Showing 21001 words to 24000 words out of 87659 words
Chapter 8 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf
9️⃣
★★★★
Abinda ya kamata ta fa’da kenan, sai dai ita da kanta ta san fa’dar hakan ba zai yiwu a wajen ta ba. Da
kunya da kunya matuk’a da gaske ta furta hakan kai tsaye. Dahda kuwa bai bar kallonta ba balle likitan da
ya kasa cire k’wayar idanunsa a kanta.
“Allah ya baki lafiya, amma dai ko meye a ranki ya kamata ki ciresa don ingancin lafiyar ki.” Likitan ya
fa’da yana sake gwada b.p d’inta. Magunguna ya rubuta mata da description d’insu kafin ya mayar da
kallonsa kan Dahda da sam hankalinsa ba ya kan su yana ta danna waya. Mik’a masa takardun da yake ne
yasa Dahdan d’agowa a fusge yana kallonsa yasa hannu ya amshi takardar. Murya a k’asa ya furta
“Thanks Doctor…” Likitan ya d’aga kai yana furta “A Kula da shan magungunan don Allah In sha Allah
every thing will be alright…” Dahda ya sake d’aga kansa yana d’an sakin murmushi ya furta “In sha Allah”
Sannan ya yi gaba Amani ta bi bayansa tana taku cikin sanyin jiki.
Massenger ya mik’awa takardar maganin kasancewar suna da file a asibitin ba buk’atar ya basa ku’di. Bai
tsaya a wajen ba ya nufi hanyar waje yana d’an tsaki ganin yarda idanun mutanen wajen suke zube a
kansu. Amani kuwa zaginsu take a ranta tana mamakin dalilin wannan Uban kallo.
Madadin su nufi gida sai ta gan su a k’ofar gidan Umma tee, don idonta a rufe yake bata san inda suke
zuwa ba sai da ta bu’de ido. Ta d’an juyo tana kallon Dahda bata yi mamaki ba don ta san a kaf Yayyensa
gidan Umma Tee kawai yake zuwa itace tasu tafi zuwa d’aya yana son Umma Tee kuma kowa ya shaida a
kaf zur’iar Hajja D.
Bai mata magana ba ya fita daga motar hakan yasa itama ta fita ta bi bayansa tana jin d’an farin ciki a
ranta don ita kanta tana sonUmma tee don macece simple da bata d’au rayuwa da zafi ba sab’anin
sauran y’an uwanta.
Filin gida ne babban gaske da yake k’unshe da wasu irin bishiyu da suka sake k’awata filin wajen. Daga
gefe can garden ne da carport mai kyan gaske. Daga shigarka gidan Umma teey zaka san suna da rufin
asiri koda baka saka su a layin masu ku’di can can ba. Za kuma ka shaida tsafta ta zauna gwargwadon iko
a gidan.
Masu hidimar guda biyu suka dinga zubewa gaban dahda suna kai gaisuwa, don sun tabbatar da ganin
Moddibo a gidan alheri ne, don kyauta yake musu kamar baya so.
Yanzun ma hannu ya saka a aljihu ya ciro ku’din da bai san ko nawa bane ya dunk’ule hannunsa ya tura
musu a nasu hannun. Sannan ya shige yana amsa addu’ar da suke masa a zuciyarsa don shi kansa ya san
a wannan yanayin da yake ciki na sark’ak’iyar addu’ar ce abinda ya fi buk’ata.
Yana cikin wani hali da shi ka’dai ya sani sai kuma Uban gidansa da ya zama musabbabin komai. Fatansa
Allah ya d’ora shi akan Uban gidansa da buk’atarsa da ya bijiro masa wanda baya jin ko sama da k’asa zata
ha’de zai aiwatar da muradin Muhammad Alwan….
