Showing 105001 words to 108000 words out of 109227 words
Chapter 36 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
muma mun gyara d'in,
duk Wanda kaji ankira da suna WANE to wlhy badaga kwance ya tsinto sunanba, saida yasha
wahalhalun rayuwa, SHUWAGABANNINMU fa suna zuwa dai-dai da halayenmu ne, to Ashe
samun tsaftataccen shugabanci da dawwamammen zaman lafiya dayake a hannunmu, idan
muka gyara kammu shugabannin kansu tsoron 6atamana zasu dingaji, dansai kazama nagarine
zamu za6eka mu kaika inda kake kwad'ayin, Ku gyara dan aza6e nagaba sonake naga
MATASANMU ne governor's, kune Senate's president, kune house of Rives kune Minister's
kune kune kune........!!!!".ν ½νΉν ΌνΏ»ββ_
Gaba d'aya wajen yarud'e da ihun sowa, fad'i suke "ALLAH yaja zamaninka, yak'ara maka
lafiya da yawancin kwana.......".
Saikuma suka koma wak'ar girmamawa agaresa (Ku saurara zan reromuku wak'ar
kujiν ½νΊΆν ΌνΏ»ββ).
'Daga musu hannu kawai Uncle yakeyi, bakinsa yakasa rufuwa saboda jindad'i da
farincikin ganin wannan rana mai tarin tarihi a history nashiβν ΌνΏ»βν ΌνΏ»βν ΌνΏ»βν ΌνΏ».
Da k'yar sukayi shiru Alhaji Sabi'u shima yay nasa jawabin cikin girmamawa, dukdai
gargad'ine akan karsu bari ayi amfani dasu wajen haddasa rikice-rikicen za6e, kowa yaza6i
za6insa cikin lumana, kuma suza6i mutumin kirki bawanda zaiyi amfani da mulkiba ya ruguzasu
suda k'asar baki d'aya, suyi amfani da shawarwarin shugaban wannan k'ungiya Alhjai
Muhammad Ahmad Labbo, kada subari kud'i su rud'esu, dansu kwana kad'an zasu k'are,
mutuncinsu dana k'asarsu kam yacigaba da sauka kenan harta koma babu abin moruwa,
suduba gobensu da jibinsu bawai yau d'insuba, shima yagudanar da nasiha mai ratsa jiki,
wadda tasaka matasan jinjinama k'ok'arinsa da yin na'am da wannan nasiha.
d'aya bayan d'aya shugabannin sukaita jawabi da nasiha ga matasan.
Taro yatashi lafiya Alhmdllh, su Uncle dole suka kwana Abuja dan sun kuma gudanar da
taro isu-isu Na manyan k'ungiyar Na jihohin Nigeria baki d'aya.
Su Amatullah duk a NTA suka kalla live. kafin kacemi taron yazagaye kafafen yad'a labaran
social media dana redio's television's, Jaridu, bawai a Nigeria kawaiba harma da k'asashen
k'etare.
Dayawan 'yan SIYASA kam lamarin ya tsoratasu, tabbas matasan da gaske sukeyi gyara
suke buk'ata 100%, gakuma sarakunan gargajiya Na kudanci da arewaci sunbama wannan
k'ungiya goyon baya 100%................βν ΌνΏ»
ν ½ν±ν ΌνΏ»
One luvν ½νΈ»ν ½νΈ»ν ½νΈ»ν ½νΈ»βν ΌνΏ»
[1/25, 5:58 PM] Aysha Galadima: *_Typingβν ΌνΏ»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*ν ½ν²‘
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceν Ύν΄ν ΌνΏ»_*
____________________
*_Number 46/50_*
____________________
Alhmdllh wannan lamari yakuma k'ara fiddo kimar Uncle a idanun duniya, nanfa wasu
manyan k'ungiyoyin duniya na matasa suka fara gayyatarsa domin zama Na musamman,
harma dawasu shuwagabannin k'asashe.
Uncle yazama babban gwaska, tauraro abin alfarin MATASANMU da k'asarmu, kowa burinsa
yayi mu'amulla dashi, dolensa ya ajiye aikin dayakeyi a bayaro, dan nauyi yamasa yawa sosai,
ga iyali ga aikin al'umma.
