Showing 48001 words to 51000 words out of 87659 words
Chapter 17 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf
kake so Didi ta ji a sanda ta sameka da wannan laifin?
Zuciyarta zata buga zata samu matsala sosai da lafiyar ta ka sani ko? Me yasa tun kana yaro ka zama Kai
je jarrabawar Didi? Kai ka’dai ne namiji Amma Kai ne kake wahalar da ita, bata Jin da’Dinka ko ka’dan
saboda ka auri matar da za’a kira k’arfen k’afa… Ban San me zan ce maka ba, Ban San wace shawara zan
baka ba….” Ta fa’da tana dafe k’irjinta da ya matsa matsa mata da wani irin bugu. Shi Kansa kasa magana
ya yi bayan idanunsa da suka yi jajur jijiyoyin Kansa suma Sun bayyana tashin hankalin da yake ciki. He
wish ace duk abin nan mafarki yake yi ba gaskiya ba. Abubuwa da dama Sun bayyana Alwan a matsayin
mutumin kirki ba zai ce ya tab’a samunsa da wani mugun abu ba, Amma me yasa ya kasa yarda da shi?
Dole zai saka ayar zargi a Kansa ya kuma zama dole ya raba jiya da shi anzo gab’ar da Sam ba zai iya
mu’amala da shi ba koda hakan yana nufin rasa rayuwarsa… ta yaya zai saka masa sha’awa da son
yarinyar…. Sai ya datse leb’ensa da k’arfin gaske yana Jin takaicin abinda yake ji d’in yana saka jikinsa
wani irin zafi kamar mai zazzab’i da sauri kuma a wani irin fisge ya mik’e ya nufi k’ofa dole ne ma yaga
Alwan a Daren nan ya gaya masa ba zai iya ba, ba zai iya aikata abinda yake so ba, sannan daga yau kuma
ya bar harka da shi koda zai mayar da shi bashi da komai ne…. Duk da kiran da Teey take masa bai juya
ba. Ta runtse idonta bayan Jin fisgar motarsa da k’arfin gaske. Ya Ilahil alameen! Fateema ta fa’da tana
runtse idonta… zuciyarta na cigaba da wani irin matsanancin bugu…
(Masu tambaya Hadarin gabas Free ne? Aa ba free bane, book 1 ne free book 2 and 3 paid ne. A saka
ku’di ta wannan account ‘din 2118666253 UBA. 500 mutane na musamman a cikin gida na
musamman 1k ne as Usual. Na gode k’warai.
Hadarin gabas zai zubar da ruwa mai tarin yawa biya ku’dinki ba zaki nadama ba, baa fara komai a labarin
ba duka wannan sharar fage ne……
JIKAR NASHE✍HADARIN GABAS……..
PAGE 19.
08033748387.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
Ko gida bai je ba, ya nufi Airport direct saboda sometimes haka kawai yana siyan ticket ma ya yi booking
koda ba tafiya zai yi ba saboda irin wannan tafiyar ta afujajan. Bai nemi ko driver ba, haka ya ajiye motar
a parking space na airport d’in ya zura key d’insa a aljihu. Ma’aikatan airport d’in sai gaisuwa suke kawo
masa, ba ya cikin sukunin da zai iya yi musu kyautar da ya saba musu ta bajinta, don haka kawai d’aga
musu hannu yake, a fuskarsa suke hango damuwa don haka basu damu ba musamman sanin cewa ba
halinsa ba ne. Ya ci mugun sa’a har an fara boarding jirgi ya shige direct zuciyarsa na wani irin hucin
