Showing 39001 words to 42000 words out of 109227 words
Chapter 14 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
dad'in baki, da dai a baya dai na
yarda, amma yanzu kam ganganne".
Siddiqa ya gyarama kwanciya a cinyarsa yana dariya, " My Neesa kice yanzu ni kinbar yarda
dani Ashe?".
"Ya zance nabar yarda dakai kuwa, na yarda dakai mana, akan wannan maganar daine kam
sai a hankali".
" lallai naga ta kaina, to maida wuk'ar, babu inda Muhammad d'inki zaije my lover, zanje
cikin garine wajen wani abokina, insha ALLAH yanzu zanje na dawo, sonake yau na kasance
daku Ku kad'ai, fitarma danta zama dolene da banyiba".
Murmushi tamasa, harda masa kiss a kumatu.
"Ya mik'e da Siddiqa a kafad'a, " humm my Neesa kishi".
Itama mik'ewa tayi tana dariyar, "yo kaga laifina ne dear?, Kasan kuwa yanda nake jinka
kuwa? ba k'aramin danne zuciyata nakeba idan naga wata mace ta ra6u da kai, amma babu
yanda zanyi, haka ALLAH ya k'addaramin raba dai-dai d'inka da wasu mata". ta k'are maganar
kamar zatayi kuka. Tausayi tabashi, dan shi kansa yasan Aneesa na matuk'ar k'aunarsa fiyeda tunanin mai
tunani, shiyyasa shima yake mata uzuri akan wasu abubuwan, murya a sanyaye yana kallon
kwayar idonta yace, " I love you so much my Neesa".
jikinsa ta fad'a, tahad'ashi shida Siddiqa ta rungume itama tace, "I love you Abadan my
Heartbest".
Sosai yakuma mannata da jikinsa, yana sakar mata tagwayen kisses a wuya.
í ¾í´£ho Uncle Muhammad kazama na......., uhm babu ruwana daií ¾í´.
Lokacin dasuka fito falo tuni Fateema ta shak'i haushi, amma kokad'an bata nuna a fuskaba,
saima wani salon kallo datake masa, hakan kuma saiya hasala zuciyar Aneesa, ta kar6i Siddiqa
a hannunsa takoma batareda tamasa rakkiyarba. Fateema kuwa taji dad'in hakan sosai, ita
kad'ai tarakashi, saida suka gaisa da mai ma yara lesson sannan yayma yara saiya dawo
Fateema tabud'e masa gate yatafi.
Duk yanda Sabi'u yabashi Address d'in haka yabi.
Tarba aka masa ta girma, sai kace Wanda yadad'e da fad'an zaizo.
Iyalansa duk sukazo suka gaisa, shima matansa biyu da yara 7, d'ansa namiji na fari harya
zama d'an saurayi.
Sabi'u yakuma yimasa ta'aziyyar Isma'il, da kuma jimamin wannan rasuwa, dan Alhaji
Muhammad sai da yasanar masa duk yanda lamarin ya afku. sosai Alhaji Sabi'u yay ALLAH
wadai da wanan hali irinnan 'yan siyasar k'asarmu da matasa, yakuma nuna fushinsa akan
yanda irin wad'annan rikice-rikicen kan faru musamman lokacin gabatowar za6e, da an kad'a
tambarin siyasa shikenan kowa yana cikin d'ar-d'ar na tsoron afkuwar tashe-tashen hankula na
rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI* dakan taso a irin lokacin.
Da wanan damar Alhaji Muhammad yay amfani wajen sanar masa manufarsa shida Brother
d'insa, sai dai mutuwa tai musu gaggawa.
100% Alhaji Sabi'u yabada goyon baya, da alk'awarin shima zai shiga a dama dashi a
tafiyar.
Alhaji Muhammad yaji dad'i da karamcin abokin Nasu, nan dai suka tattauna abubuwa da
dama dasuka shafi k'asarnan kuma suke damunmu, musamman ma yankin AREWACIN
NIGERIA.
Abubuwan tamkar an shiryasune daga plan A zuwa Z.
