Showing 18001 words to 21000 words out of 87659 words

Chapter 7 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf

soft hand ‘din ya dawo da ita tsakiyar kitchen d’in “Kin ci
abincin yanzu?” Ta girgiza kai. Kallon cornflakes d’in da ta d’auko ya yi, ba tare da ya saki hannun ba ya
sake janta har suna kusan ha’da jiki suka koma, da kansa ya ha’da mata cornflakes d’in ya saka mata ruwa
mai sanyi, yana mik’a mata cup d’in ya bi gashinta da jikinta da kallo ya furta “Kada ki sake fitowa cikin
dare a haka…” sai a lokacin wata zazzafar kunya ta rufeta duk da kasancewrsa Ubanta bai kamata ya
ganta a yanayin shiga irin wannan ba, ba a abinda ya b’uya daga halittar matan takarta, musamman
k’irjinta don rigar nylon ce da ta bi ta kwanta a jikinta. Ya dubi idonta yana d’an sakin murmushi ya furta
“Good Night.”. Daga haka ya fice daga kitchen d’in. Cup d’in ta runtse a hannunta tana furta “Me ye a
kanki Amani? He is your Dad fa..” Ta yi saurin lumshe idonta tana sakin ajiyar zuciya gaba d’aya jikinta ya
na’de k’amshin turarensa tsaf kamar ya mata wanka da shi, turaren da yake gigita mata hankali ya fitar da
ita daga tunaninta ta fa’da duniyar masoya. Numfashinta fusga a hankali da ta tuna yanayin da ta ji su
d’azu da Mommy sai ta saki tsaki ka’dan tana jan k’afarta ta fice a kitchen d’in.


Har a lokacin Imani barcin ta take peacefully. Don haka Amanin ta zauna daga parlor tana shan cornflakes
d’inta cikin wani irin yanayi musamman yarda take shak’ar turaren Dadan, ganin ba ta gane komai a shan
cornflakes d’in yasa ta tura cup d’in gefe tana jan pillow ta rungume shi a hankali tana tuno sanda a d’azu
ta rungume Dadan yanayin yana sake zafafa a tattare da ita tana nan zaune cikin wannan halin bata san
an yi Assalatu ba don bayan komai ya lafa mata sai barci ya d’an fisgeta mai cike da mafarkin Dada. Tashin
da Imani take mata ne yasa ta bu’de ido tana kallon Imanin da ta kafe ta da ido da alamar kallon tuhuma
take mata…


Ba tare da tace mata komai ba ta juya d’aki tana furta “Wak’atussalah….” Amanin ta mik’e tana kallon a
yanayin da ta yi barcin ga k’amshin Dada still a tattare da ita, da sauri ta shige toilet bayan shigar ta
d’akin. Imani ta bi k’ofar toilet d’in da kallon bayan ta sake shak’ar k’amshin turaren da ta tabbatar na
Dada ne, gabanta ya sake fa’duwa wasu tunani barkatai suka shiga bijirowa zuciyarta…. Ta runtse idonta
tana furta “Allah kada ka saka abinda nake tunani ne, da mun shiga uku!” Bata sake tsorata ba sai da
Amanin ta fito kanta a jik’e da alamar wankan tsarki ta yi, ai bata san sanda ta isa gabanta ba ta ja
hannunta tana tab’a gashin kanta… “Wankan me kika yi Amani?” Amanin ta runtse idonta tana mamakin
tambayar da Imanin ta mata, don dai sarai ta san ta saba irin wannan wankan da asuba ya zame mata jiki
meye na mata wannan tambayar Kuma? Murya a shak’e ta furta “Wankan dana saba ne duk Asuba,

