Showing 81001 words to 84000 words out of 109227 words

Chapter 28 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

sunata shan hira
dabata labarin jos.
Suma sunji dad'in yanda sukaga ta murje tayi k'yau, hakan ya nuna musu hankalinta ya
kwanta, Alhaji Muhammad yarik'e amanar d'an uwansa, dukda sunga kamar batada walwala
sosai, amma jin dad'in ganinsu Na k'ok'arin danne hakan, babu Wanda ya tambayeta
damuwarta cikin su, tunda sunsan zaman aure saidai hak'uri, komin San da kukema juna
dolene wataran a k'untatama juna, bakomai ake samu 100% ba.
Ansha hotuna kafin Uncle yafice sabgar gabansa.
Ita ta rakasu d'akin maijego Uwargida, taci gayunta cikin had'ad'd'iyar shadda popul, hakama
jaririyar anmata gayu, Ummita tana nanik'e da ita, saikuma wasu daga cikin danginta dake cin
abinci, wasu kuma hirarsu sukeyi.
Duk suka gaisa a mutunce.
Fateema ta kalli yanda Amatallah tayi k'yau cikin kwalliyarta, k'ok'arin danne kishinta tayi
kamar yanda ta saba, tayi murmushi tana fad'in Anty yara kinyi k'yaufa, kamarma kece mai
jegon".
Murmuahi Amatallah tayi, ta 6oye fuskarta jikin Ummita dake kan cinyarta tace ''kai Anty
kecema ai sarauniyar k'yau d'in, kinganki kuwa?".

Dariya wad'anda ke kusadasu sukayi, abin kuma ya birgesu tamkar ba kishiyoyiba.
Aneesa tashigo itama ta cakire cikin less jaa, tayi k'yau sosai, fleets takawo saboda bak'i,
itama Fateema saida ta tsokaneta wajen yaba kwalliyarta.
Aneesa ma ta danne zuciyarta da kishi tayi murmushi tana fad'in "lallaima Umman yara,
bakiga kankiba kenan keda Antyn yara?, karfa Ku rud'a mana Abbun Abulkhairi wlhy".
Sosai akeyin dariya a d'akin, kasancewar Aneesa a tsaye take sai kowa yaji maganar datayi.
Sosai suka birge kowa, (har nimafa�, sainaji ina sha'awar kishiya amma ta yini
d'aya�lol).
Cikin girmamawa Aneesa tafara gaida su Anty furera.......
Amatallah ta katseta dafad'in " Anty Aneesa zafasuzo Ku gaisa".
Murmushi Aneesa tayi (saboda taji dad'in wannan girmamawa, damafa Aneesa akwai son
girma�) tace, "to shikenan, bara naje Na jiraku, dama an bani sak'o nabaku keda Umman
yara".
Atare sukace to, Fateema ta kalli Aneesar tana fad'in mu taso kenan?".
"A Ku k'arasa tu kunna, nima akwai abinda nakeyi."
Okey.

Su Anty Sadiya sund'an dad'e a 6angaren Fateema kafin suje 6angaren Aneesa ma, anan
Aneesa ta had'a musu abinci, takumace anan zasuyi sallah.
Godiya sukai mata da k'ara yaba kirkin kishiyoyin Na d'iyarsu Amatallah.

Aneesa da Fateema da Amatallah kam sunacan saman Uncle, Aneesa tasanar dasu cewa
Uncle yace zaizo da bak'ine wai da la'asar, " yakuke ganin zamuyi kenan? Yace yakiraki baki
d'agaba Antyn yara".
Amatallah tace, "Na manta wayarne a d'akina mukaje 6angaren Anty".
" okey, yanzu miye shawarar abinda za'a tanadar musu?".
Fateema tace, "kai Abbun Abulkhairi ma dai akwai kwak'ule-kwak'ule, yanzu Dan ALLAH
d'azun dazai fita ba'a gabanki Na tambayi kozaiyi bak'iba a jiye musu abinci?, amma yace a'a".
Tayi maganar tana kallon Aneesa.
" to yazamuyi umman yara, kinsanshi dai ai, yanzu kawai mu nemi solution, Dan yace
bak'infa Na kunyane. Antyn yara bakice komaiba fa?".
Murmushi Amatallah tayi, "to Anty mizance, Abinne Na Uncle saishi, yanzu kawai inaga ayi
jaloff d'in shinkafa mana, ahad'a da tuwon shinkafa ko semo...., tunda ga masa za'a kawo daga
idansu Innani kamar yanda naji su Anty maijidda nafad'a. Kobaiyiba?".
" yayi kuwa sosai wlhy, akwai zo6oma, dukda muma munada namu mutanen, sai a d'an
d'iba kad'an".
''Shikenanto, dama yace shehu zai kawo drinks da ruwa asaka musu k'ank'ara". Cewar
Aneesa kenan.
Amatallah tace, "to inhakane ahad'a da kunun aya".
Fateema tace, " amma har ayi? Yanzufa biyu saura, kumafa 4 yace?".
"Walhy har ayi Anty, aigasu Anty Nazeefa ga Asiya duk zasu taimaka mana da aikin".
" to shikenan, gasuma Ramla nan, aikin mi sukeyi, duk saisu had'u ai su taimaka muku,
(k'annen Fateema ne suma, amma duk da aurensu).

Sund'an k'ara shawarta abinda zasu k'ara dashi sannan suka sakko k'asa.

