Showing 15001 words to 18000 words out of 109227 words

Chapter 6 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

takatse Ammi........, shiru tayi tareda janye hannunta daga kan
Amatallah, ta amsa sallamarsa, ya tambayi jikin Amatallah, tace da sauk'i sannan tafita.
Har taje k'ofa tajuyo takuma kallon Amatallah dake binta da kallo itama, jiki a sanyaye tafice
zuciyarta na k'una.

Kawai sai Amatallah ta fashe da kuka.
da sauri Uncle M.A yak'arasa inda take yana fad'in " subahanallahi, My Best miya faru da
kuka kuma?".
Kasa bashi amsa tayi, tacigaba da raira kukanta.

Kusada k'afafunta ya zauna yana lallashinta, shikansa gabansa sai fad'uwa yakeyi, gawata
matsananciyar fargaba da yakeji tunda safe, harma zuciyarsa tana raya masa ko jikin babane?.


________________________________

"Ka tabbatar kayi kamar yanda nace, karka bari asamu kuskure fa".
"Oga karka damu kanka, kasaka aranka kawai sun wulla, itakuma bab.. d'in tana hospital,
hawan k'awara yakamata mumata da daddare".
" karka damu, kaje afara wannan aikin first."
"Okey sir, babu damuwa".


_______________________________

Cikin mintuna k'alilan Ammi ta iso gida, a k'ofar gida sukayi kici6is da baba zaitafi salla,
tashiga shikuma yanufi massalaci.
Ramzaki dake la6e bayan wani kwano da aka zagaye bishiyar mangwaro yafito, da sauri
yashige cikin gidan, babu Wanda ya lura dashi saboda duhun magriba daya fara, gakuma garin
da alamun hadari ma.
Ko kad'an Ammi bataji motsin shigowaba, tayi alwala tashige ciki. duk Ramzaki Na la6e
yana kallonta. sai da yaga tashiga falon sannan shima yashigo cikin gidan sosai.
Bayan kamar mintuna biyu ya tabbatar Ammi ta kabbara salla. Sad'af-sad'af yashiga cikin
falon.
Tabbas Ammi taga shigowar sa cikin falon, amma taza6i cigaba da sallarta, dan duk
tunaninta 6arawone, hartayi raka'a d'aya yana tsaye a kanta, kallo yake k'are mata sama da
k'asa, duk da gefen zuciyar Ammi ya tsorata, amma ta daure batabama shaid'an damar cin
galaba akantaba bare ta sallame sallar. Ramzaki sai da yabari tayi sujidar k'arshe sannan yazaro wuk'arsa daga k'ugunsa, dai-dai
lokacin dazata d'ago ya soka mata wuk'ar a gefen cikinta na haggu.�
Babu shiri Ammi takoma Sujudar datayi niyyar d'agowa, maimakin tayi ihu saita fara ambatar
"La'ila ha illallah, muhammadarrasulullah, hazbinallahu wa ni'imal wakil". Wannan shine abinda
keta fitowa daga harshenta, har Ramzaki ya zare wuk'ar, yadawo d'ayan gefenta yakuma
sokawa. Hawayene masu zafin gaske suka fara kwarara a idon Ammi dake a sujuda har yanzun,
Ramzaki nakuma zare wuk'ar saita zube kawai awajen, la66anta dake motsawa suna kalmar
shahada har yanzu nake kallo.

*_Masu karatu nikaina ina cikin rud'ani, wannan rashin imani har INA.�_*

Ramzaki Na tsaye akan Ammi har tagama shure-shure, numfashinta yakoma fita a hankali.....
Dai-dainan baba yashigo gidan, da sauri Ramzaki yakoma bayan labule ya 6oye.
Baba yashigo cikin tsokana yana ambatar " Uwargida ran gida! kina ina? Zokiga angon

gobe........
Maganarsa ta mak'ale a mak'oshi saboda ganin jini Na mamalowa daga inda Ammi ke
kwance, kasa motsawa yayi inda take, yabi jinin da kallo kafin ya maida kallonsa ga Ammi,
takawa yayi a hankali har inda take kwance.
Da sauri Ramzaki ya kwantar da gallon d'in fetur d'in daya shigo dashi, sad'af-sad'af yafice a
falon.
Fetur d'in yafara malale falon.
Durk'ushewa baba yayi a gaban Ammi, yakama hannunta na haggu data dafe gefen cikinta
na dama dashi, a hankali yad'aga hannun, soyake ya tabbatar daga nannne jinin ke zuba ko
kuwa?.
Idanunsa yazaro, Dan ganin yanda jini ke 6ul-6ula, muryarsa na rawa yashiga kiran Saliha!
Saliha!!, ke Saliha!!..........maganarsa mak'alewa tayi saboda ganin hasken huta, yajuyo a
sanyaye.
Kasa motsawa yayi, yay sagade yana kallon wutar dakeci afalon, tanabin duk inda fetur d'in
ya ta6a. ko kad'an baiyi yunk'urin motsawaba, saima matsawa dayayi jikin gawar Ammi ya
kwantar da kansa bisa fuskarta ya fashe da kuka.�
A hankali wutar tafara k'arfi, dan har kujeru sun fara kamawa, duk da zafin wutar na dukan
baba yakasa tashi, motsin kirkima yakasayi awajen, jiyake tamkar an d'auresa da igiya. Sannu a
hankali wutar ta iso inda yake, tuni numfashinsa yafara sark'ewa saboda hayak'in wutar.

