Showing 42001 words to 45000 words out of 109227 words

Chapter 15 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

bai k'yaletaba, yamata gargad'i sosai.
To Alhmdllh babu dai wani gagarimin Abu daya faru, dan kowaccensu na gudun 6acin rai,
kuma ma ga Nazeefa, duk abinda yafaru a gidan takan sanarma yayanta.

Rashin zamanma da Amatallah ke samu a gidan saboda makaranta saiya kuma sauk'ak'a
wasu abubuwan.
Duk ranar asabar kuma suka had'u suduka sutafi gidansu Innani su yini a can.
Jikin babama Alhmdllh, dukda ciyone Na tsufa dai.

Masha ALLAH zuwa yanzun kam su Alhaji Muhammad baifi sauran 1month su dawo Nigeria
ba, kuma Alhmdllh yasamu nasarori sosai akan abinda yaje nema.
Yanzu haka kam shirye-shiryen dawowar suketayi.

Tunda kwanakin dawowar Uncle M.A yazama 10days Anty maijidda tazo gidan, wasu kayan
gyaran fata masu k'yau dana gashi ta kawoma Amatallah, ta nuna mata yanda zatayi kullum
indan zata kwanta, sai wasu turarurruka masu masifar k'amshin tsiya, Na wanka dana gashi, ga
mayuka masu k'yau da k'amshin tsiya, Sosai tama Amatallah gargad'i akan tadage karta saka wasa a amfani dasu, sannan tace
taringa shan fruits kullum safe da yamma, ga Nono shanu mai k'yau dana rak'umi tace tasaka a
fright tanasha shima safe da yamma, sai kuma had'in Zuma da kayan k'amshi da mazar kwaila,
shikuma da yamma kawai tanashan 3spoon. Godiya sosai Amatallah tamata, dukda bata fahimci dalilin Anty maijiddar Na bata wad'annan
kayanba, bakuma tasan ma'anarsu bama, tadai d'auka Na gyaran fatane dakuma murjewar jiki.
Duk yanda Anty maijidda tamata bayani haka ta dage sosai. aifa dandanan Amatallah tafara
sauyawa, fatarta harwani shek'i takeyi, dama ga bak'inta mai k'yaune, k'amshi kam ba'a
magana aii, ko da ga nesa ta giftaka saika jishi, su Goodness k'awayenta kullum cikin tambayar
miya canjata haka sukeyi?. Itadai sai dai kawai tamusu dariya bata cewa komai, dan har lokacin basu ta6a sanin tanada
aureba, duk zatonsu Uncle datake yawan ambata shike rik'onta dai, Fa'iza cema taso ta d'an
d'agota amma saita doje.
Fa'izan tace aibabu damuwa, inma tanada auren ai zasu sanine watarana.

Aneesa ba wani ganin Amatallah takeba sosai, shiyyasa bata kulada canjawar datayiba, sai dai
k'amshin datakeyi kwanan nan yana d'aukar hankalin Aneesa, harma take mamakin ina
Amatallah tasamo wannan k'amshin haka?.
Sai dai batada mai bata amsa, dodele tai gum da bakinta.🤐



____________________________


*_RANA BATA K'ARYA_*

yauce ta kama ranar dawowar su Uncle k'asarsu ta haihuwa, tunda asubahi Aneesa aka
tashi tafara gyaran 6angarensa, saida taga komai yad'au haske da shek'i, hakama tadawo

