Showing 45001 words to 48000 words out of 87659 words

Chapter 16 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf

cikin k’wayar
idanunsa ta hango k’arya yake don haka ta saki murmushi tana furta “Kiddo kada rainin hankalinka ya
biyo ta kaina, ka gaya min gaskiya ina ka kai zuciyar Amani? Don tabbas akwai abinda ake nufi da kimtsa
mata soyayyarka? So kuke ka kusanceta don ka yi ku’di ko? Don na San yanzu abinda zamanin nan ya
gada kenan? Idan kuwa haka ne Imam ka cuci kanka ka kuma cuci zuri’ar mu wallahi don tabo ne da ba
zai tab’a gogewa ba….zaka ce wani su banbance muharran da wanda ba muharram ba, sai kace wanda
basa zuwa Islamiyya.” Ta fa’da tana sakin kuka mai k’arfin gaske… Bai hanata ba kamar yarda bai fasa
kallonta ba, zuciyarsa na sake k’untacewa ga wani irin jaa da idanunsa suka yi…. Jin ba zai iya jurewa ba
kawai sai ya mik’e da sauri da niyyar tafiya. A zafafe ta ce “Kiddo hasashe na gaskiya ne kenan?” Ya d’aga
mata kai yana tura hannunsa cikin tarin sumar kansa ya fice da sauri cikin matsanancin b’acin rai. Umma
Teey zuciyarta da take bugu ta damk’e don ta San Moddi tun yana yaro bai iya k’arya ba idan ya ce haka
ne tabbas hakan ne kuma ba zai canja ba ko za’a tsire shi……
Ta zauna jiguf a saman kujera, zuciyarta bugu take sosai ga yanayin yarda idanunta suka bayyana tsoro
sosai, da gaske tana jin tsoro, tana tsoron afkuwar wani lamari mai girma da sam tunaninsu bai basu su
kawo ba. Duk da ba wata k’ofa da Moddin ya bar musu wacce zasu zargeshi. Amma a yanayin sutturun
yaransa, makarantar da suka yi da komai ma na Moddi da yake zama latest ya kamata su san da walakin
goro a miya. Tana son kiran y’an uwanta gefe guda kuma tana jin tsoro tabbas kafin ta zartar fa hukunci
ya kamata ta zauna da Kiddo ya gaya mata gaskiyar halin da yake ciki. A idanunsu take ganin ya canja ba

