Showing 24001 words to 27000 words out of 87659 words

Chapter 9 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf

duk abinda ya faru, sakacinki ne Safna me
yasa zaki tare shi da zance alhali baki zo mun masa dabaibayi ba…” Ta d’an runtse idonta tana furta “A
min afuwa hankalina a tashe yake da jin maganar saki a bakin Mutumin da nake tunanin kun gama

mallaka mun shi….” “Da saura Safna, Saboda uwarsa a tsaye take a kansa muna aikin tana karyashi da
dafin addu’ar bakinta don haka dole kullum mijinki sai ya zama a cikin aiki muke a kansa…” Ta cije
bakinta tana jin tsanar Hajja a ranta da gaske itace take b’ata mata duk wani shiri.
“Yanzu menene abin yi?” Ta fa’da tana sakin ajiyar zuciya. “Dole ki bar gidan nan na kwana biyu har sai
mun gama gagarumin shiri a kansa, yarda gaba ko Karen hauka ne ya cijeshi ba zai iya furta miki kalmar
saki ba.” Ta saki ajiyar zuciya ta kuma amince da maganar Bokanta don haka ta kashe wayar tana jin tilas
tafiya Niger jihar Bidda Gobe ya kamata.

Kaya kala uku ta Cira ta saka a akwatin ta a zuciyarta take jin Bayan Moddi da Hajja ya zama dole a kanta
ta yi maganin ibilishiyar yarinyar can abinda ta mata yau ya tsaya mata a rai har ta ji sam ba zata iya yi
mata afuwa ba. Ta tsani Amani fiye da tsanar da ta yiwa Uwarta, don ta Iman ma mantawa take da ita
don yarinyar bata fiye shiga maganarta ba, amma Amani tabbas sai ta saka an mata aikin da zata zo tana
nadamar shiga huruminta.

Dollars ta d’iba ta zuba a jakarta sannan ta ja trollyn ta fito zuciyarta na mata wani irin zafi wai itace yau
zata bar gidan Moddi da sunan sakakkiya. Har wasu tarin k’walla ta ji sun zubo mata. Ta saka yatsa ta
lakato k’wallar ta tabbata k’walla ce murmushin b’acin rai ta saki tana furta “Wallahi ba zaku zubo a
banza ba…”


A zaune ta samu Amani da Iman a parlorn fuskar Iman a caku’de da tashin hakali. Amani kuwa fes da ita
sai sakin wa k’ok’in jin da’di cikin nisha’di da walwala. Iman tana jin k’amshin Mommyn na kusanto su ta
dinga mintsinin Amanin da nuna mata ta rufawa kanta asiri ta yi shiru. Amani ta wurga mata harara
“Allah gwara ma ki k’yaleni ba wani shiru da Zan yi da Dada ma yana nan Gusto zan tafi Celebrating…”
Idanu Mommy ta kafa mata don duk abinda suke yi ta ji su. Murmushi ta saki tana girgiza kai a hankali ta
furta “You will pay for this Amani na yi alk’awarin I will change your life to be miserable….” Ta fice ba
tare da ta sake bi ta kan su ba. Mama Talatu da take tsaye tana kallon komai ta k’araso da sauri cikin
parlorn tana kallon Amani ta furta “Magajiya me kike son janyowa kan ki?” Tab’e baki ta yi ta furta
“Alheri, wallahi ba abinda ta isa ta min sai abinda Allah ya hukunta a kai na, na san labarin komai Mama
na san irin muguntar da ta dinga yiwa Maminmu ban manta cin zalinmu da ta dinga yi tun muna yara ba
idan ku kun manta ni am still remembering….” Ta fa’da tana lumshe idonta wani irin zafi take jin
zuciyarta na yi idan ta tuna wasu labaran da aka bata game da abinda Ta dinga yiwa Mamminta har
hakan ya yi ajalinta ta mutu bayan an cirosu daga cikinta kallo guda ta musu kawai rai ya yi halinsa…
Haka Hajja ta basu labari. Mama Talatu jikinta ya yi sanyi don itama kam ba zata mance ba tabbas zata iya
cewa Safna guba ce a zuriyar Malam Moddibo don itace tasu jarrabawar amma ya zasu yi? Tun da ko ta
ina kowa ya san k’arfin asiri irin na Safnan da har yau Dadan ya kasa fahimtar ta… “Amma dai Magajiya ki

