Showing 33001 words to 36000 words out of 87659 words

Chapter 12 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf

harara tana furta “Zai zo In sha Allah, ba abinda zai hana shi zuwa.
Mun gode k’warai.” Muhammad Alwan Ya yi cutting kiran, yana mamakin hali irin na matar abokinsa da
alama ko wata matsala ce ta taso nan gaba, ba zasu yi wahalar siye matar can ba. Ya saki murmushi
kawai. Yana gyara zamansa idonsa akan Boss d’insa data zuba masa ido. Hannunta d’auke da wani glass
cup mai shegen kyau tana kurb’ar ruwan tattaccen inibì. Kayan jikinta masu masifar kyau. Ita kanta
dattijuwar mai kyau ce jikinta duk ta sha adon gold wuya da hannu Har da sark’ar k’afa. Kanta ba
d’ankwali hakan ya bawa gashinta irin na larabawa damar zuba Har gadon bayanta. Muryarta very low
kamar wacce bata son yin magana ta furta. “Aikinka yana kyau Bro… ya amince zai zo goben?” Alwan ya
d’aga kai yana furta “Sure zai zo Hala. Kuma aikin ba zai mana wahala ba, don wannan matar tasa
masoyiyar ku’di ce.” Matar da Ya kira da Hala ta d’an saki murmushi tana lumshe idonta ta sake kai cup
D’in bakinta, ta yi sipping kamar bata so sai kuma ta furta “Make sure ka yi yarda na ce, bana son kuskure
you know a komai nawa bana son shirme, ku’di ba matsalata ba ce ka jik’a su da Naira matuk’ar zan samu
cikar burina…” Alwan Ya jinjina kai. Yana furta “Ba wani kuskure fa In sha Allah Hala.” “Good for you.” Ta
furta tana mik’ewa cike da tafiyar rangaji ta shige d’aki. Alwan Ya bi bayanta kafin ya mik’e shima Ya fice
tabbas gaba da gabanta ji yarda yake Boss a waje, amma anan Macece take da mulkin take kuma bashi
umarni yarda take so. Ya saki murmushi kawai ya fita don cigaba da shirin tarar Moddi da zai zo a goben.




★★

Asubar fari Safna ta tashe shi, da mamaki ya dinga kallonta don baya tunanin ta yi barcin arziki. Matar da
da sai ya yi da gske take tashi ta yi sallah k’arfe bakwai amma yau itace ta tashi da wuri haka. Ya zuba
mata ido da sauri ta ja hannunsa tana furta “Ka tashi mana Imaam, ka wani zuba min ido sai lokaci ya
k’ure? Kai komai sai ka saka shiririta.” Ta zabga tsaki tana shigewa Toilet tana jansa kamar wani yaro. A
toilet da k’yar yake wankan haka kawai sai ya dinga jin gaba d’aya ba ya jin da’din zuciyarsa ga wani irin
fa’duwar gaba da bai San ko ta Mecece ba. Haka dai ya yi wankan ya fito. Kafin nan har Safna ta fito masa

da kaya sabuwar shaddarsa ta Sallah, abinda da bata tab’a yi ba. A hanzarce ta saka shi Ya shirya ranar
har cikin bedroom ta kawo masa breakfast. Ya ‘dan kurb’i ka’dan ya ajiye yana yamutsa fuska ya ce
“Safna, bafa son tafiyar nan nake ba, gaskiya a hak’ura kawai…” “Ai kuwa tafiya kamar ka je ka gama…”
Ta fa’da idonta a cikin nasa tana danne Layar bakinta. Ba shiri ya zura hularsa kamar Wanda ake
kunnnawa da remote Har ya kai k’ofa ya jiyo yana kallonta Ya ce “Su Ama fa? Wa zai kai su School yau?” A
zafafe Safna ta ce “Kutma….” Sai kuma ta shanye zagin ta furta “Zan kai su Malam, don Allah ka fita ka
tafi kada jirgin Ya cika.” Murmushi kawai ya yi yana furta “Ta Yaya jirgi zai cika bayan kowa da wajen
zamansa, ga ma Boarding pass an turo min.” Hannunsa ta fincika suka fita waje. Sai da ta kai shi har
Airport sannan ta juyo da motar bata wani koma gida ba ta isa wajen Malaminta ta sanar da shi. A d’inke
bakin Moddi duk abinda suka ce suna buk’ata ya amsa kawai. Malamin kuwa ya d’auko allon k’arfensa ya
shiga rubutu yana k’onawa da wuta mai zafi. Ya d’ago yana kallonta yana murmushi ya ce “An gama!”
Itama murmushin ta saki ta fice daga wajen zuciyarta fes tana ji a ranta kamar Moddi ya yi arziki ya gama.