Kiddonta ba ne na da, ba Moddin Didi ba ne, wannan wani ne daban da ko yaushe zaka dinga ganin
damuwa a yanayinsa, a cikin idanunsa take hango yana cikin matsalar da ya kasa bu’de baki ya gaya
mata. Abinda da Kiddo baya yi idan zai b’oyewa kowa abinda yake ransa ba ya b’oyewa Adda Tee d’insa,
itace tasa tun suna yara ko laifi ya yi a lokacin da yake tashen rashin jinsa, ita ke saka shi a gaba da yi
masa nasiha ta kuma hana Didi ta doke shi. Abu d’aya ne ta san ta yi iya yinta wajen hana shi amma
Kiddo ya k’i ya nuna mata duk duniya idan bai auri Safna ba akwai matsala. Auren da sam ba zasu tab’a
fa’dar alherinsa ba sai zallar sharrinsa. Wasu irin hawaye ne masu zafi suka dinga zuba a saman kuncinta
tana jin zuciyarta na bugu da masifar sauri. Idanun nata a lumshe ta dinga jin kamar k’amshin turaren
Moddi ne a daf da ita, ko don bai da’de da barin wurin ba, sai dai a jikinta ta ji Moddi ne ya dawo ba
mamaki ya dawo ya fayyace mata abinda ya shige mata duhu don haka ta dinga bu’de idanunta a hankali
Har ta Ware su tsaf a kan Kiddo. Yana tsaye ya yi folding hannunsa yana kallonta cikin wani irin emotion.
Bakinta Har rawa yake wajen furta sunansa “Kiddo, ka dawo? Allah yasa ka dawo ne don ka gaya min
gaskiyar abinda yake faruwa, kada ka kassara min zuciya idan ka bar ni baka gaya min ba wallahi zuciyata
ciwo zata yi, tun yanzu ina jin kamar ta yi failing…” ta fa’da tana isa gabansa cikin wata irin slow tafiya
mai bayyana rauninta. Daf da shi ta tsaya kafin ta kama hannunsa kamar yarda suke lokacin yana yaro. Ta
yi k’ok’arin lalubar k’wayar idanunsa ta jefa tata. Da sauri Moddi ya runtse nasa idon don baya jin zai iya
jure kallon cikin idon Teey sannan ya mata k’arya, tun suna yara da k’wayar idonsu ita da Didi suke
hukunta shi a cikin ruwan sanyi. Matsa yatsunsa ta yi kafin ta saki a hankali ta matsa daga kusa da shi.
Tana furta “Jeka Kiddo, just Go don na San baka shirya fa’da min gaskiya ba, duk abinda zaka fa’da yanzu
na San k’arya kake.” Ya saka hannayensa a goshi yana murza goshin nasa kafin ya ware idonsa da suka yi
jajur ya isa gabanta ya durk’usa zuciyar tata da take bugu Har hakan ya bayyana a saman rigarta ya bi da
kallo. Cikin wata irin murya kamar ba ta Moddi ba ya ce “It’s enough teey, please!” Ya fa’da yana matsa
yatsunta a hankali ta kalle shi ya d’aga mata gira “Am sorry….” Sai ga wasu hawaye suna zubo masa daga
jirkitattun idanunsa cikin wata irin murya ya furta “Am gonna die Teeeey, Ba wancan Moddin ba ne ba
Kiddonki ba ne ki k’addara Kiddonki ya mutu wannnan wani ne daban da sam ba shi da amfani a rayuwar
nan am useless person Teeey….” Ya fa’da yana danne harshensa da k’arfin gaske jikinsa har kakkarwa
yake a tsorace Umma Teeey take kallonsa bai fasa damk’e hannun nata ba kamar yarda jikinsa bai daina
shaking ba, da alama zuciyarsa na cikin matsanancin b’acin rai… gumi kuwa fita yake a k’ofofin jikinsa
duk da sanyin a.cn da yake parlorn……….


Hadarin gabas Isn’t free it’s paid book. Book 1 ne kawai free paid for book 3 and 2. 500 cikin wannan
account din 2118666252 UBA.


Akwai wani irin zubar ruwa da Hadarin nan zai bayar nan gaba. Kada kizo kina dana sani ki biya a yi
tafiyar nan da ke. Babu Nadama In sha Allah.

Jikar Nashe★✍️hHADARIN GABAS……



NAZEEFAH SABO NASHE★✍️


08033748387.


18.



(TALLA! TALLA!!Mai Talla shi ke da riba..)

Kaso mafi yawa na jinsin maza da mata masu aure da marasa aure na fuskantar matsalar ciwon sanyi
wato Infection a turance, wanda ka iya addabar lafiyar su ya hanasu sukuni. Barin infection a jiki ba tare
da an magance shi ko anyi rigakafi yafi magani ba na zama babbar illa ga lafiyar ɗan Adam. Ciwo ne da ke
lalata tsarin jiki, ciwon ne da ke ruguza zamantakewar aure. Ƙwarai da yawa sun yi amfani da ƙwayoyi
har magungunan gargajiya da yawa don neman waraka daga cutar ta infection, wasu kuma sam basu yi
ba, Ina waɗanda suka gwada maganin infection amma har yanzu bai yi musu aiki ba? har ma da wanda
basu gwada ba to duk Albishirin ku, tabbas ku nemi ingantaccen maganin sanyi( *INFECTION FLUSHER*)
na *ALKHAIR HERBAL MEDICINE*. Maganin Infection na *AlKHAIR Herbal Medicine* na daga cikin
ingantattun magani sadidan da ke ragargaza duk wata cuta mai haifar da matsalar Rashin haihuwa, rashin
samun gamsuwa ga mace ko namiji, mata masu yawan ɓari, kuzarin namiji, warin gaba da ƙaiƙayin gaba,
jin zafi yayin saduwar aure, tsuke gaban mace, gyara gaban mace da sanya ɗanɗano, fitar farin ruwa,

ciwon mara yayin al'ada, wankin mara, zafin ciwon kai da ciwon jiki, gyambon ciki, kumburin jiki da
sauran dukkan ciwukan da cutar sanyi ke haifarwa.
Ku gwada *INFECTION FLUSHER DRINK* na *ALKHAIR HERBAL MEDICINE* a ƙalla na tsawon watanni 6
domin ganin sakamako mai kyau. Kar kuyi sakacin da zaku yi aure ba tare da kun sha wannan maganin ba
ango da amarya, uwar gida da maigidanta a nemi *INFECTION FLUSHER DRINK na ALKHAIR HERBAL
MEDICINE*.