Rikicin boko haram kamar bazai k'areba, ALLAH dai yakawo mana iyakarshi, bayan kisan
gilla da akaima al'ummar arewacinmu, sannan kuma sune ake kira da 'yan ta'addar, sai dai
muna murnar samun sauk'in bomb's sai kuma na satar shanu ya shigo, shima abin mamaki a
arewaci kawai yake faruwa kuma jama'ar yankin ke amsa sunan 'yan Ta'addar. Zaune bata
k'areba fa bayan dak'ile Satar shanu sai kuma Kidnapper's da ayanzu sune ke addabar yankin
na arewacin kasar again.
Shin wannan lamarin bazai Baku mamakiba kuwa? bakwa ganin abubuwan kamar dama
angama tsarasune daki-daki, idan wannan bai tasiriba sai a koma wancan?.
Miyasa komai baya faruwa sai'a arewacin k'asar kawai? alhalin bushewar idanun matasanmu
batakai ga aikata irin wad'annan manyan ta'addacinba.
Ba wai dan ina 'yar arewa nake maganar nanba wlhy, sai sai kawai lamarin kan bani mamaki,
yanda kowanne bala'i sun k'are a Arewacinmu. nasan kuma banima kad'ai ba, duk mai hankali
yayi wannan tunanin.
Shin a ina matsalar takene?.
Manyanmu ne?.
Talakawa ne?.
'Yan siyasa ne?.
Matasanmu ne?.
Kokuwa k'ulla mana akeyi dan a ruguzamu?".
í ½í¹í ¼í¿»ya rabbi kayi gaggawar ruguza duk mai son ruguzamu, kamana maganinsa kafin shi yayi
namu, kahanashi zaman lafiya kafin shi ya hanamu, kahanashi farinciki kafin shi ya hanamu,
kamasa abinda yadace da zalincinsa kafin shi yaci nasarar zalintarmuí ½í¹í ¼í¿».
Ubangiji gareka muke, kuma gareka muke Neman taimako, ya ALLAH karkamana hukunci
da halayen wasu wawayen dake cikinmu masu busashshiyar zuciya wajen aikata sa6onka.
ALLAH ka zaunar da k'asarmu lafiya, kabamu shuwagabbanni nagari masu k'aunarmu dason
cigabanmu.í ½í¹í ¼í¿»
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*í ½í¹í ¼í¿»
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typingâœí ¼í¿»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*í ½í²¡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* â‰
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceí ¾í´™í ¼í¿»_*
____________________
*_Number 19_*
____________________
"Assalamu alaiki". 'Amatallah tafad'a yayinda ta k'arasa ga matsiyar budurwar.
Cikin d'an murmushi ta amsa mata, tareda bata hannu alamar suyi musabaha.
Itama Amatallah saita mik'amata sunama juna murmushií ¾í´í ¼í¿».
Bayan sun gaisa Amatallah ta tanbayeta kotana a department d'in sune?.
" eh". ta amsa mata da kulawa.
''Yauwa sister dan ALLAH ko akwai lecture yanzun?".
"Yes sister, nanda 15minutes insha ALLAH".
" ok ngd sosai".
Budurwar ta jinjina mata kai tana murmushi.
Har Amatallah ta juya zatabar wajen budurwar tace "amma ke sabuwar zuwace?".
Juyowa Amatallah tayi tana gyad'a mata kai.
Budurwar tace, "Nasamu friend kenan? sunana Fa'iza Abdul-hakeem Gwarzo".
" Nice name dear, nikuma Khadija Isma'il Uba (Amatallah)".
"Woow Nice name, sunan mamana kenan".
Murmushi kawai Amatallah ta mata.
Gurinda Fa'iza ta nunama Amatallah kusada ita ta zauna, nan suka d'an fara hira
kad'an-kad'an, dukma Fa'iza ce k'arfin hirar. har dai 15minute's suka cika suka mik'e domin
shiga lecture.
Farin cikin da Amatallah ta tsinci kanta a ciki 6ata lokacine wajen bayyanashi ma.
