Showing 3001 words to 6000 words out of 109227 words

Chapter 2 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

masa ya kimtsa cikin jallabiya Brown mai gajeren hannu, ya d'an
fesa turarensa sannan suka sakko falon k'asa, yaran suna zaune suna kallon wani program na
yara a wata tashar larabci, duksun maida hankalinsu sosai a tv n. dan har Abbun nasu
yak'araso cikin falon basu saniba, jin jina kansa kawai yayi yana kallonsu da murmushi. Matarsa ta ajiye k'aramin kwano mai d'auke da dabino a agabansa, sai ruwa a jug na glass.
Kallon dabinon yayi sannan ya kalleta, "no, nifa naci dabino a mota, bani ruwan dai".
Ruwan ta tsiyaya a k'aramin Kofi ta mik'a masa, ya kar6a yana mai fad'in " jazakallahu
khairan my wify".

"Amin Nurrina".

Sai da ya shanye tas ya ajiye kofin, yana anbaton " Alhamdullah".
Tace, "saura abinci kuma".
" okey, had'amin, bara na duba jikin Saifuddeen".
Bai jira amsartaba yanufi 6angaran amaryarsa.

Tana zaune a falonta, nono take bama Siddiqa, gefenta kuma ga wani yaro zaune yana kuka da
Kofi k'arami a hannu, da alama tsaresa tayi dole yake shan abinda ke cikin kofin.
Sallamarsa ce tasaka yaron k'ara k'arfin kukansa, itakuma tad'ago kai tana kallonsa da
amsa sallamar.
Da d'an sauri yak'araso falon, kusada yaron ya zauna, "Saifudden miyafaru kuma da kuka
haka? mi kika masa?".
A sanyaye tace, " nikam mizan masa dear?, tea kawai nace yasha nabasa magani shinefa
yake wannan kukan iskancin, kadai san Saifudden ai".

Kar6ar kifin shayin yayi, ya ajiye saman table d'in gabansu, yajawo yaron jikinsa yana ta6a
goshinsa da wuyansa, jin zafi zazza6i zau, ya kalleta a k'ufule, "yanzu nan Aneesa kina nufin
saima yanzu zaki basa Magani? tun d'azun kin barmin yaro da ciwo ajiki?".
" a'a wallahi dear, nabashi Magani tun d'azun, sai dai kasanshi bayason maganin, ina
gama bashi yayi amansa, daganan yay barci, Ummansu cema tace nabarsa saiya tashi, kuma
tashinsa kenan d'in, amma Dan ALLAH kayi hak'uri".
Baice komaiba yafara k'ok'arin cirema yaron rigarsa da wando, ita dai kallonsu take, harya
gama ya d'auki yaron yashiga bedroom d'in ta, ajiyar zuciya ta sauke, tacire siddiqa daga jikin
nonon saboda tayi barci.
Bedroom d'in ta bisu, jin motsin ruwa a bathroom tagane wanka yake masa. Kwantar da
siddiqa tashiga k'ok'arin yi. tana zaune a bakin gadon yafito d'aukeda saif daya nad'o a towel.
Shima bakin gadon ya zauna nesa da ita, yace, "bani kaya masu kauri".
Tashi tayi da sauri ta d'ako kayan sanyi takawo masa. da kansa yasaka masa, ya d'aukesa
suka fice batareda yakuma tanka mataba.
Binsa kawai tayi da kallo itama. Tasan zaimayi abinda yafi haka, indai akan 'ya'yan sane.

A babban falo ya iske Umma uwargidansa ta had'a masa abinci a k'asa kan carpet, zama yayi,

ya zaunar da deen kusadashi, kafin ya maida kallonsa kansu Sahib, "Abul-khair kutaso muchi
abinci ko.
A tare sukace "to Abbu".

