Showing 90001 words to 93000 words out of 109227 words

Chapter 31 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

malan tsubbu ko
bokaye saboda rashin adalci da k'untatawar mazajensu, saikiga suna Neman hanyar 'yancinsu,
wlhy maza kuji tsoron ALLAH. Tawani fannin kuma laifinmu ne mu matan, wai Dan muna
kishiyoyi bazamu zauna hira da junaba, inma anci sa'a an zauna d'in zakiga mafi yawa hirar
habaicine da gugar zana, shin wannan kishine kokuwa jahilci?, nifa azatona kishi shine gogayya
wajen k'yautatama miji da Neman soyayyarsa shine kishi, bawai shirme tsakanina da kishiyaba,
kawai muzuba competition kowacce ta nemama kanta 'yanci awajen Wanda ya ajiyemu, bawai
mu zauna hassada wa junaba, Dan kishin yanzun hassada tafi yawa acikinsa wlhy, nabaku
Assignment ku gwada salon kishin su Ama.... Kugani wlhy koda kad'anne aciki, na tabbata
kobayan babu raina saikun tunani, Dan kishi baya hana abama abokiyar zama hak'inta Na
matsayin 'Yar uwa musulma, akwai hak'k'in k'yautatama juna tsakaninku, akwai Na mutunta
juna, wlhy karkuyi zaton ALLAH bazai muku hisabi akan zamantakewa ba kawai, kafinma azo
kan cutarwa ga juna nabin malamai da bokaye, muguwar kirsa dan kawai miji ya tsani abokiyar
zamanki wannanma zalincine babba, idan ance kiyi kissa bawai ana nufin ki cutar da 'Yar
uwarki wajen 6atata wajen miji ba, hakan ba daidai bane, kowa tata ta fisheta kawai, kinemi
fadarki Na nemi tawa, amma babu dalilin 6atanci da juna. ALLAH yasa mudace yakuma
shiryemu baki d'aya, komai dai zamuyi mudinga tuna mutuwa mai zuwa babu d'an aike,
kwanciyar kabari da tambayoyin cikinsa gaskiyace, sannan kuma Ubangiji yatanadi wuta da
aljanna, kuma kowacce zata samu mazauna cikinta, sai muyi hattara karmu bari kishi aikin
banza ya kaimu wuta, wanima kishin abin kaitaima maiyinsa kukane, dan mijinma zakiga wata
bai damu da'itaba balle yasan muhimmancin kishinsa datakeyi, kullunma mahaukaciya yake
kallonta, wlhy mata musan inda kemana k'aik'ayidai mu Sosa, dawanan shirmen kishin damuka
maida jinin jikinmu gara muduk'ufa ga ubangiji domin ku6uta daga azabarsa, saifa ka shuka
alkairine zakaga alkairin🤷🏽â€â™€, shawara tarage gamai shiga rijiya🙅🏼)._*

Basu bar falonba saida aka kirayi sallar La'asar, yatasa yaransa gaba suka tafi masallaci,
sukuma su Ama...kowacce tanufi d'akinta dantayi.
Koda aka idar da sallah saiya kwashi yaran suka nufi gidansu, tashin motarsa kawai su
Amatallah suka jiyo.
Hakanne yabama Amatallah damar shiya abincin dare, harta kammala tadawo falo inda
Fateema da Aneesa suke zaune suna hira, zama tayi itama suka cigaba dayin hirar atare,
dukdai bata wuce hirar rayuwaba da abinda ba'a rasaba.
Uncle kam yana gidansu, su Abulkhairi sunata wasansu, shikuma suka tattauna akan
maganar auren Jabeer da Nazeefa, harma baba yace shima Shehu kawai idan yanada matar
aure a hannu ayi gaba d'aya a huta kawai.
Uncle yace shikenan, hakanma yayi d'in, ALLAH ya tabbatar da alkairi.

Nace amin.