★★

Babban Hotel aka masa masauki. Ya dinga bin ko ina da kallo a zuciyarsa yana furta arziki yana wajen
masu shi. Tabbas su Alwan suna da arziki fiye da tunaninsa.Sai da suka ci abinci sannan Alwan ya ce “Ka
san me yasa na kiraka?” Imaam ya girgiza kai. Alwan ya saki murmushi yana furta “Kafin mu yarda da kai
sai ka amince zaka shigo cikinmu akan shara’din duk abinda muka saka ka za ka yi shi?” Imam ya d’an
bu’de ido yana so ya ce “Kamar me?” sai dai bakinsa ya k’i bashi ha’din kai kawai sai ya samu kansa da
furucin “Na amince.” “Good For you.” alwan ya fa’da yana murmushi “Abu na farko da zamu buk’ata daga
wajenka shine mahaifar matarka, Ma’ana ba zaku haihu da matarka ba.” Imaam ya ‘dago yana kallonsa
Ya ji kansa ya wani sarà masa, amma sam ya kasa masa musu… Alwan yana murmushi ya ce “Ka kirata ku
yi shawara…” Ya fice ya bar masa wajen. Da sauri Imaam Ya kira Safna. Tana d’agawa ta ce “Yaya? Imaam
Allah yasa dai baka musu taurin kai ba?” Ya saki huci ka’dan ya furta “Ba zan iya abinda suke so ba….”
“Zaka iya Imaam, ka yi koma me suke so? Yanzu fa ba abinda baa yi saboda ku’di, ana ya Kai Kai, mutum
yana kwanciyar da y’ar cikinsa, da Uwar data haifeshi ma saboda ku’di, ana luwa’di da ma’digo saboda
ku’di, ana bada Uwa ko y’a Yaya ko k’anwa, K’ani ko wa? Duk saboda ku’di, don haka ka yi ko me suke so
Moddi Saboda ku’di… bana son musu…” ta fa’da tana zame kanta a duk sunayen da ta ambata, bata k’i
ya yi komai ba in dai zai samar musu da ku’di, bata damu ta ji shara’din da suka bashi ba. Imaam Ya saki
ajiyar zuciya, sai ya ji ya samu k’warin gwiwar bayar da mahaifarta tunda ita ta jawowa kanta ta ce ya yi
komai saboda ku’di. A zuciyarsa Ya dinga jin baya so, amma harshensa ya kasa amince masa ya furta baya

so d’in. Ya kalli Alwan da Ya shigo d’akin idanunsa a kansa shima ya ce “Yaya Aboki? Ka yarda ko a’a? Abu
guda dana sani baka isa ka San sirrinmu sannan ka bijire mana ba…..




JIKAR NASHE.HADARIN GABAS…..

Page…14.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️


08033748387.

(Book 1 free. Book 2&3 paid ne)


Ku saka ku’dinku anan account d’in don samun Shiga paid group. 500 (0000612945 TITAN TRUST
BANK) mutanena Na Musamman cikin Gida Na Musamman 1k Dai Kacal as Usual. Jikar NASHE LOVES
YOU ALL.)

_*BRIGHT PENS...*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huɗu a sabuwar tafiyar ta second batch.

*HADARIN GABAS*

Nazeefah Sabo Nashe

*ƘARFE A WUTA*
Ayushercool

*ZAYTOON*
Zee kumurya

*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.



14.


