Showing 63001 words to 66000 words out of 87659 words
Chapter 22 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf
Bata manta garga’din Bokanta ba. “Kada ki
sake ki tare a sabon gidan nan sai kin zo mun Miki aiki, idan ba haka ba komai ma zai iya faruwa. Aikinmu
da duk abinda kike tak’ama da shi zai warware…. Jikinta Har rawa yake da tuna hakan. Don haka da sauri
ta kalli Moddi ta ce “Ina ne nan? Ba dai sabon gidan mu ba ne? Ba dai tarewa muka yi yau ba?” Ya bita da
kallo yana mamakin sauyawar yanayinta. Madadin amsa mata sai ya saka kawai zai shiga gidan. Da sauri
ta ja hannunsa tana girgiza masa kai jikinta na rawa ta furta “Kada ka shiga Imaam, wallahi akwai
matsala, ya zaka kawo ni gida ba tare da sani na ba. Me kake nufi ko zuwa muka yi mu gani mu koma.” Ya
‘d’an janye hannunsa yana furta “Mun dawo kenan, akwai matsala ne?” Saura k’iris fitsari ya zubo mata.
Ta wani irin zaro ido tana girgiza kai ta furta “Me? Wallahi ba zan shiga ba, wannan ma ai rainin hankali
ne, ta ya zaka ce min na dawo gida ba wani shiri….” Ya ‘d’an k’ura mata ido kafin ya saki wani murmushi
Ya furta “Shiri? Shirin me zaki yi? Duk wani shiri na gama shi a gidan nan, akwai duk abinda za ki buk’ata a
ciki. Didi ma tun jiya ta tare…” wannan karan fitsarin sai da ya zubo. Ta runtse ido tana tuna sauran
maganar da ta zauna mata daram a kwanya. Ta haddace ta kamar karatu. “Barin Uwarsa ta zauna inuwa
d’aya da shi, ina tabbatar miki kamar shigar ki matsaloli ne ba matsala ba. Dole ki raba Uwarsa da gidan
sa…” Idan bata manta ba shine dalilin da yasa ta dinga zubawa Didi rashin kunya da rashin mutunci har
ta gaji ta tattara ta bar gidan. Sannan yanzu ya gaya mata wai Didi na ciki. Kai ina ai ba ma zai yiwu ba.
Gaba d’aya duk ta rikice hakan yasa Moddi ya tsaya yi mata kallon mamaki su kansu su Amanin kallonta
kawai suke. Har Moddi Ya k’arasa gabanta yana murmushi ya ce “Akwai sauran shiri ko?” Ya fa’da k’asa
k’asa sai kuma ya girgiza kai “Kin shigo kenan Safna. Idan kuma kika fita nan da kwanaki masu yawa ma
ba tare da izinina ba, ina tabbatar miki a bakin aurenki.” Ta ji wata irin hajijiya tana neman kada ita. Tana
kallon su Amani suka bi bayansa Amanin na sakin dariya k’asa-k’asa. Sai da ta dafa bango tsabar yarda taji
ana wujijjigata kada fa mafarkinta ya tabbata kada wannan gidan ya zame mata BAK’IN GIDA… ganin Sun
mata nisa yasa da sauri ta mik’e ta bi bayansu. Tana aikin turawa Malaminta Message. Hannunta duk
rawa yake… a haka ta isa babbar k’ofar da taga sun shiga. Inda anan babban parlorn da ya raba sassan su
da na Didi yake. Didin na zaune a saman kujera su Umma Tee zagaye da ita. Amani da sauri ta fa’da jikin
Umma Tee d’in. Duk murna ta gama bayyana a saman fuskokinsu. Suka d’ago suna kallon Safna da yake
tsaye kamar ruwa ya ci ta. Sai fidgeting yatsunta take. Didi ta saki wani murmushi tana furta “Maraba
lale, shigo mana Safna.” Wani abu ya dunk’ule mata a zuciya sai kawai ta juya da sauri ta nufi d’aya k’ofar
da ta tabbatar nan ne part d’inta. A zafafe ta mayar da k’ofar ta kulle tana sakin huci da wani irin Zare ido.