Saida akayi sallar isha'i suka shigo gidan, yaran kowannensu yay d'akin uwarsa, Uncle kuma
yashigo d'akin Amatallah.
Zaune ya isketa kan abin sallah tana addu'a bayan ta kammala karatun alkur'ani mai girma.
ya zauna saman doguwar kujera suka shafa tare. juyowa tayi tana kallonsa, "Uncle sannunku
da zuwa, sai yanzu ake ganinku?".
Ya had'e hannayensa a waje d'aya " tuba nake my best!. Babane yarik'eni akan maganar
aurensu Jabeer".
"Lah Aure zaiyi ya Jabeer d'in?".
" uhm, harma da Nazeefa da shehu".
Tad'an zaro ido waje "da gaske Uncle?".
" insha ALLAH my heartbeat ".
" masha ALLAH, ashe munada shan biki kwanannan".
Murmushi yamata yana d'aga kansa da lumshe ido.
Tashi tayi tanad'e abin sallar da maida alkur'anin inda yake tana kuma nuna farincikinta, ta
cire hijjabin tafita dan kawo masa ruwa.
Babu dad'ewa tadawo, center table tajawo gabansa ta ajiye jug d'in data had'a kunun aya
mai matuk'ar dad'i, kallonsa tayi yana kishingid'e a kujerar yana danna wayarsa, da alama wani
Abu mai muhimmanci yakeyi.
Bata katseshiba, bayan ta zuba masa a k'aramin cup saita zauna kusadashi kad'an a kujerar.
d'agowa yayi ya kalleta suka sakarma juna murmushi, yad'an shafi kumatunta ya maida
hankalinsa kan wayar.
Batace dashi komaiba tad'an kwanta a jikinsa tana kallon abinda yakeyi, sak'onni yake
amsawa a WhatsApp, da alama wad'anda suka shafi k'ungiyarsune.
Kusan mintuna 15 ya d'auka yana amsa sakwannin sannan yakashe datar yazauna da
k'yau.
Kallon Amatallah yayi datuni tatashi daga jikinsa takoma kujerar gefensa tana game a
wayarta. "My best badai fushi kikayiba ko?".
Murmushi ta sakar masa, " Uncle miye abin fushi, suma sunada buk'atar lokacinka koyaya
aii, nakawo maka abinci nan?".
"Wayyo my best ni zanma iya cin abincinnan kuwa? Har yanzu cikina yakasa sauka".
Langa6e kanta tayi gefe, " yanzu nan Uncle duk wahalar girkinnan danasha bazakaciba
kenan?".
Ya had'iye kunun ayar daya kur6a kafin yamik'a mata hannu alamar tazo.
Babu musu tataso tazo, kusadashi ta zauna tana zun6ure-zun6ure, ya ajiye kifin kafin
yajawota sosai a jikinsa, "sorry babyna mikika dafa to?".
" tuwo miyar d'anyen karkashi".
"Humm har kinsa yawuna ya tsinke my best, namiki alk'awarin da safe ki d'umama min
zanyi break fast dashi".
" da gaske Uncle?".
"Yes my best".
Daga nan tasaki jiki sukaita hirarsu cikin so da k'auna, sai wajen 10 yatashi zuwa 6angarensa.
hannunsa tarik'e tana marairaice face.

