Showing 72001 words to 75000 words out of 109227 words

Chapter 25 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

maido kallonsa kanta, " my best kinyi k'yau da goyon kuwa".
Murmushi tayi kanta a k'asa tace, "ngd Uncle, kadawo lafiya".
Still murmushi shima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujerar yana kallonta, " ba godiya
zakiminba tunda ba k'yautar Siddiqar nabakiba, kawai kema kidage ki haifomin naki".
taji kunyar maganarsa, Dan haka ta kauda kanta gefe tana murmushi.
Yasa hannu yakamo nata, cikin zolaya yace, ''kokuwa yau zamu samune ma kawai nayi
shiri?".
Batasan sanda ta dubeshiba tana zaro ido waje, shima yayi yanda tayi, sai suka tuntsure da
dariya kuma.
Tace, "kai Uncle".
Yace, "ALLAH my heartbeat ".
Murmushi kawai tayi, shikuma yashafi kumatunta, "Matsoraciya wasa nakeyi, sorry nataho
Na barki a school ban nemekiba, 6atamin rai akayine".
'Dan kallonsa tayi da mamaki, har zatayi magana saikuma tayi shiru, gwarama kawai tabarsa
a yarigata tahowar.
"Fad'i mana".
Yayi maganar idonsa akanta.
" a Uncle babu komai, gashi can ana kiran salla".
"Alhmdllh" yafad'a tareda mik'ewa yashiga bedroom d'insa, babu dad'ewa yafito, da alama
alwala yayo da brosh. Zama yayi inda ya tashi, yaci dabino uku yasha ruwa kafin yamik'e yana
shafar gefen kumatun Amatallah, "bara naje masallaci babyna".
"Adawo lafiya" Amatallah tafad'a a kunyace".

Itama sakkowa tayi danyin sallar, ta sauke Siddiqa agadonta tashiga bayi.
Su Uncle basu dawoba saida akayi isha'i, zuwa sannan tad'an gyara fuskarta da hoda da
kwalli da d'an janbaki kamar yanda Anty maijidda da Nazeefa suka gargad'eta akan bakoda
yaushe ake zuwa wajen miji fuska a kod'eba.

Ranar dai Uncle yaci girkin Amatallah yana mata Santi, itako sai dad'i takeji tana dariya,
daga Fateema har Aneesa babu Wanda ya tanka, yara kuwa suna taya Abbunsune.
Yauma a d'akinta ya kwana, tasha kunya kamar jiya, koma nace fiye da jiya, Dan yaukam
Uncle kasa barinta yayi harda 'yan wasanni, Wanda ganin ta tsorata yak'yaleta daga baya
sukasha barcinsu, dukda yarigata barci ita tsorone ya yanata saida taji yayi.



*_5days ogo_*.

Kwanakin Amatallah 6 kenan da kar6ar miji, a kwana shidannan ba'a maganar shak'uwarsu,