babban falon gidan, 6angarentama haka, Nazeefa dai nata kallon ikon ALLAH, Amatallah ma
batasan hidimar da akeyiba, tunda tayi salla takoma barci, sai wajen 7:30 ta tashi tayi wanka, ta
shirya kamar yanda Anty maijidda takira ta Umarceta.
Bata dade da kammalawa ba Jabeer ya kirata akan tafito yazo d'aukarta.
Mamakine ya kamata, dan tasan yaudai babu school, dan Asabar ce.
Tana cikin mamakin saiga Nazeefa ta shigo itama cikin shiri. Kallonta Amatallah tayi tace,
"Anty Nazeefa tare zamu fitane?".
''Eh".
Cewar Nazeefa.
" ina zamuje to, ko wajensu innani?".
"A'a, kedai kiyi sauri ki shirya, dansu Ya Muhammad k'arfe 5pm zasu sauka, somuke kafin 3
mu dawo kuma.
Amatallah batace komaiba tak'arasa shiri ta fito. shiru taji falon, dan haka ta tambayi ina
yara?".
Jikin motar suka k'arasa Nazeefa tana fad'a mata suna gidansu wajen innani, Aneesa
kuma tafita itama.
Mota suka shiga Amatallah Na mamakin wannan Abu, ina kuma duk zasuje abar gida shiru
haka?, amma koba komai tayi murna, dama batason Uncle ya iskota agidan..................✍🏻


Nace, "humm, Amatallah kenan, zakiyi bayani dalla-dalla-dalla da bakinki��.



�👎🏻

One Luv my sweet fan'sν Ύν΅°








*_ALLAH ka gafartama iyayenmh�🙏🏻_*
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💑
_{home of expert and perfect writer's}_

*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ceν Ύν΄™ν ΌνΏ»_*


____________________
*_Number 17_*
____________________

Uncle M.A bai baro gidan Alhaji Sabi'u ba sai da suka tsara abubuwan masu yawan
gaske, harda mutanen daya dace su tuntu6a domin samun had'in kansu a tafiyar.
Bayan sun kammala tsare-tsarensu Alhaji Muhammad yaymusu sallama yataho bayan ya
ajiyema yara kud'in shan Chocolate's.

Daga gidan Alhaji Sabi'u gidansu yawuce ya gaida iyayensa, nanma yad'an dad'e sannan
yataho da burin zai koma da daddare.
Harya tada mortar ya kashe, waya ya d'auka yafara laluben Number Amatallah yana
murmushi.
Rabonsa da ita tunda yaje jos, kullum yakira saiyaji wayar a kashe, idan kuma sunyi waya da
kawunta kunya yakeji yace yahad'ashi da ita.
Cikin sai'a kuwa yau sai Number tashiga.

Amatallah na zaune a tsakar gida itada Anty Sadiya da wata yarinyar makwaftansu Asiya
tana mata kitso, Anty furera kuma nata kai kawo a tsakar gida tana girkin rana.
Game Amatallah keyi a waya hankalinta kwance, jefi-jefi takan saka baki a hirar Asiya da
Anty Sadiya.
Kirane ya shigo wayar, wannan ne kuma karo na farko da aka kirata, dan ita mantawama
take da wayar, tunda Uncle yabata suka gama gani ta kasheta. Bata kuma kunnawaba sai
yanzu dataga games a wayar Asiya ta d'akko ta tura da films.
Number babu suna, shiyyasa ko kad'an batayi zaton Uncle baneba.
d'agawa tayi tareda manna wayar a kunnenta tace, "hello".
d'an lumshe idanunsa yayi ya gyara zama sosai da kwantar da kansa a jikin kujerar
motar. Amatallah takuma fad'in " hello wanene?". cikin Nutsuwarta tayi maganar.
d'an murmusawa yayi sannan yamata sallama cikin sassanyar muryarsa datake matuk'ar
so.
Bata buk'atar k'arin bayani kam, danta ganesa. saita samu kanta da fargabar amsawa.
Sai da Yakuma maimaita sallamar da cewa "My Best! Bak'ya jinane?".

" inaji Uncle, ina yini".
"Bazan amsaba, dan kinmin babban laifi my best, Wanda kuma kika cancanci hukunci mai
girma da tsauri".
Amatallah ta marairaice murya kamar zatayi kuka, " wayyo ALLAH na, minayi Uncle?".

