Showing 12001 words to 15000 words out of 87659 words

Chapter 5 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf

a wajenki…” “Yana son ki
dai, ni ba ya wani sona ba tun yau na yi noticing haka ba..” ta Mik’e a zafafe ta shiga ha’da kayanta “Zan je
na gayawa Didi zan kuma koma gidanta ita ka’dai ke so na kowa ma laifi na yake gani, kun manta ba
laifina bane haka Allah ya yi ni…” Ta shiga ha’da kayanta a akwati Imani tana rok’onta ta bari taje ta bawa
Mommy da Dahda hak’uri wani kallo ta mata tana furta “Na bawa wannan matar hak’uri akan me? Over
my dead body wallahi, ke dai da ta mayar sokuwa ki je ki yi ta biye mata…” ta ja akwatin da sauri ta fice
daga d’akin bata kula kiran da Imani take mata ba..


A babban parlourn ta gansu a zaune Mommyn ranta fes ta kalleta da akwatin ta a ranta tana furta “Kin
tafi kenan yarinya in dai ina gidan nan ba zaki tab’a zaman lafiya da ubanki ba, har y’ar Uwar taki sai na yi
silar da zaku koma gidan jarababbiyar tsohuwar nan…” Dahda dai ko kallonta bai yi ba yana ji ta bu’de
k’ofa ta fice Iman zata bi ta yasa baki ya kirata “Koma ciki..” Turus ta yi tana kallon Dahdan ta furta
“Dahda titi ta fita fa, bata jira driver ba..” “And so what? Ai ta girma she can do what ever suits her….” Ya
cigaba da kallon T.V d’insa kamar ba abinda ya dameshi sai dai a k’asan ransa haushin d’abi’un Amani ne
yasa yake gallaza mata ba don baya sonta ba, ya lura idan ba haka yake mata ba she never change her
habits.. Imani jikinta a salub’e ta shige d’akinsu tana kallon yarda Mommy fuskarta ta kasa b’oye murnar

da take ciki sai girgiza k’afa take kafin ta ji muryarta tana furta “Ka burge ni Imaam, idan ba haka ake wa
Amani ba ba zata saitu ba yarinyar kamar mai iblisai…” A fusace ya zuba mata wani kallo “Don’t
repeat…” ya danne sauran maganar bayan ya mik’e a zafafe ya bar mata wajen. Mommy ta bi bayansa
da harara tana tsaki k’asa k’asa bata san me yasa malamanta har yau sun kasa aiki akan gayen nan ya
tsani y’ay’ansa ba. Ita kanta wani lokacin idan ya mur’de mata sai taga kamar ba Imaam Moddibo ba.


Yana shiga d’akinsa ya zauna gefen faffad’an gadonsa da ya sha shimfi’da mai taushin gaske. D’an haki ya
sauke kafin ya rik’e kansa a hankali ya furta “Amani why?” Sai kuma ya ja guntun tsaki yana mamakin
yanayin tsiwar yarinyar da rashin tsoro ko na misk’ala zarratin a tattare da ita. Shi da kansa wani lokacin
yana shakkar matar tasa, don dai namijin gaske ne da
Baya d’aukar raini ko ka’dan, banda Amani da tun lokutan yarintarta bata raga mata ko ka’dan. Ya girgiza
kai a hankali yana furta “Allah ka shirya mana.” Sau tari ya kan yi tunanin wani irin zaman aure Amani
zata je ta yi a gidan Mijinta da wannan tsiwar baki kamar parrot. Wayarsa ya yi saurin janyowa ya fara
kiran Idi driver don sai yanzu ya tuna gangancin da ya aikata Amani bata shiga motar haya me ya rufe
idonsa ya turata gidan Didi ita ka’dai? Tsoro ya shige shi a gaggauce ya yi dialling call d’in Idi driver. Tana
shiga ya d’aga “Ka bi Amani maza hanya ka kaita gidan Didi.” Ya fa’da yana zare wayar a kunnensa ba tare
da ya amsa gaisuwar Idi Drivern ba..