dan koyaya dai tasaki jiki dashi, dama kuma hakan shine fatan Uncle d'in. gashi kuma gobe
Fateema uwargida zata kar6eshi ko Aneesa, duk kuma sai Amatallah taji babu dad'i, koba
komai tasaba da kwanciyar dasukeyi tare a gado d'aya.
Da daddare suna kwance, barci sukeyi hankali kwance, Amatallah Na jikin Uncle ta
dabaibayeshi kamar zata shige jikinsa. bugun k'ofane ya farkar da Uncle, ga Amatallah kam
hakan bamai sauk'i baneba, saboda shegen nauyin barcinta.
Da k'yar yazame Amatallah a jikinsa yatashi gabansa na fad'uwa, tabbas yasan babu lafiya,
yakumafi kawo hakan ga Fateema.
Ilai kuwa yana bud'ewa yaci karo da Aneesa wadda take a rikice, sai yarfa hannaye take tana
safa da marwa.
Yana bud'e k'ofar tayo kansa, " dear Umman yarace babu lafiya, ina k'yautata zaton ko
nak'uda wlhy......"
Abinda yafaru shine tun farkon dare bayan Uncle yashiga sunyi sallama takejin babu dad'i
dajin alamomin ciwo, amma harya fita bata iya fad'a masaba dankarya tashi hankalinta, saima
ALLAH yakawo barci ya figeta da wuri, acikin barci ta farka da matsanancin ciwo, cikin azaba ta
d'akko wayarta da nufin kiransa, saidai takira har sau biyu bai d'aukaba, hakanne yasata maida
akalar kiran ga Aneesa. Arikice Aneesa tashigo wajenta, ganin nak'udace ta d'auke yaran
d'ai-d'ai tamaida 6angarenta, shine taje ta tado Uncle bayan itama takirasa bai d'agaba.
Shikuma ya danne wayarne da filo harta shiga silent bai saniba, wannan ne yasa bai d'aga
kiransuba.
Har rige-rigen shiga 6angaren Fateema sukeyi itadashi, zuwa sannan kuma Fateema
nak'uda gadan-gadan.
Aneesa tace dear mutafi asibiti mana".
"Neesa kalli agogofa, 2:41am akwai had'ari gaskiya, mudai bata taimako muga ko ALLAH
zaisa mudace ta haihu lafiya".
Aneesa tayi na'am da hakan, addu'a Uncle yafara tofama Fateema a ruwa, hannunsa
rik'eda d'ankwalinta yana share mata gumi. Aneesa kuma Na taimaka mata dawasu dabarun...
A wannan time d'inne kuma Amatallah tafarka arikice saboda mafarkin Anty Fateema datayi
tana kuka, ta laluba babu Uncle, ai babu shiri ta wantsalo daga gadon, hijjabi kawai ta d'ora a
saman kayan barci ta tafito, tundaga falo tafara jiyo nishin Fatima da maganar Aneesa tana
fad'in daure Umman yara, insha ALLAH kin kusa. Wani nishi da Fateeman tasaki yasaka Amatallah fashewa da kuka saboda tausayi, saikuma
tad'an tsagaita taji kukan jariri ko murnarsu Uncle d'in da haihuwar amma saitaji tsitt, saima
gauron numfashi da Uncle yasaki tareda fad'in "Fateema!!"...............✍


mun shiga d'ari, kardai Uwargida.....ba ruwana�.






One luv my Sweet fana











*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*�
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce_*


____________________
*_Number 29_*
____________________

"A'a dear karka damu tana numfashi, nakula tagajine kawai......
Aneesa batakai k'arshen zancenba Fateema takuma yin wani nishin mai k'arfi saiga jaririya
ak'asa tana watsal-watsal, atare suka furta Alhmdllh.
Amatallah ma ajiyar zuciya ta sauke, tana dariya tana kuka, Uncle yafito d'aura ruwa da
Aneesa ta buk'ata ya ganta tsaye ta jingina da Bango idonta arufe, ganin tana kuka da dariya
saita bashi tausayi, yajawo hannunta ya rungumeta yana fad'in ''to kukan ya Isa haka ALLAH ya
sauketa lafiya, yaushema kika tashi?". Tana share hawayenta tace, " Uncle tun d'azunne".

"To shiga ki taimakawa Aneesa Ku gyarata bara Na d'ora ruwan zafi".
" to Uncle ".