A tsorace take ta tsorata da komai ma, idan ba kallon tsoro ta yiwa Moddi ba, sai taga kamar kallon tsana
yake mata. Da wani irin hanzari ta fara kiran wayar Malamin nata. Bugu guda ya d’aga don shima yaga
message d’inta. “Safna kada ki shiga gidan nan, idan kika shiga komai ma zai iya faruwa, idan na ce komai
ina nufin komai, kada ki shiga….” Safna ta runtse ido tana furta “Na shiga Malam, Na shiga ka gaya min
ba abinda zai faru….” Daga d’aya gefen Malam ya ce “Akwai Matsala, idan zai yiwu ki fito yanzu tun kafin
abinda ake gudu ya faru….” “Malam ba zai yiwu na fito ba, ya ce idan na fito a bakin aure na….”
Muryarta ta tsaya cak ganin Moddi a tsaye a gabanta yanayinsa ya nuna ya ji duk abinda ta ce. Don
kallonta yake da birkitattun idanunsa da suka bayyana tsananin fitinarsa da rashin mutuncinsa, kamar
kallon farko da ya fara yi mata sanda suka fara ha’duwa. Hantar cikinta ta ka’da….
JIKAR NASHE✍HADARIN GABAS…..
26.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
BRIGHT PENS 2nd batch..
“Da wa kike waya?” Ya yi amfani da bu’daddiyar murya wajen tambayarta. Murya bata mata kama da ta
Moddinta da ta sani ba, wani ne wannan daban, da ya jirkita zuwa wata halitta mai furgutarwa gareta.
Bata tab’a ganinsa a wannan yanayin ba don haka razanar da ta shiga ba ka’dan ba ce. A fusacen Ya sake
cewa “Ba kya ji ne? Ki yi magana mana…. Ko sai na bayyana Miki wanene ni?” Ta ha’diye wani yawu
sannan cikin muryar da ta bayyana rashin gaskiyarta zalla ta furta “Da k’awata nake fa, da wa zan yi
waya.” “K’arya kike.” Ya fa’da direct yana kallon cikin idonta. Wata irin tsanarta yake ji a ransa. Ta sake
tsorata da yanayinsa don gani take zai iya kai mata duka. “Ka yiwa girman Allah ka kyaleni Imam me na yi
maka ne?” Cije leb’ensa ya yi sai kuma ya wancakalar da ita gefe yana jin idan har ya cigaba da tsayawa
kusa da ita zai iya zama ajalinta, a yarda yake jin zuciyarsa na wani irin zafi…. Da wani irin sassarfa ya fita
daga d’akin. Sai sannan Safna ta ja ajiyar numfashi ta shak’i iska. Kafin ta furzar da huci. Wani irin zafi take
ji a ranta. Ita yau Imaam ya yiwa haka? Ta cije bakinta wasu hawaye da ta tabbatar na bak’in ciki ne suka
zubo mata. Ta zauna tallafa da kumatunta tana jin tunanin da yake cikin zuciyarta shine kawai abinda ya
kamata ta yi. Ba dai burin y’an uwan Moddibo su tozarta ta ba, burinsu ya yi aure ya haihu zata biyo
musu ta yarda suke so. Wannan hawayen ta rantse ba zata zubar da su a banza ba. Da wani irin zafin
nama ta shiga kiran Lady boss. Bata wani b’oye mata komai ba, ta zayyano mata abinda ke faruwa. Cikin
mamaki Lady Boss ta furta “Kan Uba! Shi Imaam D’in ne ya aikata miki haka? To me ya shiga kansa?”
