Showing 30001 words to 33000 words out of 109227 words

Chapter 11 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

saita nufo motar, duk da zuciyarta tana cikeda fargabar tarbar dazata
samu a gareshi, saboda yanda suka rabu da safe.
Motar yabud'e ya fito, ganin yanda take a d'arare dashine yabashi dariya, amma saiya danne
baiyiba. yad'an kalli k'ofar falon yaga babu mai tahowa, saiya matsa kusada ita kawai ya
rungumeta da manna mata kiss a kumatunta, cikin kunnenta yace, "kinyi k'yau my Nessa".
Duk da taji dad'in kalaminsa, hakan baisata daina fargabarba, Dan tasan halinsa akan
share Abu yayi tamkar bai 6ata ransaba, saika manta ya hukuntaka akansa.
Yatsu biyu yasa ya d'ago ha6arta yana kallon fuskarta sosai, cikin k'asa da murya yace,
''koba'a murna da dawowata gidan da wurine?".
Murmushin k'arfin hali Aneesa yayi, ta girgiza masa kai, "a'a wlhy my Dear, abinda nayi
makane da safe yake matuk'ar damuna".
Murmushin gefen baki yayi kawai yakama hannunta yana fad'in "yarafa?".
Tace, " basu dawo islamiyyaba ai".
"Okay, to muje ciki, yunwa nakeji sosai, jinake kamarma zan iya cinye abincin gidannan duka
yau".
Babu shiri Aneesa ta tuntsure da dariya, " kai Dear amma wasa kakeyi ko?".
"Hh, ba wasaba fa My Nessa, tunda Na fita drink kawai nasha awajen meeting....."
Yakai k'arshen maganar suna shiga falon.
Aneesa batasamu bashi amsaba, saboda Fateema data fito daga nata 6angaren cikin
kwalliyar d'aukar hankali.
Kallonta kawai Uncle M.A yatsaya yi, saboda babu k'arya kwalliyar tata tayi masa k'yau,
amma dukda haka yayi hakanne danya bama Aneesa haushi, itama taji bak'in cikin dayaji d'azu

da safe.
A hankali yasaki hannun Aneesa da mamaki yahanata koda motsi, Dan bahaka sukayi da
Fateeman ba, sunyi shiri akan sun daina masa duk wani Abu dazai faranta ransa, amma danta
d'auketa sakarai shine taci uban kwalliya ta fito.
Uncle M.A daya k'arasa inda Fateema take sai kawai ya rungumeta yana fad'in "woow! my
tee.., kinganki kuwa? saikace wata 'yar 22?. d'agota yayi daga jikinsa ya manna mata kiss a
bakinta da yasha jan janbaki, harya d'ebo tsaraba shima�.
Kutt, zuciyar Aneesa tamkar ta fashe, ai ko ita dakeda girki bai yaba kwalliyarta haka ba,
sannan ma a kumatu yamata kiss, amma Fateema a baki, wannan wane irin wulak'ancine?.
Da sauri tabar wajen tashige 6angarenta.
Yana ganin ta shige yasaki Fateema yanufi samansa.
Binsa da kallon Fateema tayi tana gumtse dariya, sai da taga ya shige sannan tayi dariyar
mai isarta, halin Muhammad nak'ara mata sonsa matuk'a, shi mutumne da in matarsa tamasa
Abu bazai ta6a 6ata lokacin wajen mata ihu ba, sai dai yabi wata hanyar ya bak'anta miki rai,
bata raba d'ayan biyu abinda Aneesa tamasane da safe yarama. ta gallama 6angaren Aneesa
harara tana fad'in "'Yar rainin sense, da kin d'aukeni wata sakaraine ko?, azatonki na mince
mun had'a kai ko? to Fateema garas take kallonki, bar ganin shekarunmu d'aya, sabodama kin
rainamin hankali nun Yanke shawara babu Wanda zaiyi kwalliya shine kika koma d'aki kikayi
ko? A nufinki kinbar sakarai anan, haba matarnan tas nake kallonki, shiyyasama naci kwalliyar
dataci uban taki, mtsoww, sakarai wadda bata iya danne kishinta ba".
Tana gama fad'a ta shige nata side d'in itama.


Nace, "lallai Fateema kin burgeni wlhy, mata sai kuma Ku gyara�".

