Showing 36001 words to 39000 words out of 87659 words
Chapter 13 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf
Ban amince ba nafi son a bar min shi haka kamar yarda Uban Moddibo ya bar shi.
Futawar da kai ma Allah ya maka albarka lokaci ka’dan fa ya rage min a duniyar. To na me Zan zauna na
mik’e k’afa na saka jin da’din duniya a zuciyata bar ni a haka zan fi tuna lahirata Moddibo. Ba abinda ya
rage min sai fatan cikawa da Imani. Ina kuma rok’onka ka ci daga halak ka sha daga halak sutura daga
halak ka nesanta kanka da duk wata dukiya da bata halak ba. Allah ya yi maka albarka.”
Ranar kam sun da’de a gidan Didin. Ba yarda ba su yi da ita ba ta je gidan Moddin ta girgiza kai “Ba zani
ba, sai nan gaba in sha Allah. K’arshen sati dai a dinga kawo min su Magajiya don Allah.” A ranta kuwa
sam zuwa gidan Moddi ya fita daga ranta ba don komai ba sai don Matarsa da bata ganin k’imarta da
mutuncinta shi yasa taga gwara ta ja girmanta ba zata zama irin surikar zamani ba mai ja ni in ja da
surikarta ba.
★★★
A kuma wannan lokacin ne Muhammad Alwan ya bijiro masa da buk’atar da ta tayar da hankalinsa ta
kuma saka masa firgici da tsoro. Don idonsa Muhammad Alwan Ya kalla bayan dawowarsu daga tafiya.
Suna zaune a Office. Moddi farin ciki ya isheshi musamman ganin wasu irin makafin ku’di da yake samu
na ribarsa kawai. Ga company mai girman gaske Muhammad Alwan d’in Ya gina da sunansu MODDIBO
CONSTRUCTION COMPANY.. shi kansa Moddibon bai San ana ginin ba. Ruwan tea mai zafi Muhammad
Alwan D’in Ya zuba musu. Sai da Moddibon Ya shanye idanun Alwan D’in a kansa yana ta sakin murmushi
murnar fuskarsa ta k’i d’aukewa. “Akwai tafiya da muka shirya maka da twins d’inka, da nawa yaran,
zamu je su huta for some days tunda kace min suma sun yi graduating ko?” Da sauri Moddi Ya d’aga kai
yana jin farin cikinsa na sake bayyana. “Yauwa Alhamdulillah za su je Turkey zan kai ku garin mu ku gani
daga nan za su je Umara In sha Allah… tafiyar zata zama nextmonth.” Moddi ransa ya yi fari k’al hakan ya
masa da’di sau tari yana son Ya inganta rayuwar su Amanin sai dai haka kawai wani lokacin sai yaji Ya
kasa. Hakan da Alwan Ya masa ya kyauta masa. Ya sake jin k’aunar Alwan D’in a ransa.
Sanda ya koma gida suna zaune da Safna da tabi ta kanainayeshi ta bashi duk wani kayan surkulle a cikin
lemo ya sha. Ya kalleta yana sake nanata addu’ar da take bakinsa da k’yar Ya fisgo maganar da yake ta jin
tsoron fitarta. “Za mu yi tafiya da su Amani…” Safna ta wani irin waro ido, zata fara masifa sai ta tuna
layarta bata kusa don haka ta shanye masifar ranta a b’ace ta furta “Ina za’a da su? Me za su je su yi
gwara mu yi tafiyarmu mu biyu kamar yarda muka saba. Ni America ma nake son mu tafi wallahi,
maganar rashin haihuwa ta da kai ya fara damuna…” Gaban Moddi Ya d’an buga tuna maganin da yake
bata kullum idan yana da buk’atarta Wanda Alwan Ya bashi Ya tabbatar masa kuma in dai tana sha
mahaifarta zata lallace… huci ya fesar ka’dan kafin ya b’ata ransa ya furta “Dole wannan karan da su za’a
je, haka Mai gida Alwan Ya ce ba ni na biya musu ba ma, shine ya biya musu da nasa yaran gaba d’aya…”
Safna ta ha’diye wani kakkauran yawu kafin ta tab’e baki bata sake cewa komai ba jin cewa Alwan ne da
kansa ya ce za su je. Haka tana ji tana gani aka dinga shirin tafiya ba ita. Abin Ya damu zuciyarta Amma
haka ta hak’ura.