Hankalin 'yan anguwa yafara dawowa gidan baba, saboda ganin hayak'i tasaman zinc.
Wanine ALLAH ya nuna masa fitowar Ramzaki daga gidan.
Ihu yafara yana nuna Ramzaki.
Ramzaki naganin haka yakwasa da gudu, hakanne ya tabbatarma da mutane baida gaskiya.
nanfa wasu matasa suka rufa masa baya domin kamashi. wasu kuma suka afka gidansu
Amatallah dan ganin mike faruwane?.

Lokacin dasuka fara shigowa baba harya suma, Dan numfashinsa ya gagara fita, hayak'i ya
sark'eshi, wutarma tafara bin kayansa shida Ammi.
Ihu mutane suka fara tareda d'aukar botikan ruwan dake tsakar gidan suka fara watsawa
k'ofar falon, amma wutarnan kamar sake izata akeyi.

Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un.

Wutarnan batada niyyar mutuwa ko kad'an, wannan yasaka wasu fara Neman 'yan
kwana-kwana. duk da haka kuma anata watsa ruwa, makwafta sai kawo ruwa sukeyi.



******

Jikin Amatallah ne yafara rawa, ta fashe da kuka tana fad'in Uncle babana da Ammina. Dan
ALLAH ka kiramini su, inason ganinsu, Dan ALLAH kirasu........

A tsorace Uncle M.A ke kallonta, ga mamakin rawar jikin datakeyi, duk da luguden daka
da k'irjinsa keyi shima bai hanashi lallashintaba, ya kalli agogon hannunsa, 7 ta wuce, ana gab
dayin sallar isha'i.
Cikin sassanyar muryarsa yace, "Sorry my best, maybe sai sunyi sallar isha'i zasuzo kinji".
Kanta ta girgiza masa, cikin kuka tace, " Uncle kakirasu, inajin tsoro wlhy, sainakeji kamar
wani Abu na faruwa dasu Uncle, kiramin baba to yanzun".
Baice mata komaiba ya fiddo wayarsa ya kira number baba, kusan kira 4 bai d'agaba. alamun
tsorone suka fara bayyana a face d'insa shima, shikansa jiyake kamar akwai abinda ke faruwar.
Zumbur yamik'e yana fad'in "kinga ina zuwa......
Ruk'o rigarsa tayi, "please uncle mutafi tare, Nima zan bika, bazan iya zamaba wlhy inajin
tsoro".
" haba daughter, kiyi hak'uri naje, kinga bakida lafiya, insha ALLAH yanzunnan zamu dawo
tare dasu"....
Kanta ta girgiza musa alamar bata yardaba.
Ya d'anyi shiru kafin yakuma fad'in "to bara naga likitanki nadawo, saimu tafi".
Yanzu batayi musuba ta sakesa.
Fita yayi kamar zaije wajen doctor d'in, yana fita wajen motarsa yaje, yashiga da sauri yabar
asibitin.

Kusan atare Uncle M.A ya iso da 'yan kwana-kwana. jikinsane yafara rawa saboda hango
dandazon jama'a a k'ofar gidan brother d'insa, ga jiniyar motar 'yan kwana-kwana a bayansa,
fitowa yayi da sauri yana bin hayak'in dake turnik'e da saman gidan. Zufa kawai yaji tafara
ketoma jikinsa. Ya kutsa cikin mutane shima yana k'ok'arin shiga cikin gidan. Sai dai hakan ya gagara, saboda zafin wutar dukya gauraye matsakaicin gidan, mutanen
dasuke a cikima duksun fito.
Jirine ya kwashi Uncle M.A lokacinda kunnuwansa suka jiyo masa furicin wani mutum na
fad'in ai Alhaji Isma'il d'in da matarsa suna ciki, wani saurayine akaga yafito daga gidan
da..........
Baiji k'arshen zancenba ya sulale awajen yafad'i a sume................✍




Masoya kumin afuwa�nakasa cigaba da rubutun saboda kuka, wlhy kuma da gaske
nake�

*Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu�*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce_*