Zaku samu maganin a kuɗi ₦4K, mata masu buƙatar set kuma zaku same shi a ₦6500. Sai an gwada akan
san na ƙwarai, Allah ya ƙare mu da lafiya.

Domin siyan wannan magani sai ku tuntuɓi lambobin waya ta hanyar kira ko whatsapp.
08169495093/07018098175

Ba shi da Side Effect.


_*BRIGHT PENS...*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huɗu a sabuwar tafiyar ta second batch.

*HADARIN GABAS*
Nazeefah Sabo Nashe

*ƘARFE A WUTA*
Ayushercool

*ZAYTOON*

Zee kumurya

*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.





Page 18….


Dafa kansa kawai Umma Teey ta yi, ta rasa abinda zata ce, ita kanta nata jikin kakkarwa yake. Ta sani ko
me Moddi zai gaya mata ba zai zama alheri ba. Wata k’addara ce mai girman gaske take bibiyar
rayuwarsa. K’ADDARA? Ta maimaita kalmar a zuciyarta Ba k’addara ba ce, abinda Moddi ya zab’arwa
kansa ne. Ta ji k’akkkarfar zuciyarta ta bata amsa. Hakan yasa ta lumshe idonta kawai nata hawayen da
suka fi na Kiddo yawa suka cigaba da zuba a saman fuskarta. Tana jin Moddin yana wani irin kakkarwa na
kukan da yake sha mai tsuma zuciya. Murya a raunane ta ce “Why Kiddo? Me yasa? Me yasa baka cigaba
da jin shawarar DIDI ba, na maka nasiha da take akan ka ci Daga halal, ka sa daga halal, ka nesanta kanka
daga haram, na san ko me zaka gaya min ba zai zama mai da’di ba. Imaan ta gaya min tun bayan da kawo
musu chocolate ka ware guda ka bawa Amaani, daga ranar rayuwar Ama ta jirkita ta shiga yin wasu irin
birkitattun mafarki a kanka marasa da’din tunawa, wani irin mafarki da bai kamata ta yi akan kowa ba sai
mijinta ko saurayin da take masifar so. Zuciyata tana bani ka kai sunan Amani wajen matsafan da sune
silar arzikinka, ko baka fa’da ba Kiddo wannan shine amsar…” Ta fa’da tana dafe kanta hawayen na
cigaba da zuba mata da sauri. Moddibo kuwa runtse ido ya yi yana tunanin ranar. Tabbas shima hakan ce
ta kasance da shi daga ranar ya saka Ama a cikin tunaninsa, barcinsa da komai nasa, daga ranar da
Amanin ta masa rungumar duk da a lokutan baya ma ya sha jin kwatankwacin hakan a kanta, amma bai
zafafa bai yi k’arfi kamar haka ba, yana jin wani irin feeling a kanta feeling d’in da ko akan Safna bai tab’a
jinsa ba…. Zuciyar sa ta cigaba da tuna masa komai daki daki, kamar yanzu abin ya faru haka yake ganin
majigin abin cikin idanunsa…..