Tundaga wannan ranar sabo mai k'arfi yashiga tsakanin Amatallah da Fa'iza, itama Fa'iza
Ashe matar aurece, harma takusa shekara da d'an k'aramin cikinta ma.
Sosai suke maida hankali a karatunsu babu maganar wasa.
Yanzu group d'in nasu sunzama su hud'u, Amatallah, Fa'iza, Rita, Goodness, idan ka gansu
abin birgewa, duk kuma kusan shekarunsu d'ayane, Rita 'yar Taraba state ce, Goodness kuma
'yar Kaduna ce, amma duk sunajin hausa, barema Goodness, garama Rita kad'an-kad'an takeji,
bakowacce kalmar Hausa take ganewa da k'yauba. Komai nasu tare sukeyi, bazaka ta6a tunanin mabanbanta k'abilu baneba, babu raini bare
k'yamar juna, idan lokacin Salla yayi su Amatallah sukanje tareda su Rita, saisu sami waje su
zauna a wajen masallaci harsuyi su fito.
Rayuwar gidan Uncle kam agareta Alhamdllh, bata fuskantar matsalar komai, dan Nazeefa
tsaye take a kanta.
Itama kuma batasa wasaba wajen kulada abubuwan dasuka shafi gidan. tsakaninta da
yaran kam sosai shak'uwa tashiga. Ko waya sukayi da babansu saisun bashi labarin Antynsu,
da sweets datake siya musu kullum.
Sosai yakejin dad'in hakan, dan yanason maison 'ya'yansa.
_______________________________
Akwana a tashi babu wahala wajen ubangijin al'arshi, yau ga Aneesa da watanni hud'u a
Dubai, ta murje tayi k'yau abinta, dolene kaganta ta birgeka.
Yau bayan Alhaji Muhammad yadawo gidan a gajiye, ta taimaka masa yay wanka sannan ya
zauna yin bud'a baki, (kasancewar alhamis ne). dukda bawani Cin abincine dashi sosaiba
hakan bai hanata had'a masa 'yan abubuwaba wad'anda bazasu zama almabazaranci ba.
Yana shan shayi suna hira kad'an-kad'an, acikin hirar tasune yake fad'in "my Nessa kifa fara
shiri".
Kallonsa tayi cikeda kulawa, " Dear! shirin me kenan?".
'Dan murmushi yayai, dan yasan yanzu zai tsokaloma Kansa rikicinta, ya kur6i shayin yana
d'aukar remote dan rage k'aran TV, "my Nessa komawa Nigeria mana".
" Dear Nigeria kuma? to saboda mi? kona maka laifine?".
Yanda take jero masa tambayoyin saita bashi dariya, amma saiya gimtse baiyiba, ya ajiye
mug d'in yajawota jikinsa, a hankali yake mata wani salon da yasata narkewa jikinsa, "my Nessa
kinsan dai bake kad'ai bace dani, inada wasu matan ai, kuma sunada hak'k'i a kaina, yazama
tilas Na saukeshi kuma, kiyi hak'uri zaki koma ita kuma Fateema saita zo". Wani k'ududun bak'in cikine yahana Aneesa magana, ta danne kukan da yazo mata.
Jin tayi shiru ya lek'a fuskarta, " my Neesa!".
Idanunta tad'ago ta kalleshi.
yace, "miya faru?".
Yunk'urawa tayi tatashi daga jikinsa, ranta a 6ace tace, " amma ai Fateemar ba lafiyane da
itaba, itakuma d'ayar ai naga makaranta kace tanayi ko".
Guntun murmushi yayi yana girgiza kansa, wato Amatallah Ce d'ayar, batada matsayin
daza'a fad'i sunanta ita.