" ya yadai my best? ".
" Uncle please mu kwana anan mana".
Yay murmushi "tofs my best!, nan kuma? d'akinafa shi laifinmi yayi yau?".
" nidai babu laifin komai, kawai anan nake sha'awar kwana".
Yaja hancinta yana fad'in "hakan yayi my best, k'ilama ki samo mana twins yau....."
"Kai Uncle nifa ba yanzu ba?".
" kamarya ba yanzu ba?, sai yaushe kenan my best? "
"Uncle saina kammala karatuna, duk yaushe muka shiga level 2".
Shiru yad'anyi kad'an yana kallonta, ya sauke numfashi da d'ago ha6arta suna kallon juna,
" my best kodai kinashan wani abune dan karki samu ciki? Please karkimin haka Dan ALLAH,
inason ganin 'ya'yanki jinin brother d'ina danawa cakud'e awaje d'aya my best please ".
Jikin Amatallah saiyayi sanyi, ta maida kanta ta kwantar a k'irjinsa " Uncle wlhy bana shan
komai, banma ta6a tunani irin wannanba, kawai dai ALLAH bai kawo baneba, dama kaji nace
inason saina gama karatu nafad'ane kawai wlhy, bawai har zuciyata bane, amma kayi hak'uri
idan na 6ata maka rai". Murmushi yakeyi yana shafa bayanta a hankali, yaji dad'i sosai da ba wata kwaya takesha
saboda gujema cikinba, ya sumbaci kanta yana fad'in ''ngd Khadija, bakimin kaifin komaiba,
ALLAH yabamu masu albarka da tarin alkairi a yau d'innanma nake fata".
Kuma cusa kanta tayi a jikinsa tana dariyar jin kunya, shima sai yayi dariyar kafin yasaketa
yace tom ina zuwa, kiyi k'aton shirin k'ar6ar jikokin brother insha ALLAH.
hannu tasa tarufe fuskarta shikuma yafita yana dariya...............âœí ¼í¿»


Nima Uncle kad'an bani kunyafa🙈��


_'yan Kaduna state nabaku wanga page k'yauta, saboda tarbar da kukaima baba buhari, kun
burgeni ainun wlhy._
😻😻😻😻😻â¤â¤â¤â¤â¤í ½í±í ¼í¿»�



�👎🏻

One Luv my sweet fans😻

*_ALLAH ka jik'an iyayenmu_*�í ½í¹í ¼í¿»
[1/19, 10:28 PM] Aysha Galadima: *_Typingâœí ¼í¿»_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* â‰
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 36_*
____________________

Da safe haka Ama... ta tashi jiki duk yana ciwo, ba k'aramar murza tashaba wajen Uncle a
daren jiya, hakadai ta tak'ark'ara tayi break fast mai sauk'i, shikuma ta d'ind'uma masa tuwon,
bayan ta kammala gyaran kitchen d'in da babban falo tayi wanka a gurguje tanufi samansa,
tashinsa kenan a barcin daya d'an koma bayan sun dawo massalaci, toilet tawuce ta had'a
masa ruwan wanka.
Ya langyare mata akan bazai iya yi da kansaba, shi jikinsa ciwo yake masa, "jiya duk kin
bani wahala my best".
Idanu Amatallah tazaro waje, " Uncle wato nimace nabaka wahalar ko? nan k'asusuwana sai
ciwo sukeyi tamkar naje noma, shine zaka dawo da abin kaina ma".
Dariya yamata, "oh babyna zo namiki tausa saiki warware gaba d'aya".
" wad'in? tabd'i, Uncle ni zakama wayo? ai idan ka ganni lahira kaini akayi, ni yauma nayafe
kwannan wa Anty Fateema, ta had'a uku kawai".
"Lallai yarinya kinma Isa, yau ma muna tare yini guda, namaso ace girkin naki yakama
asabar da lahadine, humyim dakin fad'ama jama'ar jos".
Cikin dariya tace, " Uncle!, koda yake ni kama tunaminfa, Anty Aneesa na wucewa nima
zan had'a kayana sai jos, wata biyu zanyo".
Wani kallo yamata na idan na kamaki saikin fad'i dawa kike. yashige toilet yana murmushi
da cije le6ensa na k'asa.
Itama dariyar tayi tahau gyaran gadon, kafin yafito tagama gyaran bedroom d'in tsaf takoma
falo yafito, bai katse mata aikintaba yayi shirinsa da kansa, k'ananun kaya yasaka, Dan babu

inda zaije, yana gida cikin iyalinsa yau.