A tsaye Umma tee take tana zuba turaren wuta a burner da take hannunta ta tsinkayi sallamarsa. Cak ta
tsaya tana amsa sallamar fuskarta a washe don rabonta da Moddibon ya tako gidanta tsawon wata uku
kenan.. “Muryar wa nake ji kamar ta Kiddo, Moddin Didi.” Ya d’an watso mata kallo yana mata nuni da
Amani. “Wannan sunan ba zai bar bakin ki ba at my 40 ages kike kira na Kiddo’s.” Harararsa ta yi tana
k’arasawa inda yake ta furta “Har yanzu kallon da nake maka kenan Moddi, baka wuce Kiddo ba a wajena
ya gida yau an tuna da mu kenan?” Sosa kai ya yi yana zama ya saki ajiyar zuciya yana furta “Dama ban
manta da Tee ba kina zuciyata kawai komai ne ya caku’de min…” “Zancen kenan, kulllum da an yi
magana kace wani kana busy ban tab’a ganin ma’aikacin gwamnati da zama busy irinka ba, kamar wani
mai company…..” Ya d’an ji bugun zuciya ka’dan ya same shi ya runtse ido don an zo wajen da yake fa’dar
masa da gaba wajen da zai zo ya tari y’an uwansa ya sanar da su tarin arzikin da yake da shi. Abinda yake
ba shi tsoro amsar da zai basu a duk sanda suka bijiro masa da tambayar a ina ya samu ku’din? Shi yasa
har yanzu ya kasa gaya masa waye MODDIBO A BADINI, don ya tabbata ZAHRIN MODDIBO kawai suka
sani…. Bai farka daga tunanin da yake ba sai da ya ji muryar Fateeman a sama tana furta “Ama ki shiga
Haulat na ciki.” Sannan ya dawo da hankalinsa kanta. Ya tarar ta kafa masa idanunta da ya san duk sanda
ta masa wannan kallon kamar tana karantar har cikin zuciyarsa ne… “Kiddo me kake b’oyewa a cikin
zuciyarka wanda baka so mu sani?” Ta fa’da tana nutsa manyan magananta cikin nasa idanun da ya
lumshe su ba shiri, yana kuma matse hannunsa da d’an k’arfi. Tsoro ne ya kamata bata san sanda
hankalinta a tashe ta mik’e ta isa inda yake zaune ba, sai ji ya yi ta kama tattausan hannunsa a cikin nata
yarda take masa kenan yana yaro idan tana son taji damuwarsa. “Bu’de idonka ka kalleni Moddi…” Kasa
musu ya mata sai da ya ware idonsa tarrr a kanta yana sakin huci ka’dan tare da taune leb’ensa wata zufa
ka’dan tana zubo masa. Fateema ta lumshe ido tana furta “Oya tell me exactly what is happening? Kada
kace min bakomai don na san tabbas there is….” Ya girgiza kai yana furta “Ba wani matsala ba ne fa Tee,
amma dai ku taya ni da addu’a akwai business da na shiga na samu ku’di sosai kuma a business d’in sai
dai a k’arshe inaga kamar business d’in zai zame min mara amfani…. “ Ya sake sakin ajiyar zuciya “Mu
ajiye wannan a side, don na san ba lallai ki fahimceni ba, ba mamaki ki fassara ni da abubuwa da dama a
zuciyarki. Yanzu abinda nake so ki min ki yi duk yarda zaki yi Hajja Dee ta dawo gidan da na gina nake so
na tare da ita a railway….” Fateema ta waro ido ta furta “Kai ka ka san ba ni da wannan damar, amma ni
ba wannan bane a gaba na wani business ka je ka jefa kanka? Alhali ni dai na san kai government worker
ne ajiye aikin gwamnatin ka yi a ina ka samu ku’din da har ka Gina gida a railway? Unguwar da na ji ana
fa’dar sai Wanda ya ci ya tada kai.” Ya d’aga kai “Na da’de da barin aikin gwamnati na fa’da business ban
gaya muku ba ne don na san zaku iya hanawa yanzu haka ina da company a Abuja ina da shi a kano zan
bu’de next week a kuma ranar nake so na tare a sabon gida na, Ending month kuma zan yi lunching
sabon jirgina da zai fara jigilar passengers zuwa k’asashen waje da suka danganci………” sai sannan ya
lura da shock d’in da Umma tee ta shiga, ta dinga kallonsa baki sake idanunta ko motsi basa yi. Har sai da
ya yi clapping hannunsa a fuskarta sannan ta saki wani gwauran numfashi tana nuna shi da yatsa ta mik’e
tsaye tana ja da baya. Firgicin da Moddibo ya shiga yafi nata da sauri ya mik’e ya bi bayanta sai dai ko
kafin ya cimmata ta shige d’akin da yake bayanta da sauri ta rufo da key. Don tabbas tana buk’atar nazari.