dinga yi a hankali baka nunawa mak’iyi kai mak’iyi ne a zahiri gudun cutarwarsa gareka. Mami ta mutu
kuma kowa ya shaida tata ta yi kyau sai dai fatan Allah yasa tamu ta yi kyau irin tata ki rage tuna komai a
ranki duk abinda ta yi Ai don kanta…” wani kallo ta yiwa Mama Talatun kafin murya a cunkushe ta furta
“I will never forget balle na yi forgive ina nan har abada da k’udirin ramawa Mammi cin zalin da ta mata
muguwar mata kawai mai kama da inyamurai…..” Karaf idanunta ya sauka a cikin na Dada da ya shigo
gidan yanzu. Girgiza kai ya yi yana amsa gaisuwar Mama Talatu ya shige ciki. Amani wata irin zuciya ce da
ita da ko shine ya mata laifi bata yafewa ya rasa ya zai fahimtar da ita illar abinda take son ta aikata.. ya
cije leb’ensa kawai bayan ya tub’e kayansa ya fa’da toilet a gaggauce kansa banda bala’in ciwo ba abinda
yake masa. Ga shi ya zama dole ya tafi Abuja yau, zai je su yi ta su k’are tsakaninsa da Alwan.

Wankan ya yi ya shirya cikin wasu irin suit masu taushin gaske ash color masu rigar ciki bak’a sai tie da ya
matse wayansa shima bak’i. Combing kansa ya yi ya masa gyara na musamman har da turaren gashi sai
shining yake. Idan ka gansa zata zaka yi bai zarce 35 ba bata yarda za’a yi kace ya haifi y’an mata kamar
Iman da Amani. Takalmansa ya saka as usual black silifas masu taushin gaske.


Ya fita da k’aramin brief case a hannunsa. Still suna zaune a parlorn ana sake tausar zuciyar Amani da
take ta kuka tana sake gaya musu bata manta muguntar Mommy ba a kan su da Mamminsu. Ya d’an
k’arasa wajen ganin yarda take kukan tana sakin ajiyar zuciya duk hawaye ya b’ata fuskarta. Isowarsa yasa
Mama Talatu da Inna laraba barin wajen. Idanunta a runtse take kukan da yake jin sa har tsakiyar ransa
bata san yana wajen ba sai da ta ji masifaffen k’amshin turarensa sannan ta ware idonta a kansa. Ido
shima ya zuba mata hannayensa a cikin aljihu yana nazarin fuskarta da ta damalmale da hawaye. Cikin
tsare gira sosai ya furta “Wiped your tears Malama kin fini son Mammin naki ne? Ko kin tab’a ganinta?”
Ta runtse idonta ta bu’de tana jin kalaman nasa sun mata wani iri “Mammi na fa?” Ta furta Numfashinta
yana son d’aukewa ganin wani irin bala’in kyau da ya mata “Mammin naki.” Ya furta a hankali. “Zan fita
zan dawo ko mai dare idan naji labarin kin sake wani abin ranki zai b’aci Stubborn child kawai ki ta
jawowa kan ki fitina….” Ya juya yana kallon Iman ya furta “Ku shiga ciki, and close the door kada a bar
kowa ya shigo har sai na dawo..” Iman ta d’aga kai ya fita da sauri ganin time yana son k’ure masa. Amani
ta bi bayansa da kallo tana mamakin furucinsa ashe yana son Mamminsu haka amma ko zancenta bai
tab’a yi ba sai yau da ta ji kalmar a bakinsa. Wani farin ciki ya baibaye zuciyarta har ta saki murmushin da
bata shirya masa ba.. Iman na kallonta ta furta “And the smile …?” Lumshe idonta ta yi tana rungume
Iman d’in ta furta “Ashe Dahda na son Mammin mu?” Iman murmushin itama ta saki don yau furucin na
Dahda ya musu dad’i, wani abu ne da basu tab’a jinsa ba tun yarintarsu har yanzu da suka girma…