Idan bai manta ba Spain suka je a lokacin, Spain d’in da ya dinga murna da zakwa’din zuwanta, don alheri
ne zai samu mai yawan gaske, alherin da bai san zai jirkice ya zame masa sharri ba. Sanda Alwan ya gaya
masa da shi zai yi tafiyar murnar sa kasa b’oyuwa ta yi. Ya dinga kallon Alwan cikin tsananin murna yana
furta “Ni kuma Sir!” Dole abin ya bashi mamaki don mutane manya da dama Sun saka rai a yi tafiyar da
su, sai gashi Alwan ya ce da shi zai yi tafiyar duk da shi d’in bai ko farce ba a arzikin wa’dancan. Alwan ya
jijjiga kai yana murmushi ya furta “Da Kai za’a Friend don haka ka zama cikin shiri, tafiya ce mai tarin
alheri da ina tunanin arzikin da zaka samu a cikinta ya isheka rayuwa har ka Mutu, koda a ce kuwa zaka
daina komai ne. Zaka shiga cikin jerin masu ku’din Nigeria da ko gwamnati sai ta sarà musu. Kasa barci ya
yi a ranar ya dinga hango Kansa Didi da kaf y’an uwansa cikin wata irin daula da zai zo ya shimfi’da musu.
Safna kanta farin cikinta ya kasa b’uya ta dinga Jin zuciyarta na kumbura kanta na girma hango ta a
matsayin matar matashin mai arziki da Nigeria ma zata San yana da shi. Ta dinga hango gwalagwalan da
zata dinga narkawa a jikinta tana saka manyan Kayan da sai matan shugabannin k’asa ne za su dinga
sakawa. Manyan motoci babban gida da komai na Jin da’di ma. Idan haka ya tabbata kuwa ya zama dole
ta raba Moddi da danginsa, ya zama dole ta saka katanga a tsakaninsu ta nesanta shi da su Nisan da ko
Uwarsa sai ta so ta gan shi zata gan shi, sai taso ta yi masa hidima zata masa.


Bayan komai ya kammala a tafiyar, an kuma yi nasara a abinda suka je nema. Ya shiga yiwa y’an uwa da
abokan arziki tsaraba bai manta da ta twins d’insa ba, ya dinga Jidar musu chocolate da suke masifar so.
Sai da suka koma masauki suna ha’da Kayan sannan Alwan ya cillo masa wata chocolate d’in mai tsadar
gaske yana dariya ya ce “Tsarabar Dada’s Girl.” Moddi ya cafe yana ware ido yana dariya ba Wanda bai
San son da yake wa yaransa ba, musamman Amani da ta zama ta gaban goshinsa rigimar yarinyar
shagwab’arta duk yana son su. Gefe guda kuma rashin tsoro da tsiwar da take wa Safna abin yana bashi
mamaki. Ta wannan b’angaren kam ya sarawa Ama don bata da tsoro ko ka’dan. Chocolate d’in ya bi da
kallo da ku’din da aka siyeta ya ware ido cike da mamaki yana sakata cikin akwatinsa ya ajiyeta a inda zai
ganta. Yana fa’din “Thank you Boss, kamar ka San Amaa ba abinda ta fi so a duniya irin chocolate…” “Na
sani…” Alwan ya furta tana kallonsa yana dariya. Moddi da mamaki shima ya kalleshi ya ce “How do you
know?” Murmushi kawai Alwan ya saki ya ce “Na gani a barci….” Bai wani bawa abin mahimmanci ba
don a time d’in Alwan bai sake bijiro masa da wata buk’ata ba da zata sa ya dasa zarginsa a zuciyarsa….”




Sanda suka dawo Amani ta rungumeshi daga ranar ya fara Jin wani irin zazzafan feeling a kanta. Feeling
d’in da kawai mata da miji ya kamata su ji shi. Rayuwarsa ta jiye tunanin Amani ya dinga bijiro masa tun

yana yakice abin har yaga abin fa da gaske ne, gudun sab’awa Allah yasa ya bawa Kansa mafita, mafitar
da yake ganin shi Kansa ba daidai ba ce ba kuma ta dace ba, amma ba yarda zai yi dole hakan zai aikata
da wani zunubin gwara wani…..