“Rashin mutunci, ko na ce Uwarsa da y’an uwansa suma sun je sun yi nasu k’ulunboton to wallahi
wannan karan na shirya musu zan tabbatar musu ni gaba nake da su a iya shege, zan b’ata musu sunan
dangin da suke alfahari da shi, da ina jin ba zan iya aikata abinda Alwan ya saka ni ba, amma yanzu
zuciyata tana jin zan iya fin haka ma, zan iya sakawa Moddi ya yi zina da Uwarsa ma ba y’arsa ba. So nake
na samu Makamin da zan hana shi aure. Na shirya wannan karan Lady Boss, kuma Didi ko da bala’i sai na
rabata da D’an nata, sai ta gwammace bata ma haifeshi a duniya ba….” Lady Boss da take jin komai ta
saki dariya ta ce “Yanzu za ki iya kenan da kika ji Uwar bari, dama can ai ke kika saka tausayinsa a ranki da
kishin ba kya son Ya kusanci wata matar. Idan banda haka Uwar me ye a cikin Uba ya yi zina da y’ar sa,
y’ar ma da ba taki ba, y’ar da ba kya so. Ai ko da Uwarsa aka ce ya yi Ban zata za ki yi wannan da’dewar
baki aikata ba. Riba biyu fa kenan ga ku’di ga b’ata masa suna.” Safna ta ja ajiyar zuciya tana furta “Ki jira
nan da kwanaki ka’dan za ki ji dadda’dan labari, zan saka zur’ar Lamid’o a cikin Bak’ar rayuwa, da sai sun
gwammace ba su takale ni da fa’da…” “Bana jin ki, na San za ki iya.” Lady Boss ta fa’da. Safna ta Zare
wayar kafin ta sake mayar da kiran kan Malaminta. Ya tabbatar mata zai yi aikin da take so, zai kuma aiko
mata da kayan aikin ta birne a cikin gidan inda kowa ba zai ganta ba. Amma ta tabbatar a sanda zata yi
aikin kowa na barci cikin tsakiyar dare. Ba shakka ba komai ta ce ta amince…..
Da tafiyar sassarfa Ya koma sashen Didin, inda ya bar y’an uwansa. Yau kam zuciyarsa fresh yake jinta,
cikin tarin soyayya da k’aunar y’an uwansa. Kamar wani labulai ne aka yaye a cikin zuciyarsa ya bu’de
idonsa daga duhun da ya mamaye ganinsa. Ya dinga Jin abubuwan da Ya aikata bai kyauta ba. Jikinsa a
sanyaye ya zauna daf da Didi da Kan Amani yake samanta. Tana sosa mata gashin. Idanun Amanin a
lumshe tana shak’ar k’amshin Dahdan. “Zan yi magana da ku, yaran nan su bani waje.” Moddi ya fa’da
cikin wata irin Husky Voice da take d’auke da karyewar harshe mai da’din sauraro. Duk yaran wajen suka
mik’e, banda Amani da ta yi kamar barci take. Ta gefen ido ya kalleta kafin ya furta “Ke ba zaki tashi ba
ne?” Don ya san sarai ba barci take ba. Idonta ta sake lumshewa sai kuma ta mik’e daga jikin Didin ta tafi
cikin d’akunan da suka kasance nasu. Moddi sai da ya ji rufe k’ofarta sannan ya mayar da kallonsa kan
y’an uwansa. “Da ku zan fara, Don Allah idan da Wanda yake rik’e da ni a ransa ya yi min uziri Ya yafe
min..” Ba Wanda bai zuba masa ido a wajen ba cikin wani irin tsananin farin cikin dawowar d’an uwansu
cikin hayyacinsa. Didi kuwa murmushi take saki hannunta cikin na Moddi da ya damk’e sosai. Tana jin
yarda jikin nasa yake rawa. “Mun yafe maka.” Shine abinda suka dinga fa’da. Sai kuma ya zube a gaban
Didi. Ya kama hannayenta kasa furta komai ya yi sai hawaye da ya fara zuba sharrr daga idonsa. Didi ta
kama shi tana girgiza maka kai. “Ban tab’a rik’e ka da komai ba Moddi, na yafe maka abinda na San ka
aikata da Wanda ban sani ba…” “Na amince Didi zan yi aure, zan auri duk matar da kike son na aura na
amince ko gobe ki d’aura min aure…” zallar farin cikin da zuciyar Didi take ciki ta kasa b’uya a saman
fuskarta kawai sai ta rungume Moddin a jikinta tana furta “Barakallahu fika Moddibo, Allahu Akbar Allah
ka nuna min girmanka, ka nuna min komai yana faruwa ne cikin buwaya da izzarka tabbas kai Alhakimu
ne mai yawan hikima… ka cancanci a kiraka Alwahhabu mai kyauta da k’ari. Almujibu mai amsar addu’ar
bayansa. La Sharika laka, Allah ka cigaba da kare min zuri’ata. Ba ni da boka bani da Malam.” “Ameen”
suka amsa gaba d’aya Umma dee ce kawai bata wajen.