Tsaf Aneesa da Amatallah sukaita hidimar taimakon Fateema, Aneeaa taima jinjira wanka,
Amatallah ta gyara wajen, yayinda Uncle ya taimakawa matarsa shikuma, kafin Safiya komai
yayi tsaf, tasha tea ta kwanta itada sargad'ed'iyar jaririya dansu huta. ALLAH ma ya taimaki
Amatallah lecture biyune da ita suma duk Na yammane. Da safema bayan sunyi sallar Asuba basu hutaba, saida sukaga yara suntafi makaranta,
Uncle kam yana d'akinsa yanata barci tunda suka dawo salla.
Ai yara Na tafiya daga Amatallah har Aneesa kowacce takoma gado, dama yara tea and
bread suka basu Dan Neman sauk'i.
Gidan yayi tsit, mai jegoma barci ta takeyi Na ramuwar kusan kwanaki, Dan tunda suka
dawo bazatace ga randa tasamu isashen barciba, kullum rabi da rabine, itadama tafiya nak'udar
tsaye, shiyyasa haihuwar takanzo mata da sauk'i kuma randa tatashi.
Sai kusan 9 Uncle yafara tashi, shima yau dai kasuwa dama kawai zaije.
Yasha mamakin jin gidan tsit, Fateema yafara lek'awa yaga har lokacin barci take daga ita
har jinjirar, ya lek'a Aneesa itama, tayi d'ai-d'ai abinta a gado, ta danne Siddiqa da k'afa d'aya
alamar k'ila barcin taso hanata shiyyasa tamata haka.
Murmushi yayi yafito zuwa d'akin Amatallah, nanma abin yabashi dariya yanda tabaje abinta
tana shak'ar barci, kansa ya girgiza kawai. Aransa yace lallai su mata anji jiki yau.�
Kitchen yashiga abinsa, ya had'a tea da soya kwai uku yad'auki bread yafito, shikam da
yunwa yatashi yau, kodan jiya dayasha ruwa bai wani ci abin kirkiba saboda zuwan alhaji sabi'u
gidan, bayan tafiyarsa kuma barci ya takurashi dole ya kwanta batareda ya nemi abincinba.
Dole yatashi da yunwa kuwa, ga matan nasa yau kowacce taji jiki wajen kar6ar hauhuwa. A falon k'asa yazauna yayi break fast d'insa, kafin yatashi zuwa d'akin Amatallah, har yanzu
barci ta takeyi, waya yad'akko yafito babban falo.
Baban Fateema yakira kawu yakubu, ya gaidashi a ladabce kafin ya Sanar mass ansami
k'aruwa, kawu yakubu yamasa barka da addu'a ga jaririya kafin suzo.
Daganan Anty maijidda yakira itama, saikuma Nazeefa Dan bazai iya fad'ama Innani ba,
baba kuma bayama iya waya sosai saboda ba'ajin maganarsa da k'yau. Dan danan dangi aka
rud'e da farin ciki.

Sai wajen 10 daga Aneesa har Amatallah suka tashi, hakama mai jegon kanta, shima
hayaniyar su Nazeefa ne ya tadasu, dan danan gida ya kacame da surutu saboda dangi dasuka
fara cikashi.
Dole Uncle yay shiri yabar musu gidan zuwa kasuwa.
Can d'inma manyan kasuwar yasamu suka zauna meeting akan kafa k'ungiyar matasa,
dolene kowanne abun alkairi akwai k'alubale acikinsa, a tashin farko Uncle baisamu had'in kan
wasunsuba, dukda dogon bayani Na gamsarwa dayay musu, wasuma saisuka fara d'auka
Siyasa yakeson shiga kawai, dukda ransa ya6aci haka ya danne, yasamu mutane hud'u kacal
acikinsu dasuka aminta da tafiyar tasu, hakanne kuma yad'an rage masa 6acin ransa.
Bayan sun kammala yakira Alhaji Sabi'u ya labarta masa yanda sukayi.
Hamdala Alhaji sabi'u yayi, yace, "to inaga zuwa yanzun saimu zauna kuma mu tattauna

kafin tsare-tsare su biyo baya, yanzu dai munada manyan mutane kusan 10 kenan, kuma
kowannenmu babu matsalar rayuwa dazata takurasa yakasa fidda d'an wani Abu Na taimako
koda 5k ne kacal aduk wata".
" wannan gaskiyane".
"Yawwa to saimu zauna kenan a tattauna, insha ALLAH zan shigo wajjen naka zuwa dare
nayi barka, daganan saimu tattauna".
" babu damuwa Alhaji ngd sosai, saikazo".
Daga haka suka yanke wayar.

Badan Amatallah tasoba taje makaranta, tasha tsokana wajen su Fa'iza kuwa wai itama
insha ALLAH bad'i iyanzu itace zata haihu musu, ai ko ranarma dai zee tasha harara kamar
kullum da Amatallah kemata (itako zee batama San Amatallah tana yiba ma�.)
Bayan antashi suka ajiye magana akan ranar asabar zasuzo musu barka, dan gobe Friday
basuda lectures ma ko d'aya.