Umma ta ta6a wuyan Saifudden tana fad'in ''Deen ya jikin? zazza6in ya sauka ko?".
Yaron yad'aga kansa yace, " Umma zansha ruwa".
"To deeni na".
Ruwan tazuba a Kofi sannan tasaka masa abaki, yasha kusan rabi, Abbu yace, " barsa haka,
karya cika cikin da ruwa".
Batace komaiba ta janye kofin daga bakin Saifudden. tadawo gabansa ta had'a masa abinci
Suma yaran haka.

Fruits salad yafara sha, idonsa nakan yaransa dakecin abinci a tsanake, babu mai magana,
saboda ya kafa musu dokar duk Wanda yake cin abinci yana magana saiya zanesa, shiyyasa
ko Ummita k'aramarsu bata surutu in sunacin abin.
Ya maida kallonsa kan Umma dake zaune gefe tana canja charnel a TV. "Ku bazaku ci
abincin ba?".
Murmushi tamasa, kafin tace, "zamuci mana".
Bai ce komaiba ya maida kansa ga bowl d'in dayake shan fruita salad d'in.


____________________________

Dole Baban Ama... Sai a gida yayi salla, dan baisan yanda yanayin garin ya kwanaba.
Amatallah kam sai gabannin asubahi barci ya d'auketa, ga zazza6i mai zafi daya saukar
mata.
Bayan sun idar da salla baba ya kalli Ammi dake zaune bayansa kad'an tana azkar,
" yakamata ki tada mamana tayi salla saimu tafi asibiti ko?".
Kanta ta jinjina masa, sannan ta mik'e.

Da taimakon Ammi Amatallah tayi salla, sai rawar sanyi takeyi tana hawaye, manyan idanun
nan sunyi luhu-luhu saboda rashin isashen barci, ga kuka datasha.
Tana idarwa basu 6ata lokaciba suka nufi asibiti. Alhmdllah garin ya kwana lafiya, saboda
'yan sanda sun kama mafiya yawa daga cikinsu zike.
Sun d'an jima a zaune, kafin su sami ganin doctor, saboda halin da Amatallah take ciki doctor
ya kwantar dasu za'a mata k'arin ruwa da allurar barci tasamu nutsuwa.


_________________________

*_Two days ogo_*

Har zuwa yau Amatallah tana hospital, doctor ya rik'esu, saboda firgita da takeyi bata

samun isashshen barci, sai dai ayita mata allurar barci.
Sosai lamarin yafara tsorata iyayenta, Dan basuyi zaton abin zaiyi tsamari hakaba, duk da
sunsan dama Amatallah tanada tsoro sosai, gata da rik'e Abu a zuciya.

Ammi taje gida danta watsa ruwa, Baban Ama.. Ne kawai a asibitin, yana zaune kusada gadon
da Amatallah ke jinya, hankalinsa nakan waya yana latsawa, da alama wani yake son kira.
Amatallah na zaune ta jingina da gadon, dukta rame, sai idanu kwala-kwala, rik'e take da kofi
tana shan fura, bata iya cin abinci, daga fura sai tea, duk da dama abincin bai dametaba.
Baba yay saurin kara wayar a kunne, kasancewar wanda ya kira ya d'auka.

"Assalamu alaika my brother".

Daga can aka amsa masa, bayan sun gaisa da tambayar iyaliansu.
yace, " ya jikin baba?".

Daga can ya amsa da "Alhmdllh my brother, ina my best daughter?".

" gatanan a gadon asibiti".

"Gadon Asibiti kuma? Miya farune?".

" humm, kabari kawai brother, d'iyar takace sai ahankali, sai dai kashigo Mayi maganar, nazata
ma wlhy yau zaka shigo mu koma wajen maganin baba".

A jiyar zuciya ya sauke daga can yace, "brother ya jikin nata yanzu?".

" lah karfa ka tada hankalin ka, da sauk'i Alhmdllh, barama mugama magana nabata kaji, nasan
ka da girmama Abu. yanzu yaushe zaka shigo?.