Tafin da UMMA T ta yi a fuskarsa ya saka shi bu’de ido da sauri yana kallonta. Birkitattun idanunta da
suka bayyana b’acin ranta tsantsa ta zube a Kansa tana furta “Gaya min gaya min komai Imamu idan
kuma ka b’oye min wallahi ba zan yafe maka hakk’in y’an uwan taka ba….” Cikin wani yanayi ya jingina
Kansa a kujera muryarsa cike da rauni ya ce “Idan na fa’da Miki zai zama sirri a tsakanin mu har na samu
mafita?” Ta ha’diye wani Abu da take Jin kamar ya tokare mata numfashi. Murya a shak’e kamar ba tata
ba ta ce “Idan na b’oyewa kowa ba zan b’oyewa mahaifiyar da ta haife mu ba, ko bakomai ya kamata Didi
ta sani….” Moddi ya dinga kallonta cikin tashin hankali yana girgiza Kai ya furta “Bana so Didi ta sani, ba
na so ki dasa mata b’acin ran da zai zama sanadiyyar ajalinta Ban San yarda zan iya rayuwa ba idan na
zama silar mutuwar Didi…. Ki zame mayafin Sirri na Teey….” Ya fa’da yana matsa yatsun hannunta da
sauri. Teey ta dinga kallonsa kafin ta ha’diye wani yawu. Ko kafin ta yi magana ya mik’e da sassarfa ya isa
bayan kujera yana zagaye parlorn Teey dai ta zuba masa ido tana jiran Jin abinda ya ce “Kin amince as
secret na gaya maki komai…” Ba yarda ta iya banda ta amince d’in tunda tana son ji, tana son Jin
matsalolin Kiddonta ta San hanyar da zata bi ta samo masa solution idan abin bai fi k’arfinta, don haka
bisa ta tilas ta ce “Na amince…” Ya zagayo gabanta yana mik’a mata hannu ya ce “Promise…” Nata
hannun ta saka ya dunk’ule waje guda hakan ya tabbatar da Sun k’ulla yarjejeniyar alk’awari a
tsakaninsu… ya zauna daf da ita ba tare da yana kallonta ba ya hau matsa hannunsa yana furta “Tun
muna yara na amince soyayyar da take tsakani na da ke mai girma ce, kin fi kowa so na a cikin y’an uwana
ke ce solution na duk wata matsala da ta tunkaro ni, ko a wannan karan na so naje Miki da tarin
matsalolina Ban San me yake dabaibaye ni na kasa aikata hakan ba. Teey ki amince ba ganganci na yi da
rayuwata sai K’addara da ta saka ni jefa kaina cikin ramin da ba mai fitar da ni sai Allah, na San ni mai laifi
ne Fateemah Amma wallahi Ban San yarda hakan ta faru ba….” Tun kafin ya ce komai hankalin Fateemah
ya tashi zuciyarta ta dinga rawa ta San koma meye zai fito daga bakin Kiddo ba mai da’di ba ne, muninsa
mai saka k’una da ra’da’din zuciya ne, ba mamaki da zarar ta gama ji zuciyarta ta buga ta Mutu, Amma
duk da haka tana son ji, tana son Jin Matsalar Kiddo ko da zata zama ajalinta… don haka cike da k’arfin
hali ta ce “Ina Jin ka Imaam…” a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya shiga bata labarin ha’duwar su da
Muhammad Alwan har zuwa yanzu da komai yake Neman ya dagule masa, ko na ce ma ya Dagule
d’in…..


Kafin ya gama bata labari tuni duk wata gab’a ta jikinta ta fara rawa kakkarwa take sosai ga wani tarin
gumi da yake tsatstsafo mata. Idanunta da suke disashewa ta zube a kan Kiddo, tana son ta gano gaskiyar
abinda ta gani a k’wayar tasa idanun. Tsoro ne sosai a cikinsu tsoron da ya bayyana har a sassan jikinsa ta
hanyar sanyin da gabbansa suka yi. Bata tab’a ganin karaya a tare da Moddi ba tun tashinsa har girmansa
sai yanzu da yake zube a gabanta cikin Neman mafita…. Raunatattun idanunsa ya zuba a kanta yana

fatan Tee d’in ta samo masa mafita, mafitar da zata zama alheri gareshi da ahalinsa gaba d’aya hawayen
take zubarwa kafin ta d’ago cikin karayar zuciya da ta murya ta ce “Idan har na gane abinda ka fa’da
Moddi, ka jefa kanka ne cikin k’ungiyar matsafa masu Neman ku’di ta ko wani hali. Me yasa Moddi? Me
yasa naka ajiye kanka inda Allah ya ajiyeka ba? Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login