b’acin rai, tana kuma bugawa da k’arfin gaske. Burinsa ganin Alwan ya
Kuma yi baran baran da shi, ko zai cire musu k’ullin da ya k’ulla tsakanin sa da Amani. Tunda suka shiga
jirgin har jirgin ya tashi idanunsa a lumshe suke, bai kuma bu’de su ba kamar mai barci sai dai ba barcin
yake ba tsabar damuwar da ta cika masa zuciya ne yasa baya buk’atar ganin komai. Yana jin ana
tambayarsa ko akwai abinda yake so, idanunsa a lumshe ya girgiza kai. Duk da yana buk’atar ruwa yana
buk’atar ya sha ruwan ko don yarda mak’oshinsa ya bushe sai dai b’acin ran da yake ciki ba zai bari ya sha
ruwan ba. A haka dai Allah ya taimake shi jirginsu ya yi landing a Nmadi azikwe airport ba tare da
zuciyarsa ta tarwatse ba. Sai da ya bari aka gama turmutsutsun fita sannan ya bu’de lumsassun idanunsa
da suka masa wani irin masifar nauyi da yake jin su sosai. Hannu ya saka ya ciro black shade d’insa da
baya rabo da shi ya saka a fuskar tasa, yana sakin ajiyar zuciya muryarta a kunnensa kamar yanzu ta masa
furucin “Dada you look gorgeous in your new Shades, pls kana sawa kullum….” Daga ranar kuwa bai fasa
saka wa ba tunda ta furta ya kuma siyo irinsu da dama duk ba don komai ba don Ama ta ce ya yi masa
kyau. Girgiza kai ya yi sau tari ya kan yi abinda take so ko da shi baya so hakan ya zame masa dole. A
hankali ya fita daga cikin jirgin. Sai sannan ya tuna bai sanar zai zo ba don haka ba wani driver da zai gani
balle guards d’insa. Ya d’au wayarsa kawai ya kira Bold, ya san kafin ya fita Bold d’in tazo ba zai iya jiran
Drivernsa ba duk da yana da su kusan guda hu’du. Zuciyarsa a k’agauce take da son ganin Alwan, He is
eager to see him. Yana fita kuwa ya ci sa’a Bold ta zo don haka yana shiga ya fa’da masa inda zai kai shi.
Companyn Alwan ba wani b’oyayye ba ne don haka ba Wanda bai San Turkey group of Companies ba
saboda girmansa da shahararsa.
Suna parking ya fita bayan ya cikawa drivern ku’din da shi kansa bai San ko nawa ba ne. Ya zura hannu a
aljihu yana tafiya cikin wani irin taku mai bayyana jarumtakarsa ta d’a namiji a yarda yake jin zuciyarsa
yau ko dambe da Alwan ne zai iya yi don ya rabu da shi ya kuma cire dabaibayin da ya saka ya na’de shi
shi da Amani. Yana tafiya yana tuno ranar farko da ya fara zuwa companyn cikin murna da zakwa’din
zama matashin mai ku’di, ashe zai dawo shi cikin bak’in ciki da tarin dana sanin ha’duwarsa da Alwan. Bai
wani jira an masa iso ba, saboda ba wanda bai san shi ba a companyn ba kuma wanda bai San girman
matsayinsa a wajen Alwan ba. Ya tura babbr k’ofar glass d’in da zata shigar da shi Office d’in. Alwan ya
d’ago yana kallonsa fuskarsa cike da murmushi bai yi mamaki ba don ya san dole zai kawo kansa duk da
k’ok’arin guje masa da yake yi gashi nan kuwa bai kira shi ba bai yi komai ba ya kawo kansa.