Moddibo ya d’an saki murmushi kawai kafin ya mik’e ya bar parlorn. Shikkenan hirar ta koma kan kalar
matar da ya kamata su samowa Moddibo kowa ya dinga fa’dar albarkacin bakinsa. Na irin matar da ta
dace da Moddin.
★★★★
Driving d’in take idanunta sanye da black shade da ya yi masifar yi mata kyau, ya kuma sake bayyana
gayunta. Chewingum take ci. Fuskarta cike take da damuwa. Ta samu gefen Titi ta yi parking hannunta ta
saka ta Zare shades D’in da ya saka ba’a ganin jan idanunta suka yi. Muryarta a dashe ta ce “Alwan ka
kasa cika min buri na, me yasa? Da Kai na yarda duk wani hope d’ina yana wajenka. Ka San dai rashin
cikar burina yana nufin komai ko?” Alwan ya saki ajiyar zuciya ransa a b’ace ya fara furzar da huci shi
kansa zuciyarsa bata masa da’di Akan hakan, amma ya zai yi? Duk ta inda ya b’illowa Imaam sai ya
waske…. “Ko wata dabarar zamu canja?” Ta fa’da idanunta suna lumshewa. Sai kuma ta bi Alwan da kallo
cikin karyayyan harshenta da bai gama k’warewa da Hausa ba ta furta “Ina Jinka? Ya kake ganin zamu
b’illowa lamarin?” Alwan ya saki murmushi bayan ya lumshe idonsa sai kuma ya ware da sauri ya furta
“Done! Wannan karan na samu mafita na San ba zai tsallake wannan tarkon da zan d’ana masa ba.” Shiru
ta yi tana binsa da kallo kafin ta cije leb’e ta furta “Kai ne Last Hope d’ina, bana son loosing dukkan
opportunity d’ina a wannan karan.” Daga haka ta ja motar a fusace ta hau Titi tana furta “Ina son barin
Nigeria in the next Five months, kafin nan ina son na tabbatar da cikinta a jikinsa, idan ta Kama zan iya
tafiya da ita can don ta haihu…” Alwan ya gya’da kansa “In sha Allah hakan zata faru…” “Rabbi Ya sha’a
ta furta tana sake danna motar da gudu, don da haka ta k’ure da tuk’inta…
★★
Cikin daren da ya yi tsit ya kuma nuna alamun dare ne sosai. Kamar an tashi Amani haka ta farka tana
kallon windown da yake cikin sabon d’akin nasu. Gefenta Imaan ce da ta kasa yarda su raba d’aki… zafin
da take ji a zuciyarta na yanayin da take cike ne yasa ta mik’e don isa kitchen ta samu ruwa ta sha. A part
d’in su Dahda suka kwana cikin d’akunansu na sashen don b’angaren Didi cike yake taf da y’an uwanta da
suka zo yi mata murna. Shiru parlorn baka Jin k’arar komai sai na A.c. Ta dinga Jin wani tsoro yana
shigarta Amma yarda take Jin k’ishi yasa ta k’i yarda ta koma ba tare da ta sha ruwan ba. Ruwan ta sha
sosai kafin ta zauna a parlorn idanunta a lumshe. A hankali ta bu’de idonta Jin motsin da take ji yana sake
yawaita. Ta kai dubanta zuwa wani walk way, inda ta nan ne za ka shiga b’angaren Dahda. Duk da tana Jin
tsoro sai ta ji tana son sanin menene ake yi a wajen. Ta mik’e don isa k’ofar da da rana suka shiga suka
tarar da wani garden mai kyawun gaske. Labulan windown ta ‘daga kafin ta Ware ido tana kallon abinda
ya kusa dugunzuma kwanyarta. Da sauri ta waro ido. Sai kuma ta yi saurin toshe bakinta tana son sani me
Safnan take a wannan tsohon Daren. A tsaye take zigidir hannunta rik’e da wani kasko da wuta a ciki tana