Moddi ya tsaya a bakin k’ofar yana buga mata k’ofa da rok’on ta bu’de amma ta masa shiru a cikin d’akin
sai furzar da huci take Me Moddi ya d’auke su mak’iyansa ko me? Da wannan gagarumin cigaba zai same
shi amma ya kasa bu’dar baki ya gayawa ko mahaifiyarsa, Saboda matarsa ya d’auka mutum, matarsa tafi
su mahimmanci…. Ba ma wannan ba wace Sana’a yake da ta Samar masa ku’di masu yawa haka? Shine
abinda ya fi razana ta.
Bugun da yake mata ne ya isheta don haka a zafafe ta ce “Imaaaam live me alone pls! Ka fice min a gida
kafin na aikata maka komai, me zaka ce mana? Saboda ka auri matar da bata san mutuncin mu ba, matar
da bata daraja mahaifiyarka shi yasa ka kasa gayawa Hajja abin alherin da ya sameka, ka tafi ka yi
rayuwarka da matarka da y’ay’anka bana buk’atar jin komai daga gareka…” Shiru ya yi yana d’an cije
leb’ensa kafin ya ja k’afa ya koma cikin parlorn ya zauna a kujerar da ya tashi idonsa a lumshe. Hannunsa
cikin tarin sumar gashin Kansa ta asalin Fulani mai sulb’i da taushin gaske. Tee ma kenan ta kasa
fuskantar sa balle kuma sauran da suka fita zafin zuciya ya tabbatar Dee sai ta masa marin da ya sai ya
kusa ganin wuta. A yanzu yake ganin wautar sa da bai gaya musu ba tun a farkon fari ya sani yana da laifi
da matarsa ce ka’dai ta san duk wani cigabansa don ko yaransa ba su san komai ba. Hannayensa yake
fusgar gashinsa da su. Idonsa a lumshe yana jin yarda jijiyoyin kansa suka tashi. Bai san tsawon lokacin da
ya d’auka a nan ba ya dai ji an kai glass cup bakinsa. Yana bu’de ido yaga Tee ce a tsaye da cup d’in ruwan
mai mugun sanyi ta kai bakinsa, duk da fuskarta a ha’de take ga idanunta da suka nuna alamun ta yi kuka.
sai da ya saki murmushin k’asan leb’e ya ha’de hannunta da cup d’in ya shanye ruwan tas, dama ya sani
ko kowa ya yi fushi da shi Tee ba zata iya ba…
“Ka bani mamaki Kiddo, kuma zuciyata ta d’au zafi banda Abbansu Haulat ya tunatar da ni abinda na
manta, ya kamata na ji uzirinka na kuma saurari abinda kazo min da shi kafin na zartar da hukunci…
Menene sana’arka kuma ta ya aka yi ka samu wa’dannan mak’udan ku’di haka da mu ba mu san
mafarinsu ba… tunda da kanka ka fa’da rabonka da aikin gwamnati an d’auki shekaru goma balle nace ko
ku’din Albashinka ka juya kake kasuwancin da su? Na san baka da komai don Uban mu bai mutu ya bar
mana komai ba sai tarbiyya da ilimin addini da na boko? Wace Sana’a kake yi Kiddo? Kada dai kace min
rashin jin da ka yi da yarinta shine ya dawo, sana’arka halal ce ko haram? I want to know Kiddo?” Ta fa’da
tana ha’diye wani yawu mai d’aci ga hawaye ba zuba daga kwarmin idonta. Tsoro take ji bata son abinda
zuciyarta take gaya mata ya tabbata… Duk da ko Makaho ya san amsar tambayar koda bai kalli idanun
Moddi ba zai iya gano gaskiyar amsar. Ba sana’ar arzikin da za’a b’oye sai dai idan ta tsiya, tabbas ba
halastacciyar Sana’a Moddibonsu yake yi ba, kamar yarda zuciyarta take sake tabbatar mata don haka ta
sake ware idonta a kansa “Ina jin ka Imaaaam? Ka fa’da min ko na tara Hajja da kafatanin y’ay’anta ka