Tafiyar tasu ta yi tsaho sosai don sun shafe kusan 50days suna yawo a k’asashe da dama. Su Amani suka
Saba da yaran Alwan sosai. Suka gaisa da y’an uwa sabon da suka yi da danginsu Alwan abin har mamaki
ya dinga bawa Imani. Haka dai suna ji suna gani suka dawo Nigeria. A lokacin ne kuma Alwan ya bijirowa
da Moddi buk’atar da ya ji hankalinsa ya tashi. Yana kurb’ar tataccen inibin kamar yarda shima Moddi
yake kurb’a ya zuba masa ido yana fa’din. “Muhammad Moddibo, lokaci na biyu yazo da zaka cika mana
d’aya daga cikin shara’dinmu….” Moddi ya d’ago yana kallonsa neman k’arin bayani don shi ya manta ma
da wani shara’di banda yanzu Alwan D’in ya fa’da… Alwan ya d’aga masa gira yana murmushi kafin ya
dafa kafa’d’arsa ya furta “Don’t worry my friend ba wani abin tsoro ba ne. As all we know kafin ka yi
signing contract da mu sai da na gaya maka dukkan shara’din zama a cikin mu, ka kuma amince Right?”
Moddi ya ha’diye wani yawu da k’yar yana jin bugun k’irjinsa yana k’aruwa da k’yar ya d’aga kansa. Alwan
ya saki murmushi yana jingina da kujera ya lumshe idonsa yana furta “Our next shara’di shine, as from
today, sau d’aya a sati biyu muka amince ku yi having sex da matarka….. Sau d’aya zaka kusanceta, idan
ka ji ka kasa kuma sai dai ka yi aure, amma wannan kam ta haramta a gareka saboda kamar k’ashin
arzikinka a jikinta yake, to dole da ita zamu dinga nemar maka arziki. Wannan shara’din dole ne ka bi….”
Ya mik’e yana d’aukar phones d’insa ya bar wajen. Moddi Ya bi shi da kallo cikin tashin hankali yana
tunanin ina ya kawo kansa. Ranar dai kam bai San ya aka yi Ya je gida ba.
Safna ta tare shi hankalinta tashe tana tambayarsa abinda ya faru. Bai yi nauyin baki ba ya gaya mata.
Wani irin duka zuciyarta ta yi Cab’di ina zata iya wannan? Moddin da shi ka’dai yake kashe mata
k’ishirwar sha’warta shine za’a bawa wannan shara’din. “Ya tabbatar min dole ne mu aikata haka idan ba
haka ba komai namu zai zama babu” Moddi Ya fa’da yana kafeta da ido. Don shi wannan abin dama ba
wani damunsa ya yi ba, tun bayan rasuwar Uwar su Iman Ya tabbatar Ya yi rashin mata a wannan fannin.
A zabure ta kalleshi ta furta “Haka ya ce.” Moddi ya d’aga kai “Idan baki yarda ba, you can ask him…” Ya
fa’da yana bata compliment card mai d’auke da numbers D’in phones D’in Alwan. Ta dinga kallon card
d’in da ta da’de tana nemansa don son samun numberr Alwan D’in. Murmushi ta saki ta amshi card din
da niyyar zata kira shi. Moddi ya shige d’aki Ya barta a zaune tana danna kiran Alwan.
★★
Daidai lokacin kamar ha’din baki itama Safna tana can zube a saman gado zuciyarta na tuno mata da
hanya mai sauk’i ta ruguzuwar rayuwar Amani, dole ta mik’e tsaye ta cikawa Alwan burinta ko itama nata
burin zai cika, ta San duniya da mutanen cikinta zasu tsani Amani idan suka ji ta nemi mahaifinta da
kanta. Wajen Bokan Neja da zata je Ya zama dole ta bijiro masa da zancen ko da taimakon da zai yi mata.