____________________

Washe gari kuma Aneesa ta kar6i girki, Amatallah tashan kallo, kai kace Aneesa zata canja
gidanne, saboda shirye-shiryen kar6ar boss.
Washe garima Aneesa Nata rawar k'afa, ko kunyar 'yan barka bataji ma, saima shi Uncle
d'in take bari da kunyar.
Su Fa'iza dasukazo barka sukace kinga yanda ake tattalin miji aii, wlhy kimik'e idanma zaki
mik'e, yanzu dai mijin nakune Ku biyu, tunda Uwargida tana jego, nanfa suka shiga fanfata da
koya mata abubuwa, su goodness masu ido bud'e kam ai salon yanda ake soyayya iri-iri suka
shiga koya mata, Fa'iza tasaki baki tana sauraren ikon ALLAH itada Amatallah, duk da tarigaya
tasan yan dama rayuwar k'abilunnan take, baruwansu iyashegensu sukeyi tun suna a waje,
saikagama yarinya tabaro k'auyensu tazo takama d'aki a binni wai tazo neman kud'i, kuma
bazata ta6a amsa sunan ita karuwa baceba (ALLAH ya k'yauta dai), Fa'iza kam girman Kano
Ce, bakomai tasani gameda suba sosai.
Haka dai sukasha hirarsu suka tafi.

Bayan Aneesa tagama kwanakinta Uncle yadawo hannun Amatallah, tabbas yaga canji a
wannan karon, danta rage tsorata idan ya ta6ata, kuma tasaki jiki dashi babu laifi, dukda haka
kuma bai nemi komai gareta ba ya had'iye kwad'ayinsa Dan bata lokaci, Duk da kuma acikin
muguwar zak'uwa yake da son kasancewa da ita d'in, hakanne yasaka Ama... Sakin jiki dashi
sosai, aganinta yabarta bayanzuba, k'ilama saita kammala karatunta(zaki bayani lol�).


***********

Akwana atashi babu wahala wajen Ubangiji, yau kam kwanan Fateema shida da haihuwa,
gobene sunan baby, a yau d'inne kuma Uncle zaidawo hannun Amatallah bayan yagama kwana

biyu ga Aneesa.
Nazeefa data dawo gidan tun haihuwar Fateema ta fahimci babu abinda yashiga tsakanin
Amatallah da yayansu, hakkane yasata k'udirin kafa musu tarko yau sudukansu, tasamu Anty
maijidda ta sanar mata cewar sutafi plan B akan Amatallah d'in, dukda bata fito fili ta sanarma
Anty maijiddah komaiba, amma itama tadad'e da fahimtar Amatallah har yau batasan mijiba,
kodan yanda bata kishin matan yayansu sosai kamar yanda su suke kishi da ita.
Dawuri ranar Anty maijiddah tazo gidan saboda aikima.
Hummm fad'a muku yanda Anty maijidda tagyara Amatallah ranar ai 6ata lokacine kawai,
saidaifa hummm!! Ina mai tabbatar muku yau Uncle bai Isa iya control d'in kansaba, gashi dama
kwana biyun dayay d'akin Aneesa ma tana Off.