gaya musu….” Shiru ya mata idonsa a lumshe yana murzar goshinsa murya a k’asa ya furta “Baki yarda
da ni ba Teee…” “Ban yarda da kai ba Moddi, har sai ka sanar da ni sana’ar da ka ke…” “Yankan kai…”
ya fa’da cikin cunkusashshiyar murya kafin ya mik’e yana d’aukar wayarsa ya yi hanyar waje bayan ya
shafa kumatunta “Zan dawo idan kin saka yardar Imam Moddibo a ranki, amma for now ba zan gaya miki
komai ba, don ina hango abubuwa da dama a idonki… Moddibo d’an yankan kai, k’ungiyar asiri.. mai
Fataucin k’waya… mugayen makamai ko kuma Moddibo D’an kidnapping na san ba abinda ba zai zo ranki
ba… nagode sai anjima…” Ya fa’da yana ficewa ya barta da baki sake tana kallonsa zuciyatta kuwa banda
tsalle ba abinda take, da gaske tsoro take ji. Sai da ya isa mota ya shiga ya zauna idanunsa a lumshe ya
ware A.C sosai ya daidaita yanayinsa sannan ya d’au waya ya kira Amani muryarsa a cunkushe ya furta
“Hurry up fito mu tafi…” Ya katse wayar yana daidaita numfashinsa da yake fisga da k’arfin gaske ya cije
leb’ensa su ma kenan sun masa wannan kallon inaga jama’ar gari….
H
Knocking take yi a hankali suna tsaye ita da Haulat amma sam bai ji ba, sai da ta sake bugawa da k’arfi a
fisge ya bu’de lock d’in motar yana zuba mata wani kallo da ya saka hantar cikinta ta ka’da don bata tab’a
ganinsa a irin wannan yanayin ba. Ta shiga jikinta a sanyaye gaisuwar Da Haulat ma take masa bata sani
ba ya amsa ko bai amsa ba ta ji ya fisgi motar da mugun gudun da ya sata runtse idonta don ta san isarsu
gida lafiya k’alau sai abinda Allah ya yi….
ℯ ℯ★✍️ℍℝℕ ♥︎♥︎♥︎
ℯℯ ℯ★✍️
08033748387.
★★★★★ ℊℯ 10.
★★★ ★★★
★★★
A hankali ya lumshe Idonsa yana sakin ajiyar zuciya ya furta “Sana’ata ta Halak ce Hajja…” Hajjan ta zuba
masa ido tana son gano gaskiyar zancensa muryarta a ciki ta furta “Sana’arka ta halak ce, jarinka ne na
haram kenan?” Bai furta komai Saboda wani abu da ya ji ya tsirga a zuciyarsa, tun kafin ma su je su ga irin
gidan da ya gina da company sun fara jero masa irin wannan tambayar a yanzu kam ba shi da amsar da
zai ba su, don bai isa ya kalli Didi ya sanar da ita silar arzikinsa ba. Yana kuma tsoron zuwan ranar da zata
san mafarin arzikinsa. “Ya mayar da mutane y’an iska, ai wallahi Hajja ba zai gaya miki gaskiya ba.
Moddibo ne fa. Moddibon da kika sha fama da shi lokacin samartakarsa, ta yaya mai hali zai fasa
halinsa….” Idonsa ya bu’de akan Dijatu da take fa’dar maganar. Ya tsuke fuskarsa cikin b’acin rai ya yi
k’wafa. Kwata kwata jininsu bai ha’du da Dijatu ba. “A dai bi shi a hankali Adda Dee, In sha Allah zatonmu
ba zai zama gaskiya ba.” Fateemah ta fa’da jikinta a sanyaye don ta san Moddibo tsaf yanzu zai wanke
Dijatu da rashin kunyarsa. Ya mayar da kallonsa kan Fateeman sai kuma ya saki d’an banzan murmushi
mai nuni da alamun ke kika jawo komai ai. Mik’ewa ya yi tsam ya koma gaban Hajja ya kama tafin
hannunta yana matsawa a hankali kamar yarda yake yi a lokacin samartaka idan ya aikata gagarumin lefi.