“Na amince…” Shine abinda ya ce yana jin kansa yana wani irin sarawa. Alwan ya d’ago yana murmushi
kafin ya zare glass d’in fuskarsa ya furta “Ka kyautawa kan ka, wannan ya zama sirri a tsakanin mu, Zan
baka maganin da zaka mata amfani da shi a lemo komai zai tafi yarda muke fata successfully. Sannan
Daga haka zaka samu duk abinda kake buk’ata zamu ajiye ka a companyn da zaka dinga samun ku’di ba
k’akkautawa kafin wata buk’atar ta bijiro… Congratulations Mr. Imaam Moddibo and welcome to the
Family…” sakin ajiyar zuciya ya yi yana furzar da huci ka’dan gani yake kamar ya yi gaggawar amincewa
da buk’atar da suka zo maka da shi. Idanunsa a lumshe Alwan ya mik’a masa ruwa mai sanyi. D’an bu’de
lumsassun idanun nasa ya yi yana kallon Alwan d’in da yake kallonsa fuskarsa cike da murmushi ya d’aga
masa kai “Sha…” Bai yi musu ba ya karb’a ya saka a bakinsa ya shanye tas. Sai ya ji kamar an tafi da
tsoron da yake zuciyarsa wata nutsuwa ta shige shi. Alwan ya mik’a masa wani dogon file me d’auke da
takardu a ciki “Ka yi signing. Ka kuma cike form d’in company.” Hannunsa har rawa yake ya aikata abinda
aka ce masa.

A ranar Alwan ya kai shi masauki sannan ya saka aka kawo masa abinci mai rai da motsi bai bar hotel ‘din
ba sai da Imaam ya ji alert d’in 50million a account d’insa. Yana ware ido yake kallonsa da neman k’arin
bayani. “Na siyan kayan sawa, waya da duk abinda kake buk’ata. Ai kana da y’ay’a ko?” D’aga kai kawai
Imam ya yi don ba shi da karsashin amsawa. “To ka musu hidima ka ajiye musu duk abin buk’ata zamu yi
wata tafiya da kai zamu yi 2weeks don zan nuna maka yanayin business d’in da zaka dinga mana. Zan
sake jaddada maka bama son surutu, ka gane ko?” Imaam ya d’aga kansa yana kallon Alwan ‘din ya fice
da sauri saboda kiran wayarsa da ake ta yi.

Sai sannan Imaam ya saki ajiyar zuciya yana rik’e kansa da ya ji yana sara masa ka’dan. A ransa yake
jinjina girman wautar sa na amsar tayin kasuwancin da bai san menene ba? Ga bayar da mahaifar
matarsa da ya yi. Anya bai yi kuskure ba duk da wata zuciyar na tunasar da shi Ku’di Imam! Ku’di zaka yi
yaranka zasu huta Hajja su Huta da Yayyenka… matarka Kuma ai ita ta janyo koma me ya faru… wayarsa
da take k’ara ce ta dawo da shi cikin hankalinsa idanu ya kai kan wayar ganin numberr wife sai da ya ji
gabansa ya fa’di da ya tuna abinda ya aikata mata.. bari dai ya gaya mata idan ta yarda shikkenan idan
kuma bata yarda ba kawai sai ya hak’ura…

Yana saka wayar a kunnensa ta furta “Hope dai kun gama kuma ka amince da dukkan shara’dansu?” Shiru
ya yi yana jan ajiyar numfashi “Moddi baka ji na ne?” Ya furzar da iska ya furta “Ina jin ki.. sun zo min da
abinda nake tunanin ba mai yiwuwa ba ne….” “Ba wani abu da ba mai yiwuwa bane Moddi a duniyar
nan Moddi ka amince da komai suka ce maka. Duk duniyar haka ta riki’de ta koma yanzu kowa ka gan shi
ka k’yaleshi kawai da guntun kashinsa a gindinsa…don haka in dai ni zan baka shawara kawai ka aikata
abinda suke so yanzu ake yankan kai ma don a samu ku’di….” Imam ya d’an waro ido “Yankan kai fa?”
“Eeh yankan kai kai in gaya maka mai k’ank’at mutum yana sadaukar da Uwarsa ko y’arsa ko y’aruwa don
ya yi ku’di….” ta cire mata don koda wasa ba zata so Moddi ya bada ita a yi tsafi don ya samu ku’di ba,
amma bata k’i ya bada Hajja ko Y’ay’ansa ko Yayyensa ba. Moddi ya ji wani abu ya daki k’irjinsa ya ce
“Haba dai? Allah ya kiyaye.” “Ameen, ai ina gaya maka ne ka amince da duk me za su ce maka, har luwa’di
ake da mutum don ya samu ku’di…” Wannan karan sai da Moddi y runtse idonsa ya ji gabansa yana wani
irin bugawa. Ajiyar zuciya ya yi ya furta “Shikkenan, bari na kwanta.” Ya latse wayar yana sakin murmushi
sai ya ji zuciyarsa ta daina nauyin da take masa ya ji ya amince da sallama mahaifarta tunda ita ta jawowa
kanta. Wato tana tunanin ya bada uwarsa da y’ay’ansa amma bata tunanin ya bada ko farcenta? Ya tab’e
bakinsa kawai yana kurb’ar lemonsa mai sanyin gaske….