"Okey".
" kabari kawai, yau nai niyar shigowa wlhy, saboda naga maganin yana aiki, dan kwana
biyunnan baba baya Complain d'in ciwon baya sosai, saikuma wani meeting da za'ayi Na
kasuwa ya rik'eni, amma babu damuwa insha ALLAH da an gama zan taho, saina kwana
kawai".
"Kodai ka hak'ura zuwa goben brother? tafiyar dare batada dad'i aii".

" no, karka damu, insha ALLAH zanzo da wuri, bazan iya hak'uri banga jikin my best daughter
yanda yakeba, batama phone d'in naji muryarta".

Murmushi kawai baba yayi yamik'ama Amatallah wayar. kar6a uncle d'inkine.

Duk da halin datake ciki sai da tayi d'an murmushi, tanason Uncle M.A a rayuwarta, saboda

yanda yake matuk'ar nuna mata kulawa....
Maganarsa ta katse mata tunani.
"My best daughter! baki da lafiya amma brother bai fad'a minba? ya jikin naki?".
A hankali ta lumshe idanunta, saboda jin dad'in sassanyar muryarsa, tana son muryar uncle
d'inta over.
tace, " uncle da sauk'i, na warke ai".
"Kai my best ban yardaba, kinji muryarki yanda tazama very slowly kuwa?. duk da nasan
dama daughter d'ina cool girl ce. anyway koma yaya insha ALLAH yau a jos zan kwana".
" Uncle da gaske?".
"Insha ALLAH my Darling".
" thanks you uncle, please ka tahomin dasu Abul-khair to".
"To amma my best daughter school fa? kokin manta gobe akwai? kiyi hak'uri next time insha
ALLAH zasuzo miki hutu".
Idonta harya tara kwalla tace, " to uncle saika zo, amma ka gaidamin su, hardasu Aunty's da
innani da baba dasu anty Nazeefa".
" okey, zasuji insha ALLAH, saina zo".
Kanta ta gyad'a batareda tayi maganaba ta mik'ama babanta dake kallonta tun d'azun yana
murmushi wayar, duk yanajin hirar d'iyar tasa da abokinsa.
Kar6a yayi suka cigaba da tattaunawa..........✍




*_Assalamu alaikum_*

_please maganar gaskiya a wannan karon bazan turama kowa buk ta PC ba idan nayi nisa,
saboda wasu uzurina dana had'a da typing d'in, inkinga kinmin magana kan turomin daga farko
ban amsakiba karkiji haushi. idan ba yanzu zaki karantaba, please ki tara, amin afuwa�._


*Nasa kogi state acikin jihohin Yoruba, wasu suna ganin kamar nayi kuskure.*
*akan Sani na rubuta hakan, dukda kogi ba tsagwaron Yoruba bane acikinta, akwai wani yanki
Na jihar da Yoruba sukeda yawa kwarai da gaske. shiyyasa kogi tashigo lissfi.*
*kogi state tana iyaka da kwara state ne, kwara kuma k'asar Yoruba ne, kunga dolene
yarabawa su sami kutsawa cikin kogi state ai, kokuma wasu k'auyikansu su shafi jihar, akwai
garin KABBA zamu iya cewa 90% Yoruba ne aciki. So nima bisa binciken masana nake, su
sukasan dalilinsu nadaka kogi cikin yankin Yoruba d'in* Wannan shine hujjata, ba kai tsaye nayiba�.

(Wad'an da sukamin gyara kuma, kumin afuwa ba gwaleku nayiba, saida nayi bincike
nima�, amma ngd da tunatarwa.)