Shima tunda ya shiga motar ya ji abinda ya fa’da d’in ya tsaya masa. Ya lumshe idonsa yana tuno y’ar
rigarsa… Y’ar ruga dai masoyiyarsa da ya dinga wulak’antawa saboda son zuciya da zallar yarinta da gata
da ya masa yawa. A hankali ya furta “Allah ya gafarta miki ya sadamu a Aljanna…”



Tunda jirginsu ya sauka airport d’in yake jin gabansa na wani irin fa’duwa har sai da ya nemi waje ya
zauna. Kafin zuciyarsa ta dawo saiti. Baya son irin wannan meeting d’in da ogansa don ya san ba sa
kwasheta da da’di. Har sai da ya samu daidaito da nutsuwar zuciyarsa sannan ya mik’e ya fita inda ya
tarar da bak’ak’en motocin yaransa jeeps guda uku suna jiransa. Sai kuma motar da ya tabbatar shi ka’dai
yake hawanta da drivernsa a ciki. Addu’a ya yi sosai kafin ya shiga motar yana jin bugun zuciyar tasa yana
raguwa.

Har suka isa companyn nasa idonsa a lumshe yake ba kuma komai yake tunawa ba kawai hankalinsa ne
bai gama amincewa da wannan ha’duwar tasu ba.



Fuskar Muhammad Alwan yau ba walwala yake kallonsa ta cikin farin glass d’in da yake sanye a fuskarsa.
Su biyu ne kacal a babban office d’in ba ka jin komai sai k’arar air condition…. Ya d’ago ya sake kallon
Imaam d’in ya furta “Ban fahimci duk abinda ka gaya min ta waya ba don haka na gayyaceka nan mu yi
magana one by one….. bana son magana biyu meye decision d’inka akan buk’atarmu?” Yawun bakinsa
ne ya kusa k’afewa ganin wannan karan Muhammad d’in bai zo da wasa ba…. “Ka canja wani abin, ba
zan iya aiwatar da wancan umarnin ba…..” Dariya sosai Muhammad Alwan ya saki kafin ya mik’e yana
zagaye kujerun da suke zube a office d’in fuskarsa a murtuke yake amsa wayar hannunsa yana magana
k’asa k’asa ya furta “Okay..” Ya dawo wajen da Imaam yake ya zauna daf da shi. Muryarsa a cunkushe ya
furta “Moddibo kana wasa da rayuwarka, me ye abin wahala a cikin abinda muka umarceka kada ka
manta alfarmomin da muka maka, muka d’aukoka daga cikin rana muka saka a inuwa me yasa kake son
ka mata butulci? Meye abin wahala a abinda muka ce maka? Y’arka fa kawai muka ce to da mahaifiyarka
muka ce fa?” Imaam ya wani irin waro ido yana jin zuciyarsa na wani irin tafasa huci kawai yake yana
kallon Muhammad Alwan da sam abinda ya fa’da d’in bai razana shi ba, sai ma wani irin murmushi yake
saki ganin duk da sanyin A.cn da yake wajen gumi yake yi… idanunsa sun ka’da sun yi jawur.. sai ciza baki
yake ya furta “Na gaji, ba zan iya ba na amince na fita daga cikin ku na amince na rasa komai nawa akan

yi muku abinda kuka ce…” ya fa’da yana runtse idonsa sautin dariyar Muhammad Alwan yana ratsa
kwanyarsa “Baka Isa ba Imaaam dole ka yarda da abinda muke so Ai sai da ka yarda da terms and
conditions d’inmu sannan ka shiga cikin mu, ka san sirrin mu sannan kace zaka fita? Ya zama dole ka
yarda da buk’atar mu…….” “Never” ya fa’da a fusace idonsa a rufe jijiyoyin kansa suna tashi ra’da rad’a
ya mik’e a zafafe da nufin barin wajen….



�� ���ℯ★✍️

�ℰ���� ℬ��ℋ......✍️HADARIN GABAS…..