Shikam yana shiga nasa d'akin dariya yayi shima, sannan yashiga k'ok'arin cire kayan jikinsa.
Harya fito wanka babu labarin Aneesa, bai damuba Dan yasan yanzu tahau sama. Farar
jallabiya yasaka, yad'an fesa turare sannan yadawo falonsa, zamansa yayi dai-dai da shigowar
yaransa da gudu su hud'u.
Duk kansa auka fad'a suna fad'in "oyoyo Abbunmu".
Shima rungumesu yayi cikin farincikin ganinsu, yace, " my Children's oyoyo, andawo
islamiyyar?".
Atare sukace "eh abbunmu".
" masha ALLAH manyan gobe, ALLAH yayi muku albarka kunji, mi'aka koya yau?".
Rige-rigen fad'a masa suka farayi, barema Ummita da take bisa cinyarsa.
"Kunga afad'a d'ai-d'aya, kungafa banason hayaniya nagaji sosai". yafad'a a kalar tausayi.
Suma duk sai suka marairaice suna "sorry Abbunmu".
Murmushi yayi, yabi dukkan kumatunsu ya sumbata, sannan suka shiga fad'a masa d'ai-d'ai.
Ana haka Aneesa tashigo d'aukeda tire, fuskarta kawai ya kalla yasan tayi kuka, (sai dai a
k'asan ransa rayuwarta tana burgeshi, ko kad'an Aneesa batada rik'o, in har zaka 6ata mata rai
dazaran tayi kuka kota amayar da maganar to shikenan kuma ta huce).
Kallon yaran tayi tace, " kunga, kowa yaje yacire Uniform ko, abar Abbu yaci abunci".
Atare sukace to momy. Duk suka fita.

Sai da ta tabbatar sun sauka daga benen sannan ta tako a hankali inda Uncle M.A ke zaune
yana kallonta.
Saman cinyarsa kawai ta zauna, batareda tace komaiba ta had'e bakinsu waje d'aya.
Bashida za6in daya wuce kar6arta hannu biyu.


🚶🏻â€â™€bara na koma falon k'asa, idan sun dai-daita saina dawo�.


Kusan mintuna 5 sannan Na koma, tararwa nayi tana zuba masa abinci suna dariya.

Na rik'e ha6a ina fad'in lallai (mata da mini said ALLAH), kuma gaskiyar Nazeefa, zaman
gidannan Sai mai wayo, Dan rayuwa akeyi ta kissa da kishin masu Ilimi, masoyan Amatallah
saiku mik'e sosai, dan saikun mata training akan zaman wanga gida da ake kishin 'yan
bar.....🤭ban dai Ce komaiba Ba ruwana bara Na tsuke bakina kar masoyan Aneesa da Fateema su caskalani🤊
Da kanta tabashi abincin suna hira cikin so da k'auna, sai da yagama tsaf sannan yay alwala
suka sakko k'asa tare, ya tasa 'ya'yansa maza gaba suka tafi masallaci sallan magrib.

Saidai sukayi sallar Isha'i sannan yaturo yaran gida, shikuma yatare Napep sai gidansu dukda
garin yafara canjawa kamar hadari zai had'u.

Nazeefa da Amatallah suna zaune a d'aki tareda Innani, Tuwo sukeci suna hira kad'an-kad'an
domin d'aukema Amatallah kewa.
Sallamarsa kawai suka jiyo a tsakar gida, Nazeefa ta amsa dad'an k'arfi yanda zai jiyosu.
Sai da ya lek'a d'akin baba yaga barci yakeyi sannan yadawo d'akin Innani dayajiyo muryar
Nazeefa, nanma sai da yay sallamar aka amsa dabashi izinin shiga sannan yashiga.
Idonsa Akan Amatallah yafara sauka, wadda tunda taji sallamarsa gabanta yashiga fad'uwa,
sai ma taji tuwon yafita kanta, koda yashiga bata d'aga ido ta kalleshiba.
Kusada Innani yaje ya durk'usa yana gaisheta da tambayar jikin baba.
Ta amsa tana kauda kai gefe kamar yanda ta saba masa. sunama gama gaisawar tamik'e
tafita daga falon.
Nazeefa ya kalla dake gaisheshi, bayan ya amsa yace, "Jabeer da shehu fa?".
''Yaya basu shigoba tukunna".
" Okay".
Cikin d'an rawar murya Amatallah ta gaidashi itama, idanu kawai ya zuba mata batareda ya
amsaba.
Takuma maimaita gaisuwar a karo Na biyu.
Yanzunma bai Amsaba, sai cewa da yay "my best! alk'awarin kenan? tunkan muyi nisa harkin
karya?.
Cikin dabara Nazeefa tazare jikinta ta fice tabarsu.
Cikin muryar kuka tace, " kayi hak'uri Uncle ban karyaba".