Daga Anty Sadiya har Asiya baki suka sake suna kallonta da mamaki, su gani sukeyi tana
sane takeyi, saboda sungane Uncle d'in tane na Kano, kuma Mijinta a yanzu.
Itakam kokad'an ba haka bane, babu wata manufa aranta, sai dai saboda shagwa6ar
datakema babanta abayane kawai, saikuma take ganin Uncle d'in kamar shine Baban ayanzun,
shiyyasa takan masa Abu tamkar yanda takema babanta, dan ita tama manta dawani batun
aurensa dake kanta.
Ba k'aramin canja tunaninsa shagwa6ar Amatallah tayiba, saiya samu kansa dakuma
narke mata shima, ya manta matsayinta na d'iyar Isma'il brother d'insa, yarinyar da aka Haifa a
tafin hannunsa harya rad'a mata Suna.


"Uncle please, kafad'amin laifin dan ALLAH?".
" Ajiyar zuciya ya sauke, yakuma k'asa da muryarsa sannan yace, "miyasa kika kashemin
waya? tunfa dana tafi bakiko nemeniba my best".
" kayi hak'uri Uncle. ALLAH mantawa ma nayi da wayan, sai d'azun natuna dazan tura
games aciki".
"Uyim an manta da Uncle, amma ba'a manta da tura games da Films ba ko? zan ramane
ai nima".
" wayyo Uncle bazan sakeba ALLAH insha ALLHU, kaji Dan ALLAH".
"Shikenan, amma idan kin sake zan hukun taki, kin amince?".
Kanta ta d'aga masa kamar yana gabanta, tace, " to Uncle, sai kuma tace uncle katafine? ".
"A'a ban tafiba dai tukunna, amma insha ALLAH gobe k'arfe 3pm zan wuce".
"Ayya, ALLAH ya kaimu lafiya Uncle, yasa kaje a sa'a kadawo da Nasara".
" amin my best daughter, ALLAH yamiki albarka kinji, ya gafartama su brother ".
Murya a raunane ta amsa da amin.
Sallama sukayi akan zai kuma kiranta anjima Dan yaji muryarta tafara canjawa, bayason jin
kukanta ko kad'an.

Tana ajiye wayar Asiya ta tuntsure da dariya harda rik'e ciki.
Kallonta Amatallah tatsaya yi da mamaki tareda k'ok'arin had'iye kwallan data cika mata
idanu.
" Asiya lafiyarki kuwa?".
"Ah, k'alau nake kuwa, Amatallah irin wannan lobayya haka".
" lobayya kuma Asiya? Uncle d'inanefa".
"Uhm ai Nasan Uncle d'in nakine nima, ALLAH dai ya kaimu Kano kawai musha kallo,
ALLAH da nacema Abba banson karatu a Kano, amma yanzu kodan ke can zanje".
Baki Amatallah ta ta6e, tace, " k'yadai ji dashi".

Anty Sadiya dai batace komaiba, sai 'Yar dariya datakiyi itada Anty furera.
Amatallah bata fahimci duk inda suka dosaba, tacigaba da game d'inta, sai dai k'asan
zuciyarta tana mamakin a salon da Uncle ya amsa mata waya yau, sai kuma narke murya yake
k'asa sosai, dukda tasanshi shid'in dama k'arshe ne awajen golden voice.

Shiru Uncle M.A yayi yanabin wayar da kallo, kai kace acikine zaiga Amatallah ta 6ullo,
gemunsa yashafa a fili ya furta " Muhammad mike damunka hakane? d'iyar Isma'il cefa, wadda
a tafin hannunka aka haifeta". Ya k'are maganar da fad'in "ya salam!" tareda furzo iska daga
bakinsa. Ya dad'e yana sak'awa da kwancewa Kafin yatada motar yanufi gida.