Wannan shine mafarin samuwar arzikinsa don daga lokacin da suka yi tafiya ya je yaga yanayin business
d’in, shikkenan Alwan ya sakar masa jan ragamar companynsa na turkey da yake Abuja. Bai fiye zuwa
Kano ba. Ya kuma kasa sanarwa da Didi sana’ar da yake ya dai ce mata companynsu sun koma Abuja an
kuma yi masa k’arfin girma. Fatan alheri ta masa tana furta “Ka dai kula Moddi, ka saka Allah a gabanka
ka kuma kula da amanar da Allah ya baka ta yaranka bana jin da’din yanayin yarda yarannan suke rayuwa
a gidanka..” D’aga kai shi kansa sau tari baya son irin rayuwar da suke sai dai ba yarda zai yi ne, idan ya yi
nufin tsawatarwa sai Safna ta janye hankalinsa. Sau tari Didin na zuwa ta kwana musu biyu don ita da
kanta ta ce su dawo hannunta Umma Dee ce ta hana tana furta “idan suka dawo Didi Ai makirar matarsa
sai ta yi murna ta ci galaba akan mu, gidan Ubansu ne dole su zauna wallahi.” Hakan ne yake togace Didi
daga janye yaran zuwa gidanta. Don kam bata ja da duk abinda Dijatu ta ce.

Ranar da ya gama gininsa da yake ciki a yanxu, kasa gayawa Didin ya yi sai Gidan Umma Tee ya ya sanar
mata ga shi a lokacin ma Safna ta riga ta matsa masa sun tare cikin murna da zakwa’di tana ji dai da
fankamar mijinta ya zama mai ku’di.

Umma Tee kallonsa ta dinga yi tana mamakin abinda ya ce mata. “Ka gama gida Moddi? Har kun tare a
ciki ba tare da Hajja ta je ta gani ta saka albarka ba?” A hankali ya sunyar da kansa yana jin kansa da
jikinsa sun masa wani irin nauyi tabbas ya san bai kyauta ba, amma baya sanin rashin kyautatawar tasa
sai ya aikata abin rashin kyautatawar sannan yake dawowa cikin hankalinsa. “Abin ne yazo bagatatan ki
rufa min asiri don Allah kawai ki je ki gaya mata…” Tsam ta yi da ranta tana nazarin idanunsa “Wai Anya
kuwa Kido baa canjawa Didi kai ba?” Ta fa’da wata k’walla na shirin zubo mata. Idanunta sun ka’da sun yi
jawur. Shima sai ya samu kansa da zubar k’wallar “Ni kai na Tee ban san me ya same ni ba? Wasu irin
abubuwa nake aikatawa da ban san ya aka yi tunani na yake gocewa ba sai na aikata na ji ina da na
sani….” Hawayen ta share ta ce “Shikkenan akwai Allah, yanzu ka tashi mu je gidan Didin ka gaya mata
da kanka ka kuma bara hak’urin rashin sanar da ita da baka yi da wuri ba. Zaka iya cewa gudun kada ta
maka fa’da ne.” Ya d’aga kai yana amincewa da shawarar da ta ba shi. Suka tafi gidan Didin. Tun a mota
ita kanta Fateeman ta dinga mamakin zundumemiyar Motar Moddin mai kyan gaske. “Kiddo sun k’ara
maka matsayi a wajen aikin ne?” Ta furta don ta kasa shiru. D’an murmushi ya yi yana d’aga kai ya furta
“Eeh, sun k’ara min mantawa na yi ban sanar da ku ba…” Ta saki ajiyar zuciya kawai tana furta “Anya
Kido kana dagewa da Azkar kuwa?” Ya d’an saci kallonta a idanunsa ta ga rashin gaskiya don ya kasa
kallonta sai d’an cije leb’en da ya zame masa jiki yake yi. “A kula dai da addini da Azkar ba don komai ba
sai don duniyar yanzu gaba d’ayanta abar tsoro ce.” Ya d’aga kai kawai daidai lokacin suka zo gidan Didin.