d'an murmushi yayi tareda girgiza kansa.
Sai kuma yataso yadawo inda Nazeefa ta tatashi yana lek'a kwanon tuwon da sukeci.
"Uhm my best babu tayine?".
d'an murmusawa tayi tace, "a'a to bismillah".
gyara zamansa yayi, cikin dai-daita murya dan soyake ta saki jikinta dashi.
Yace, "Sai da Na rok'a my best!?".
"to kayi hak'uri, bara nakawo maka wani wannan ya k'are".
"A'a ngd".
Kallonsa tayi, a shagwa6e tace, " uncle fushi kayi ko?". 'Tak'are maganar tamkar zatayi kuka'.
Yanda tayi maganar a shagwa6e sai yaji wani iri daban, bak'aramin birgesa tayiba, jiyay
zuciyarsa Na kissima masa wani Abu daban, yay saurin fad'in ya salam, kai zuciya ta, mikikeyi
hakane? Amatallah d'iya tace.
"Kaji Uncle, please mana"....
Maganarta ta kuma saukar masa bisa kunne.
tsintar kansa kawai yayi da mairairaice murya shima, harda langa6e kai gefe kamar yanda
tayi.
"Ni dai gaskiya na k'oshi my best".
Dariya sosai Amatallah takeyi, shikuma ya kafeta da ido yana kallonta da murmushi. sai da
tayi sosai sannan ta daina.
" uhm, dama haka kika iya dariya my best?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta, "ALLAH uncle kaine kaban dariya, shagwa6afa kayi".
" lah da gaske? aini bamma San nayi wani abuba. tashi ki wanke hannu kizo muyi maganar
School d'in da kikeso".
"To". Tafad'a tana mik'ewa d'auke da kwanon.
Har taje k'ofa ta juyo, yanda taga yana kallontane yasata k'asa da kanta sannan tace, " uncle
tuwonfa?".
"Kansa ya girgiza mata sannan yace, " a'a Na k'oshi, wasa nake miki, ban dad'a dacin
abinciba ne da naci".
Kai kawai takad'a ta fice tana mamakin wannan sabon salon da Uncle kemata a yanzu,
tamkar ba Uncle d'in taba, babuma abinda ke takurata kamar yawan kallonta da yakeyi.


*******

Ganin yara sun dawo babu shi yasaka Aneesa kiran Abulkhairi ta tambayesa.
"Momy bansan ina yajeba, yacene mu shigo gida shi zaije wani waje".
Shiru Aneesa tayi tana kallon yaron, k'asan ranta haushi da kishi na cinta.
Sallamar Abulkhairi tayi, ta d'auki waya ta kirasa.

Amatallah na fita daga falon kiran Aneesa na shigowa, murmushi yayi dayaga my Wife Neesa.
d'agawa yayi, cikin sanyin muryarsa yamata sallama.
Batareda ta amsaba tace, " dear wai ina kuma kaje a darenan?".
Bai iya k'aryaba, dan haka kai tsaye yace, "ina wajen Khadija ne my Neesa".

Ai tamkar yadaki zuciyarta da mashi, ta dai daure tace, ''amma a darennan?".
"uhm akwai abinda najeyine mai muhimmanci, amma bazan dad'eba zan dawo, kedai kawai
kishirya kar6ar tsoho yau, dan dolene mu goga raini ki tabbatar da saurana har yau".
Shiru tayi, takasa cewa komai.
" hello, bak'ya jinane Neesa? ko harma kin tsoratane?".
Dariyar basarwa tayi, "saika zo d'in, nima na shirya".
" ko babyna?".
"Eh mana". cewar Aneesa.
Murmushi yayi mai sauti, dan hartana jiyosa, yace, " my Siddiqa zatayi k'ani ko k'anwa
kenan yau"....
Da sauri ta katseshi da fad'in ''my dear!, dan ALLAH bar fad'e, wasa nakeyi wlhy, sai ka
dawo...."
Bata jira cewarsaba ta yanke wayar.
Girgiza kansa yayi yana murmushi, A fili yace, ''my Neesa m......
Shiru yayi bai k'arasaba sabida ganin Amatallah tsaye a bakin k'ofa, baisan tashigoba ko
kad'an.
Itakam bama tadad'e da shigowarba taji yana waya, duk da taji da wacce yakeyi hakan baisa
taji komaiba azuciyarta, zama tayi nesa dashi.
Shikam duk saiyaji babu dad'i, a zatonsa zatayi kamar yanda su Aneesa ke masa, sai yaga
ko'a jikinta. Saima Neman waje tayi ta zauna.


Nikam nace, "Hhhh, yo Uncle ita kishin mi zatayi? tunda har yanzu batasan mi akema
kishinba🤣 ai da sauran timeí ¾í´.


List d'in sunayen Schools yabata taza6a, tace itadai kowacce ma ya za6a mata, daga
k'arshe dai sai Nazeefa da ya Jabeer ne suka za6ar mata.
Kusan 10pm yay musu sallama ya tafi, akan zuwa gobe zai kawo mata form ta cike.

*********

Ai ko daya koma gida saida yasha fama da Aneesa kafin su dai-daita.