Zata sakawa a sawa Amanin son mahaifinta kamar ta Mutu da tsananin sha’awarsa Har shi Moddin daga
haka burin ta zai cika. Zata yi amfani da wannna damar wajen mallakar Moddi ita ka’dai, don da zarar ya
bijiro da maganar aure zata sanar da shi zata nunawa duniya vedionsu tsirara da y’arsa suna fasik’anci.
Shikkenan ta jefi tsuntsu biyu da dutse guda. Ta b’atawa Amani rayuwa ta yarda ko Mijin aure bata ji zata
samu….. ta tuno yarda suka yi da Muhammad Alwan a daren da ta je gidansa bayan samun numberrsa a
wajen Moddi…
Sai da wayar ta yi ringing sosai Ya d’aga. Nan ta sanar masa Matar Moddibo ce, Yallab’ai naji wata magana
kuma, ai rayuwa ba zata yiwu ba wannna harkar ba, ina a dai sake wata.” Alwan ya saki murmushi yana
furta “Dole haka ne zai faru. And ina son ganinki ma personally ki gaya min when zamu ha’du?” Wata irin
dariya ta saki ranta fes ta furta “Yaushe kake so?” “Yau da daddare” Ya furta a hankali zan turo Miki
address na gida na.” Farin cikin da zuciyar Safna take ciki ya kasa b’uya. Ba ruwanta wallahi ko me yace ta
yi yi zata yi in dai zai mayar da ita Hamshak’iyar mai ku’di. Ko ta baya zai biya buk’atarsa da ita zata
amince, ba ance yanzu duk da haka ake ku’din ba.
Da daddare wani irin shiri tayi na musamman, ta saka shegun kayan barcinta kafin ta bulbula sihirtaccen
turare a jikinta. Maganin barci ta bawa Moddibo ta fice ba tare da ya sani ba.
Tana shiga gidan ta San ta shiga inda ake kira Aljannar duniya. Burinta da son duniya ta ji Sun k’aru. Zama
ta yi a parlor na musamman da Alwan yasa aka kaita. Tana zama sai ga shi ya fito. Waya a kunnensa yana
magana k’asa k’asa. Tana ganinsa ta saki murmushi kafin ta cire Hijab D’in ta yar. Alwan runtse idonsa Ya
yi kafin ya furta Subhanallah Ya juya da sauri yana furta “Rufe jikinki Madam, ba na kira ki don haka ba
ne.” Jikinta a sanyaye ta rufe jikinta hankalinta Ya yi mugun tashi. Ya zauna fuskarsa a d’aure yana kallonta
Zubewa ta yi a gabansa zata fara bashi hak’uri ya d’aga mata hannu. “Ya isa, ba zan gayawa Mijin ki ba,
but da shara’din nima zaki min abinda nake so, idan yaso daga baya if ina buk’atarki zan gayyaceki yanzu
dai ba don haka na kira ba. Idan kin k’i amjncewa kuma ina da CCTV cameras har a parlorn nan zan
nunawa mijinki abinda kika aikata.” Da sauri ta ce “Ka gaya min ko menene zan maka.” Alwan ya saki
murmushi yana gyara zama ya furta “Na San Mijinki ya gaya miki yarda muka yi da shi yau.” Ta d’aga kai.
“Na San zai Miki wahala Amma ki yi hak’uri for sometimes ne, ina son ki taya ni wani aiki idan har abinda
muke so Ya samu ina tabbatar miki Mijinki zai yi wani irin masifaffen arziki da duk Nigeria ma sai an San
da shi, ba mamaki ma Ya fi ni.” Da sauri Safna ta ce gaya min koma menene wallahi zan saka shi, ko baya
so ko wajen boka zan kai shi.” Alwan ya jima yana kallonta kafin ya furta “Za ki iya saka shi ya kusanci
y’arsa ta cikinsa Amani?” Zuciyarta sai da ta buga, amma da ta tuna maganar ku’di sai kawai ta d’aga kai
“Zan iya koma Uwarsa ne ba y’arsa ba, akwai hanyoyi da dama da zan bi sai hakan ta faru.” Alwan ya
mik’e yana zagayeta kafin ya dure mata akwatin ku’di a gabanta ta Ware ido tana kallon ku’din. Ta ce “Na
menene?” “Naki ne, akwai ni ki su uku idan komai ya tafi successfully. Zan farà bijiro masa da buk’atar
hakan ke kuma ki cigaba da taya ni yak’i. Allah yasa ya amince.” Ta wani zabura tana furta “Dole ne ma zai
amince ko baya so wallahi…..”