Hajja ta lumshe idonta tana jin yarda zuciyarta take bugun masifa wanda bana komai ba ne, sai na tashin
hankalin da Moddi ya sata a ciki. Tana tsoron faruwar duk abubuwan da zuciyarta take gaya mata
faruwarsu akan Moddibo. “Kada ki saka komai a ranki Didi, bakomai a yanzu ba zan gaya miki komai ba,
amma na yi alk’awarin idan y’an saka ido ba sa nan zan dawo na gaya miki, ko kuma na gaywa Tee ta fa’da
miki…” “Na fi so ka gaya min da kan ka.” Ta fa’da idanunta zube. A kansa. Ya girgiza kai yana murmushi
ha’de da d’ora kansa a saman cinyarta ta san nufinsa ta saka masa albarka. Don haka ta d’ora hannunta a
gashin kansa ta furta “Allah ya yi albarka Moddi. Ya tsareka daga dukkan abin k’i ya baka Mace ta gari da
zata so ni ta so y’an uwanka burina kenan a kullum.” Addu’ar da ta masa kenan, da take ji kamar a ranta
Allah ba zai amsa addu’ar ba, ko shi yasa ma har yanzu Allah bai mayar mata da Moddin yarda yake ba,
saboda gagarumin lefinsa. Zuciyarta ta raunata Amma bakinta bai fasa furta addu’ar ba, tana fatan kada
Allah ya dubi laifin Moddibo ya yi duba da ita da ta kasance mai rauni. Ameen ya amsa har k’asan ransa
yaji da’din addu’ar Didin. Umma Dee ya zubawa ido da ta ha’de rai kamar zata ha’diye zuciya saboda
tsabar fushi. K’asa-k’asa ya furta “Wanda duk ya ce zai shiga tsakanin d’a da Uwa shine a wahale…” Ta
juyo a zabure tana furta “Da ni kake Moddibo?” Ya d’aga mata girarsa d’aya yana sakin wani murmushin
da ya bayyana rashin jin sa muraran ashe dai Amani shi ta gado. “Kan Uba lallai shaharar taka ta kai
amma zan yi maganinka sabgarka zan daina shiga gaba d’aya don naga ni ka d’auka a matsayin abokiyar
gaba ina matsayin babbar yarka.” Ya d’an tab’e baki yana saka kai zai fita daga d’akin ya ji Didi na furta “A
dai yi hak’uri Addarsu na rasa dalilin da yasa har yanzu ba kwa jituwa da Moddibo kin san halinsa sarai sai
addu’a hayagaga ba zata shirya Moddibo ba…” Fuskarta ta k’ara ha’dewa ta d’au Hijab d’inta ta zura tana
furta “A’a Hajja, ke kike d’aure masa gindi tun yana yaro kin kasa d’ora shi a hanyar da ta dace kullum
shine da gaskiya ga shi nan idan baa yi wasa ba wata k’ungiyar ya je ya cilla kansa ya yi ku’di na ban
mamaki…” Moddibo da yake bakin k’ofa ya jijjiga kansa har da k’wafa ka’dan kafin ya fice daga gidan a
hanzarce don ya san dole da yamma ya isa Abuja yana da gagarumin meeting da Muhammad Alwan…..
★★
Tun bayan fitar Moddi ta saki labulen windown d’akinta tare da sakin ajiyar zuciya. Ranta ya b’aci
hankalinta a tashe ta figi wayarta ta shiga kiran babban bokanta don wannan karan bata bi ta kan Boss
lady ba don abin kunya ne a gareta ta sake gaya musu Moddi ya mata koren kare. Ta da’de tana ringing
kafin ya d’aga cikin bu’daddiyar muryarsa ya ce “An sanar da ni