Dukda wad'annan nauye-nauyen hakan bai hanashi cigaba da tattalin iyalansaba, saima
abinda yay gaba, suma kuma suna tattalinsa dabashi kulawa, kowacce tana kishinsa da
k'ok'arin kafa babbar fada a zuciyarsa.
Duk d'insu yana yabama k'ok'arinsu da jinjinama halin dattakonsu, dan kishinsu shine
yakamata asamu akowanne gidan aure, saidai yasan wani zafin kishin yakan had'a da zalincin
wasu mazanν ½νΉν ½νΉ.
ALLAH dai ya shiryesu Uncle.
**************
Ana gab da za6e sukasha binkin Aysha da Dr yazeed, Wanda Uncle ne komai a bikin, duk
wata hidima daya kamata iyaye suyi shine yayma Aysha, kuma baigazaba wajen zuwa takanas
ya fad'ama danginta komai, harma da rok'onsu wasu sushiga lamarin auren, koba komai dai
d'iyarsuce, kimarsa da halin dattako yasakasu nad'o gari zuwa bikin, tabbas jikinsu yayi sanyi
daganin Goodness (Aysha) bata rasa komai Na rayuwaba, saima d'aukaka da ALLAH yak'ara
mata, ga miji ga karatunta mai yankeba, Wanda fatansu tasha wahala sabida rashin tallafinsu, a
haukarsu hakan zaisa tadawo addininsu, shiyyasa suka koreta, to Ashe Na kwarai basa
k'arewa, saigashi ALLAH yaymata nasibi da samun wasu dagin masu k'aunarta.
Bata nuna musu komaiba, saima kar6arsu da nuna musu har yanzu sunada muhimmanci a
rayuwarta, dan ba'a canjama tuwo suna.
Su Ama.... Sune amarori k'irjin biki.
Ahakadai taro yatashi lafiya, amarya tatare gidan mijinta, Innani harda hawayenta Na rabuwa
da Aysha, dan harga ALLAH tana k'aunar yarinyar har cikin ranta.
To shatu ALLAH yabada zaman lafiya da zuria d'ayyiba.ν ½νΈ»ν Ύν΄ν ΌνΏ»
************
Za6e yagudana cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yanda su Uncle sukayi fata,
Alhmdllh kuma ansamu biyan buk'ata daga matasan wajen za6en shugabanni Na gari masu
kishin k'asar dason cigabanta.
Sannan matsan dayawa sunsami wasu fannoni Na madafun ikon k'asar , kamadaga
ministers, Commissioners, da wasu fannoni daban-daban Na muk'amaiν ½ν±ν ΌνΏ».
Saimuce ALLAH yatayaku rik'oν ½νΈ».
******* ****** *******
Yau takasance Juma'a, tunda Uncle yadawo sallar juma'a shida yara bai sake fitaba, sukayi
Lunch gaba d'aya kamar yanda yazama doka yanzu agidan, duk weekend tare sukecin abinci
suda yaransu.
Sallar La'asar tasaka taron firar watsewa, Uncle da yara suka tafi masallaci su Aneesa kuma
kowa tashige d'akinta.
Da sauri Amatullah tak'arasa gaban gadon ganin Raihana dake barci Na neman sakkowa,
tatashi tuni, kasancewar yarinyar tanada matuk'ar hak'uri ko kuka batayiba, tagaji da wasa
agadon shine tafara k'ok'arin sakkowa, ALLAH ma yakawo Ama... d'in datasha k'asa.
Dungure mata kai Ama... tayi tana fad'in "mamana dakin fad'o Aida kinjamin masifa wajen
Uncle nasan bawai zai ragamin baneba".
Kamar Raihana taji mi Ama... ke fad'a saita ta6e Baki tana niyyar yin kuka, rawa Ama...
tafara mata tana rera mata wak'a kamar yanda take musu itada Rayyan idan suna rigima.
Tuni Raihana tayi shiru takoma 6alle Baki tana dariya, Ama..... ta sauketa tana dariyar itama,
yauwa Ammi Uwa mai dad'i, zauna kiyi wasa nayi salla kafin Rayyan yatashi shima, yau inada
Shiga kitchen".
Idar da sallarta babu dad'ewa tajiyo kamar ana magana sama-sama daga babban falo,
kuma tamkar muryar Aneesa.
Cire hijjab tayi ta d'auki Raihana dake wasa a k'asa tafita (dan tuni yaran sunama rarrafe).