Saboda na yi mafarkin da na saba…” Ta fa’da tana kallon tsakiyar idon Iman d’in. Iman ta cije leb’enta
tana furta “Yau a mafarkin naki har wanka Dadan ya miki da turarensa?” Sosai hantar cikin Amani ta yi
rawa ta zauna a gefen gado dab’as tana saka towel ta rufe kanta sabida sanyin da ta ji ya shiga jikinta har
tsakiyar kanta, ta runtse idonta leb’enta na rawa ta furta “Zargi na kike da mahaifin da ya haifeni Imani?
Zargi na kike da aikata zina da mahaifina Iman….?” Wani irin kuka ne ya kub’uce mata. Iman dai na tsaye
itama nata hawayen zuba yake sam kukan Amanin bai tab’a mata zuciya ba don tata zuciyar tafi ta
Amanin karaya ya zama kuma dole ta gaya mata gaskiyar abinda ya faru tun kafin su zo aji kunya… “Ba
zargi nake ba, na tabbatar yau kin ha’da jiki da Dada kamar yarda duk rigar ki ta baibaye da k’amshin
turaren da duk wanda ya san Dada ya san na sane, ki gaya min gaskiya Amani me ke tsakaninki Da
Dada?” Ta fa’da a tsawace wannan karan hawayen idonta ba su bar zuba ba duk jikinta ma rawa yake.
“Ba ki yi k’arya ba, tabbas yau na rungume Dada a jikina…..” wani irin Mari Iman ta sakar mata ta kai
mata shak’a a wuya cikin gigita ta furta “Wani irin banzan tunani ne ya hau kan ki? Mahaifinki Amani shi
kikewa soyayya irin ta Miji da Mata? Yau lamarin ya zarce mafarki har ta kai ga kin kai kan ki wajensa , to
hell with you Amani…..” Kasa magana Amani ta yi illa runtse ido da ta yi hannayenta dafe da wajen da
Iman d’in ta mareta ba tare da ta sake ko kallonta ba ta mik’e ta zura rugar sallarta ta fara sallah,
idanunta na zubar da hawaye, Iman jikinta a sanyaye itama ta tada sallahr hawaye ba bin idanunta wani
bayan wani sallahr kawai take ba tare da ta san abinda take fa’da ba don sam ba nutsuwa a cikin sallahr
kamar yarda Amanin itama tata sallahr ba nutsuwa. Tunda suka yi sujjada kowa ya kasa d’agowa suna
gayawa Allah buk’atunsu cikin shashshek’ar kuka.


Ko bayan da suka idar, Imani sake juyo da Amani ta yi ta fuskacenta sosai idanunsu cikin na juna ta furta
“Ki gaya min exactly what happened between you and Dad… Amani ina tsoro ina tsoron faruwar komai.
Ki tuna maraicin mu ba mu da Uwa Amani me kike son duniya ta d’auke mu?” Madadin amsa mata
Amani fa’dawa jikinta ta yi cikin kakkarwar jiki tana sakin kuka ta furta “Da gaske Iman ina son ya
kusanceni ina son na ji shi kusa da ni, ina son na shak’i k’amshin turarensa tausassan hannunsa da
sussulb’an lips d’insa Ina son Dada ya zan yi Iman ki gaya min ya zan yi na daina jin abinda nake ji game
da shi, da gaske yau na rungumeshi a kitchen in a romantic way amma wallahi ba a hayyacina ba ne
shai’dan ne Iman bayan wannan ba abinda ya faru tsakanin mu…..” Ta fa’da cikin wata irin karyayyiyar
zuciya. Itama Iman d’in tata zuciyar a karyen take kasa magana ta yi illa sake rungumar Amanin da tayi
tana jin yarda zuciyarta take bugu sosai idanunta a lumshe ta furta “I love him to the extent Iman I wish I
can marry him…..” Daga haka ta saki wata ajiyar zuciya mai k’arfin gaske da ya razana Iman ganin tabbas
da gaske suma ta yi don ga shi nan jikinta ya saki ta kuma mata nauyi. A ru’de ta janyeta ta saka ta a kan
pillow sannan ta shiga toilet da sauri ta d’ebo ruwa ta zuba mata a jiki da fuska, wani irin nishi ta yi
alamar ta dawo hayyacinta daidai lokacin Da Dadan ya shigo yana kallon Imanin ya furta “Ke Lafiya me ya
sameta?” Jikin Imani har b’ari yake ta juya tana kallon Dada a ranta tana jin gwara ta gaya masa gaskiya
amma ta ce me? Zuciyarta ta cigaba da sanar da ita gwara kawai ta gaya masa gaskiya.