★★★
Ya bu’de idonsa a hankali bayan ya gama dawowa daga tunanin mafarin arzikinsa da ya yi. Idanunsa sun
ka’da sun yi jawur. Ya kai dubansa kan agogo jin wani nocking mai k’arfi da ake masa. 4:00 na dare
gabansa ya wani irin fa’duwa haka kawai ya mik’e jikinsa a sanyaye ya na furta waye?” Muryarta can k’asa
da k’yar take fita ta furta “Nice Dahda…” Sake ji ya yi gabansa na tsananta bugu ya saka hannu ya bu’de
k’ofar ya kai idonsa kanta. A firgice take hankalinta a tashe ta furta “Dada na shiga uku……”
★✍️HADARIN GABAS….★
PAGE 15.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
_*BRIGHT PENS...*_
2nd batch
Zazzafar tafiya mai abin ban mamaki, tawayen jerin marubuta huɗu a sabuwar tafiyar ta second batch.
*HADARIN GABAS*
Nazeefah Sabo Nashe
*ƘARFE A WUTA*
Ayushercool
*ZAYTOON*
Zee kumurya
*MUTALLAB*
Nimcyluv Sarauta.
(Book one is free Book 2 and 3 paid. 500 Mutane Na
Musamman cikin aji na Musamman 1k
2118665253 UBA
15.
★★★★
Kallonta yake kawai shima cikin tashin hankalin yana jin duk wata jijiya ta jikinsa tana mik’ewa. Da k’yar
ya d’aga tattausan lips d’insa ya furta “Me ya faru?” Imaan sai da ta ja ajiyar numfashi sannan ta ce
“Amani ce bata da lafiya, she is unconscious….” Tun kafin ta k’arasa ya janyeta gefe da sauri cikin
matuk’ar tashin hankali ya nufi hanyar da zata sada shi da d’akinsu. Tsoro yake ji sosai baya son wani abu
da bai shirya masa ba ya samu Ama d’in…
A durk’ushe take a bakin gadon hannunta rik’e da k’asan cikinta tana mirgina kanta cikin wani hali. Zufa
ko ta ina sai zuba take a jikinta kamar ba A.c a d’akin. Dahda ya k’arasa cikin sanyin jiki kusa da ita yana
furta “Ama… me ya faru?” Jin muryarsa ya sata sake runtse idonta musamman da ya kusanceta ya
durk’ushe a gabanta. Idonsa ya kai kan hannayenta da ya dafe cikin da su. Ya saki ajiyar zuciya yana kallon
Imani ya furta “Period cramps ne ko?” Imani jijjiga kai ta yi tana furta “Wallahi Dahda ba shi ba ne, ina
zaton dai ko Aljannu ne suke son tab’a ta saboda duk dare sai ta yi wani irin mafarki mai nuni da ta na
having se……” “Imaan!” Amani ta fa’da tana d’ago kanta cikin wata irin kakkarwa ta fara girgiza mata kai.
“Bana so kada ki ce komai…” Dahda da ya shiga shock duk da Imaan bata k’arasa abinda ta fa’da d’in ba
ya san ragowar zancenta… Ya rik’e kansa a hankali cikin wani irin matsanancin tashin hankali. Daidai
lokacin ciwon ya sake turnuk’e Amani ba abinda take so irin tabbatuwar abinda yake cikin mafarkinta ta
gan shi a zahiri.. tana son ta ji d’umin Dahdah yana kusantar ta yana mata duk wani hot romance da take
gani a mafarkin ta… Dahda ya dinga kallonta yana observing yanayin da take ciki. Tsoro ne ya kama shi
har ya dinga jin zuciyarsa na wani irin abu. A hankali ya kalli Imaan “Ki matse mata lemon tsami a kitchen,
ki kawo mata da ruwan tea…” Imaan ta mik’e da sauri ta fice don yanayin Amanin itama yana bata tsoro.