NAZEEFAH SABO NASHE★✍️
�ℯℯ� ���ℯ★✍️


08033748387.

★★★★★ 1️⃣1️⃣





HADARIN GABAS…..

NAZEEFAH SABO NASHE.★✍️


�ℯℯ� ���ℯ★✍️


08033748387.

★★★★★ 1️⃣1️⃣





�ℰ���� ℬ��ℋ......✍️



Hannun Muhammad Alwan ya ji a kafa’darsa cikin wata irin murya mai bayyana lallashinsa ya furta “Kada
ka yi abinda zaka yi nadama Imaam, ko ka yarda ko baka yarda ba sai hakan ta faru gwara ma ka yarda
d’in….” Girgiza kansa ya yi yana kallon cikin idon Alwan d’in “Ba zan yarda ba, don ba abinda zai saka ni
nadama na ji na tsani kaina a rayuwa kamar abinda kake son saka nin… kuke son tursasa min sai na
aikata shi…” Wannan karan Murmushi Alwan ya yi ya saki kafa’dun Imaam d’in yana furta “As you
wish… ba zan hanaka yin abinda kake so ba you can do what suits you… amma ka sani kana so ko baka
so sai hakan ta faru gwara ma ka so d’in…” Tsaki ya zabga ya fice daga office d’in da sauri. Alwan ya bi shi
da kallo kafin ya zare handky d’in da ke aljihunsa ya goge fuskarsa yana cigaba da mamakin taurin zuciya
irin na Imaam. Ya san kuma dole abin ya faru da son sa ko ba son ransa. Ya lumshe ido kawai zuciyarsa a

time d’in ba abinda ba ta raya masa. Kada dai ya zama duk abinda suke so ya kasa faruwa dalilin taurin
kan Imaam…







★★★

Har jiri ne ya dinga d’ibansa kafin ya je gida tun a cikin jirgi yake jin zuciyarsa ba daidai ba. Da k’yar ya isa
cikin motarsa inda drivernsa yake jiransa ya yi saurin shiga cikin motar yana amsa gaisuwar Drivern.


Gidan shiru alamar kowa ya kwanta don haka kansa tsaye ya nufi d’akinsa. Wanka ya yi sosai kafin ya
ha’da coffee mai zafi ya sha burinsa ya ji ya daina jin abinda yake ji d’in sai dai hakan bai samu ba.


Da k’yar ya samu ya runtse idonsa yana tunano mafarin ha’duwarsa da Alwan da ya zama sanadiyyar
shigarsa cikin wannan matsalar…


10YRS BACK…

★✍️

Wani irin zafin rana da ake ne ya saka shi parking machine d’insa a gefen wani babban company. Ya zauna
a saman bench yana jin kamar kansa zai tsage. Daga aiki ya taso k’aramin ma’aikaci ne shi a lokacin a
ma’aikatar aikin Jarida da take k’ark’ashin gwamnati. A lokacin ma rahoto ya je d’aukowa sai ya samu
kansa da matsanancin ciwo shine dalilin da yasa ya ajiye machine d’in ya zauna a saman bench. Don sam
ba zai iya cigaba da tuk’ashi ba duk da k’ok’arin da ya yi na aikata hakan.