Shin kuna ganin ta gayawa Dadan gaskiyar kuwa? Wannan wani irin al’amarin ne? Me ke faruwa Da
Amani haka ko dai mutanen b’oye ne? To ko dai Dada ne……


Bari dai na yi shiru ba zaa ji mutuwar sarki a baki na ba.


�� ��ℯ✍️HADARIN GABAS…..


�ℯℯ� ���ℯ✍️


08033748387.

★★★★★ 8️⃣

_*BRIGHT PENS...*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huɗu a sabuwar tafiyar ta second batch.

*HADARIN GABAS*
Nazeefah Sabo Nashe

*ƘARFE A WUTA*
Ayushercool

*ZAYTOON*
Zee kumurya

*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.



★★★★★★
K’arasawa cikin d’akin ya yi idanunsa akan Amanin da still har yanzu numfashinta bai zama normal ba, ya
zube a gabanta yana bin idanunta da suke lullumshewa da kallo, ya saki ajiyar zuciya ka’dan ya
Juyo yana kallon Iman “Me ya
Sameta?” Iman tana hawaye ta furta “Ta d’au tsawon lokaci tana shiga wani irin yanayi a cikin barci
kamar mai aljannu to kuma yau abin sai ya kai har da suma…..” Dahda ya d’auke kai yana furzar da
numfashi ka’dan kafin ya furta “Yanayi wani iri? Kuma mafarkin mai take?” Iman ta bu’de baki zata yi
magana Amani ta yi saurin cafkar hannunta ta rik’e tsam a
Cikin nata da raunatattun idanunta take kallonta kafin cikin sanyin jiki ta girgiza mata kai. Dahda kallonta
kawai yake kafin ya tab’e baki ya kalli Iman ya ce “Samo mata Tea mai zafi, kuma kada ki fitar mata da
sirrinta tunda bata son kowa ya sani, right?” Ya fa’da yana kallonsu da wani irin yanayi da Iman ta kasa
fassara shi. Sakin ajiyar zuciya ta yi ta mik’e tana d’aga kai ta fita daga d’akin don samo wa Amanin tea
d’in. Zaman da ya yi daf da ita yasa zuciyarta cigaba da wani irin bugu har hakan yana bayyana ta saman
rigarta, Dahda bai fasa kallon ta bakamar yarda take jin hakan a jikinta ta sake runtse idonta tana jin
kamar ta zunduma ihu. “Tashi zaune…” Ya furta cikin Husky voice.. Da ta sake sakata runtse ido ba shiri
sabida wani yanayi mai wuyar fassara da ta ji ya tsarga mata. “Ki tashi na ce…” Ya sake furtawa kai tsaye
yana kallon yarda take mutsu-mutsu. Kamar ta zunduma ihu haka ta ji ta mik’e idanunta a kansa tana jan
jikinta ta matsa daga daf da shi. “but for now karatu nake son ku yi, ku ka’dai Allah ya bani don haka nake
son ku zama educated ta yarda nan gaba zan yi alfahari da hakan You are too young to fault in love….

Understand?” D’aga kai suka yi a hankali Imani ta furta “Noted…” Ya jijjiga kai yana furta “Allahumma
Barik..” ya fice daga d’akin yana sake jaddada su shirya yana jiransu.

Fitar sa ke da wuya Amani ta saki ajiyar zuciya mai nauyin gaske, Iman ta juya tana kallonta cike da
tausayawa ta ce “Me yasa baki bari na gaya masa halin da kike ciki ba?” “Saboda abin kunya ne a gareni a
ce ina son mahaifina so irin na aure….” Ta furta tana zuk’ar tea d’in da lumshe ido. “Ki tashi ki shiga
wanka mu je kiga doctor..” Ta mik’e ba don tana son Ganin Doctorn ba sai don a rayuwarta ba abinda
yake faranta mata irin su fita da Dada a mota guda tana shak’ar k’amshin turarensa. Wani irin moment ne
da baya gogewa a k’wak’walwarta.