A kunyace Ya shiga gidan Didin tana zaune a tsakargida tana gyara zogale. Gidan yana nan yarda yake ba
abinda ya canja masa duk da tarin arzikin da Allah ya ba shi. A Ransa ya ji rashin kyautatawar sa ko ka’dan
ga matar da ta sadaukar da dukkan farin cikinta saboda su. Amma shi ya samu arziki bai damu da ita ba

yana dai ajiye mata abinci da abubuwan da suka danganci kayan masarufi. Ya ja ajiyar zuciya yana zama a
saman kujera ha’de da kai idonsa kan Didin da fuskarta ta kasa b’oye farin cikin da take ciki. Yaushe
Rabon da taga Moddibo idan bata manta ba wata guda da rabi kenan cur sai dai ya kirata a waya shima
sai ya bushi iska. Kullum addu’a take masa amma lamarin k’ara ta’azzara yake. Ba b’acin rai bakomai ta
tare shi. Ya durk’ushe a gabanta yana dafa cinyarta. Shafa gashin kansa ta yi ta furta “Yau Moddin Diddy
ya tuna da ita?” Saukar da idonsa ya yi k’asa hawaye na zuba a idon ya furta “Diddy ki yafe min….” “kada
kace komai Moddi ban rik’eka da komai ba kuma kullum addu’a nake maka Allah ya shige maka gaba a
dukkan lamarinka, ya tsareka da dukkan abin k’i.” Fateema sai da ta saka gefen mayafinta ya share
k’wallar tausayin Diddy da Moddin da aka raba ta k’arfi da yaji. Diddy ta shafa kansa “Rok’ona d’aya
Moddi ka kula da amanar da Allah ya baka ta marayun yaranka.” Ya d’aga kai murya a sark’afe ya furta “In
sha Allah…” wani rauni yake ji a jikinsa tun daga k’afarsa har tsakiyar kwanyarsa don tabbas yaran nasa
ma ba wani kula yake da su sai ya shafi sati biyu ma bai gansu ba. Makaranta dai ya ajiye musu driver
yana kai su ya d’aukosu sai abincinsu da yake bawa Mama Tala da kansa sai dai abin haushin yana tafiya
Safna take k’wacewa ta cigaba da basu duk abinda taga dama.

“Diddy Moddinki fa ya miki laifi.” Fateemah ta fa’da tana k’ok’arin kawar da yanayin da zuciyatta take ciki
akan fuskarta. Ta k’ak’alo fara’ar dole ta aza fuskar. Diddy ta kalleta da son k’arin bayani. Fateemah ta yi
murmushi “Ya tare a sabon gida bai gaya miki ba, don yana gudun fa’da.” Shiru Diddy ta yi duk da lamarin
ya daki zuciyarta sai bata nuna ba ta saki d’an murmushin da yanayinta kawai zaka kalla ka san bai kai
zuciyarta ba. “Allah ya sanya alheri Allah ya saka da dukiyar halak ka samar da shi, shine kawai fata na.”
Imaam wani abu ya ji ya masa yarrr a jikinsa ya lumshe idonsa kawai yana furta “Ameen Diddy.” Hawayen
da ya rasa dalilin zubarsu suna masa suntiri a fuska Diddy ta saka hannu ta share masa kwallar “Kukan na
menene Moddi?” Girgiza kai kawai ya yi yana futta “Didi ya kamata a rushe gidan nan a sabunta gininsa.”
Ta girgiza kai “Sam!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login