*_Washe gari_*

Misalin 2pm yasamu rakkiyar matansa da k'annen sa zuwa airport, yara sunsha kuka har
saida yamusu wayo sannan. kafin jirginsu yatashi saida yay k'ok'arin kiran Amatallah amma
wayarta a kashe, ya kira kawunta kuma yace baya gida wlhy. baiji dad'in rashin samuntaba,
haka dai yashiga jirgi suka shilla. Jabeer ya maidasu Fateema gida da yara.
Anty Maijiddah da Shehu da Nazeefa suka shiga keke napep suma suka tafi, dama anan
sukazo.



___________________________

Tunda Uncle M.A yabar k'asar rayuwa gidansa ta canja salo, sunkoma rayuwar babu ruwan
wani da wani, ko wacce harkar gabanta takeyi, idan an had'une dai za'a gaisa kowacce takama
tsaginta.
Tafiyarsa da kwana biyu Nazeefa ta had'o kayanta tadawo gidan, wani d'aki dake can sama
kusada nasa ta gyara.
Hakan kam bak'aramin haushi yabama Anresa da Fateema ba, amma babu yanda suka iya,
Dan Nazeefa bata raga musu, shiyyasa duk suke shakkarta, ko Fateema dake 'Yar uwarta bata
d'agama k'afa.
Kullum Jabeer zaizo da safe yaga lafiyarsu, da yammama idan yadawo aikima yakan zo,
shima shehu randa 'yan arzik'in ke kansa yana lek'owa, wadda kuma tamasa kallon banza a
cikinsu kotak'i basa abinci yamata wankin babban bargo yay tafiyarsa. Anty Maijiddah ma takan
lek'o ganinsu.
Alhmdllhi jikin baba ma babu laifi, yasamu sauk'i, dukda lokaci-lokaci ciwon kan motsa masa.
Kullum ta ALLAH Alhaji Muhammad yakanyi k'ok'arin kiran kowa yaji lafiyarsa, dakuma k'ara
nuna soyayyarsa ga matansa, shiyyasa kowacce kejin kanta On top, tamkar ma mijin yafi
kulawa da ita da yawan kiranta.

Basusan inhar yakira d'aya dasun gama waya zai kira d'ayarba. Harma Amatallah dabawani
sakewa take suyi hiraba, bare akai ga zancen soyayya, yakan daiji lafiyarta sukumayi hira
kad'an.
Hakanne kuma yafara tasirantar da shak'uwa a tsakaninsu, koyaya takan d'an saki jiki dashi,
yayinda shikuma kanyi mamakin kansa a yanda yake gaza controlling d'in tunaninsa akan
Khadija d'iyar Amininsa, wadda yake mata kallon d'iya abaya, a yanzunkan yafara ganin
canjawar wancan matsayi. Datake dashi aransa, dan ko yaushe tunaninta Na mak'ale da
zuciyarsa, a da yakan d'auki hakan tausayinta ne dayakeyi, amma a yanzu shi kansa yafara
k'aryata zuciyarsa,

Ita kanta Amatallah bazatace batajin wani Abu dangane da Uncle d'intaba, sai dai kunya da
d'aukarshi a matsayi kamar babanta yagaza ganar da ita har k'agara take ya kirata a waya Dan
taji muryarsa kawai, Dan dama can tana bala'in son muryar Uncle d'in nata.
Gameda damuwar rashin iyayenta kam tana nan tanayi, kullum ta ALLAH saitayi kukan
rashinsu da kewarsu, kuma takan dage wajen musu addu'ar Neman gafarar ALLAH kamar
yanda Uncle kullum kan tunatar da ita.
Ana cikin haka Result d'insu ya fito, Alhmdllh Amatallah tasamu kaso mai tsoka a WAEC
d'inta, NECO ma haka dukda batakai WAEC d'inba, tayi farinciki sosai. hakama Uncle M.A.