A guje Idi yake driving har ya samu ya cimmata a gefen titin sai fama take da akwati kici kici, don sam
Amani sai tsiwar amma bata da k’arfi ko ka’dan to ina ma ta ci abincin arziki balle ta samu k’arfin. Kuka
take son yi musamman ganin inda duk ta wuce idanu a kanta masu motoci sai tsayawa suke don su rage
mata hanya, ta ha’de ranta tsam kamar bata tab’a dariya ba. Zata iya cewa bata tab’a shiga motar haya
zuwa ko ina ita ka’dai ba don haka ta rasa ma ya zata yi. Hawaye kawai ta ji ya fara zubo mata tana sake
tsinewa Mommy a ranta. Jin horn da ake bai saka ta ta juya ba, don a zatonta mutanen da suke ta
tsayawa don su rage mata hanya ne. Har sai da ta ji Muryar Driver yana furta “Hajja k’arama, ki shigo in ji
Alhaji na kai ki gidan Hajja Babba…” ta d’ago ranta a b’ace kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta turo
bakinta ta furta “Just go Baba, zan tafi da kaina..” ta cigaba da tafiya ba yarda Drivern bai yi ba akan ta
shiga ta k’i har ya gaji ya kira Moddi. Jin abinda ya ce Moddi ya saki k’aramin tsaki ya furta “Give her the
phone, bata wayar.” Kamar ba zata karb’a ba sai dai ta saka hannu ta karb’i wayar ta kai kunnenta “Ki
shiga motar nan before I knock your head.” Haka ya furta cikin Murya mai tsaurin gaske.. “Da….” “I said
Enter the car..” Ya katseta ba tare da ya bari ta k’arasa maganar ba. Idanunta ne ya kawo ruwa ta shiga
motar da zafin nama ranta a b’ace. Idi ya shiga ya tayar da motar yana furta “Sai hak’uri Hajja K’arama, in

dai aka ce yaro maraya ne yana rayuwa a koma ina ne sai ya yi hak’uri Allah yaji k’an mahaifiyarku
mutuniyar kirki.” “Ameen ta furta tana lumshe idonta ta jingina da jikin kujera. Haka kowa yake ce mata
amma ita ta kasa yarda, ba yarda za’a yi don uwarta bata raye a dinga takata
A gidan Ubanta ta hak’ura ina wallahi ba’a yi mata ba. Hawayen da ya fara zubo mata ta saka tissue ta
goge don ma kar a cigaba da ganin gazawarta..




A k’ofar gidan Didin ya tsaya babban gida ne irin ginin zamanin da don Didin sam ta k’i yarda a yi
renovating d’insa daga waje. Babu gate a gidan sai maka makan zaure. Daga wajen gidan kuma akwai
bishiyoyi guda biyu na guava da na mangwaro. Sai garejin ajiye mota guda d’aya.


Zaure uku zaka wuce kafin ka isa faffa’dan tsakargidan da ya ji malalan suminti mai santsin gaske tun na
zamanin Da don shima Didi ta k’i yarda a zamanantar da shi ta ce ba za’a canja mata fasalin gida daga
inda Uban Moddibo ya bar shi ba, ba za’a kawar mata da tunaninsa ba a goge memory d’insa. Bishiyu ne
a tsakar gidan guda uku maka-maka, daga gefe can kitchen ne irin dai namu na gargajiya.


Parlourn Didin jibgegene d’auke yake da wani carpet mai taushin gaske a saman carpet d’in kuma
Dadduma ce ta manyan
Mutane sai tun-tun da aka zagaye parlorn da su ba kujera a parlourn. A jikin bango kuwa T.V ce plasma
babbar gaske ita ka’dai ta yarda a sabunta mata da ta Zamani don Didi akwai son kallo. Amma daga gefe
ga ta Uban Moddibo nan da ya bar
Mata gado. Da radio irin ta da babba.


A zauren da zai sadaka da cikin gidan Amani ta ja tunga da akwatin ta ta tsaya ta daddage ta rusa ihu..
“Na shiga Uku Didi na, Dada da Safna suna shirin kasheni don an ga bani da Uwa wayyo Allah na….”