Bayan fitar Imaan Dada ya
Janyeta daga jikinsa a hankali sai kuma ya ce..
“Amani ya kike ji?” Ya furta idanunsa a kanta. Cije leb’enta ta yi tana bu’de idonta a kansa sai kuma ta
runtse take fuskar Dahdan ta zame mata irin waccen fuskar da take gani a cikin barci mai nuna mata
tsananin k’auna. Da ciwon ya sake murd’deta bata san sanda ta shige jikin Dahdan ba ta kai masa wata
irin runguma Dahda runtse idonsa kawai ya yi yana jin wata irin kakkarwa da Amanin ta saki a jikinsa
kafin ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe idonta. Sai sannan ta samu sassauncin abinda take ji. Rungumar da
ta yi masa da k’amshin turarensa da ta ji su suka saka ta releasing abinda ke jikinta. Dahda ya dinga
kallonta k’irjinsa na bugu. Ya mik’e yana kallon Imaan da ta shigo da cups a hannunta “Ki bata ta sha, ta
kwanta ta yi barci kuma idan zaku kwanta you make sure kun kunna karatun Alk’ur’ani ku dinga kuma
rufe jikinku, ji fa irin rigar da take jikinta ba dole koma mutanen b’oyen bane su samu mafaka.” Imaan ta
d’aga kai tana sake kallon y’ar ficilar rigar da take jikin Amanin da ta bayyana duk wata sura mai nuna
cikar d’iya mace. Ta gyara mata gashinta sannan ta tasheta zaune. Dahdan yana tsaye yana kallonta abin
duniya duk ya dameshi so yake ya yi nazari ya gano bakin zaren don an zo gab’ar da ya kamata ya binciki
al’amarin mai kama da Almara. Amani kasa ha’da ido da shi ta yi ga kunyar rigar da take jikinta wacce da
ita da babu duk d’aya. Imaan ta sha yi mata fa’dan kwana haka amma bata ji. Dahda ya juya yana fita
daga d’akin da saurinsa.
Tunda ya shiga d’akin bai zauna ba, zagaye kawai yake zuciyarsa cike da tunani… Dole akwai ayar
tambaya me yasa al’amarin yake faruwa haka? Bai bar tunanin ba sai da ya ji kansa yana neman tsawa
sannan ya zauna rik’e da kan nasa yana danna numberr Muhammad Alwan don kamar shi ya kamata ya
tambaya. Me yasa abubuwan suke tafiya a haka kamar wani sihiri? Duk da san dalili. Ya ja fasali a hankali
ganin Alwan d’in bai d’aga waya ba ya saki tsaki ya yi cilli da wayar. A lokacin kamata ya yi ya mik’e ya Yi
sallah sai dai ya kasa. Hannu kawai ya saka cikin sumar kansa yana yamutsawa a hankali.
A safiyar ranar da al’amarin zai faru. Safna..ta ziyarci wani Daji a Bidda da ke jihar Neja.
….. Motar su tana tsayawa a k’aramin Dajin Safna ta saki ajiyar zuciya tana jin tazo inda duk wata
buk’atarta zata biya. Boss lady dai kallonta take tana sake jaddada mata “Ki nutsu Safna ki gaya masa duk
abinda kike so, wallahi aikinsa kamar yankan wuk’a ne.” Ta d’aga kai “Dole ma ai, nifa naga abinda na gani
k’awa. Tsawa fa Moddi yake min kamar ba wanda da yake tsoro na ba. Ba ma wannan ba, ni yanzu burina
na cikawa Alwan buk’atarsa ko na samu ya zube min manyan ku’din da ya alk’awarta min. Idan har na
samu haka wallahi Boss lady ni da duk wani nawa mun yi hannun riga da talauci.
Tunda suka shiga wajen suke jin tsigar jikinsu na tashi sabida wasu irin abubuwa da suka dinga karo da su
a bukkar.
Sun kusan minti biyu zaune kafin matar ta ‘dago da jajayen idonta tana kallonsu. “Mun san
Me ke tafe da ke… Kin yi wani kuskure a rayuwarki, da baki