" momyn yara lafiy......."
Maganar Ama... takatse lokacinda idonta ya sauka akan zee-zee dake zaune itada Rita
dawasu 'yammata biyu Wanda duk Amatullah ta sansu amma ta manta sunansu.
Aneesa ta katseta da fad'in "kokin sansune Auntyn yara?".
Sosaima kuwa, aiduk school mate d'inane, ''amma lafiya kuwa Rita?".
Yatsine fuska Rita tayi tana wani taunar cingom, a yangance ta nuna zee.
Ama.... Ta maida kallonta ga zee d'in, ''Zainab lafiya?".
Saida Zee tamata wani kallon sama da k'asa sannan tace, "maigidan nazo nema".
Fateema dake fitowa tace, " maigidan kuma? shikam Nurri miya had'ashi da wad'annan masu
kamada kilakin?".
Daga zee har muk'arabanta babu wacce ta tanka, saima taunar Cingom sukeyi, jikake k'ass!
k'ass!! k'ak'as!!!.
Saida suka gama shan k'amshinsu sannan d'aya daga cikin 'yanmatan biyu tace, "Amaryarku
ce tazo gaisheku ".
Kallon juna Aneesa da Fateema da Amatullah sukayi, Aneesa sarkin rashin hak'uri tafara
lailayo musu zagi.
K'in tankawa sukayi, saima cigaba da iya shegensu sukayi.
Ana haka maigidan yadawo, kallon matan nasa dasuka tsareshi da idanun tun shigowarsa
yayi, " lafiya kuma kukam?".
Aneesa Ce ta nuna masa su zee tana k'ara kumbura baki.
Gabansa yafad'i, azuciyarsa yace yarinyarnanfa ta gundureni, yanzu abin yakai harma
gidana..........?
Fateema ta k'atse tunaninsa, "Nurri waisu waye sune?".
Kallonta Uncle yayi, sannan ya kalli yaransa dake tsaye cirko-cirko suna kallon iyayensu da
wad'annan bak'i dabasu san kosu wayeba.
" Abulkhairi ja k'annenka kuje tsakar gida kuyi wasa, kar Wanda yadawo sai an kirasa".
"To Abbu".
Suna fita Uncle ya kalli su Zee.
" miya kawoku gidana Zainab?".
Kanta ta sunkuyar k'asa tana wani murmushi, "nagane kusan 2weeks baka picking calls
d'ina shiyyasa nace bara nazo naga lafiya".
Tsayuwarsa yagyara sosai, hannayensa zube cikin aljihun blue d'in jallabiyarsa, ya fiddo
d'aya yashafa gemunsa sannan ya maida, cikin sauke numfashi yace, " k'alau nake, kawai
ayyukane sukamin yawa, ngd".
Yana gama fad'a yanufi samansa batareda yakuma kallon kowacce acikinsuba, harsu
Amatullah d'inma.
Wani mayataccen kallo zee tabishi dashi, yanda ma yake taka steps d'in benen kawai abin
birgewane, harya kai k'arshe kuma bai juyo ya kallesuba.
Su Aneesa suncika sunyi FAM, shin me mijin nasu yake nufine? Budurwar tasace kenan da
gaske?.
Ai bak'inciki hana Amatullah maganama yayi, saita juya 6angarenta kawai.
Aneesa ce tafara masifa, "to gayyar tsiya arna a idi sai a tashi abar mana gida ko, tunda bana
gado baneba".
Su Rita zasuyi magana Zee ta hanasu, tamik'e tsaye tana fad'in " kutashi muje, karku wani
damu kanku, kwana nawane nazama matar gidan nima, kowacce shegiya acikinsu saita bar
gidan da k'afafunta, dan nikad'ai nakeson kasancewa da abin sona, duk d'unsu basukai
matsayin Na had'a kishi da sub.......
Dukan da Aneesa takaima bakinta yasakata yin shirun dole, tadafe baki "kai kai nikika
dakarma baki?"....
" andaki bakin naki, Ku kama gabanku ma kafin mu jigataku a falonnan''. Cewar Fateema.
Kwafa su Zee sukayi suka fice.
Fasifa k'awayen nata suka hau yi bayan sun fita, akan miyasa bata bari sun koyama
matannan hankaliba.