Hajja Didi da tada sallahr azahar d’inta kenan ta yi saurin sallame sallahr ta fito a guje tana furta “Wa
nake ji haka kamar muryar magajiya Uban waye zai kashe kin?” “Buzuwa da Mijin Buzuwa…” Amani ta
amsa mata da irin sunan da take kiran Moddibo da matar tasa.. Didi ta ce “Jar uba, to shigo magajiya in
dai ina raye ba mai tab’a ki ya kwana lafiya mik’o min Salula ta ki kira min Mijin Buzuwar na ji dalili….



JIKAR NASHE✍HADARIN GABAS….

NAZEEFAH SABO NASHE.★✍️


�ℯℯ� ���ℯ✍️


08033748387.

★★★★★ �ℊℯ6️⃣




——-
Salular ta mik’a mata sai kuma Hajja Didin ta wurga mata harara tana furta “Duba kiga zaki ga k’wallo
guda shidda itace lambar Uban naki..” Amani ta kuwa duba sai ta ga an yi saving da hotunan ball guda

shidda murmushi ta saki wato ta inda Hajja Didi take gane numberr yaranta kenan. Dahda shine d’a na
shidda a wajen Didi ya biyo bayan mata biyar cur! Ta danna numberr kafin ta saka a handsfree don ta san
a haka Didin take waya. A duk sanda zata duba wayar sai Didi ta canja wani abin da yake banbanta mata
yaranta. A da tambarin hula ce alamar da take gane Dada, yanzu kuma ta
Mayar da shi 6Balls.


Dahda da yake tsaye kan Imani da take wani irin kuka ya kai dubansa kan wayar hannunsa yana d’an tsaki
“Ba zaki min shiru ba ne?” Ta yi k’asa da kanta kawai ba don ta daina kukan ba still idanunta na zubar da
hawaye. Yana ganin numberr First Love kamar yarda ya yiwa Didin saving ya d’an saki guntun murmushi
don ya san yau kam tunda ya tab’a Magajiyar Didi ba zaman lafiya. Wayar ya kara a kunnensa yana k’asa
da muryarsa kamar yarda ya saba “Hajja Didi….” “Tsaya Moddi ban buk’aci gaisuwarka ba, Uban me
Magajiya ta yi ka koreta daga gidanka?” Ya d’an fesar da hucin numfashi yana murza goshinsa abinda ya
zame masa al’ada, sannan cikin wata murya da bata fiye fita sosai ba ya furta “Bata gaya miki irin rashin
kirkin da take a gidan ba? ta fitini kowa ita shikkenan ba zata zauna lafiya ba?” “Bata gaya min ba, ba
kuma na buk’aci a gaya min d’in ba, yo Ai yarinta ce kuma kowane yaro da irin yarinyartarsa abu guda da
zan gaya maka ana iya canza mata banda d’a balle kai da sukkenan k’walli biyu Jalla ya baka, a haka ya
kamata ka kula da su? To kazo yanzu ka d’auketa Ai na sha gaya maka ba ta yarda za’a yi kana raye ace
y’ay’anka ba zasu zauna a gidan ka ba saboda son zuciya irin na matarka to bata isa ba gida dai gidan
Ubansu ne sai dai ita Buzuwa ta fice fit daga gidan. Mintuna ashirin na baka kazo ka d’au Magajiya Ka
mayar da ita gida….. Zan kuma zo har gidan na ja kunnen buzuwa..” Daga haka ta zame wayar a
kunnenta ba tare da ta kasheba don yana jin ta ta ce “Yi shiru kin ji Magajiya yanzu zai zo ya
Mayar da ke, ba a yi matar da zata hanaki zama gidan Ubanki ba..” “Ni gaskiya ki daina ce min Magajiya,
Ni wallahi Dahda ya cuceni da ya saka min sunanki…” “Ai inye ni kike gayawa haka? Bayan na gama
kwatar miki y’ancinki yanzu..” Dahda da yake jin komai ta cikin wayar ya saki murmushi a zuciyarsa ya ce
da’din abin kema bata kyaleki ba. Wannan yarinyar lamarinta sai addu’a sai kace Mai jinnu. Ya saka wayar
a aljihunsa yana kallon Imani ya ce “Sai ki rufe min baki yanzu zan je na d’aukota ke kanki wahalar da ke
take amma koda yaushe kin fi son ki Ganki a tare da ita. Ya saki tsaki yana furta ranar da aure zai rabaku zan ga ya zaku yi?” Iman dai
murmushi take sai a lokacin hankalinta ya kwanta jin zaa d’auko mata Amanin. Ta bi bayan Dahdan da
kallo da ya fice cikin shigar black
Jallabiya da ta masa kyau sam ba zaka ce Dahdan ya diresu ba wani irin murjajjen jiki ne da
Shi mai kyan gaske da kullum baya tsufa ko don abin ya ha’du da arziki ana kuma cin mai kyau… Ta shige
kitchen don k’arasa abinda take ranta ta furta “Saura Inna Talatu In sha Allah itama sai ta dawo a yau.”