Hannayenta yakamo ya rumtse cikin nasa yana murzawa a hankali, "hakane My Neesa,
saidaifa kin sani Na Sani wanan ba hujja baceba dazan kare kaina a wajen ubangiji, abindama
yasa kikaga babu Amatallah a tafiyar saboda haryanzun bata gama sabawa daniba, saboda
yanda Auren namu yazo, tana buk'atar nagama koya mata yanda zata saba dani a matsayin
miji kafin tasan hakan a aikace, rashin lafiyar Fateema bazai hana tazo gareniba kingane".
Hannunta kawai ta zare daga NASA, ta tashi tabar masa wajen.
Binta yayi da kallo harta shige bedroom d'insu.
Iskar bakinsa ya furzar, ya girgiza kai tareda cigaba da bud'a bakinsa
****
Tundaga ranar bai sake ma Aneesa maganar tafiyaba, yanata mata dai shirye-shirye da had'a
mata tsaraba.
Fateema ma anan tanata shirye-shirye, dan bazataje da yaro ko d'ayaba, Ummita ma
anasata a school.
Randa Aneesa zata taho ranar Fateema zata tafi.
Koda Amatallah taji batun tafiyar bataji komai arantaba, saima tunanin yanda zasu zauna
da Aneesa ita kuma, tanata Addu'ar ALLAH yasa itama Tamaka kamar Fateema, sauk'in tama
akwai Nazeefa a gidan.
Komai Na tafiyar Aneesa ya kammala, ana gobe zata tafi Alhaji Muhammad yasha
rikicinta, hakadai ya shareta yanata lallashi.
Washe gari su Amatallah sukama Fateema rakkiya har airport, basu baroba saida sukaga
tashin jirginsu. yara basu damuba, tunda ga Anty Nazeefa gakuma Amatallah, garama Ummita
tad'anyi kuka kad'an dataga Ummanta tashiga jirgi ta barta, saida Shehu yace mata allura
Umma zataje sannan tayi shiru.
Daga canma Alhaji Muhammad yayima Aneesa rakkiya, baibar airport d'inba saida yaga sun
taso, harda kukanta kuwa.
Saita bashi tausayi, har yakai ga mata addu'ar ALLAH ya sassauta mata kishinnan nata.
Koda su Aneesa suka sauka Jabeer ne yaje ya d'akkota. tunda ta shigo gidan taketa
faman ta6e baki, dan ganin fentin da gidan yasha, hakama dasuka shiga falon gidan taga an
maido da k'ofar 6angaren bak'i ciki, taita baza ido don son ganin Amatallah, amma komai kama
da ita bata ganiba, daga yara sai Nazeefa. Bayan tahuta taci abincin da Amatallah ta girka kafin ta wuce school, saita hau gyaran
6angarenta, (India tsaftace badaga bayaba Matan Na Uncle, dan Aneesa ma tafi Fateema
tsafta gsky, dukda itama Fateeman bawai k'azama baceba, sai dai Aneesa irin matannan ne
dakomai sunfi sansa k'al-k'al). Bata tambayi kowa Amatallah ba, har yara daketa bata labarin abinda antynsu ke musu,
barema Saifudden dake nanik'e da ita. siddiqa ma nata yawo cikin 'yan uwanta danta fara tafiya.
Amatallah kam yau lectures d'in yammane da ita, shiyyasa saida tayi girki ta tafi school, basu
fitoba sai around 6:pm, a gurguje tamasu Rita sallama tashiga napep d'in dasuka tare mata,
dansu a hostel suke, yau kuma Fa'iza ma batazoba, maybe jikintane dan cikinta yafara tsufa.
Ana kiraye-kirayen sallar magriba Amatallah ta shigo gida, babu kowa a falon dan haka
tashige 6angarenta kawai. hijjab kawai tacire ta tashiga toilet dan d'auro alwala.
Koda aka idar da sallar magriba bata fitoba, dan fargabar had'uwa da Aneesa, da akayi sallar
isha'i sai kawai tashigama wanka, tana fitowa ta shafa mai kawai tasaka bak'ar jallabiya. Yunwa
takeji sosai, bataci abincin ranaba tafita, harta kai k'ofar fita tadawo falonta kuma, tayi haka yafi
sau uku kafin tayi ta maula ta fito. Tana fitowa yara Na sakkowa daga sama suda Nazeefa, da gudu suka iso gareta suna mata
oyoyo, duk rungumesu tayi tad'auki Siddiaqa da itama tashiga rubibin 'yan uwanta.