Tace, "kubarsu, lokacinsune, daga sanda nashigo gidan babu mai sake yin tari acikinsu, kudai
kusaka ido kusha kallo."
Dariya suka shek'e da ita damata jinjina.
Koda su Zee suka fita sai Aneesa da Fateema suka nufi saman Uncle, a zaune suka iskeshi
hankali kwance yana searching tasha a TV, sallamarsu kawai ya amsa batareda ya kallesuba,
dan yasanma miya kawosu.
Fateema tace "wai yanzu nan Nurri wannan kuma wacece?".
Kallonta kawai yayi ya kauda kansa,
Aneesa takuma maimata masa tambaya, " Dear maganafa mukeyi! Wacece wannan kilakin?".
"To mikukeso Na fad'a muku? Nace ba abinda kuke tunanin bane, kumin kallon mayaudari,
kokuwa nace sona take ni bana sonta ku kirani mak'aryaci, inama mai baku shawarar karku
tasirantar da abinda bakuda ilimi akansa a zuciyarku.
Babu wacce ta tanka masa acikinsu, sukayima ficewarsu suka barmasa falon.
Kallo kawai yabisu dashi, ya sauke ajiyar zuciya ta 6acin rai, tabbas lokaci yayi dazai takama
yarinyarnan Zainab birki akan haukarta, tunda har tsaurin idonta yakai ta kwaso k'awaye tazo
masa gida wajen iyalansa, harma tadunga musu furuci mara k'yau, (dan yana jiyo duk abinda
yafaru bayan barinsa wajen), iyalinsa sune mutuncinsa, martabarsa da dukkan sirrinsa, bazai
lamunci wata ko wani ya raina masa suba ko 6ata rayukansu, yayi kwafa yana jingina kansa
jikin kujerar da lumshe idanu.
Yakai tsawon lokaci yana tunani awajen kafin ya sakko k'asa, babu kowa a falon, yarama
suna tsakar gida suna wasa, ya kalli 6angaren Aneesa yaga arufe, Fateema ma a rufe, saiya
nufi Na Amatullah.
Tunda Ama... tajiyo k'amshin turarensa ta ajiye Rayyan datake bama nono tashige
bathroom, tanajin Rayyan d'in ya fashe da kuka amma bata kulaba tarufe bayin.
Da sauri Uncle ya k'araso ya d'aukeshi, jijjigashi yafraayi yana fad'in "oh my brother na, waye
yasaka kuka? Ina Antyn tajene?".
Rayyan yayi shiru tareda lafewa jikin babansa, sai ajiyar zuciya, zama yay falon yana jiran
fitowarta, amma bulum, mamaki yakamashi, yatashi yalek'a bedroom d'in babu kowa, sai
Raihana a kan gado data koma barci, zama yayi abakin gadon yana jiran fitowarta, nanma shiru
kakeji. Ama.... kuwa zamantama tayi a toilet d'in tana charting hankalinta kwance, duk kuma bidirin
da Uncle keyi tana jiyoshi. tashiyay yafara knocking d'in k'ofar bathroom d'in, amma shiru kakeji.
mamaki yakamashi, kodaima bata d'akinne? wannan tunaninne yasakashi ficewa da Rayyan a
hannu, tsakar gida yafita inda yaran ke ball, zama yay yana kallonsu da tunanin lamarin matan
nasa fal a kansa, wato dai sun had'e masa kai kenan, yay murmushi da k'arajin k'aunar matan
nasa a ransa.
Kiran Sallar magriba tasakashi tasa yaran maza gaba suka tafi masallaci kamar yanda
yasaba, yabama Ummita Rayyan suka koma falo itada Siddiqa da mah-mah.
Jin sunfita masallaci Ama.... tayi sallah sannan tashiga kitchen nata, tadafa cus-cus.
taimaza takai masa nasa ta sakko kafin su dawo.
Koda yadawo bai nemesuba, yaransa yatasa gaba suka tafi falonsa, acan sukaci abinci
sunata masa hirar makaranta, shikuma yabiye musu, dan yau sune abokan hirar tashi.
Saida yaga wasunsu sun fara gyangyad'i sannan yatashesu, yarakosu k'asa, kowa yashiga
d'akin mamansa, shikuma yashiga 6angaren Ama.... domin kaimata Rayyan da shima yay barci.
