Showing 84001 words to 87000 words out of 109227 words
Chapter 29 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
nufin zuwa?".
" k'asa mana Uncle".
Shiru yay kawai yana kallonta da hango zallar rashin wayonta, kusadashi ya nuna mata
yace, "dawo ki zauna nabaki magani kisha kafin ki tafin".
Batayi musuba tadawo ta zauna, azatonta maganin zai bata da gaske. shiru babu mai
magana acikinsu, har yagama cin abincin, kwanikan yamatsar gefe yana fad'in Alhmdllh, ya kalli
Amatallah dake gyangyad'i.
Ya murmusa tareda jin tausayinta a zuciyarsa, yasan harga ALLAH tagaji d'in. TV ya kashe
daduk kayan wutar, ya haska fitilar wayarsa ya sauka k'asa, Generator yaje ya kashe, ya maida
NEPA dukda babu wutar, amma in case koda an kawo suna barci basai yatashiba.
Amatallah da barci ya d'auka batama san ya fitaba, ya tadata tareda kama hannunta suka
tafi bedroom d'insa, batace masa komaiba saboda barcin dake idonta, ya zaunar da ita abakin
gado yabata magani tasha tana yamutse fuska, kafinma ya ajiye ruwan hannunsa hartayi
kwanciyarta, gyara mata kwanciyar yayi yafara mata tausa ahankali, wani barci mai dad'i ya
d'auke Amatallah saboda dad'in tausar datakeji. Saida ya tabbatar yamata yanda zataji dad'in
barci sannan yabarta, yaymusu addu'ar barci ya rungume kayarsa.
Nima akorikurar k'afafuna najawo zuwa wajen nawa boss d'in.
_washe gari_ koda Uncle yafita masallaci itama Ama... Saita sakko k'asa abinta, taredasu
Nazeefa tayi salla, babu Wanda yace mata k'ala, bata koma barciba tanufi kichin Dan neman
abincin Karin kumallo.
Bata dad'eba Anty maijidda tashigo ta taimaka mata. Lokacin dasu Uncle suka dawo
masallaci shida yara yaji motsi a kitchen amma baiyi zaton Amatallah bace, Dan haka yawuce
samansa, wayam yagani alamun ta gudu, yay guntun murmushi kawai.
Su Nazeefa suka fito suma suka fidda wanke-wanke, Anty badiyya da Aneesa kuma suka
fara k'ok'arin tsaftace gidan, ganin haka su Anty furera kuma suka hau yimasu Sahib wanka.
kasan Cewar aikin kowa Yakama saiya yimusu sauri, Dan danan suka kammala, gidan ya
dai-daita. Bayan sun kusa kammala girkin, Dan kad'an ya rage Anty maijidda ta kalli Amatallah tana
fad'in "yauwa maza kije kiyi wanka, kafin kidawo na had'ama mijinki saiki kaimasa daganan ki
gyara masa 6angarensa, karnaga k'afarki a k'asa sai idan ya sakko zai fita".
Amatallah tace " to Anty".
Harga ALLAH tana kallon Anty maijidda ne tamkar Ammi agabanta, Dan ko'a shekaruma
zasuzo d'aya da Ammi, ita kanta Anty maijiddan Dan d'anta nafari namijine kuma yarasu, Na
biyunma namijine, amma da macece k'ilama tana shirin aurarwa kam.
Duk yanda ta umarceta hakan tayi, dama yau tanason zuwa makaranta, tayi kwalliyarta cikin
gown d'in atanfa, d'inkin Yamata k'yau, simple kwalliyarta tayi tamkar yanda ta saba, tad'an fesa
turare sannan tafito.
A falo ta iske su Anty maijidda tana zubama yara abinci, su Nazeefa ma suna zaune suna
karyawa, gajiya tahanasu cin abincin dare, shiyyasa suka tashi da yunwa.
Kitchen tashiga ta d'akko tiren abincin da Anty maijidda ta had'a mata, yaukam saitaji
batajin kunyar kowa yaganta Dan zataje wajen mijnta. A hankali take taka step d'in tamkar
bataso, tayi sallama a k'ofar falon kafin tashiga dukda ba'a amsa mataba, falonma babu kowa,
ta ajiye tiren, falon tahau gyarawa batareda tashiga bedroom d'inba. Duk Uncle najiyo motsinta daga ciki, yana wankane.
