Showing 54001 words to 57000 words out of 87659 words

Chapter 19 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf

Advertisement

Don k’iri da muzu suka kalleta suka furta “Ai sai ki aurar da y’ay’an naki, sanda Ubansu ya Mutu
ba nuna mana kika yi ba zamu rik’e su ba, sai yanzu da aure ya zo zaki neme mu ashe muna da rana?”
Didi ta ha’diye wani yawu mai zafi tana tuna Uban Moddibo da dukkan alherinsa ga y’an uwansa, burinsa
kyautata musu koda last kobo da ya rage a aljihunsa ne idan Har zata yi magana sai ya ce Maryama
kenan? Idan baka taimaki y’an uwanka ba wa zaka taimaka? Sam bani da burin samun ku’din da wani na
waje ma ba zai ci ba, balle jini na.” Didi sai ta ce “Mhmhn, Malam kenan, Allah yasa bayan ba kai su rama
maka abinda ka musu…” “ba zasu rama ba, har abada kuma bana neman ramuwarsu don Allah na yi
kuma gareshi nake neman sakamako.” Sai ta ja bakinta ta yi shiru. Haka suka dinga fafutuka Har Allah ya
fitar da su kunya don dai Fateemah Mijin marainiya ta aura take ya ce baya buk’atar a kaita da komai sai
zallar Fateemansa ita yake so da halayenta ba kayan d’aki ba da zasu zo su Mutu ko mu da’de ko mu jima.
Ingancin tarbiyyyarta da nagartar halayenta ya fiye masa tilin kayan d’aki. Didi taso ta turje amma sai
iyayen Ahmad suka nuna dattako suka ce basa buk’ata kuma har abada ba gori tsakaninsu da Fateema
sun yaba da halayenta da tsatson da ta fito. Don haka duk wani shiri na Didi sai ya koma kan Dijatu aka
siya mata kayan d’aki da duk wani abu da zata buk’ata. Haka aka yi biki aka k’are cikin kwanciyar hankali.
Zo kaga abin tausayi ranar rabuwar Fateemah da Kiddonta. Wunin ranar zama ya yi kamar marar lafiya,
haka zai shige d’aki ya saka kuka don baya son a ga kukansa Didi na hankalce da shi murmushi kawai take
saki don itama ji take kamar ta fashe da kukan, tabbas ka ga auran y’ay’anka babbar ni’ima ce, amma fa
rabuwa da su akwai ra’da’di mai zafin gaske. Musamman yarda ta taso da y’ay’anta kamar k’awayenta,
haka dai ta daure tana ji tana gani aka rabata da su zuwa gidan aure. Kiddo dai bai raka Dijatu ba, don ita
murna yake da tafiyar ta Adda T kawai zan raka ya furta kansa tsaye yana kallon Dijatun. Ta kuwa zabga
masa harara har da rank’washi ta furta “Sai me idan baka raka ni ba? Kuma koda wasa kada naga k’afarka
a gidana ka zo kwa’dayin kaza.” Ya janye jikinsa kafin ya furta “Ke ma ki samu kazar tukun, wannan
k’ulumin ne zai siya Miki kaza?” Ta bi shi da duka sai dai kafin ta cim masa ya fece da gudu, kamar lokutan
baya da suka Saba. K’wafa Dijatu ta yi kafin ta sake rushewa da kuka tana furta Ai Didi tana Jin abinda ya
ce mata Amma ta k’i yi masa magana saboda ita ba’a sonta shine d’an so…..


Haka rayuwa ta cigaba da gangara musu, da da’di ba da’di suna cikin godiyar Ubangiji don shi ke bayarwa
ya kuma hana a sanda ya so ya kuma ga dama. Moddibo na girma kyansa da wani irin kwarjini yana sake
bayyana tattare da shi. Shekara 19 idan ka gan shi sai ka zata wani babban saurayi ne, saboda son gayu
da Allah ya bashi. Bai k’i ba ko last kobo ne a jikinsa ya saka ya siyi riga da turare duk don ya je makaranta
ya yi burga ya shiga cikin gayu kuma yafi kowa. Sau tari idan ka ganshi zata zaka yi wani shegen d’an mai
ku’din ne, duk da bai d’au girman Kai ya ‘dorawa Kansa ba Amma yanayin suturunsa da fatar jikinsa da ta
bayyana tsananin Hutu duk da naturally haka take, wannan zai saka ka yi zaton Uban Moddibo attajiri ne,