_Kina inane *Ummu Basheer!?* maza ki matso kusa, wannan page d'in nakine ke kad'ai, kiyi
yadda kikeso dashi dear, ki tabbata kina can k'asan zuciyar bilyn Abdull, ina alfahari dake,
ALLAH yacigaba da jagoanci a lamarin rubutunki kema my dear, ya raya manasu Abdul ke
d'in tadabance._

*_Happy marriage life Ayush Ilyasu, Ubangiji ALLAH yabaku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba,
yasa alkairi da farinciki a rayuwar aurenku�._*
_writer's d'inmu dasuka hallacci bikin suka wakilcemu ALLAH yabar zuminci�._
Nina naje, Baku ganni bane kawai, INA bayan Maman bobo da sadnaf ne, Ummu abrar ta
6oyeni da hawwer�, saura kuce k'ayya nayi�. A tambayi hassy da Ummu Alisha ma ehe�.




____________________
*_Number 8_*
____________________

Tun Amatallah na sauraren dawowar Uncle M.A har tafara fidda rai, kuka sosai takeyi
Wanda yafara dawo da hankalin mutane kanta, sauka tayi daga gadon tafito, duk da bazata iya
gane motar Uncle M.A ba hakan baihanata waige-waige ba, amma ko maikama dashi bata

ganiba, harabar asibitin tafara zagayawa tana lek'a motocin mutane, a nufinta kozataga uncle
d'inta.
K show yace, "yauwa Oga kaga babyn can, maybe akwai abinda take nema, kaga tama
sauk'ak'a mana aikinmu, basai mun shiga cikiba".
Wata dariya zike yayi, ya lashe la66ansa yana gyara tsayuwa. Kad'an ya bigi kafad'ar k
show yana fad'in " wannan ai tanada amfani kafin ta wulla itama".
Dariya shima k show d'in ya tuntsure da ita danya gane inda ogan nasa yadosa, ahankali
yace, "Oga please nima ko sid'one abani inka kammala".
" hhhhh kar ka damu k show nawa".

Amatallah ta jingina da bango takuma fashewa da kuka, ta tabbata uncle wayau yamata ya
gudu.
Gani tayi wasu doctors biyu da nurses sunfito da d'an gudu, motar ambulance suka shiga ta
asibitin suka fice da gudu.
Tsayawa tayi da kukan tabi k'urar motar da kallo, k'irjinta sai kuma dukan uku-uku yakeyi.
Su zike dake a la6e har yanzu suna kallonta suka fito, dai-daita Kansu sukayi suka nufota,
suna daf da zuwa inda take doctor Joshua yafito yana waige-waigen nemanta, danya zo zai
mata allurar k'arfe 8pm ne yaga bata nan, mutanen dake wajen suke masa bayani akan tafita
kusan 18munutes, shine yafito nemanta. Can ya hangota jikin wata mota ta tsurama waje d'aya ido tana hawaye, ga wasu samari
biyu Na tunkarota. kafin ya k'arasa wajen su zike sun k'arasa, k show ya saka mata
handkerchief d'in hannunsa a hanci.
Da gudu doctor Joshua ya k'araso wajen yana fad'in "kai! Kai!.....
Daga k show har zike sun tsorata, sakin Amatallah sukayi a k'asa, tafad'i yaraf saboda
abinda suka shak'a mata.
Jikin doctor sai rawa yakeyi, bata su zike yakeba, dan ko kallonsu bai kumayiba har suka
fice. Kin kimar Amatallah yayi yakima ciki da ita.
A dai-dai nan motar Ambulance tadawo.

Innalillahi..... Kawai nake maimaitawa saboda ganin wad'anda aka fiddo daga Ambulance
d'in�.
Ammi ne da baban Ama, sai uncle M.A, wanda daka masa kallo d'aya zaka tabbatar a rikice
yake,.
Har aka shiga dasu baba ciki ban iya Na motsaba daga inda nake, saboda tashin hankali.


___________________________

Su zike na fita da gudu sukaci karo da yaran gagis, wad'anda tundaga bayan gidan Mr Pam
suke binsu abaya dama, amma basu saniba.
Daga k show har zike a tsorace suke kallon dabar matasan, wad'anda zuciyarsu tarigada
tagama bushewa, kowanne rik'e yake da makami mai had'arin gaske.
Fitsari kawai k show yafara a wando, Dan yasan babu makawa yau d'innan suma zasu

wulla inda suke wulla wasu.
Babu 6ata lokaci yaran gagis suka far musu kawai, a cikin mintuna dabazasu wuce 20 ba
suka zama labari, tuni yaran gagis suka watse a wajen, sukabar gawar zike da k show kwance
jina-jina.