Kusan 5pm tashiga kitchen d'inta domin yin girki, Kitchen d'in tsakar gida su Anty maijiddah
sunata aikin abubuwan daza ayi Na suna gobe, Dan haka tanufi kitchen d'inta danyin girkin
dare, yau kuma ne rana ta farko fazatayi girki a cikin d'inta, ta fiddo tukwane a kwali ta wanke
daduk abinda tasan zata buk'ata, kafin tafara had'a miyar Agusi d'inta datasha busashen kifi ga
wadataccen naman tantakwashi, tunifa gida ya d'auki k'amshi su Anty maijidda sai fad'i suke
Amatallah zaki kashemu da k'amshi.
(Nima dai Amatallah zata kasheni da kwad'ayi Anty maijidda� lol)
Batasanma sunayiba aiki ya d'auke hankalinta, ta had'a lemon kankanarta dayasha madara
da kayan k'amshi, ta fere doya mai k'yau ta d'ora, harga ALLAH bazata iya daka sakwarar
mutane kusan 15 ba, Dan bayansu Kansu da yara sunkai goma ga kuma Anty maijidda nazeefa
sai yayyen Maijego biyu da kanwarta zaliha ga gwaggo rakkiya, ga kuma wata dattijuwa k'anwar
Maman maijegon, kuma duk gidan zasu kwana, yayyen fateemar ne kawai tasan komin dare
k'ila zasu wuce, Nazeefa Amatallah takira domin Neman shawarar yazatayi.
Dariya Nazeefa tayi tana fad'in "amma ke ragguwace, kina nufin Yaya kawai zakiba
sakwara? to bamu yardaba".
" kai Anty Nazeefa ki tausayamin, ALLAH ba abune mai sauk'iba dakan sakwara".
"To Na tausaya miki 'Yar Uncle, yanzu dai dafa doyan saiki d'iba iya wadda zaki daka masa,
nikuma sainakai sauran babban kitchen ahad'u adaka gaba d'aya".
''Yauwa Anty Nazeefa ngd, shiyyasa nake sonki".
Dariya sukayi gaba d'aya Nazeefa tafice.

Zuwa magriba ta kammala komai, suma su Nazeefa sun daka waccan, ta had'ama Uncle
abincinsa ta d'auki tukunyar miyar duka ta kaima Anty maijidda.
Abincin ta d'auka takai samansa, takuma saka turare kamar yanda Anty maijidda tace mata,
saida taga komai yayi dai-dai har ruwan wanka ta had'a masa Dan tasan yana gab da dawowa,
ta had'ashi da zafi sosai yanda sanda zai dawo yayi daidai wanka.
d'akinta takoma ta shirya itama, dama tayi wankanta tunkan tayi sallar magriba, kwalliya tayi
mai sauk'i tayi d'aurinta mai k'yau yanda Fa'iza ta koya mata, (Amatallah duk irin wad'annan
abubuwan bata iyasuba, saboda batada k'awaye gakuma yanayin inda ta tashi, barta dai da
tsafta ga nutsuwa, amma irin dai iyayi Na 'yammata bata iyaba�). K'amshi take tamkar tayi 6arin turare a jikinta, kodai mace taji k'amshina nan nata saita firgita
balle kuma.....humm.lol

Ana kuwa idar da sallar isha'i Uncle yashigo gidan

Yarane kawai a falon, dan haka suka iso da gudu suna ihun murnar masa oyoyo, rungumesu
yayi yana murnar ganinsu shima, harma da yaransu Anty maijidda, zaliha dake tare da yaran a
falon Dan tana fashin salla ta gaidashi, cikeda fara'a ya amsa yana fad'in "autar mama kamar
kiyi zamanki tare damu kawai". 'Yar dariya tayi tana fad'in " Yaya aikuma makaranta".
"Anya kuwa ba wayo bane?".
" ALLAH kuwa Yaya".
"Shikenan to na yarda". yay maganar yana nufar hanyar 6angaren Fateema, bayan Sahib ya
kar6i ledojin hannunsa yanufi samansa dasu.
Ya iskesu Anty maijidda zaune a falon Fateema, Mariya Na salla itada gwaggo rakiya,
risinawa yayi ya gaida inna Nafi dake zaune tanama jaririya wanka, su Anty maijidda suka
gaidashi suma itada Anty maimuna, sunata d'aura kayan rabo.
Anty maimuna tace, " Yaya Muhammad fatin tana cikifa".
Murmushi yayi yanufi bedroom d'in Fateema, Anty Mariya data idar ta kalli su Anty maijidda
tana murmushi "kai ya Muhammad Na birgeni saboda kunyarsa wlhy".
Duk dariya sukayi , Anty maijidda tace kad'anma kikagani Indai ya Muhammad ne.
A zaune ya tadda Fateema tana ware kayan fitar suna dayay musu suduka, amma ita kala
biyar, sukuma su Amatallah uku-uku itada Aneesa.
Murmushi sukaima juna kafin ya zauna kusada ita ya rungumeta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login