Cikin nishad'i sukayi break fast atare yau ma, daganan suka fito harabar gidan shan iska,
yara suna wasan 6uya tareda Amatallah, Uncle da su Aneesa suna musu dariya, abinne ya
burge Uncle yashiga shima, ganin haka Fateema da Aneesa suma suka shigo, akabar Siddiqa
tanama Mah-mah wasa. Fateema ta d'aurama Uncle k'yallen a fuska aka rufe masa ido, daganan kowa yanemi
wajen 6uya, Uncle kuma yafara lalubensu, daga bayansa Aneesa taja rigarsa, yajuyo da sauri
yakai hannu zai kamata ta zille tana dariya, Amatallah ma ta ta6a hannunsa, itama ta zille
masa, Sahib yazo gabansa yana fad'in "Abbu gani ka kamani". da sauri Uncle yajuyo inda yake
shima, amma Sahib ya gudu, Dariya suketa masa suduka, shikuma yana bin sautin dariyar
amma yakasa kama kowa, daga k'arshedai ya damk'i Saifudden, nanfa suka saka masa tafi da
ambatar an kama Saifi! an kama saifi!!.
Handkerchief d'in Uncle yacire yana dariya shima, Saifudden aka d'aurama sa, kowa ya
matsa, shima ta6asa sukaitayi suna guduwa da dariyar yanda yake laluben san kama wani,
Abulkhairi yazo ta6ashi ta baya ALLAH yabama saifudden ikon damk'oshi, shima aka d'aura
masa, Abulkhairi baisha wahalar damk'e Aneesa ba shima, yahau dariyar yakama momy
Yakama momy, su Uncle na tayashi da tafi, itama Aneesa aka d'aura mata, aiko da k'yar
takama Ummita itakuma, Ummuta koda aka d'aura mata dawayo tad'an d'aga kad'an tana gani
da ido d'aya, tashin farko ta damk'o Amatallah, itama aka d'aura mata, itama tafi shan wahalar
kafin ta damk'o Fateema da Sahib lokaci d'aya, akadai d'aurama Fateema, sunta zagaya gida
ana dariya Sam ta kasa kamo kowa, sai can tarutsa Uncle dayaja mata d'an kwali tayi azamar
kama damtsen hannunsa...�
Haka suka yini cikin nishad'i, daga wannan wasa su koma wancan har lokaci yaja, kowa
yagaji suka shige ciki aka zube a falo ana maida numfashin gajiya. Amatallah tashiga kitchen ta
had'a abincin rana, daganan kowa yad'an watsa ruwa saboda zufar dasukayi wajen wasa, sai
bayan sallar la'asar Uncle yad'an fita zuwa gidansu. Yau ma haka suka kashe juna da soyayya shida Amarsa.
Washe gari suka yini gidansu Innani suduka har yaran, koda suka dawo da daddare miji
yakoma hannun Fateema, itama haka taita shagalin damk'e kayanta, Yakuma kar6eta tamkar
ba ranar yarabu dawata macenba, ya nunu mata soyya mai tsayawa arai da tattalinta tamkar
itakad'aice gareshi. Washe gari Monday, yara da Ama..... Duk suka tafi makaranta, shima Uncle yafice harkokin
gabansa, kasuwa yafara zuwa ya gaggaisa da jama'a da duba yanda komai ke tafiya, sannan
yad'an Shiga B.U.K, bai dad'eba yafito danufi tafiya, Amatallah ma batasan yazoba, tanacan
sunata hirarsu dasu Rita bayan sunfito lecture a gajiye sunad'an hutawa kafin ashiga wata. Harya bud'e mota yaji ana masa sallama a bayansa, juyowa yayi batareda ya rufe k'ofarba.
Yad'an had'e fuska Dan ganin yarinyar datake Neman takura rayuwarsa a kwanakinnan
(zee), inhar zaishigo b.u.k saitazo wajensa, dukda bata fito fili tace tana sonsaba take-takenta
sun nuna masa hakan.
Canjin fuskarsa baisa tadamuba, ta gaisheshi cikeda ladabi.
Amsawa yayi yana tambayarta ya karatu.
Tace, "Alhmdllh ya iyali?".