Tsaf ta shirya cikin wasu shegun Riga da siket masu colour d’in baby pink da touchés d’in maroum a jiki,
hakan yasa ta yana mayafinta maroum ta yi kyau sosai kamar ka saceta har Imani ta dinga kallonta da
mamaki ta furta “We are going to hospital fa Malama, ba gidan biki ba..” murmushi ta saki tana watsa
hannunta ta ce “Me kika ga na yi?” Bata sake mata magana ba ta cigaba da shirin ta tana gamawa ta saka
dogon hijabinta har k’asa ta mik’awa Amanin nata. Amani ta waro ido a ranta tana furta Tab’di Allah ba
zan saka Hijab ba… A fili kuwa amsa ta yi ta ajiye tana furta “Attak’wa Hahuna Ustaza… ba sai ka saka
Hijab bane zaka amsa sunan mai tsoron Allah…” Daga haka ta ja y’ar ficilar jakarta da ta cilla wayarta a
ciki ta fice parlour cikin annashuwa da tarin farin ciki. Iman ta bita da kallo sai kuma ta fita ta bi bayanta
tana d’an tab’e baki a fili ta furta “Rabbi Yahdiki ya Ukhteey…”


Amani na zuwa parlorn ta tarar da Dada a zaune da cup d’in coffee a hannunsa sai zuba k’amshi tea d’in
yake yana turiri amma a haka yake zuk’arsa ko zafinsa ba ya ji idanunsa akan laptop yana pressing da
tattausan hannunsa cikin nutsuwa. Zama ta yi a kujerar da take kallon tasa ya d’an d’ago yana kallonta
kafin ya cigaba da abinda yake idanunsa akan laptop d’in ya furta “Good Morning Amani?” Kunya ce ta
kamata tunawa da ta yi bata gaisheshi ba yau gaba d’aya. Ta fara fidgeting yatsunta tana furta “Am sorry
Dahda ina kwana…” Bai amsa ba ya cigaba da abinda yake kafin Imani ta shigo a gefensa ta durk’usa
tana furta “Dahda ina kwana?” Ya d’ago yana kallonta cike da murmushi ya furta “Good girl, lafiya lau.”
Idanunsa akan Amani da ta cigaba da fidgeting yatsunta tana murmushi k’asa-k’asa. Girgiza kansa kawai
ya yi yana ajiye tea cup d’in ya mik’e bayan ya d’au mukullin motarsa ya kallesu yana furta “Let’s go.. duk
da naga kamar ma ta ji sauk’i….” Amani ta d’an langwab’ar da kai ya girgiza kai kawai yana d’an
murmushi ya furta “Stubborn child ke kuma son zuwa asibitin kike? Ba kuka kuwa idan yace allura zai
miki agree?” Ta girgiza kai don ta san bata da wannan juriyar.