Sannu da zuwa Nazeefa Tamata, tace, ''badai sai yanzuba?".
"A'a Anty Nazeefa, tun magrib nadawo, kuna cikine shiyyasa. Ashe 'yan tafiya sun iso?".
" kina fita suna isowa, dan inaga daga kaiki ma ya Jabeer yawuce ya d'akkosu".
''Ayya bara Na shiga Na gaisheta to".
"Okey, kishiga tana ciki".
Cikeda fargaba Amatallah ta nufi 6angaren Aneesa d'aukeda Siddiqa, d'ayan hannunta
kuma tarik'e Ummita.
Muryarta nad'an rawa tayi sallama, Aneesa dake zaune a falo tana fiddoma Siddiqa
kayanta ta amsa.
Shigowa Amatallah tayi, Aneesa ta d'ago ta kalleta, sukaima juna kallon ido cikin ido,
kowannensu saida yaji fad'uwar gaba, amma Amatallah saitamata murmushi.
Yayinda Aneesa ta kauda idonta, fuskarta kadaran kadahan, ba ad'aureba bakuma a sakeba
kamar ta Amatallah.
" bismillah ki zauna". Aneesa tafad'a tana zuge zip d'in jakkar kayan Siddiqa.
Zama Amatallah tayi a d'ofane saman kujerar kusada ita, ta d'ora Siddiqa a cinyarta, yayinda
Umminta ta ra6u da jikinta itama, cikin dauriya tace, "ina yini, kundawo lafiya".
" lafiya lau, yamuka sameku?".
"Lafiya lau Aunty".
Daga nan kuma falon yay tsit, sai dariyar Siddiqa da Ummita kema wasa.
Kusan mintuna uku babu Wanda yasake cewa komai, sai kuma Aneesa ta katse shirun da
fad'in " ya karatu?".
Amatallah tace, "Alhmdllh Anty".
''Masha ALLAH".
daga nan kuma suka sake yin shiru, kowa da abinda yake kissimawa a zuciyarsa kan d'an
uwansa.
Mik'ewa Amatallah tayi tace, " bara mu barku Ku huta ". Bata jira cewar Aneesa ba ta fice.
Aneesa tabita da kallo tanamai jin wani irin kishi a k'asan ranta, dukda tafi Amatallah haske
da hanci Dan Aneeaa farace, koma nace k'yau, hakan bai hanata jin zafintaba da fargabar
had'a miji da ita.
Amatallah kam babu komai a ranta, sai dai ta kula halin Aneesa ya banbanta sosai da
Fateema, a ranta tace ALLAH yabani ikon zama da kowannenku lafiya nidai.
Nace, " amin Amatallah".
A canma Fateema ta isa Dubai lafiya, sun rungume juna ita da mijinta cikin kewar junansu,
tun a mota yake nuna mata yayi matuk'ar missing d'inta, sai shafa cikinta yake yana kissing
wuyanta.
Itadai murmushi kawai takeyi da mamakinsa, saikace ba yau wata matar tabar wajensaba.
Koda suka isa gida dakansa yamata wanka, yakuma ciyar da ita abinci, daga nan kuma aka
koma soyayyaí ¾í´,
su Uncle fa babu dama, dole matanka suyita tsula kishi a kankaí ¾í´¥.
í ½íº¶í ¼í¿»â€â™€
_____________________________
Abubuwa suncigaba da faruwa, wasu masu dad'i wasu marasa dad'i.
Zaman Aneesa da Amatallah dai sai a hankali, babu wani kulawa babu kuma gallazama
juna, dan ba gargad'in wasa Uncle yayma Aneesa ba akan zaman lafiyar gidan, yakuma
tabbatar mata inhar yaji wani Abu daban ita zai hukunta, tunda itace babba.
Itama Amatallah