haka Didi take furtawa a duk sanda taso ta tsokane shi. Murmushi yake saki ya ce “Didi ki yi shiru fa, nan
gaba baki san me Moddi zai zama ba, idan bai zama D’an Attajiri ba zai iya zama attajirin da kansa….”
Didi ta kan ce “Allah ya bada masu albarka, amma a rage dogon buri, rayuwar ma nawa take gaba
d’ayanta Moddi? Duk arzikin da zaka yi wani ya yi fiye da shi tun kan a san asalinka, don haka ka yi fatan
masu albarka kuma na Halak.” Idan kuwa Dijatu na kusa harara take zuba masa ta ce “Da charging wayar
za ka yi arziki? Ko da siyar da raken?” Idan Moddi ya juyo da birkitattun idanunsa Didi ce kawai take
rusunar da su ta hana ya Kai mata duka, sai ko idan Fateemah tana nan.



Sanda Moddi ya shiga Jami’a yana shekaru Ashirin cif, a sannan za su ce k’addararsa ta fara daga ranar da
suka ha’du da Safna daga ranar basu sake gane kan Moddi ba, har bayan auren da aka masa da y’ar riga
da mutuwarta…..” Didi ta saki ajiyar zuciya Jin hannuwan Moddibo a kafa’darta ta d’ago tana kallon
idanunsa da yake binta da natkakken kallo, mai nuni da yana son sanin menene a ranta me take tunani?
Duk da bai furta ba, hakanan ta sanar masa murmushi tana Shafa gefen fuskarsa ta furta “Ina tunanin
Moddi ne, ina tuna Uban Moddi da duk wata rayuwar mu ta baya mai cike da k’alubale, ina tuna wancan
Moddin masoyin Didinsa, wancan Moddin Wanda ya zama majinginar y’an uwansa, ba wannan ba da
gaba d’aya ka canja a idanunka nake hango rashin gaskiya Moddi, tun bayan ha’duwar ka da Safna ban
sake farin ciki ba Moddi, na yarda ha’duwarka da Safna shine silar rugujewar farin cikin zuri’ar Lami’do
Uban Moddibo….” Moddibo ya runtse idonsa yana Jin wani irin zafi a zuciyarsa, haka nan idanunsa wani
irin ra’da’di suke, da alama so yake kawai ya zubar da hawaye. Hannu ya cusa aljihu yana cizon gefen
leb’ensa, shi da kansa ya San Safna itace silar rushewar farin cikin ahalin Lami’do. Zufa ce kawai take zubo
masa ya runtse ido yana tuna ranar da k’addara ta caku’de zuciyarsa da ta Safna wace guda, daga ranar
ya canja daga Moddibonsa ya koma wani mutum daban…..


Da sauri ya dinga shiri saboda murna da zakwa’din shigar sa Jami’a. Jami’ar da da yasan Safna zata zamo
k’addararsa a ciki da koda wasa bai je ta ba. Wanka ya fesa sosai ya kuma k’ure Adaka cikin wani
rantsatstsen jeans black da Jar shirt da ta yiwa fatar jikinsa masifar kyau. Ya kawo P.Cap black ya saka a
kwantacciyar sumar sa ta asalin fulani. Sannan ya saka Black shade a idonsa. Idan ka gan shi wallahi ba
zaka zata haihuwar Nigeria ba ne cikin garin Kano a unguwar Yola, saboda tsananin kyan da ya yi. Kamar
yarda ya Saba a duk sanda zai fita daga gida sai ya isa wajen Didi ya zube a gabanta ita kuma sai ta
sunkuya saman Kansa ta karanto masa addu’oin tsari. Wannan karan saboda azarb’ab’i yana shiga
Jameelah ta ce masa Didi tana wanka. Ba zai iya jira ba don haka ya ce idan ta fito ki ce mata na wuce
saboda abokaina suna jira na.” Jameela ta bi shi da kallo kafin ta furta “Addu’ar fa? Yau ka yafe?” Sai ga
Didi ta fito da d’an hanzari tana furta “Tsaya Moddi, bana son fitar ka gida ba addu’a, duk saurin da kake
ka dinga tsayawa ina maka addu’a saboda ido da bakin al’umma, don na lura Kai Sam addini da addu’a

