Showing 108001 words to 109227 words out of 109227 words

Chapter 37 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

3years later�🤣


ALLAH mai girma da d'aukaka, yau gasu Ama... ana bikin yayesu amatsayin manyan
likitoci kwararru, bakunansu sunkasa rufuwa saboda tsabar farin ciki, hakama Na danginsu
wad'ada sukayi tururuwa halattar taron.
Ciki hardasu Uncle da matansa duka, Anty maijiddah Nazeefa zaliha Asiya su aunty Firera
da mazansu su kawu Hafizu, matansu Alhaji Sabi'u da dangin su Fa'iza, harda dangin Su Aysha
(goodness) wad'anda ayanzu sun sakko suna ziyarar 'Yar uwarsu itama tana ziyaryarsu, harda
d'anta Muhammad (Wanda taima Uncle takwara�) suna kiransa Yaseer. Angudanar da taro cikin sha'awa da birgewa, tareda kar6ar k'yaututtuka dasu Ama.... suka
samu, Uncle jiyake tamkar ya had'iyeta saboda dad'i da k'ara sonta, Dan har yanzu Ama.... tana
cikin k'uruciyarta, yanzunema take kuma kilewa tana zama hamshak'iyar mace, ga 'yan yaranta
su Rayyan abin sha'awa, sunyi girma sosai da wayo, har sun shiga school tuni, tundagasu
kuma bata sakeba, koda yake Fateema ma da Aneesa shiru, tundaga Abubakar Aneesa ma
bata sakeba, hakama Fateema tunga mah-mah.
Sunsha hotuna tamkar babu gobe, harda Innani da gwaggo Rakiya wadda su shehu suka
matsa tilas sukazo suma, Nazeefa da Zaliha da Asiya ma duksun sake haihuwa tuni.
Tarodai yatashi lafiya cikin farinciki da annashuwa, kowa yakama gabansa.

Su Uncle suka nufi gida inda acanma Uncle yahad'a liyafar cin abinci saboda farantama
Amatullah rai, anci ansha an gyatse kuwa, lamarin sai sambarka.

*_Kishi kumallon mata🤣_*

Tunda su Fateema sukaga Amatullah tafara aiki sukayi tsalle suka dire akan suma aiki
zasuyi, kowacce ta kakka6o takardunta daga k'asan jaka.
Uncle yay dariya sosai sannan ya had'e fuska.

"Amma lallai bakuda hankali, ai kuda aiki saidai Na gidana, idan kun manta bara Na tuna
muku to, alokacin dana aureku babu wacce ta shekara a gidana Na tuntu6eku akan kozakuyi
aiki?, ince kowaccenku nunamin tayi batada ra'ayi, Ku kulawa dani kawai kukasa agaba, ban
gajiyaba nakuma muku hannunka mai sanda akan Sana'a, nannama kukayi kunnen uwar shegu
dani, saikuma yanzu dan kunga Khadeeja kuma kuce saikunyi? to idanfa ba 6acin rai kuke
nemarwa gidanmu ba kuma ajiye wannan maganar mucigaba da rayuwarmu, itama data nuna
batason aikin ko karatun bazan bartaba, amma tun farko ta tabbatarmin hakanne burinta,
shiyyasa nabata goyon baya wajen cikarsa, Ku kama kanku, mud'in ba yara baneba balle kuce,
yanzu inada k'aton saurayin yaro dake shirin kammala Secondary, banason shashanci, dan
haka kutashi ku bani waje".
Haka suka tashi kowacce ranta a jagule da Dana Sanin k'in amincewarsu tun farko, dayanzu
suma sunzama manyan hajiyoyi da ake damawa dasu, amma sukaima Kansu sakkiyar da babu
ruwa, gashinan suna zaune Ama... tafara karatu harta mammala tazama hamshak'iyar likita
abin alfahari ga mata��.
Bayan kwana biyu suka bashi hak'uri ganin yanata faman fushi dasu.
Shima saiya hak'ura, harma ya k'ara musu da k'yautar jari akan suyi kasuwanci, harda
Ama.... itama yabata kamar yanda yabasu dukda dai bawasu kud'i masu yawa baneba.
Tundaga lokacin kowacce takama kasuwancinta, Amatullah kan su kawu hafizu tabamawa
akan sucigaba da juya mata anasu kasuwancin, itakuma tarik'e aikinta kawai tunda batada
matsalar ci ko sha balle sutura, mijinsu yana iyakar iyawarsa wajen sauke wannan hak'in nasu.
Humm, idanfa kukaga Amatullah dolene takuma birgeku yanzu, tayi k'iba ta murje, daka
ganta kaga mata hamshak'ai masu aji, gata da k'ok'arin taimakon mata akan kowanne fanni,
kullum cikin basu shawarwari takeyi ta yanda zasu tattali Kansu da yaransu, gata da sauk'in kai
da tausayin marasa lafiya, koyaya kake Ama... bata k'yamatarka, dantace ai itama talakance,
mizaisa ta k'yamaci 'yan uwanta talakawa, gata da taimako, Rabin albashinta duk kan marasa
lafiya mabuk'ata suke tafiya, 'yan yaranta abin sha'awa, kullum cikin godiya takema ALLAH
dayabata su da miji irin Uncle, Wanda ayanzu shine duniyarta, shine babanta shine Amminta,
shine Uncle d'inta shine kuma miji shine dangi shida danginsa, takowanne fanni sun kare mata
mutuncinta da nuna mata k'auna da d'unbin tausayi saboda rasa mahaifanta wad'anda kullum
cikin musu addu'ar Neman gafara take dayin sadaka domin ladan yakai garesu, itakam babu
abinda zatacema ALLAH sai godiya, danya canja mata rayuwa fiyeda zaton mai tunani, kullum
cikin ambaton ALHAMDULLAH takeâœí ¼í¿»í ½í±Œí ¼í¿¼.