Tana shiga bedroom d'in yana fitowa, juyawa tayi da niyyar fita tabashi waje ya shirya
yace, ''hii".
Cak ta tsaya amma bata juyoba, k'arasowa yay gabanta yana kallon yanda rigar ta zauna
ajikinta d'as, "my best shirinafa? Wazai mini?".
Kad'an ta kallesa ta janye idonta dan ganin dagashi sai towel, murmushi tayi tana d'an
Susar wuyanta alamar kame-kame, " Uncle ina kwana".
Amsawa yayi yana murmushi, ya kama hannunta suka k'arasa bakin gadon, dolenta ta
ajiye kunya gefe ta taimaka masa kamar yanda ya buk'ata, yay gayunsa cikin lemon green d'in
boyal, yauma itace tamasa karin hula ta saka masa akansa, ya rungumeta yana fad'in "Thanks
my heartbeat".
Itama ahankali tace, "I... love... you my Uncle". Da d'ai-d'ai tafad'a tamkar mai koyan
magana.
Da sauri yad'ago kanta yana kallon fuskarta, "my best really!?".
Tana murmushi ta d'aga masa kanta.
Kuma rungumeta yayi yana fad'in Thanks you so much my heartbeat, I love you more".
yakuma d'ago fuskarta yana bata tagwayen sumbata, yaukam Amatallah taga ikon ALLAH
itadai, tana kallon Uncle d'in nata nadabanne acikin maza.
Bayan sun kammala breakfast tace masa yau zataje makaranta.
Yace ta hak'ura tunda dai su Anty Sadiya basu tafiba sai yamma. Baikuma dace tafita ta
barsuba ai, gobe saitaje idan ALLAH ya kaimu da rai.
Hakan dole ta hak'ura, aikam yini guda sukasha hirarsu, sai k'arfe biyu sukayi shirin tafiya,
tabasu alkairin da Uncle yabata, itama tahad'a da nata, Fateema ma ta had'a musu kayan suna,
Aneesama ba'a barta abayaba, tare suka fita dasu Anty maijidda, sukaje suka gaida su Ammi
sannan Nazeefa tarakasu tasha suka hau mota. Gida kam yazama dagasu sai su, su Anty badiyya ma da inna Nafi suna kammala suyar
Nama suka tafi.
Amatallah da Aneesa suka kuma dagewa suka k'imtsa gidan tsaf, daganan Ama... takoma
gefe tana kallon Aneesa data kasa zaune takasa tsaye saboda yau miji a hannunta yake.
Duk abinda Aneesa keyi Amatallah k'arin ilimine a wajenta, tsaf take k'ara karantar komai da
nazarinsa, tanaji a ranta itama lokaci yayi daza'a dama da ita. (lol.)
************
Alhmdllh, su Uncle sun sami hallarar inda zasu gudanar da meeting d'insu. Su 12 suka
halarci wajen, dukda ba iyakarsu kenanba, akwai wad'anda suka yanki form kusan su 26, to
amma su sun ware kan nasune amatsayin shugabanni wad'anda zasu tattauna akan kafa
k'ungiyar, dukansu masu ilimine, kuma babu Inda zasu shiga ba'a dama dasuba a k'asar. Alhaji Sabi'u ya gudanar da addu'oi kafin su fuskanci abinda ke gabansu.
An tattauna da mahawara mai zurfin gaske, sukace dole Uncle ne zai shugabanci k'ungiyar,
Dan shine yafi cancanta da hakan, kodan k'ok'arinsa da k'yak'yk'yawar manufarsa.
Ya nuna musu shifa baya buk'atar shugabancin, Dan haka abama Alhaji Sabi'u ko Alhaji
Murtala mai daura. An dad'e ana tata6urza akan sudai shid'in sukeso, kuma harsu Alhaji
Murtalan.
Dolen dole Uncle ya kar6a wannan shugabanci, Alhaji Sabi'u mataimakinsa, saikuma Alhaji
Murtala mai daura sakatare, saikuma wasu muk'aman dasuka biyo baya irinna ma'aji da dai
sauransu.
Tun anan suka fara wasu tsare-tsaren, kamar yad'a manufarsu ga matasan dakuma jawo
hankalin masu zuciyar taimako domin zuba sadak'atujjariya a bitalmanin k'ungiya, saikuma
bud'e wasu businesses k'anana dazasu tallafi k'ungiyar wajen samun kud'in shiga dadai
sauransu.