Tun Moddi bai yi magana ba Alwan ya kalleshi cikin ginshira ya ce “Ka gama Hide and seek d’in
Moddibo?” Moddi cikin b’acin rai ya dinga zuba masa wani irin kallo bai ce komai ba. Alwan ya mik’e
yana murmushi ya fara zagaye shi ya ce “I know dole ranar nan zata zo, sai dai ta yi saurin zuwa. Me yasa
ka fara regretting tun yanzu? Alhali baka gama fulfilling mana promise d’in mu ba, don’t put your self into
trouble Moddi think twice before decides….” A wani irin zafin zuciya Moddi ya isa gabansa ya ce “Yes I
regret meeting you Alwan, a yau kuma na zo ne don na gaya maka Am no longer with you… ina buk’atar
ka cire hannunka a kai na, ka cire abinda ka k’ulla a kai na da y’ata… bana son arzikin ko zan koma inda
nake da, na fi farin ciki fiye da wannna tashin hankalin da kake so ka sani… ba zan yi abinda kake so ba,
ba zan yi zina da y‘ar cikina ba…” Alwan Ya isa har inda yake yana sake jifansa da murmushi ya ce “You
loose your opportunity tunda tun farko sai da muka gaya maka shara’din mu kuma ka amince…” “sai na
ce maka na yarda zan yi zina da y’ar cikina?” Alwan ya girgiza kai… “Choice biyu fa aka baka idan ba zaka
iya wannan ba ka yi wancan mana,….. it’s simple as Abcd fa…” wani kallo ya watsa masa da birkitattun
idanunsa kafin ya datse leb’ensa ya ce “I said bana son dukiyar ko dole ne? Ku amshi duk abinda kuka
min silar samunsa ku bar ni da rayuwata wannan wace irin masifa ce? Sanda muka ha’du da kai ai baka
gaya min dukiyar ka ta haram ba ce….” Alwan a fisge ya ce “Who told you dukiyar haram muke da ita?
Kai da kanka ka San k’aryar ka ka kira dukiyar mu ta haram…” “To ta halak ce?” Ya fa’da yana masa wani
kallon rainin hankali “Idan Har ta halak ce while all those things? Me yasa kuke neman abinda yake kun
san aikata shi ba daidai ba ne?” “Menene ba daidai d’in ba wancan ko wannan?” Sai ya yi murmushi
“Don’t deceive yourself Moddi, ni da kai mun san Wanda yake haram da Wanda yake halal so idan ba
zaka iya haram d’in ba go to halak d’in mana simple Man…” Moddi ya runtse idonsa yana dunk’ule
hannunsa yana jin kamar ya kaiwa Alwan naushi jikinsa har rawa yake musamman jin hannun Alwan d’in
a saman kafa’dunsa yana girgizawa ya ce “Mr. Man ka tafi ba abinda zai canja daga abinda shigaba take so
dole ne haka zai faru whether you like it or not so kawai ka yi hak’uri wishing you best of luck…..”
Daga haka ya fice daga Office d’in Living Moddi cikin wani irin yanayi da ya tabbatar idan ya cigaba da
tsayawa Moddin zai iya masa duka. Yana dariya k’asa k’asa ya rufe k’ofar…. K’arar rufe k’ofar ne kuma ya
dawo da Moddi cikin hankalinsa ya bu’de idanunsa da suka birkice cikin wani launi ya zubawa k’ofar ido
yana datse lips d’insa da k’arfin gaske kamar zai huda su. Hannayensa cikin gashin kansa yana birkitasu
kamar zai cire sumar…. A hankali ya furta “Kai No Impossible wallahi even if it means everything…….”
Shima ya fice a mugun fusace burinsa ya tarar da Alwan sai dai bai gansa ba ko Inuwarsa bai gani ba ga
companyn da girma ba lalle ya san inda ya shiga ba. Don dole ya zauna yana kiran wani Bold d’in da zai
kai shi gidansa na Abuja ya kwana a can bayan ya turawa Safna message yana Abuja ba zai dawo ba sai
gobe. Ya kashe wayoyinsa gaba d’aya nutsuwa yake buk’ata nutsuwar zuciya da ta gangar jiki Wanda zai
bashi damar yin tunanin da ya dace ya samo mafita tun kafin Didi da kowa ma su fuskanci halin da yake
ciki tunda gashi Fateema ma ta fara fuskantar abinda yake ciki, ita kanta yarinyar ta fara feeling abinda
shima ya jima yana feeling wannan wane kalar abin kunya ne yake neman aikatawa wanda duniya zata yi
tur da shi wane kallo duniya zata masa? Ba wanda ya jefa shi cikin wannan matsalar sai Safna da ta dinga
nuna masa ba wani abu ba ne shi kuma kamar idonsa ya rufe ya dinga bin duk abinda ta ce masa. A
daren ranar kam sam bai runtsa ba mafita kawai yake nema kuma ya samu… aurar da Amanii zai yi cikin
lokacin k’ank’ani… kafin ta kai shi ga aikata abinda zai zo ya ji da zamansa a duniya gwara mutuwarsa duk
da gefe guda yana sanar masa ba wani abu ba ne kuma akwai hanyoyi da dama da zai bi Wanda ba lallai
a gane ba. Amma ba zai yi ba ba zai aikata d’in ba ne ba kuma yaso Alwan ya ci galaba a kansa.