Tonima dai bilynku nace ALHAMDULLAHI.

_ina godiya ga UBANGIJIN Al'arshi daya bani ikon fara wannan littafi da kammalashi cikin
Aminci, Abinda nafad'a dai-dai ALLAH kabani lada, wanda nayi kuskure ALLAH ka gafarta
mini._

_Kulum ina k'ara rok'on masoyana akan su kasance masumin gyara yayinda sukaga kuskure
a buks d'ina, insha ALLAH zan kuma fahimcesu da ganin k'imarsu, ina ganin darajar Wanda
zaicemin Na gyara kuskurena, Dan haka karkuyi sanya Dan ALLAH, gyaran kuma yazamto ta
k'yak'yk'yawar hanyar dazan fahimta, Ngd da k'aunar dakuke nunamin, nima ina matuk'ar
k'aunarku wlhy._🥰

Naso buk d'innan yafi haka fad'ad'a, amma matsalar wayata yasakani tilas Na datse labarin
iya nan, kumin afuwa, ina kuma fatan iya hakanma zai gamsar daku da amfanar daku.

_Babbar nasarata shine Ku tasirantu akan abinda yake mai k'yau a labarinnan, sannan kuyi
watsi da kuskurena kasancewar nid'in 'Yar adamce Azija.�, ina kuskure, bakuma komai
nasaniba._


*_Tawan Miss xoxo ina godiya agareki, ked'in tadabannce a zuciyar Bily, babu abinda zance
sai ALLAH yabar mana zuminci._*í ¾í´í ¼í¿»í ½í¸½í ½í¸»í ½í¸»


_Masu min comments kullum dama mahaifina addu'a batareda gajiyawaba kuma ngd sosai,
ina alfahari daku, matsalar wayata bazai bari Na lissafokuba, amma kuna k'asan raina, kuma
bazan manta dakuba, zuwa nan gaba kuma zan tabbatar muku da hakan.�í ¾í´í ¼í¿»í ½í±í ¼í¿»._


*Bilkisa Ibrahim musa (bilyn Abdull).�*

�👎🏻

Marubuciyar...

_Rashin sani!!_
_Auren k'addara ko biyayya!?_
_K'anwar uwace ko kishiyar uwa!?_
_Ni da Aminiyata!!_
_Nawaff!!_
_Ban saketaba!!_
_Abdul-maleek bobo!!_
_karayar arzeek'i!!_
_Ciki da gaskiya!!_
_Sanadin bikin sallah!!_
_Sabon Al'amaree!!_
_Kukan kurciya.....!!_
_Siyasa ko k'abilanci!!?_

_Wanda bai karantaba ya nema a kasuwar social media🤣, karku bari ayi babuku��👌🏼._


Ngd sosai.


One Luv😻😻😻😻😻😻�👌🏼.






*ALLAH ka gafartama mahaifanmu dadukkan sauran 'yan uwa musulmai dasuka rigamu kwanta
dama, ALLAH ka jagoranci al'amuranmu akan wannan za6e dake tunkaromu, Rabbi ka
azurtamu da shuwagabbani nagari masu zinariyar zuciya, ALLAH karkabama dukkan wani
azzalimin shugaba damar hawa kujerar da suke kwad'ayi, ALLAH yasa ayi lafiya a gama lafiya
batareda tada rikicin SIYASA KO K'ABILANCI ba, ALLAH ka d'aukaka Nigeria yarmu.*


NIGERIA is One Nation One people.🇳🇬�í ½í±í ¼í¿»í ½í±Œí ¼í¿¼


*_HATTAR MATASANMU👈🏻👉🏻, Idan k'asarmu tarikece kune👉🏻, idan anyi tsaftataccen za6e
kune👈🏻, Dan da k'arfin samartakarku da wautarku ake amfani wajen tada rikice-rikice yayin
za6e, inkunk'i bada had'inkai amfaninkune, dan kowa rai yayma dad'i BARAN MAI
SHINEí ½í¹í ¾í´í ¼í¿»._*

_masoyana saikuma bayan Sallah k'arama idan munkai da darai, ALLAH ya had'amu da alkairi,
kushirya da k'yau, zandawo muku da sabon salo insha ALLAH�, buk d'ina nagaba hummmm
bara dai nayi shiru🤭�, kuma karkuce komaifa�🤗._


*_NEXT LEVEL_*�🥰�






*_BILYN ABDUL CE🤙🏻_*😻😻😻😻😻😽😹.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login