basu wani zauna a ranka ba, kullum kuma fa’dan hakan nake maka.” Ya ‘dan turo baki yana furta “To ki yi
sauri Didi, bana son na ja layi da yawa.” Ta fa’da yana mik’a mata kansa bayan ya rusuna ka’dan. Addu’ar
ta masa sai kuma ta tofa tana furta “Allah ya tsare sharrin mutum da Aljannu Allah ya kareka.” Ya amsa da
Ameen yana ficewa daga gida. Mamaki yake me yasa har yanzu Didi take mayar da shi yaro. Ya saki
murmushi shi ka’dai bayan ya d’ane bayan machine D’in abokinsa da ya fara tsokanarsa “D’an Autan Didi,
wallahi ka ji da’dinka, ka samu Uwa mai kula da dukkan lamarinka, inama duka iyaye haka suke?”
Murmushi kawai ya saki shi Kansa yana alfahari da Uwa kamar Didi.


Makarantar ta B.U.K dank’am take da y’an mata da samari, kasancewar a ranar duk aka fara registration.
Shigowar sa filin wajen ba wacce bata kalle shi ba a jikinsa ya dinga Jin hakan. Tsaki ya d’an ja yana kallon
abokinsa ya furta “I hate kallo wallahi, su kuma matan yanzu basu da kunyar hakan.” Salihi ya ce “Aa fa
wallahi kada ka zargesu kana da duk abinda suke so ne yaro, ai dole su kalleka Ma sha Allah.” Ha’de ransa
ya yi sosai kamar bai tab’a dariya ba, yana Jin yarda y’an matan wajen suke furta “Subhanallah, Allah ya yi
halitta bala’i.” P.CAP d’insa ya ja ya rufe fuskarsa yana kallon Salihu ya furta idan an zo Kai na please ka
kira ni, ina k’asan bishiyar can.” Kafin Salihi ya amsa masa har ya wuce cikin wata kalar tafiyar sassarfa da
ta sake jan hankalin y’an matan wajen. Suka bi shi da kallo. Ya zauna a saman wata kujera yana jan tsaki
duk sai ya ji ransa ya b’aci Sam baya son mata marasa aji. Idonsa a rufe cikin P.Cap ya dinga Jin ana buga
table D’in gabansa ga wani masifaffen k’amshi da baibaye wajen. Cikin kunnuwansa ya dinga Jin sound
D’in yarda take taunar chewingum… da wani irin masifa ya cire P.Cap D’in daga fuskarsa idonsa ya fa’da
cikin nata data kafe shi da mayataccen kallo tana cizar leb’enta………





Jikar Nashe★✍️HADARIN GABAS….★✍️

23.

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️

08033748387.