*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu�_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_


*_Bilyn Abdull ce_*

*_HASKE WRITER'S ASSOCIATION_*
```{Home of expert & perfect writer's}```

*Assalamu alaikum*
_nasan zakuyi mamakin fara typing d'ina, so nayi dubu da yanayin buk d'in, dakuma time
d'in damuke ciki, idan nace sai new year lokacin zai k'ure saboda sak'on dazan Isar insha
ALLAH, kuma za6e yana tunkaromu. sai dai kuma banyi alk'awarin muku typing kullumba
gaskiya, ALLAH yasa zaku bani had'inkai._ Love you so much all❤❤


____________________
*_Number 2_*
____________________


.........Matasa ne Kusan su ashirin suka fito daga wani k'aton gida, Wanda kallo d'aya zakamasa
kasan mamallakin gidan yagama jik'uwa da Naira.
Duk d'insu Matasane da shekarunsu bazasu haura daga talatin zuwa k'asaba.
Hayaniyar dasukece taja hankalina Kansu.

Wani yadaka tsale yadire yana fad'in "impossible wallahi!!, bamu yarda da wannan shawaranba,
a raba kawai abama kowa kasonsa yakama gabansa!!".
Wanda alamomi suka nuna shine babbansu yaja birki daga tafiyar dayakeyi, manyan
idanunsa dake jajur yashiga juyawa, ransa a 6ace yace, " kaifa zike! Shiyyasa banason harka
dakai wallahi, wai kai wakafi iya shegene? dama tun agaban Oga saiwani fa zak'ewa kake,
kakama kankafa guy, idan ka kaini bango babu ruwana dawata sanayyarmu ko SIYASAR data
had'amu, am telling you saina maka eyane, ka dai sanni aii".
A fusace zike ya matso yana hura hanci, "kai gagis karka fad'amin mai d'aci mana, kasanfa

bawai zan raga maka baneba, barganin katara wannan sharan yaran naka, dagani harkai Abu
d'ayane ya taramu, shine *BANGAR SIYASA*, to kawai tun muna shaida juna karaba mana
kud'i da kayan harka kamar yanda Oga yace maka, bamu yarda da wata shawarar sai gobeba,
danni da yarana tun yau da daddare zamu fara lik'a posters d'in mai gida. Zuwa dasafe kuma
muga tsageran da zai cireta a garinnan."
Tsaki gagis yayi, ya fiddo kud'in dami guda daga aljihunsa yana harar zike, Wanda yafara
k'ok'arin zaro wuk'a a k'ugunsa, amma ganin gagis ya fiddo kud'in saiya maida wuk'ar yana
gyara riga.

Tafiya take cikin d'an sauri da sassarfa, saboda hadarin daya gama gauraye garin, yanda
sararin samaniya kawai tayi bak'ik'k'irin zai tabbatar maka ruwan yana gab da sakkowa.
Wani d'an lungu tabi, dan a ganinta shine zai zame mata shortcut d'in da zataje gida da wuri.
Gaban tane yay wata fad'uwa, saboda hango gungun matasan anguwarsu marasa jin
magana (su zike), yanda suke hayaniya kawai zai tabbatar maka fad'a sukeyi. jitai kamar
takoma da baya, amma babu dama, saboda tazo gab dasu, wasu kuma sun ganta.
Ta kuma yin k'asa da kanta tana karanta *"Hasbinallahu wa ni'imal wakil"* a zuciyarta. Harta
giftasu babu wanda ya tanka mata acikinsu, saboda hankalinsu nakan kud'in dake hannun
gagis yana irgawa, ga kuma kwali Wanda batasan komiye acikiba dake hannun wani.
Ta kusa k'ure lungun taji sun saki ihu gaba d'ayansu, waigowa tayi dantaga miya sakasu
ihun......?
A razane tazaro ido waje, dan ganin gagis kwance a k'asa wanwar, gawani a kansa yana
zare wuk'a daga cikinsa.
Tamkar Amatallah zata suma dan firgici, ta kwasa da gudu tareda sakin jakkar makarantar ta
a wajen, dama daga islamiyya take.