*******

Ramzaki kam daya kunnama su Baban Ama wuta da k'yar ya tsira shima daga farmakin
matasan anguwar su Amatallah, ALLAH yabashi sa'ar fad'awa d'akin wasu matasa 'yan
k'abilarsu.
Tambayarsa suka shigayi miya farune?.
Ramzaki ya tak'ark'are ya mako k'arya, wai wasune zasu kasheshi saboda sun zagi
yarensu ya rama.
Tuni matasan suka mik'e suna hura hanci, kafin kace me sunshiga zaro makamai kala-kala a
k'ark'ashin katifar d'akin. Wani ramine a k'asan katifar, shak'e yake da makamai kala-kala.
Dad'ine yakama Ramzaki, shima yakar6i biyu suka fice........ ‍♀


*********

Koda yaran gagis suka bar bakin asibiti sai suka nufi gidan uncle d'in zike, Dan sunyi
alk'awarin k'arar da dukkan ahalinsa.
Babu maganar Neman ba'asi ko dalili suka haikema Mr Marcel Wanda baijiba bai ganiba da
iyalansa, hasalima kullum cikin yima zike fad'a yake a kan rayuwar daya saka kanshi. yakashe
kud'i babu adadi akan yayi karatu amma zike yay watsi da maganarsa, sai gashi yau ta
sanadinsa anzo har cikin gida an kasheshi shida matarsa da yaransa biyu�.

____________________________

A asibiti kam lamarin ba'a cewa komai, ALLAH yayima Ammi rasuwa�.
Tunkafin wuta dama tarasu ita, saboda wuk'ar da Ramzaki ya soka mata sau biyu. Baba ma
dai lamarin sai addu'a, danba k'aramar k'onewa yayiba, likitoci kusan hud'une a kansa.
Uncle M.A yakasa zaune yakasa tsaye, jiyake tamkar zuciyarsa zata fito waje daboda
tashin hankali, yana tsaye a k'ofar d'akin da'aka shigadasu baba shida wasu makwaftan Baban
Ama d'in, sai kaikawo sukeyi, da jimamin lamarin, abin tamkar wani film.




*_washe gari_*

A washe gari saiga k'aramar magana tazama babba, domin kuwa ba k'aramar 6arna su
Ramzaki sukayi a anguwar su Amatallah ba.
6angaren yaran gagis ma saita kwa6e, dan kisan su Mr Marcel yayan zike tasaka danginsu
maida murtani, kafin k'arfe 2pm komai ya cakud'e, sallar azuhur ma tagagari jama'a, sai a gida
aka yita.‍♀


_____________________________

Hankalin Uncle M.A yayi masifar tashi, gani yayi inhar yabari suka kai dare a jos to tabbas
dagashi har Amatallah d'inma bawai tsira zasuyiba, musamman yanda yaga ana kawo masu
raunika asibitin, wasuma sun rasu. abinda kuma yak'ara tada hankalinsa shine bayanin likita
akan jiya wasu sunzo sace Amatallah. har zuwa yanzu abunda suka shak'a mata baima
saketaba.
Da sauri yamik'e ganin su doctor Joshua sunfito daga d'akin da baba ke kwance, har yanzu
an hana kowa ganinsu.

"Doctor yaya?".

Numfashi doctor Joshua ya sauke, tareda fad'in lamarin babu sauk'i Alhaji, zafin wutar
hayak'inta yayi mugun ilata lafiyar Alhaji Isma'il gaskiya, amma muna kan aikinmu, zakuma muyi
iya k'ok'arinmu akansa".
Uncle M.A ya jin jina kansa, muryarsa na rawa yace, ''matarfa?".
Shiru doctor Joshua yayi, saikuma yad'anyi murmushi, da sauri yace, " itama dai hakan". bai
jira cewar Uncle ba yay saurin barin gurin.
Cikin sauri Uncle M.A yabi bayansa yana kiran "doctor!".
Harya kama handle d'in k'ofar office d'insa zai shiga ya dakata, saurin maida kwallan sa yayi,
haka kawai yaji yana tausayin Amatallah da wannan mutumin dabaisan dangan takarsa da
iyayen Amatallah d'inba.
Uncle M.A daya k'araso yace, ''please doctor inason muyi magana inhar bazan shiga
aikinkaba".
"Babu damuwa Alhaji, zaka iya shigowa". 'Yay maganar yana shiga office'.
Bayansa Uncle M.A yabi.
Bayan sun zauna Uncle M.A yace, " doctor inason tafiya dasu Kano gaba d'aya, kaga
garinnan kuma harmutsewa yakeyi, dukda bamuna fatan damuwar da'ake ciki tawuce hakanba,
amma sunada buk'atar kulawar gaggawa suda Amatallah, please doctor ka taimakeni".
Cikin tausayawa doctor Joshua yake kallonsa, ya gyara zamansa yana jinjina kai, "nabaka
goyon baya d'ari bisa d'ari Alhaji, nima ina ganin hakan shine mafita. yanzuna nan zan shirya
muku tafiya kawai".
Sosai Uncle M.A yaji dad'i, sai godiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login