Anan take kowannensu yay alk'awarin bada gudunmawa dai-dai k'arfinsa, dan haka aka
bama ma'aji damar bud'e Account da sunan k'ungiya dan a fara zurara kud'in dasuka tara,
ansama k'ungiyar sunan *_YOUTH AWARENESS FORUM_*, bayan ankawo sunaye
daban-daban dai suka tsaya akan wannan d'in. Uncle dake jawabi yabisu da kallo d'ai-d'ai yana murmushin jin dad'in had'in kan daya
samu nasu, bayan yayi doguwar godiya agaresu yad'ora da fad'in "to Alhmdllh 'yan uwana,
yanzufa saimunyi hak'uri da juna, muji muk'iji, mugani muk'i gani, karmu d'auka wannan yak'in
namu zai zama mai sauk'i, dolene zamu fiskanci k'alubale daga matasan Kansu, dan basu
ganin irin wad'annan abubuwan a yankinmu, sannan akwai marasa son gaskiya dazasu fara
sukarmu, musammanma jam'iyun siyasa, amma wannan bawai damuwa baneba, dan mud'in
bawai 'yan siyasa baneba, amma munason mukawo sauyi akan yanda siyasar kejan ragamar
rugujewar matasanmu damu kanmu, inhar kace zaka tara al'uma koyin wani Abu mai k'yau da
amfani arayuwa dolene kayita fuskantar k'alubale, wani mai dad'i, wani maicin zuciya, wanima
harkaga yata6a iyalinka. abu nagaba shine mu tsaftace harshenmu, muringa sanin kalmomin
dazasu fito a cikin bakunanmu, danfa ayanzu komai namu zaizamto abin ajiyewa ga 'yan jaridu
dakuma al'umma, sai lokacin damuke hangen nasa ayi amfani da wannan a 6ata mana suna
kocin zarafinmu. Saikuma mu kammu muji tsoron ALLAH karmu kasance munafukan juna
kokuma fidda wani sirri Na k'ungiyarnan, yin hakan zai iya zama illa agaremu, muyi hak'uri da
juna domin ALLAH, duk Wanda ya sa6ama wani yakirasa ya sanar dashi a fiskanci juna tunda
mud'in ba yara baneba. a yanzun kiranyenmu zai farane daga kan matasa masu shaye-shaye,
dan anfi samun nasara akansu wajen haddasa rikice-rikicen *SIYASA KO K'ABILANCI*, yanzu
dai gashi an kad'a tamburan siyasa, kuma naga gangar shaid'an tafara aiki a jikkunan
matasanmu, dan haka zama bai ganmuba kenan, zuwa nanda kwana uku saimuyi zama Na
musamman akan wannan matsalar, mu tattauna da duba hanyar data kamata mubi koya kuka
gani?".
Gaba d'aya sunyi ma'am da zancensa, sunkuma yabama k'ok'arinsa, Alhaji sabi'u ma
yatashi yay jawabi, daganan kowa daki-daki yayi nasa, kafin taro yatashi cikin addu'ar samun
nasarori da fatan alkairi waa juna..............✍
_kuyi manage da wannan, ban yini a gida baneba._
One luv my sweet fan's
*_ya rabbi ka gafartama iyayenmu_*
[1/19, 8:33 AM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce_*
_gaisuwa da fatan alkairi, *Dan mom and Sani Ilyasu*_
____________________
*_Number 34_*
____________________
Rayuwa tacigaba da tafiya cikin Nasarori da fuskantar k'alubale irinna rayuwa, wani mai
dad'i wani akasin hakan, zuwa yanzu kam Amatallah tashigo gari, itama tazama 'yar hannu,
yanda matan Uncle ke taku d'ai-d'ai da rawa da bazarsu haka itama takeyi, rayuwar gidan
takoma ta competitions, kowa so take tazama gaba a zuciyar maigidan. Iya k'ok'ari Uncle yanayi akan matan nasa, k'yautatawa iya gwargwado yanama kowacce,
baki isa kisan wadda yafi soba a zuciyarsa, dan kowacce takasance agabansa nuna mata
yakeyi babu ya ita, wannan yasa kowacce takejin kanta on top.