Gudu take iya k'arfinta, ga ruwa yafara sauka, gakuma duhun magriba data kawo jiki.
Ta gaban majalissar wasu dattijai tabi zata wuce, yawancinsu duk abokan baban tane ma,
Baban natama nanne wajen hirarsa, majalissar tasu rumface, shiyyasa duk da ruwan da aka
fara suna a wajen, saima shirin sallar magriba dasukeyi, wad'anda kuma basa sallan suna
zaune kan tabarmar dake wajen, wasu kuma saman kujerun plastics. A guje tashigo rumfar tana kwala kiran babana! Sun kasheshi, wlhy sun kasheshi.......
Tun shigowarta duk suka mik'e tsaye, harda masu alwala, Wanda ke kusada ita yarik'o
hannunta, danya fuskanci a rikice take.
"K! Amatallah nutsu kifad'a mana miya farune?".
"Uncle wallahi agabana suka kasheshi, na rantse nagansu da idona". sai kuma tafashe da
kuka, jikinta sai rawa yakeyi.

Sukam su zike, gagis ne yakasa kud'in uku, yabama zike da yaransa kashi d'aya, kayan
mayenma dake cikin kwali kad'an ya d'ibo.
Da sauri Zike yace, " miye kake nufi?".
Gagis yace, "abinda kagani, wannan shine Rabon naku, nikuma sauran nida yarana, tunda
mun fiku yawa, kuma munfiku iya aiki, shi Kansas Oga baisan kud'in k'ananun kwari bane
shiyyasa ya had'amu aiki daku, amma gobe zan masa bayani....
Kafin gagis ya k'arasa maganar wani acikin yaran zike ya caka masa wuk'a, yana ''fad'in aiko

zaka fad'a inka mutu".
duk sunga Amatallah wannan yasa koda takwaso da gudu wasu suka biyota. Suna ganin
tashiga majalissar dattijan nan sukaja birki, basu k'arasoba.
'Daya a cikinsu yace, " o shit!! Banzan yarinyar can fa a gabanta K show yakashe gagis,
yanzu yazamuyi kenan? Karta tona mana asiri fa".
Wanda ke kusada shi yaja gajeren tsaki, cikin fusata yace, "ta fad'a mana stupid girl kawai,
magana d'aya ce, kawai kowa ya kwanta da shirinsa, dan tabbas komai zai iya faruwa.....
Bai kai k'arshen maganarba ya hango abokansu guys Na gudu, hakan ya tabbatar musu
fad'a ya kaure tsakanin dabarsu da yaran gagis.
Basu jira komaiba suma suka kwasa da gudu.

Amatallah kam tana kuka tana bama su babanta daya k'araso wajen yanzu dan yin sallar
magriba labarin abinda tagani.
Duk d'insu sun razana.
Kafin su sami damar magana suka hango mutane Na gudu. a take suma suka tarwatse,
Baban Ama... Yaja hannunta suma suka bar wajen, suka nufi gida dan Neman tsira.


*

A tsorace Ammi da ke alwala tad'ago tana kallon Amatallah da babanta.
"Lafiya kuwa baban Ama...?".

" da sauk'i dai kam....... a ta k'aice yabata labarin abin da yafaru".
Ta zaro manyan idanunta da Amatallah ta gada awajenta, tana sallallami da tafa hannaye,
jiki a sanyaye tace, ''to ALLAH ka sauk'ak'a mana ".
Amatallah da babanta sukace amin.

Sallar da baban Ama... Bai fitaba kenan, sai a gida yaja iyalansa jam'i.


__________________________

*KANO STATE*

Kallo d'aya zaka masa ka tabbatar a gajiye yake Driven d'in, a hankali ya furta "ya sallam".
saboda go slow d'in daya hango agabansa, ya sauke ajiyar zuciya, tareda yamutse fuskarsa
mai cikeda kwarjini, a gogonsa ya kalla dake d'aure a tsintsiyar hannunsa Na haggu, ya dafe
goshinsa dan ganin yanda lokacin sallar magriba ya gabato sosai. Gaba d'aya ransa a 6ace yake, dayasan zai gamu da go slow d'inan daya hak'ura yayi salla
kafin ya taho.....
Tunanin sane yakatse saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login