Daidai lokacin Mommy ta fito tana kallonsu cikin mamaki ta furta “Sai ina kuma Moddi?” “Hospital” ya
furta kansa tsaye yana d’an gimtse fuska don ya tsani halayyar ta ta rashin tashi da wuri sai dai ta barwa
yara aiki tana kwance ita hakima shi yasa ga shi nan tana ta k’iba banda yana da babban dalili na rashin
ha’da mata biyu da tuni an wuce wajen to ya san bai isa ba a yanzu dai kam idan ba so yake komai ya
dawo baya ba… “Asibiti? Waye ba lafiya?” “Ama…” ya furta kai tsaye don sau tari haka yake gajarce
sunan mutane, Mommy ta ware idonta tana kallon yarinyar da aka ce ba lafiyar bata ga komai a tare da
ita ba banda ma wani shegen kyau da ta k’ara.. sai dai ta san bata isa ta furta komai ba a yanayin da
Moddibo yake na tsareta da ido yaga action d’inta. Ta d’an tab’e baki tana furta “Allah ya bata lafiya,
amma kuma idan Imani zata bi ku waye zai zauna ya taya ni preparing breakfast?” Abin ma haushi ya ba
shi wato ita in dai ba yaran nan ba zata iya komai na gidan ba, banda baya son tashin hankali da tafiya zai
yi da su duka to sam baya son mita don haka ya kalli Imani ya furta “Ki zauna ki tayata ke…” Imani data ji
wani irin bugu da zuciyarta ta yi da k’arfi na tsoron fitar Dahda da Amani ita ka’dai sai da ta d’an waro ido
har Dadan ya kalleta ya furta “What?” Ta girgiza kai tana furta “Nothing I should stay….. sai kun dawo.”
Dada ya girgiza kai ya fita Amani ta bi bayansa cikin matuk’ar farin ciki da ta rasa dalilinsa. Front seat ta
shiga wata irin ni’ima na fusgarta musamman jin k’amshin Dadan da ya zauna ra’dam a cikin motar har
sai da ta lumshe idonta. Addu’a ya d’an yi a hankali ta hawa abin hawa sannan ya ja motar ya fita daga
gate d’in. Shiru cikin motar ba mai magana ita ta lula duniyar tunani shi kuma yana bin sautul k’ur’an a
hankali cikin suratul bak’ara. Har suka isa asibitin idanunta a lumshe suke kamar mai barci sai dai kawai
kallon Dadan take ta cikin lumsassun idanunta tana mamakin yarda Dadan yake da masifar kyau da kyan
jiki kamar shi ya halicci kansa, bata ga aibun Mommy ba da take matuk’ar kishinsa… tana ji ya yi parking
sai dai bata motsa ba so take sai ya yi mata magana ta ji husky voice d’insa kusa da ita. Ai kuwa ta samu
abinda take so don sai da ya juyo ya kafeta da ido kafin ya saki ajiyar zuciya ya furta “Mun zo…” Ta motsa
ka’dan tana bu’de idonta da suka yi wani kalar juyewa da k’yar ta d’aga lab’b’anta ta furta “Okay….”
Dadan ya fara fita kafin tabi bayansa tana jan Hasbunallah a ranta don lamarin nema yake yafi k’arfinta.


Cikin takun girma kamar wani sarki yake tafiya tana bayansa duk inda yabi idanun mutane a kansa
musamman idan aka juyo masifaffen k’amshin turarensa, mata da dama har sake juyawa suke su kallesu,
Amani kuwa duk wacce ta ha’da ido da ita sai ta zabga mata harara. Suna zuwa daf da wata budurwa da
ta kasa d’auke ido a kansa Amani ta furta “Auzu bikalimatil lahi tammmat maye ya ci kansa…” Murmushi
budurwar ta yi ta furta “Ai fa sai kin yi hak’uri y’an mata tunda kika auri kyakykyawa kuma ingarmar
namiji Ai dole a kalleshi….” Amani ta waro ido tana watsa mata wani kallo “Uban wa yace miki Mijina
ne? To mahaifina ne….” Ji ta yi kawai Dada ya cafki hannunta ya runtse cikin nasa tattausan hannun don
ya san yanzu ta tara masa jama’a. Zata sake magana ya furta “Shshhhhh bana son magana…” Bai saketa
ba sai da suka isa ga office d’in likitan sannan ya zame hannunsa ya kuma tsare gira sosai ya zauna kafin
ya dubeta ya furta “Zauna…” Zaman ta yi fuskarta a cukurku’de don wani irin haushin mutanen da suka
kalli Dadan take… Likitan ya bi su da kallo bayan ya gaishe da Dahdan ya furta “Me ya samu Ama Ta
sanya Dada fitar sassafe?” Ajiyar zuciya ta saki ta furta “Zuciyata ce take bugu da k’arfin gaske ban san me

yasa ba?” Ido Doctorn ya zuba mata kafin ya furta “What time take miki haka? Ko any time haka kike jin
ta?” D’agowa ta yi tana kallon Dada ta rasa amsar da zata bawa likitan da shima ya kafeta da ido yana
nazarinta “Ki gaya masa mana, kike kallo na….” “Idan na ga Dahdah ko na ji muryarsa ko naji k’amshin
turarensa a mafarki ko a zahiri…”



�� ���ℯ….✍️HADARIN GABAS……


NAZEEFAH SABO NASHE.★✍️




�ℯℯ� ���ℯ★✍️


08033748387.

★★★★★

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login