BRIGHT PENS SECOND BATCH


Takaici bak’in ciki, da b’acin rai ne suka dabaibaye zuciyarsa, a lokacin da ya kalli Safna, Ya dinga Jin wata
irin tsanarta a ransa kamar ya saka hannu Ya bugeta. Wani irin rashin aji ne haka? Shi fa yana son Mace
Ma aji wacce idan ka kalleta ma zata zuba maka harara ba irin wannan da take gabansa ba. Shi yasa ko
aure zai yi zai sha wuya wajen neman matar aure don sai ya tantance sosai kada ya auro B’ARAGURBI. Ya
sake gintse fuskarsa Har girarsa tana alamar tattarewa gefe guda yana fin cikar leb’ensa al’amari ne da
yake nuna kaiwa k’ololuwa wajen b’acin ransa. Madadin fushi daga Safna dariya ta saki ka’dan irin dariyar
shahararrun y’an bariki ta kuma ja ta tsaya hannayenta a k’irji ta furta “Dole ka yi, kai da kanka ka San ka
ha’du, nice to meet you sunana Safna addu’a ta guda Allah yasa department D’in mu d’aya.” Idan kai da
baka wajen ka yi magana to Moddi ma ya yi magana, shiru ya yi bai amsa mata ba ya sake mayar da P.Cap
d’insa kawai zuciyarsa na gaya masa ya tashi ya falla mata mari. Sai dai kawai ya share yana k’ananan
tsaki ya furta “Bar nan wajen.” Safna ta ware ido tana kallonsa ta ce “In ji ina? Ai ni nan naga wajen
zama….” A zafafe ya mik’e Har yana y’ar da P.Cap d’insa ya saka hannu don d’auka hannunsu ya sauka
tare da na Safna ya bi hannun da kallo da ya sha zak’ala zak’alan farce kamar ba y’ar musulmai. Caraf ta
rik’e P.Cap d’in Har da manna ta a k’irjinta tana furta Alhamdulillah na yi babban kamu wannan hular tafi
min samun 100k yau…..” Moddi cikin b’acin rai ya d’aga mata hannu sai dai ya rasa mai zai ce mata kawai
sai ya danne lips d’insa da harshen sa ya furta “Fuck you…” kansa tsaye yana kallon cikin k’wayar idonta.
Safna ta yi murmushi ta ce “Thank you.” A hassala ya bar wajen yana jin idan ta sake biyo shi wannan
karan sai ya mareta sai Allah yasa bata bi shi ba ta wuce da hular a hannunta, tana shinshina turarensa da
k’amshin sa ya mak’ale a jikin ta. Hararar k’asan ido ya bita da ita kafin ya tauna lips d’insa a hankali yana
furta “Rubbish.”


Daga ranar Ya zama na duk inda Safna ta San zasu ha’du sai ta bi shi. Ya yi mata jan idon amma sam bata
ji. Gashi ajinsu d’aya don department d’insu guda. Tun kowa bai sani ba har jama’a da dama suka targa da
yawan nacin da take masa, shi kuma baya gajiya wajen yarfa ta a gaban kowa. Mata da yawa bayan ita
Sun kawo masa tayin abota ko soyayya, sai dai kallo guda yake musu su bawa wandonsu iska. Don a
idonsa suke hango wani kwarjini da alamun rashin wasa a tattare da shi. Kullum girarsa a tsare idan ka
gan shi yana hira to cikin y’an uwansa maza ne, wannan kuwa zaka tarar da shi yana faffa’dan murmushi.

Bai san abubuwan da suka faru, sai dai lokaci guda ya samu kansa dumu dumu cikin wata irin zazzafiyar
k’aunar Safna, da ko a mafarki bai tab’a zaton zai riski kansa a haka ba. Sha’awarta mai zafi ta kama shi ya
dinga yin wasu irin mafarkai a kanta abin kamar sammu ko sihiri. Tun yana daurewa yana sharewa Har dai
da kansa ya kai kanta wajenta wata ranar Laraba da ba zai tab’a mantawa da ita ba. Address D’in gidansu
ya nema. A shekaru irin nasa Ashirin sai ya dinga ji kamar ya yi k’ank’anta da zuwa wajen budurwa Amma
abinda yake ji a ransa ya hana shi togace kansa daga zuwa wajen Safna. Wanka ya tsala sosai ya shirya
sosai cikin shigar da yake tafiyar da Imanin mata. Jikinsa ya d’au k’amshin masifaffen turarensa na MIYAKI
Wanda a lokacin sai ka kai ka kawo kake fesa shi. Ya fita tsakargidan sai da ya ji gidan shiru sannan ya
tuna basa nan sun tafi biki k’auyen su Didin, sai ya ji missing Didi da addu’ointa. Ya d’an Shafa kansa kawai
yana sakin murmushi da tana nan da ta tuni ta tofe shi da addu’a. Fita ya yi daga gidan bayan ya ja
k’yauren gidan ya datse da mukulli, bai damu da ya yi addu’ar ba ya nufi bakin titi direct don samun abin
hawa. Inda za shi ya sanar da mai abin hawa unguwar Lamid’o crescent. Tabbas Ya san unguwar masu
ku’di ce don haka yake ganin kamar ya yi tsalle Ya kai kansa inda Allah bai kai shi ba.