……. Da matsanancin ciwon kai ta tashi ciwon kan da ta dinga jin kamar zai zama ajalinta. Da k’yar ta
bu’de ido tana kallon Imani abin mamaki yau koda wasa bata yi wancan kalar mafarkin ba, wani abu da ta
Lura da shi in dai bata gidansu bata yin mafarkin, a gidan nasu in dai Dada baya gari baya kusa da ita bata
jin k’amshin turarensa bata fiye yin mafarkin ba. Ta saki ajiyar zuciya a hankali tana zura k’afarta k’asa
Iman da take zaune ta zuba tagumi ta juya tana kallonta fuskarta d’auke da damuwa ta ce “Sannu kin
tashi?” Amani ta d’aga kai tana mik’ewa a hankali ta shige toilet wanka take son yi ko ta ji sauk’in abinda
take ji cikin ranta. Har ta fito daga wankan Imani na zaune inda ta barta kallonta ta d’an yi sai kuma ta
furta “Me ya faru Half?” Imani ta sauke ajiyar zuciya tana mik’ewa ta ce “Nothing Half, am just missing
Mameey da tana nan da wannan abin duk bai faru ba, ni na San tabbas wannan abin ba haka kawai yake
faruwa ba akwai wani abu a k’asa something da Allah ne ka’dai ya barwa kansa sani sai dai ina addu’a
koma menene Allah yasa k’arshensa ne yazo. Ki shirya ina k’asa ki gaida mutanen gidan tun jiya fa baki
sake sauka ba.” Amani ta d’aga kai tana jin wata k’walla na shirin zubo mata ta yi saurin mayar da ita. Ko
man bata Shafa ba ta zura wata riga simple ta Haulat ta kama kanta ta d’aure da ribbon ko taje shi bata yi
ba don irin mai mugun santsinnan ne sai shinning yake irin dai gashin asalin fulani. Fuskarta fayau ta zura
hula ta fice. So take ta yakice abinda yake cikin ranta itama ta yi rayuwa irin ta kowa ta samu sauk’in
zuciyarta. Don haka ta aro fuskar walwala as usual dama ita bata fiye b’ata rai ba ko yaushe fuskarta
d’auke take da murmushi don haka ake saurin ganewa in dai tana cikin damuwa. Silifas mai taushin gaske
ta zura a k’afarta ta sauka zuwa downstairs d’in. Idanunta akan mutanen parlorn da suke zube suna
breakfast saboda ranar weekend ce ba makaranta sai Islamiyya ita kuma sai after zuhr suke tafiya. Umma
Teey ta dinga kallonta fuskarta cike da tausayin y’an biyun nasu. Sai kuma ta mik’a mata hannu tana furta
“Taho nan Amani, zo ki zauna ki ci abinci ina lura da ke tun jiya baki ci abincin nan ba.” Ta k’arasa jikin
Umma T da takewa kallon Uwa. Abincin Umma T ta zuba mata ta tura mata gabanta tana furta “Na ga
kwano yanzun nan…”Burhan d’anta na farko da zai auri Imaan yana dariya ya ce “Gwara dai wallahi ki
fara mata d’ura don wannan ku kaita gidan Mahmud a haka b’al zai b’allata yarinya kamar sillan kara…”
Harara ta zuba masa zuciyarta na wani irin bugu ambatar sunan Mahmud a matsayin mijinta da ya yi, da
gaske bata son Mahmud kuma bata tab’a jin son nasa ba, amma dole haka zata aure shi. Cikin son kawar
da damuwar da Umma Teey ta gani a tare da ita ta ce “Ai hakan ya fi, kai dai kaje ka ji da y’ar lukutar
Imaninka da kullum take zama kamar ana hurata kai k’iba ita k’iba zan ga wani kalar yara zaku haifa….”