Duk abinda zakiyi mara k'yau agaresa bazaiyi gulmarki agaban 'Yar uwarkiba, sannan
bazaici mutuncinkiba, Indai kun ke6e dagake saishi zaiyimiki kam, hakan yabada taimako Na
musamman wajen hana kawoma juna raini a tsakaninsu, saidai kowacce tana tsantsar kishin
mijinta, musamman ma Aneesa dabata iya 6oyewa, a salon iya taku kuwa sai Amatallah ta
nunama Fateema bata iya komaiba, Dan ko agaban maigidan Amatallah bata ta6a nuna kishi
ga 'Yar uwarta, har mamaki yakeyi, wani lokacin yakanyi wani Abu danyaga ko zata nuna 6acin
ranta amma ko alamar hakan baya ta6a gani (dukda kuma tanajin haushin amma saita danne)
wannan duk Anty maijiddah Ce ke d'orata a network.
Sukansu su fateemar abin nabasu mamaki, Aneesa takansha yima Amatallah abu amma
koda afuska bata nuna mata tasan tanayi balle ma ta 6ata ranta, duk sun rasa gane lagon
Amatallah.
Duk hanyar da Fateema zatabi ta 6atama Aneesa rai tasanta, amma takasa samun Na
Amatallah, salon yarinyar Na bata mamaki da d'aure kanta, gashi kota k'udiri k'untatama
yarinyar saita karya mata tanadinta ta hanyar son 'ya'yansu datakeyi, yanda Amatallah kema
yaransu bazaka ta6a d'auka yaran kishiyoyinta bane, yanzu haka mah-mah (Aminatu) saita
wuni a hannunta inhar batada makaranta.
Amatallah kuwa dukda tana kishinsu hakan baisa ta d'auki damuwar k'untata musuba a
zuciyarta, gaba d'ayama hankalinta nakan karatunta, ta dage sosai kamar yanda kullum Anty
maijidda da Nazeefa ke bata shawara, ita saima suyi Abu sau nawa batasanma sunyiba, harkar
gabanta takeyi basu isheta kalloba, a salon kulada mijikam hummm, sukansu sunfara zama
'yan kallo, to kullum Fa'iza tsaye take akan Amatallah wajen koya mata salo-salo Na kissar
kama miji, hakama Anty maijidda, gasu Anty furera agefe, kowadai tausayinta yakeji, ga maraici
ga zama da kishiyoyi wad'anda suka girmeta nesa ba kusaba.
Nasarorikam ana samunsu fiyeda zaton mai tunani, Dan Uncle koda bai fito ya fad'aba
musan Amatallah takafa bishshiyar gamji a zuciyarsa, wadda tasaki rassa da 'ya'ya
tako'ina.
Fa'iza ta haihu kusan wata hud'u kenan, su Amatallah ansha sunan baby (Munirat). Fa'iza
ALLAH ya raya mana to.
A 6angaren Uncle ma abubuwa suna tafiya akan nasarori, yanzu haka suna rik'eda matasa
masu yawa kusan 50 wad'anda shaye-shaye yafara ruguza rayuwarsu, suna kar6ar magani da
horaswa akan wasu sana'oi. Saikuma masu lafiya wad'anda ayanzu haka suketa cuku-cukun
sama musu wajen aiyuka a 6angarori daban-daban, sunkuma bud'e islamiyya daza'a ring a
koyar da matasan ilmin addini da dabaru Na rayuwar, dukda k'arancin kud'i dasuka fara
fuskanta hakan bai hanasu fara fad'ad'a ayyukan nasu zuwa wash local governments ba,
musamman akan matasa 'yan shaye-shaye da had'a daba ta 'yan gani kasheni.
Wad'annan nasarorinne suka maida Uncle d'in busy sosai, ga iyali ga ciwon baba dukda
Alhamdllh akwai sauk'i, ga harkar kasuwancinsa da Aikinsa, idan kagansa dolene ka tausaya
masa har wata rama yayi ta yawaita zirga-zirga.
K'alubale kam suna fuskantarsa musamman wajen manyan k'usoshin k'asar, wasu suna
ganin kamar wata jam'iyyar siyasa sukeson kafawa a kaikaice, suna yawanjin sukarsu da akeyi
a gidajen redio ko talabijin musamman in ana hira dawani d'an siyasa.