Kishi kumallon mata kenan, bana ganin laifin Aneesa kam, sai dai gaskiya mata kud'an ringa
rage zafin kishi, musamman ma agaban miji, dan yana ragema mace daraja wlhy. ko zakiyi
kishin kiyi mai aji kamar na uwargida Fateema�👌🏼.



____________________________

Alhmdllh komai ya kammala gameda exam d'in Amatallah, ta kuma maida hankali sosai a
karatun, musamman da taimakon da Nazeefa ke bata sosai, shima Uncle idan yaje gidan yata
bata haske kenan akan abubuwan, tunda yasan sirrin jarabawar. kowa k'arfafa mata gwiwwa
yakeyi agidan.
Baba kuma ya sanarma Uncle M.A yakamata yaje Jos dan Neman dangin Ammin Amatallah,
yakamata a sanar dasu komai gameda rasuwar 'Yar uwarsu da mijinta, dakuma aurensa da
Amatallah tunda hankali yad'an kwanta zuwa yanzu saboda sojoji aka zuba a jihar jos d'in da
Kaduna. Sosai Uncle M.A yayi Na'am da batun, bai kumayi k'asa a gwiwwa ba ya shirya yaje jos.
Sosai lamarin ya tsa6a zuciyarsa, yanda yaga gagarumar 6arnar da akayi a jihar sakamakon
rikicin da ya afku, har yay sanadin rasa d'an uwansa.
A dangin Ammi ma mutane da yawa sun rasu, wasu kuma suna asibiti suna jiyya, nan dai
ya kwashe komai ya sanar musu, sunsha kuka sosai, dan dama sunata nemansu, ashema sune
farko-farkon rasuwa.
Duk sunyi na'am da zancen auren, sun kuma saka albarka, sai dai sun rok'i alfarma ya dawo
musu da Amatallah nan bayan ta kammala Exam, sai ayi biki kafin a maidota Kano gidansa.
Godiya yamusu, da alk'awarin maido Amatallah d'in, dan aganinsa hakan ma zaisata tad'an
rage wani rad'ad'in, takuma dingajin an mata aure irin na kowacce mace.
Sosai yamusu alkairi sannan yatafi suna zabga masa albarka da addu'oin fatan alkairi.


Su Amatallah sun cigaba da zana jarabawa cikin nasara, ahaka suka kammala NECO &
WAEC cikin farin ciki.
Har zuwa yanzu kullum Amatallah saitayi kukan rashin iyayenta k'oda a 6oyene saboda kar
Innani ko Nazeefa wani yagani, bakamar randa suka gama exam tasha kuka tamkar ranta zai
fita, jitake inama Ammi da baba nada rai, suga wannan rana dasukaita buri.
Da k'yar ranar aka samu kanta a gidan, harda zazza6i tayi.
Satinsu d'aya da kammala exam Uncle M.A da Nazeefa suka kaita Jos wajen dangin
mahaifiyarta, tayi matuk'ar farin ciki da ganinsu, sai dai ansha kuka ranar itada dangi, daga
baya dai suka sakama ransu dangana tunda kuka bazai dawo da wad'anda aka rasaba.
Zamanta cikin dangin mahaifiyarta saiya rage mata wani rad'ad'in, tad'an samu sauk'in
k'unar zuciyar datake ciki sosai, gashi kowa tattalinta yakeyi saboda tausayin datake basu.


**********

Uncle M.A kam dasu Nazeefa sai suka shiga kewarta, dan d'an zaman datayi yakawo sabo da
shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakaninsu.
Su Aneesa kam da Fateema dad'i sukaji, dan koba komai yanzu yarage zarya gidansu, sai
dai yana zuwa kamar yanda yakeyi da, da safe kafin yatafi kasuwa ko aiki, kokuma idan ya
taso.
A kuma wannan tsakaninne tafiya wani Cause a Dubai na tsawon watanni tara ya sameshi.

kuma cikin gaggawa.
A daddafe yaje sukai sallama da Amatallah, yakuma sanar mata data shirya Jabeer zaizo
akan makarantarta idan result ya fito, amma sai dai tayi hak'uri, k'ilan zata koma Kano da zama
fa.
Kanta ta jinjina masa tana k'ok'arin maida hawayenta.
Shiru yayi yana kallonta, murya a sanyaye yace, "bak'yason Kano ko my best?".
Da sauri tace, " a'a Uncle, inaso wlhy".
Guntun murmushi yayi kawai, yace, "OK shikenan to, ammafa ba wajen Innani ba wannan
karon".
Kallonsa tayi, murya na rawa tace, "Uncle ina to?".
Shima saiya kalleta da d'an murmushi yace, " gidana, kobak'ya son zama?".
Hawayen datake mak'alewane suka zubo, amma batace komaiba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login