A kuma wannan tsakanin ne Fateema tafara laulayin ciki, hakanne yasaka Alhaji Muhammad
yanke hukuncin Aneesa saita biyoshi, amma za'a bar Saifudden anan saboda school. zatayi
wata hud'u tadawo sai Fateema taje, lokacin tasamu lafiya cikinta yayi kwari.
Hhhh, tofa abin mema yasamu ga Aneesa dan batasan tsarinsa natayi wata hud'u bane ta
dawo, ta d'auka indan ta tafi shikenan sai kuma ya kammala karatu su dawo tare🤣�.
Ai kam tashiga yauk'i da gwalangwaso anama Fatima kallon nice a sama.
Duk da hakan ya Sosa ran Fateema saita danne, ta nuna murnarta da tafiyar Aneesa, dan
itama batasan cewar Aneesar wata hud'u zatayi ta dawoba, duk ya 6oye musu bai fad'aba.
Shiri sosai Aneesa tayi, Jabeer yashiga shigi da fici wajen shirya tafiyar tata.
Watansa 1 da sati 2 Aneesa tabi bayansa.
Ranar Fateema tasha kuka, dan 100% tagama yadda mijinta yafison Aneesa, ko kad'an bata
bari Nazeefa da yaranta sun gane halin datake cikiba, saima ta wayance da laulayin cikine
kawai.
Nazeefa mutumce mai bin kwaf-kwaf akan mutaneba, wannan yasa itama bata kawo komai
a rantaba ta d'auka gaske laulayine ya maida fateemar haka.
Tafiyar Aneesa babu dad'ewa aka kammala komai Na makarantar Amatallah, kasan cewar
Uncle M.A yanada fad'a aji a B.U.K d'in.
Komai ya kammala zata karanci Medicine
Amatallah tayi murna sosai, dan kullum burinta kenan ta karanci fannin lafiya, tun iyayenta
Na da rai kullum labarinta kenan, Uncle M.A yarigaya yasan da wannan burin nata, shiyyasa ya
cika matashi da amicewar Ubangijin al'arshi.
Aikam ranar tayi tamkar ta fasa masa dodon kunne saboda murna.
Farin cikin data shigane shima ya jagoraci nasa farincikin, har yakejin bashida wata matsala
a rayuwarsa dan kullum burinsa yaga farinciki Amatallah baiwar ALLAH, marainiya.

Samun makarantar Amatallah kuma yasa aka fara 'yan gyare-gyare agidan Uncle M.A, dan
saita tare zata fara school.
6angaren daya ware dama dan babanta idan sunzo Kano su ringa sauka aka gyara, dan
shima girmansa d'aya da 6angaren matansa, sai dai shi k'ofarsa ba ai nahin cikin babban falon
gidan takeba, tana cikin corridor d'in dazai sadaka da falon ne, wannan yasa Uncle yace a
maido k'ofar tadawo cikin falon, sai a toshe waccan. Haka kuwa akayi, Shehu ne yatsaya akan aikin, aka kammala komai tsaf aka sake sabon
fenti har waje, dan danan gida ya d'auki haske da shek'i, daka gani kasan sabuwar amarya zata
shigone.
Fatima bataji zafin kishiba sosai kamar sanda akai aure Aneesa, dan yanzu harda ita akaje
wajen had'a lefen Amatallah.
Ita da Anty Maijiddah da Nazeefa da Jabeer, sai Gwaggo Rakiya k'anwar Innani, akwatina
Hud'u masu k'yau, kuma sun zubo kaya masu k'yau da inganci.
Kwana biyu da had'o lefen suka shirya suka kai jos.
Ranar Amatallah kam tasha kuka sosai, dan abin Na bata mamaki, wai Uncle ne mijinta,
mutumin datake kallo a matsayin babanta, wayyo tasan dasu baba nada rai da hakan bazai
ta6a ya faruba, shi kansa Uncle bazai kawo hakan a ransaba, amma yanzu k'addara taragayi
fata. Babu Wanda bai zubda kwallaba a wajen, haka akama su Anty Maijiddah shatara ta arzik'i
suka dawo Kano a ranar, suna mai jin tausayin Amatallah sosai.
An tsaida tarewarta nanda kwanaki goma, ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login