Showing 87001 words to 87659 words out of 87659 words
Chapter 30 - HADARIN GABAS Book Complete By Nazeefa Sabo Nashe.pdf
kira da su.
Da alama Boss ba y’ar Nigeria ba ce don muryarta bata mata Kama data y’an Nigeria ba. Karyayyiyar
Hausa take, mai caku’de da wani irin English mai da’din saurare. Sai ta ajiye wayar tana sakin ajiyar
zuciya. Turo k’ofa aka yi Sadiya ta shigo fuskarta still da murmushi ta ce mata “Akwai Wanda suka zo zasu
miki predicare da manicure, zaku ma a Miki gyaran gashi…” Amani kallonta kawai yake kafin ta furta “Ina
son ganin uncle.” Sadiya ta San wa take cewa Uncle don haka ta ce “Baya k’asar, zasu dawo da Ma’am
gobe, saboda suna da taro….” Amani ta bita da kallo kawai har masu gyaran jikin suka shigo. Cikin
babban toilet ‘din akwai komai da suke buk’ata wasu kuma Sun zo da su don haka suka fara aikinsu kawai.
Sai ga Amani ta fito ta sake wani masifaffen kyau. Duk da cikinta watanninsa biyar Amma bai fito ba, ya
dai ‘dan tasa ka’dan. Jikinta ya yi wani irin soft and silk kamar na jarirai. Bin su take kawai da kallo kawai
don Boss zata da ita taro sai an mata wannan irin gyara kamar wacce bata wanka…
Kashegari kuwa da wani irin fa’duwar gaba ta tashi. Don haka har yamma tana na’de a gado. Sai da aka ce
ga mai shirya ta tazo sannan ta mik’e. Ta yi wanka aka kuma shirya ta cikin rantsatstsen Hkg lace. Aka
mata Light make up. Sannan around 5:30 Sadiya ta ce ta fito su je, motocin da zasu kai su airport sun zo.
A airport taga Uncle Alwan Amma bata ga Boss ba. Don haka da sauri ta isa wajenta sai Ya mata alamar
da su tafi cikin jirgi kawai. Haka ta saka k’afa ta bi shi sai a sannan ta San a Abuja suke zasu tafi Kano… ta
dinga Jin dama Alwan ya kaita gidansu sai dai bata da halin tambaya.
Babban hall d’in Event D’in ya cika mak’il da manyan mutane. Haka kawai Amani ta dinga jinta
Uncomfortable don haka ta cafki hannun Sadiya da take kusa da ita ta damk’e. Tana kallon yarda
mutanen wajen suka sha kwalliya, ba Wanda ta sani a wajen, banda Sadiya da Uncle Alwan. Sai ta dinga
Jin fargabarta tana k’aruwa ta yi saurin jan mayafinta rufe fuskarta. Bata San da shigowar Boss ‘d’in ba, ta
dai ji ki’dan Band ‘din ya canja sai kuma Mc ya dinga kwararaton shigowar mai girma shugabar taro. Ta
‘d’an bu’de idonta tana kallon Hamshak’iyar matar mai masifar kyau da ita… suka ha’da ido matar ta
sakar mata murmushi tana zama a wajen da aka tanada don zamanta. Aka cigaba da gudanar da taron
yarda ya kamata kafin Boss ta amshi mic D’in. Cikin muryarta mai bayyana ajinta ta furta “Mak’usidin
wannan taron don ku taya ni murnar ha’duwa da gudan Jini na a yau da nayi bayan d’aukar tsawan
shekaru ina gujewa ha’duwar mu. A yau nake son nunawa jama’a ita tare da sanar da su auren ta da aka
‘d’aura da Uban rik’onta Imaam Moddibo…. Ta fa’da tana nuna Moddi da Safna da suka shigo a lokacin
bayansu y’an Uwan Moddi ne da Didi da Imaan. Boss ta sake furta “Thank you Moddibo come and meet
your Wife Amani Moddibo………
Anan Book 1 ya k’are don samun cigaban book 2 a biya 500 kacal cikin account 2118666253 UBA aji na
musamman 1k.
HADARIN GABAS….. yanzu aka fara zubar ruwansa kuma yana gaba. Shin wani irin zama za’a yi tsakanin
Moddin Didi da Amanin Dada? Wacece Boss shin ko dai y’ar riga ce take raye? Idan kuma y’ar rigar ce da
gaske kenan da cikin su Amani ta je gidan Dada? Wai ya abin yake ne? Don samun amsa ku siyi Book 2
Wanda zai sauka a telegram
JIKAR NASHE✍
Ina jinjina ga BRIGHT PENS..
Nimcyluv
Ayshacool
Zee kumurya