Kokad'an hakan baya damunsu, saima alkairi yake zamo musu, Dan yakansa wasu masu
nagartatattun halaye Dason cigaban k'asar da kishinta sukan kawo Kansu cikin tafiyar domin a
dama dasu suma. aifa kafin kace mi sai manufofinsu suka fara fitowa fili, ayanzuma basai sunyi
kiranyeba matasan dakansu suke kawo Kansu saboda suma fatarar babu da yawon tazubar ya
ishesu, masu kwalayen result a akwati saisuka fara lalubowa suna kakka6ewa danufo ofishin
dasu Uncle d'in suka bud'e domin kar6ar k'orafe-k'orafen Masan, masu raunin kasuwanci ko
rashin madafa ma gaba d'aya suma suka fara tururuwar gangamin shigowa wannan k'ungiya.
Hummm hakanfa bak'aramin shankan su Uncle lamuran suka faraba, sunyi kiranye kuma an
amsa harma amsawar tafi k'arfin bitalmaninsu, Dan ayanzu babu abinda sukafi buk'ata samada
zunzurutun kud'in Shiga a tafiyar tasu. A 6angaren Islamiyya kam tagama cika mak'il da
matasan da suke damuwa da raunin ko k'ishirwar rashin ilimin addinin Nasu su Kansu, malamai
kuma magadan annabawa sunyima lamarin caffar fisabilillahi, dansu ajiye wasu daga cikin
ayyukansu sun d'aura d'ammarar yad'a ilimi ga matasan koda hakan zai kawo mana raguwar
wasu masifun, kullum nasiha da wa'azi maishiga jiki da 6argo shi Malaman kan zazzaga bayan
kammala karatu a ajujuwanin dasuka kasance uku kacal, duk suncika harma sun batse ana
Neman tallafin k'arin wasu.
Tofa ahankali lamarin wannan k'ungiya yafara haskawa, taurarinsu suka fara haske, dattijai
da iyaye mata suka fara d'okantuwa daganin 'ya'yansu a tafiyar suma, hakama k'ananu 'yan
siyasa masu Neman madafin iko da jama'a suka fara shirin k'utse cikin wannan k'ungiya danufin
samun mabiya a matasan, saidai kuma tuni su Uncle sukayi tsawar datasaka masu rawar k'afa
a 'yan siyasar ja baya koyin likimo Dan tsorata da gargad'in su Uncle Na ik'irarin Suba 'yan
siyasa baneba.
Hakan kuma sai yaso zama k'ilu zata jawo bau, Dan masu ri6a66iyar zuciya kuma suka
sami abun fad'a da kayayatu akafafen tazo mujita irinnan talabinjin rediyo da yanar gizo.
Kunnan uwar shegu su Uncle sukayi da kowa, tamkarma basusan anayi dasu baneba, sai
suka bar karnika NATA haushinsu sukama sunata aikinsu dukda bitalmali Na neman agajin
tallafin wasu 'yan kud'ad'e a tafiyar.
Amma abin birgewa su Uncle basukai wani k'orafi ga wani shahararre komai mulkiba, sai suka
duk'ufa wajen baje hajarsu a kasuwa dawasu 'yan abubuwa dazasu kawoma k'ungiyar kud'in
shiga koda babu yawane, aka kuma had'a hannu da matasan dasuka sami wasu k'ananun
sana'oi a hannu ko aikinyi tasanadin k'ungiyar, haraji aka yankama kowannensu Na naira d'ari
biyar akowane k'arshen sati, da wannan kuma za'a tallafi 'yan baya masu tasowa suma.
A wannan tsakanin ba'a cewa komai akan Uncle da sauran shugabannin k'ungiyar, Dan
kowanne yaji ajikinsa, hattada kasuwancin wasinsu saida yad'an girgiza musamman ma Uncle
daya maida komai nasa Na taimako, to ALLAH dai gafurin rahimun yacigaba da rik'e k'ungiyar
da ikonsa dukda k'alubalen kud'i dasuka tsinci kansu. a yanzu dai haka dole sun ajiye ranar
ashirin gawata domin zaman meeting akan k'ungiyar da fatara irinta kud'i datake fuskanta,
yazamana dole su k'yalla idanu wajen lalubo mafitar kubta koda cigaban cimma manufofinsu da
burukansu.
Yau takama Juma'a, kuma Amatallah ce da miji, dukda Aneesa ma tanata ahirye-shiryen
ziyartar k'asarta ta haihuwa Dan ganin gida da danginta (Ghana).
Bayan sun fito daga lecture ta k'arshe Rita da goodness sukayoma Amatallah da Fa'iza
rakkiya dansu sami abun hawa.
Tafiya suke suna