Kwance ya taddata tana bama Raihana nono, wadda keta d'aga k'afa d'aya tana wasa
dashi saboda dad'in shan nonon datakeji. Kallo d'aya Ama... tayi masa ta kauda kanta, guntun
murmushi yayi, ya sauke Rayyan dake a kafad'arsa saman gadon, baimata maganaba yabud'e
dirowar yaran ya d'akko kayan barcin Rayyan ya fara saka masa, sai lokacin idon Raihana
yakai Kansa, sakin nonon tayi da sauri ta rarrafo wajensa tana murnar ganinsa (yanda Uncle
yake tattalin yaransa da yawan d'aukarsu yasa sukayi mugun sabo dashi, zakiga duk k'iwar da
yaronsa zaiyi dawuya shi yayi masa), d'aukarta yayi yafara cillata sama tana dariya shima
yanayi, sai Rayyan kuma yasaka kuka shima a d'aukesa. dariya Uncle yayi tareda zama
yajawoshi jikinsa shima yana fad'in "jealous ko my Sweetheart".
Amatullah dai duk tana jinsu amma tayi kamarma batasan sunayiba, shirin barcinta kawai
tayi tazo gefen gadon ta kwanta.
Shima shareta yayi, saida yaga ya lalla6a yaransa sunyi barci sannan yatashi ya fice.
Mintuna k'alilan yadawo bayan ya shishshiga sashen su Aneesa yayima yara addu'a yafito
bai kula kowaccensuba. Shi dariyama suke bashi wlhy.
Idon Ama.... biyu, tanajin sanda ya shigo harya kashe fitilar d'akin ya hawo gadon.
6oyayyar Ajiyar zuciya tasaki, shikam yayi tashi a fili yana fad'in " I miss you my heartbest".
Shiru tamasa.
Acikin kunnenta yace, "wai duk kishinne ginbiyata? kinsan ko matan duniya sun k'are babu
abinda zanyi da yarinyar can, yakamata Ku shedeni aii, amma keda 'yan Uwanki kun had'e min
kai kunata fushi dani".
"Fushinmi zamuyi dakai, namu ALLAH ya sanya alkairine aii, miye namu danzakayi
amarya".
Sassanyan Murmushi yayi yana shafa kanta, ganin kalaman baki bazasu mataba yakoma
salon dazata fahimcesa. (ν ΌνΏββnayi nan).
Bayan wani d'an lokaci Na koma, saina taras Uncle Na lallashin Ama... dake kuka, yabata
labarin tundaga farkon had'uwarsa da Zainab (zee) har zuwa yanzun, yak'are damata kalaman
kwantar da hankali da lallashi, ya tabbatar mata itace autar mata a gidansa har Abadan insha
ALLAH. cikin dai hikimarsa ya shawo kanta harta yarda dashi da bashi hak'uri. Yay dariya da kuma rungumeta yana mata daddad'an kalamai.
Hakama Aneesa saida yakoma d'akinta ya lallashi abinsa, damata bayani dallah-dallah akan
zee kamar yanda yayma Ama...., itama Fateema hakan yamata, duk suka gamsu da komawa
tattalin mijinsu tamkar da, amma saida suka saci number zee a wayar Uncle suka had'a kai su
uku bayan sun kirata sun saka Hans Free suka mata tatas da gargad'i mai zafi akan mijinsu.
Hakanne yasaka zee kiransa tana kuka dafad'a masa abinda matansa sukai mata, yana
k'ayataccen murmushi yana saurararenta, saida takai k'arshe sannan yay k'aramar dariya yana
gyara zama a kujera (dayake a kasuwa yake).
Cikin sasaanyar muryarsa dake kashe ga6o6in Zee yace
"To kinga ai saikiji gargad'insu kifita hanyar mijinsu, nidai babu ruwana, tuni na sanar dake
banida burin k'ara aure, matana sun isheni, dan haka kisama zuciyarki salama ki sami miji kiyi
aurenki, nabarki lafiya inakuma baki shawarar karkiyi gigin sake zuwa gidana, Dan babu ruwana
idan matana suka miki wani Abu, nid'in mijin hajiyoyine, ALLAH yabamu alkairi.
Tundaga wannan ranar zee tafita harkar Uncle, bata sake kiransaba balle turo masa
messenges.
Haka kuma rayuwar tacigaba da turawa.