“Ta kori Inna Talatu ma ta ce a yau ta bar mata gidanta.” Didi ta ware ido tana furta “Ita buzuwar? Eeh to
lallai lamarin nata azimin ne, ban san sanda da na haifi Moddibo nace mata na bar mata shi ba? Irin
wannan iko haka da k’afafa sai kace ita ta min wahalar Moddibon? To Bari yazo na ji ko shine ya sahhale
mata ta dinga ikon da ta ga dama a gidan. Talatu kam ko bayan raina ba zata bar gidan Moddibo ba,
matar da tun daga k’uruciyarta take wahala da ni sai kawai don Moddibo ya yi arziki ya auro Hurul aini sai
ta koreta bari yazo na ji dalili?” Amani ta saki murmushi don ta sake kunna Didi ta furta “Didi wai wacece
Uwargida ne da Mamanmu da Buzuwa?” Didi ta saki tsaki don ko zancen bata so ta furta “Allah dai ya
gafartawa Uwarku mace ta gari salihar baiwa. Ita mai sunanta Ai kwafinta ce kwabo da kwabo Ke kuwa
ba wanda kika gado sai Dijatu itace na sha wahala da ita tana yarinya kai Allah dai ya yafewa Dijatu amma
ta yi abin da tayi lokacin yarinta shi yasa nake cewa Moddi ya k’yaleki kema zaki daina duk da har yanzu
idan Dijatu ta tubure sai kowa ya ji a jikinsa… Sallamar Dahda ce ta katse musu hirar. Didi ta amsa a
k’asan mak’oshi Amani kuwa ido ta zuba masa tana hango yarda ya gimtse fuskarsa kamar bai tab’a
dariya ba. “Tashi Magajiya ki samo masa bulala don a fuskarsa na hango so yake da ni da ke ya rufe mu
da duka, idan banda haka meye na shigowa fuskarsa a turb’une kamar dai an sanar da shi na mutu…”
Moddi d’an murmushi ya yi ya zauna a gefenta yana kama hannayenta ya furta “Allah ya rufa min asiri ba
dake nake ha’da rai ba, ni ba zan dakeki ba amma idan aka cigaba da tafiya a haka Magajiayr taki tana daf
da fara dukan mu ni da matata…” Didi ta ware ido tana furta “Allahumma ajirni! Mugun fatan da kake
mata kenan, to ba zan ga wannan ba, d’a dai kiwonsa Allah yake bawa Bawa, idan ka k’i kula da shi Allah
kai zai kama, kuma gida ba zata bar shi ba tunda gidan Ubanta ne ba na Uban buzuwa ba, don haka ka
d’auketa ku tafi a yi ta mata addu’a kurwar Yayarka Dijatu ne a tare da ita…” Moddi ya wara ido jin
abinda ta ce ya furta “Wallahi Didi ki bar maganar nan anan Kada Adda Dija ta ji ki…” “Ba zan bari ba
Dijan Uwata ce? Ai ba k’arya na fa’da ba, ba ta inda ta baro kaf halayenta, sawunka a likkafa ka d’auketa
ka bar min gida…idan ta gagareka ka kaiwa Dija ita nima ba zan iya ciwon kai ba..”
Amani ta zuba mata ido tana turo baki ta furta “Ni nake saki ciwon kai kenan? Kuma wallahi sai na
gayawa Umma Dee abinda kika ce mata.” Didi ta sake ha’de fuska duk da a ranta ta ji d’an fargabar a
gayawa Dijatun abinda ta ce sai dai bata nuna ba, ta furta “Ki gaya mata d’in tsoronta nake? Uwata ce
Ko Ubana ko kuma ita d’in ta maye gurbin Uban Moddibo ne?”
Shi dai Dahda a k’asan ransa yake murumushi a bayyane kuwa harara ya zubawa Amanin yana cije
leb’ensa. Amanin ta d’an turo baki tana kallon Didi ta furta “Allah ya kai mu asabar zaki amsa da bakin
ki…” (Asabar itace ranar da duk ahalin Didin suke bayyana a gidanta da yaransu da jikokinsu. Sak Jikin
Didin ta yi kafin ta furta “Magajiya fitina dai barci take Allah kuma ya tsinewa mai tayar da ita….” Ta
D’auke kai tana furta “Oho ashe ba kya son na gaya mata sai a bayan idonta ki yi ta zaginta
Kina ce mata mai bak’in hali amma a gaban idonta ba abinda kike iya yi sai abinda ta zartar kamar dai
Umma Dee d’in Uwarki ce?” Dahda ya waro ido kafin ya furta “Amani zagin Didin zaki yi?” “Ah to yau Kai
ka fara jin ta zageni, ai ba sabon abu bane wajen Magajiya kai kanka Ubanta ma idan ba ka nan ce maka