zagaye wani waje da ta tabbatar rami ne… jikinta har rawa yake Amma hakan bai saka ta bayyana kanta
ba. Ta toshe bakinta tana sake jaddada rashin Imani irin na Safna idan har ba idanunta ba ne ya gane
mata ba daidai ba wannan abinda take Kai tsaye za’a kira shi tsafi… Tana kallonta har ta gama ta mayar
da k’asar ta rufe… A fili da kuma d’an k’arfi ta ji tana furta “Imamu na rabaka da Uwarka har abada! Na
rabaka da aure har abada!! Na rabaka da y’ay’anka da matarka har abada. Ni ka’dai zan yi rayuwa da
Kai….” Sai kuma ta saki wata dariya. Kafin ta mayar da kayan jikinta. Amani ta runtse idonta tana sake Jin
haushin kanta da bata fito da wayar ta ba. Da tabbas sai ta yi vedio D’in komai ta nunawa kowa don
hakan ya zama tsanin da zata raba Safna da Dahda har abada… tana kallo ta mayar da kayanta jikinta
sannan ta kashe wutar kaskon ta nufi k’ofar da zata mayar da ita cikin gida. Da sauri Amani ta sake
takurewa waje d’aya don bata son Safna ta ganta. Lamarin matar yanzu tsoro yake bata. Tana kallo ta
shigo har ta shiga cikin d’akinta ta kullo k’ofa. Zubewa Amani ta yi a wajen hannunta dafe da k’irjinta. Ta
kasa aikata komai sai zufa da take zubo mata. Sai da ta samu nutsuwa sosai sannan zuciyarta ta tunatar
da ita … “Idan baki cire abin nan ba komai zai iya faruwa, zata samu nasara a kanku ki je ki cire Amani ki
lallata sihirinta, ki cire duk wani tsoro da fargaba da take ranki…” Cikin k’warin gwiwa ta fice daga wajen.
Ta isa wajen duk wani tsoro da take ji ta ji ta nemeshi ta rasa. Daidai wajen ta hak’a ta Ciro abinda yake
ciki wasu irin tarkacen abubuwa ta gani, ga wani irin Abu mai warin gaske. Ta toshe hancinta ganin har da
jini yana d’iga a jikin abin. Da sauri ta tsuguna a kai ta yi fitsari don ta karanta a wani littafi hakan yana
karya ko wani irin sihiri. Gigicewar da ta yi da warin da take ji na abin yasa ta manta bata mayar da Ramin
ta rufe ba, ba kuma ta lura da mayafinta da zoben ta Sun fa’di a wajen ba. A Gigice ta shige cikin gidan.
Abinka da sabon wuri sai bata lura da inda take saka k’afarta ba, bata San d’akin da ta shiga ba ita dai taga
d’aki a bu’de ta danna kai ciki. A razane ta dinga kallon Dahdah da abinda yake yi a cikin d’akin da sauri ta
bu’de baki zata saki ihu da saurin gaske Dahdah ya toshe mata bakinta cikin tashin hankali a tsawace ya
ce “Waye ya ce ki shigo d’akin da na jaddada muku kada koda wasa ku shigo shi? Yanzu kin shigo ko kin
ga abinda bana son ku shigo ku gani, kin ji da’di? Na ce kin ji da’di yau kin gane min sirrin da na yi shekara
da shekaru ina b’oye shi?” Ina Amani ma bata San yana yi ba don tuni ta sume a jikinsa….. shi D’in ma
yarda yake Jin Kansa kamar ya suman, dama zai Mutu da shi da ita duk su bar duniya su huta…..
To fa! Me Amani ta gani ne da ya fitgitata har ta suma?
JIKAR NASHE★✍️HADARIN GABAS…….
27.
NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
08033748387.
Bright pens second batch….
★★★★
Jikinsa har rawa yake, cikin tashin hankali ya dinga jijjigata yana