Iman ta yi saurin mik’ewa ta bar wajen tana dariya kunya duk ta bi ta cikata. Umma Tee tabi ta da kallo
tana murmushi ta furta “Just like Mahaifiyarta Allah y’a gafarta miki y’ar riga da tana raye da duk Kiddo
bai shiga wannan matsalar ba idan bata kusanta shi da mu ba, na tabbatar ba zata wargaza zumuncin mu
ba, balle wannan matsala mai girma ta rufto dole zata saka Moddi a hanya…” Ta fa’da tana ha’diye
sauran maganar idanunta na ‘disar da k’walla da alama lamarin Kiddon nata yana damun zuciyarta…
Amani ma hawayen take kewa da k’aunar mahaifiyarta yana sake narkar da zuciyarta. Abincin da ta kasa
cigaba da ci kenan sai tea da ta dinga Kurb’a shima tana jinsa kamar magani.. da k’yar ta sha half cup ta
ajiye kawai tana saka kanta a saman kafa’dar Umma Teey d’in idanunta a lumshe ta ji sallamar Mahmud
da sauri ta bu’de idon nata ta saka a cikin nasa so take ta ji ko zata ji irin abinda take ji idan ta ga Dada, a
fisge Mahmud yana kama da Dada kowa yana fa’da. Yana sakar mata murmushi ya isa ya zauna sai dai
Amani bata ji
B’urb’ushin sonsa ba ko ka’dan bata ji kuma heartbeats d’in da take ji ba idan taga Dada. Ya zauna yana
furta “Alank’osa so kike dai ki b’alla wa Umma Teey k’afa.” Ta gyara kwanciyarta kamar bata ji me ya ce ba
ta sake lumshe ido tana shak’ar k’amshin turarensa tana son ta ji ko zata ji abinda take ji idan ta ji
k’amshin turaren Dada Amma bata ji komai ba sai ma ji da ta yi kamar tana jin rashin da’din turaren…..
Mahmud ya gyara zama yana furta “Umma Teey
Maganar lefe fa nazo mu yi da ke bana son na bawa Umma D a samu matsala kin san halin yayarki….”
Gaban Ama ya fa’di ta mik’e tana rangaji da niyyar barin parlorn don sam bata son maganar lefen… da
auren ma gaba d’aya. Numfashinta ne yaso d’aukewa ganin Dada ya bu’de k’ofar ya shigo cikin wani irin
lafiyayyen farin yard da ya kwanta a jikinsa luf hannayensa sanye a aljihu sai zabga k’amshin turarensa
yake. Kansa kuwa ba hula hakan ya bawa gashinsa damar k’ayata kwalliyar sa bak’i si’dik da shi sai
walwali yake da tsilli tsillin furfura a kan nasa ka’dan. Ya zuba mata ido ba tare da shi kansa ya san yana
kallon nata ba… “Kidddo…..” Fateema ta furta cikin wata irin murya da ta dawo da su cikin hankalinsu.
Mahmud kansa kallonsu yake yana mamakin yanayin kallon da suke wa juna kamar dai…..
JIKAR NASHE✍HADARIN GABAS……
Page 20.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
(Book 1 ne free, Book 2 and 3 paid ne… to subscribe pls contact 08033748387.)
Ko da ta koma gida ba ta yi wani jinkiri ba, ta ha’da maganin a cikin cup. Kallon cikin cup D’in take mai
d’auke da madara fara k’al ba ta yarda za’a yi ka ce akwai wani d’ison magani a cikinsa. Murmushi ta saki
irin murmushin da yake bayyana muguntar mutum. Sannan a hankali ta k’walawa Imani kira. Imaan da
sauri ta amsa kiran kafin