take Mallakak….” Wata irin sufa Amani ta yi ta dira a gabanta tana toshe mata baki “Allah ki ka gaya
masa sai na fa’dawa Umma Dee maganar rannan da kika gaya min…” Tsaf Dada ta shanye zancen. Dada
dai lumshe idonsa ya yi kafin ya
Mik’e yana wurga mata harara don yana da wajen zuwa da yamma ba zai iya da Didi da Magajiyatta ba
“To Didi bari mu wuce..” “Allah ya yi maka albarka, Yauwa Moddi ya maganar mu ta kwanaki ne? Baka
samu matar auren ba ne har yanzu? Ko sai na tara maka y’an uwanka, wace irin masifa ce ta sameka ace
kana zaune da mace ba haihuwa ta hanaka aure balle ka samu magaji, ka san dai y’ay’a mata ba naka
bane gidan wasu zasu ko?” Moddi ya koma ya zauna ya rik’e kansa kafin ya d’ago yana kallon Didi ya furta
“please Didi ki bar maganar nan, kin san dai sau uku ina neman aure bai yiwu ba to ba mamaki k’addara
ta ce a haka?” Ba wata k’addararka a haka, ni na samo maka mata yarinyar arziki shekaranjiya suka zo da
Kakarta k’awata Bintalo, ina ganin yarinyar na ji na maka sha’awarta don haka in dai ba so kake na
ha’daka da Dijatu ba ka yi azamar zuwa ku daidaita da yarinyar nan…” Yarinya kuma Didi ni zan auri
yarinya k’arama ina da wa’dannan y’an matan a gabana na auro sa’arsu ai abin kunya ne..” Didi ta saki
baki tana kallonsa kafin ta ce “Mhmn! To sannu Moddibo ina fatan ba kai ka yankewa k’asa cibiya ba? Ce
maka na yi sa’arsu ce? To nauyin aure ta yi don na san a k’alla zata yi shekaru ashirin da shidda idan ma
bata fi ba, a haihuwar tumaki ai ta haifi yaran naka.” Dahda dai ya yi shiru ba don yana jin zai iya ba. Ya
mik’e yana furta “Ke wuce mu tafi, kina zaune idanunki k’uri a bakunan mutane suna magana.” Ta mik’e
tana k’unshe dariyarta don ta san yau Didi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login