Babban gida mai girman gaske nan Mutumin da Ya tambaya ya nuna masa. Nan shine gidan Aliyu
Mak’arfi d’an samari wani ka zo nema a gidan?” Kallo guda ya yiwa gidan ya ji kamar Ya koma sai dai so
da k’aunar Safna tasa ya kasa barinsa komawa. So yake ya bata surprise tunda har yanzu ya san tana son
sa ba abinda zai faru In sha Allah. D’an d’aga kai ya yi yana amsawa Dattijon mutumin. Sai mutumin ya yi
murmushi Ya dafa kafa’darsa yana furta “Ka kula, ka yi takatsantsan don jama’ar gidan basu da mutunci ,
basu San mutuncin d’an Adam ba, gani suke tunda suna da ku’di za su taka Uban kowa bakomai ba ne a
wajensu.” Moddi ya d’aga kai yana yiwa mutumin godiya sannan ya k’arasa bakin gate D’in. Suka gaisa da
mai gadin da yake masa wani gani gani sannan ya gaya masa Safna yake son gani…” Mai gadin Ya bi shi
da wani kallo kafin ya furta “Dama kai ne bak’on da Safna ta ce min ko mu da’de ko mu jima zaka zo, idan
kazo kuma na barka ka shiga. Na zata zan ga wani gwaska sai na ganka a kan sawayenka….” Moddi ya cije
bakinsa yana tattare girarsa waje guda, sai mai gadin ya shiga taitayinsa ganin Alamun Moddi bai zo da
wasa ba ya ce “Bari na kira maka ita, shiga da ciki…” Moddi ya girgiza kai yana mik’ewa ya ce “Batta
kawai.” Da sauri Maigadin Ya ce “Afuwa d’an samari, Ban fa’da fa don wani abu ba. Abin ne Ya bani
mamaki ganin irin manyan mutanen da suke zuwa wajenta su fita a mota yau kuma sai na ga kai dai
matashi ne da baka zarce shekaru ashirin ba, kuma da alama baka da ……” “Ba ni da ku’di.” Moddi ya
fa’da yana zuba birkitattun idanunsa kan na Mai gadin yana jin wani zallar b’acin rai. Me yasa jama’ar
yanzu Sun fi girmama ku’di ne fiye da mutunci? Da sauri Maigadin Ya girgiza kai yana furta “Afuwa ban
san da Soja nake tare ba…” ya furta yana k’ok’arin zubewa a gabansa. Moddi ya saka hannu Ya d’aga shi
yana sakin murmushin da bai shirya ba ya ce “Baba wa ya ce maka ni Soja ne?” Mai gadi Ya girgiza kai
yana furta “Ai ba sai an gaya min ba, kwarjinin idanunka ya isa ya tabbatar da haka, ka godewa Allah

irinku ko ido ba’a iya ha’dawa da ku, irinku k’alilan ne cikin Al’umma. Bari na kira maka Safnan.” Ya shige
ciki ya bar Moddi a tsaye cikin zafi da tafasar zuciya ji yake kamar ya juya Amma kuma ya kasa aikata
hakan kamar Wanda ake controlling d’insa da remote soyayyar Safna ce narke a zuciyarsa….


Ko minti biyar ba’a yi ba, sai ga Safnan ta fito fuskarta fal annuri ya ga ta zuba masa ido. Shima kallon
nata yake yana jin kamar ya rungumota a jikinsa. Tana isa wajensa ta furta “Mu shuga daga ciki, na dad’e
ina jiran wannan ranar sai gashi ta zo yau, gani ga My love.” Bai yi musu ba ya bita. Tana cigaba da sarrafa
jikinta ba don komai ba sai don ta susuta tunaninsa. Ta kuma ci sa’a don gaba d’aya sha’awar Moddi sai
da ta gama tashi. Sitroom ta kai shi. Bayan zamansa ta shiga gida don samar masa abinda zai ci. Jingina ya
yi da kujerar yana jin abinda yake ransa yana sake hauhauwa bai San ta shigo ba don idonsa a lumshe
yake sai da ya ji ta zauna a daf da shi ta kuma rungumoshi kamar jariri. Ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login