Tsawon mintuna yana zaune idanunsa a lumshe ya dinga jin wani irin k’amshin turare mai da’din gaske
yana ratsa k’ofofin hancinsa. Da k’yar ya bu’de ido jin ana cewa “Sannu bawan Allah..” Muryar bata masa
kama da ta hausawa ba sai dai mutanen k’asashen waje. Ai kuwa kamar yarda hasashensa ya ba shi wani
kyakykyawan saurayi ne tsaye a kansa yana sakar masa murmushi. “Sannu.” Ya sake furtawa yana kallon
gefe da gefen hanya. “Na da’de a tsaye anan baka sani ba, sai naga kamar akwai damuwa ko?” Imaam ya
tsuke fuskarsa don shi a rayuwarsa bai fiye son a shiga sabgarsa ba. Amma Alwan bai k’yaleshi ba sai da
ya zauna kusa da shi yana furta “Nima aiki ya kawo ni Nigeria so kuma ban san ko ina ba… ina so na
maka tambaya?” “Allah ya sa na sani.” Imaam ya furta yana kallon wani waje. “Apartment nake so mai
kyau na rent da zan zauna wanda ba zai ba ni damuwa ba…” Imaam ya yi shiru kamar ba zai amsa shi ba
sai kuma ya ce “Hotel ko gida?” “Any one.” Alwan ya furta yana sakin murmushi abinda Imaam ya lura da
shi Alwan ma’abocin murmushi ne. “Okay.” Daga haka ya mik’e yana d’an ka’de jikinsa saboda Imaam tun
bai zama wani abu ba d’an gayu ne na gaske. Ya hau machine d’insa ya ce ya biyo shi. Alwan bai masa
musu ba ya bi shi suka tafi har wani Apartment mai kyau ya ja ya tsaya yana kallonsa. “Yauwa ka shiga sai
ka musu bayani, ni zan wuce.” Hannu Alwan ya saka ya rik’e shi. Hakan da ya yi yasa Imaam ya ‘dago ya
tsareshi da ido. Alwan murmushi ya sakar masa yana d’aga masa kai. “Me yasa zaka tafi? Bayan ina
murna na samu aboki a inda ban san kowa ba. Ka taimake min mana nima fa musulmi ne.. ko baka son
lada?” Ya fa’da cikin gwamutstsiyar Hausarsa. Haka kawai Imaam sai ya ji ya amince da son kyautata
masa “Yanzu ya kake son a yi? Ni bana jin da’di ne ina son na je gida.” Cikin muryar tausayawa Alwan ya
furta “Oh Sorry, Amma pls mu yi exchanging number so that muna communicating..” Imaam bai masa
musu ba ya amshi wayarsa mai d’an banzan kyau ya saka masa numberrsa ya kuma yi saving da Imaaam
Moddibo..” Alwan ya kalli sunan yana furta “Nice…. Ni kuma sunana Muhammad Alwan. From Turkey
hope na samu d’an uwa.” D’aga kai Imaam ya yi daga nan ya masa sallama ya burga machine d’insa ya
wuce.


Koda ya koma gida bai wani kira Alwan ba ya ma manta da shi. Y’an biyunsa Iman da Amani ya yiwa wasa
ya shige d’aki.Safana ta bi bayansa ganin kamar baya jin da’di. Bai b’oye mata ha’duwarsu da Alwan ba ya
gaya mata komai. Murmushi ta saki tana furta “Allah yasa ha’duwar ta zama alheri…”

Da sassafe ya dinga jin wayarsa tana ringing. Yana dubawa yaga Muhammad Alwan ne sai da ya mik’e ya
zauna sosai sannan ya saka wayar a kunnensa “Morning” Alwan ya furta cikin nutsuwa “So ka tafi ka bar
amanarka da Musulunci ya baka, baka sake kirana ka ji ya nake ba na kira kuma baka d’aga ba.” Imaam ya
d’an saki ajiyar zuciya ya furta “Am sorry..” “No problem yanzu ina so kazo ka raka ni inda za ni pls!”
Kallon agogo Imaam ya yi ya furta “Ina zuwa aiki yanzu…” “please ka zo idan akwai yiwuwar ka samu
wani aikin da yafi naka sai kaga ka dace muna da companies a Nigeria and menene qualification naka? Ko
da yake sai kazo dai..” Ya fa’da yana kashe wayar. Safna da ta ji komai kasancewar wayar a handsfree take
ta mik’e da sauri tana furta “Alhamdulilah Moddibo ka maza ka shirya ka je ba mamaki wahalarmu ce
tazo k’arshe, dama aikin gwamnati bakomai a cikinsa sai wahala..” D’an kallonta kawai Moddibo ya yi ya
tab’e baki ya shige toilet ba wai don yana ji zai amince ya karb’i tayin da Muhammad Alwan ya masa ba.
Wanka ya yi ya shirya cikin k’ananan kayan da ya saba sakawa ya fito fes da shi sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login