wayar ba hannunta
na rawa. Amani ta saki wani malalacin murmushi a ranta take sak’a Lallai Ma Dada, ya aikata abin sannan
Ya ce ba ya son a gayawa y’an uwansa, ai ba y’an uwansa ba ma duk duniya sai an ji in dai tana raye, sai ta
tona masa asiri mutane sun masa tofin Allah Ya tsine. Don haka ta ji ta samu wani irin courage da sauri ta
saka hannu ta d’au wayarta tana hararar Dada da gefen ido. Direct kiran Umma T ta yi. Basu farga ba sai
ji suka yi ta rusa kuka ta furta “Umma T. Pls Ki zo Didi ba lafiya” ta fa’di jin abinda ta ce yasa Da wani irin
hanzari Ya fisge wayar da take hannunta, yana kallonta cike da mamakin abinda ta aikata. Itama kallonsa
take kamar yarda bai rusunar da k’wayar idonsa ba itama k’in rusunar da tata ta yi ta kafe shi da Wild
eyes d’inta da take jin kamar suna fitar da turirin hayak’i tsabar kallon tsanar da take masa. “Have you
come to your senses? Lets settle this peacefully. Tara mana jama’a kike son yi?” Ta runtse ido tana furta
“Yes ba ni da hankali, bani da hankali ka cuce ni ka saka min hauka kuma ba zan tab’a yafe maka ba, sai
na saka jama’a Sun maka tofin Allah Ya tsine, I hate you Dada, I am fed up with seeing your face.”

“Ke, Amani ki lura da Wanda yake Miki magana mana, mahaifinki ne fa.” Safna ta furta fuskarta na wani
irin blushing sam farin cikinta ya kasa b’uya. Amani da Imani suka mata wani irin kallo kafin Amani ta
dartse leb’enta tana jin kamar ta shak’e Mommyn. Tsabar takaici ma kasa furta mata ko kalmar ‘a’ ta yi.
Dada ya koma saman kujera ya zube hannunsa cikin tarin sumar gashin kansa ta asalin fulani. Yamutsa
gashin yake kamar zai cire shi. Duk duniyar ta masa wani irin duhu. Tsawon lokacin ba wanda ya iya furta
komai sai Amani da take ta kuka tana jin kamar zata rasa ranta….


UMMA T…

Tunda Amanin ta kirata ta ji wani irin mummunan fa’duwar gaba ta sameta. Salati ne kawai a bakinta, sai
Kalmar Innalillahi da take furtawa a hankali. Ji take kamar Amani ta ce mata Didin ta Mutu. Haulat da
take gefe ta dafa ta tana furta “Ammi calm down, bafa mutuwa Didin ta yi ba, mu je asibitin mu gani
kada ki tashi hankalinki…” Fatima ta zubawa y’ar tata ido tana fatan abinda Haulat D’in ta fa’da Ya zama
haka ne. Allah yasa Didi ba yanzu zata Mutu ba. Suna son Didi suna son kuma rayuwa da ita fiye da
komai. Hijab Haulat ta zura mata sannan ta mik’e hannunta cikin na Haulat D’in suka fice daga gidan.
Haulat ce take jan motar don duk sun san asibitin tun bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login