Bai amsaba yace, " yau ma tambayarce?".
Murmushi tamasa tana gyaran tsayuwa, "eh to kusan haka, amma tayau tasha banban data
ranar sir".
" lallaikam, gashi kuma ni INA saurine" yay maganar yana kallon agogon hannunsa da
gyaran babbar rigarsa ta farar shadda.
"Babu damuwa sir, in ban takurakaba kawai kabani number d'inka, koda ta test message
ne saina turo tambayar".
Yad'an kalleta kad'an, sanye take cikin gown ta material bak'i da d'igon Fari, sai siririn
gyalenta Fari data yafa akanta, doguwace babu laifi, sannan tanada haske sosai, kuma yakula
'Yar gayu ce, ko magana a yangance take yinta, zata iya Girman Amatallah koda da shekara
uku ne ko biyu, kauda idonsa yayi batareda ya tankaba, ya d'akko card d'insa d'aya yabata
sannan yashige motar.
Cikin salonta tace, " INA godiya da wannan karamci, daka mini".
Wani murmushi kin gundireni yamata yatada motar yatafi.
Ta sumbaci card d'in tana wani lumshe idanu da shak'ar k'amshinsa daya mannewa card
d'in sannan tabar wajen tana mai addu'ar ALLAH ya mallaka mata bawan ALLAHn nan.


Nace hummm.


Alhaji Sabi'u dake zaune gefensa Wanda soyayya tarufe idon zee ko ganinsama ita batayiba
ya kalli Uncle d'in yana 'Yar dariya.
"Mutumina kodai ta hud'uce?".
Uncle yakuma dafe sitiyarin da k'yau yana murmushi, ''haba Alhajina ai ka tausayamin
kaima, inani ina mata hud'u? Uku nan sun isheni, ni banima da kud'in aure a yanzu balle inda
zan ajiye matar, kawai dai yarinyarce nima naga take-taken nata auren suka dosa".
" a kawai kashiga kaima, indai kud'in aurene matsalarka ALLAH zai kawo".
"Hhh lallaikam Alhaji Sabi'u, to aini yanzuma babu wani gurbi da wata mace zata samu a
zuciyata, matana sun mamaye ko ina da ina, harma bana kallon matan dawani fasali, kainema
yakamata kashiga ta uku kawai wlhy".
" a to tunda abin kaina zai dawo abar maganar kawai".
Dariya sukayi gaba d'aya suna cigaba da tsokanar juna har suka kai inda zasuyi meeting d'in
nasu.
Kusan kowama ya hallara su ake jira. babu 6ata lokaci suka fara abinda ya tarasu.
Sun tattauna akan abubuwa masu yawa dasuke damun k'ungiyar sannan suka koma kan
neman hanyar samun kud'in shiga, kowa yana kawo shawararsa.
Alhaji Murtala yace, "toko zamuci bashin bankine mu kafa wasu sana'oi kafin muga abinda
ALLAH zaiyi".
"Amma Alhaji murtala bama tsoron gudun Matsala nan gaba? Idanfa adadin maida kud'in
yayi bamu sami yanda muke soba akwai matsala kenan".
" ito dakuma wannan, to'ai munada sauran kud'i mizai hana muduba wani kasuwanci mai
saurin kawo kud'i".

"Wannan shawarar tayi kam, toga wata hanya danake d'an shakkar fad'arta da".
" wace hanyace? Kafad'a kawai kanka tsaye Alhaji Isa".
Nisawa yayi kafin yace, "kwangilace dama ta gwamnati, tun kwanaki governor yamin
maganar amma nad'ank'i bashi had'inkai saboda wani dalilina, to yanzu mizai hana mu kar6a
amatsayin k'ungiya, ni dama banason amsane alokacin gudun gutsiri tsomar 'yan siyasar
k'asarnan". Uncle ya jinjina kai yace, " yayi sosai, yanzu saikamasa maganar kenan?".
"Shikenan, saimuje a k'ungiyane to, zan sama mana damar ganinsa kenan".
" okey shikenan to".
(Alhaji Isa sirikine ga governor, shiyyasa yakeda lasisin ganinsa cikin kwanciyar hankali
akuma duk sanda yaso, yak'i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login