Da taimakon su Nazeefa suka had'a abinci da abinsha masu k'ayatarwa, harda suyar kaji,
abinka da hannu dayawa dandanan asuka kammala, aka had'a komai a falon bak'i dakecan
waje, komai yayi babu yanda za'ayi suji kunya kuma, harda alalan dasukayi Na jama'arsu duk
suka d'iba suka ajiye, zuwa sannan gidan kam ya d'inke da jama'a. Su Amatallah duk aka canja kaya, komai tanayinshine kawai, amma jikinta duk babu dad'i,
saidai Alhmdllh tana k'ok'arin daidaita tafiyarta, kasancewar dama ita mutumce mai sanyi, komai
NATA a nutsuwa takeyinsa, su Anty Sadiya suna 6angaren Aneesa takasa ta tsare. Sai
6angaren Amatallah yazama Na yaran mata, su Nazeefa da k'annen Fateema, dadai
yara-yaran matan danginsu, suna falon Ama sunata shan shargallensu ana barkwanci da
tsokanar juna.
Saigasu Fa'iza Goodness Rita dawasu k'awayensu Na makaranta da'ake gaisawa.
Nanfa fili yakuma kacamewa da hira, kokad'an babu Wanda yanuna k'yama gasu goodness
kasancewarsu ba addininsu d'ayaba, suma tun suna d'ari-d'ari har suka saki jiki anata hira da
dariya.
"Amatallah ta kalli Fa'iza cikin tsokana tace, " sannu uwar uku, ALLAH nazatafa bazaki iya
zuwaba?".
Hararta Fa'iza tayi cikin wasa tace, "a'a uwar 12 ba ukuba, kenifa garau nakejina ko reren
gudu saimuyi ehe".
" tab dawa zakiyi reren? Aiko zan barki a taku biyu harnaje Na dawo baki motsaba".
"Hawaba yarinya, badan karnama Uncle d'inmu asarar sabon babyba danace muyi".
" sabon baby a ina?".
"A cikinki". cewar Safina wata cousin d'in su Uncle.
Aiko nan tsokana tadawo kan Amatallah, ta dage tana kare kanta, nandai Ramla da Bilkisu
suka shiga kare mata suma.
Sun kacame da surutu wayar Amatallah nata ringing bata saniba.
Anty maijidda tashigo tana magana da k'arfi yanda zasuji.
" oh ni Hauwa'u, anya kuwa wani najin maganar wani a cikinku? Kunjikuwa yanda kuka cika
mana kunnuwa? Amatallah mijinki nata kiranki a wayama baki saniba kenan?".
Da sauri Amatallah ta kalli wayar, gata a gefenta amma batajiba, dayake wayar a silent take,
kuma ta kifeta, mik'ewa tayi tana fad'in "ALLAH banjiba Anty".
" yazakiji kuna wannan zuba tamkar rediyoyi, kizo to".
Tsallakowa tayi tafito, Fa'iza da goodness da Rita suka kalli juna suna murmushin jin dad'i,
dansunga sauyi ga aminiyar tasu, atunaninsu bazata mik'eba kai tsaye hakaba saita nuna jin
kunya, (amma sai sukaga babu kowani alamar hakan tare da ita) basusan dauriya Amatallah
tayiba kar ai mata dariya�, (Dan tak'aru da hirar yaran matan da tund'azun akan gidan aure
dama aketa surutun).
A waje ta iskeshi shida Aneesa tsaye suna magana, kishi da haushi suka kamata, (ya ita
da miji wata dafara zuwa wajensa�) (Ama... An fara kishi kenan....lol ).
Danne zuciyarta tayi ta k'arasa, sannu dazuwa tamasa, ya amsa idonsa akan kwalliyarta data
tafi dashi, maganar dasukeyi da Aneesa ya maimaita mata.
"Abokainane gasunan kusan su goma, kokad'an banyi zaton zuwan nasuba, saida nafitane

Alhaji Sabi'u ke sanarmin sunce zasuzo ganin baby, naji dad'in k'ok'arinku, ALLAH yaymuku
albarka kunji my wife's".
Atare sukace Ameen, kowa kishi nacinta a zuciyarta, amma a fuska bazaka ganeba,
(Aneesa ma anfara k'ok'arin dannewa�).
" yauwa to yanzu saikuma Fateema magana, idan mun kammala cin abincin saikuzo Ku
gaisa kenan, akawo Aminatun. Sai daifa bahaka zakuzoba k'attin banza su ganeminku, asawo
hijjabai".
Daga Aneesa har Amatallah dariya sukai masa.
"To ai gaskiyane, danma karsuce, ALLAH da har nik'af zance kusa, kunsan inada kishi,
khadeeja Ce kawai bata gama saninaba, amma ahankali zaki fahimci hakan kema"., yay
maganar da kanne mata ido d'aya.
Murmushi tayi ta kauda idonta akansa.
Sarai Aneesa ta gansu, kuma taji zafi sosai, harma saida fuskarta tad'an nuna, amma tayi
k'ok'arin waskewa dafad'in ''ALLAH nagaji over".
" sorry my neesa". Uncle yafad'a cikin tausayawa, ya kalli Amatallah ma yace sorry my
best, nabaku wahala ko?".
"Lah babufa komai Uncle, ai alsunan babynmuce, damunyi barci gajiyar zata ware ko
Anty?".
Murmushin yake Aneesa tayi, ta kad'an kanta kawai, amma mamakin Amatallah takeyi, dama
tana magana haka? Dan tuni ta lura Amatallah miskilace.
Ciki suka koma, uncle kuma yakoma wajen bak'insa.

Kamar bayan 1hour yakirasu duk awaya akan suzo sun gama, kowacce cikin hijjabi tafito,
Amatallah ta kar6i jaririyar daga hannun Fateema suka jera abin sha'awa suka nufi falon.
Sallama sukayi ak'ofa, saida aka amsa musu sannan suka shiga.
A mutunce suka gaisa, Uncle ya amshi Ameenatu a hannun Amatallah yabasu, fita sukayi
suka bar musu ita tunda barcima takeyi.
Duk saida suka gama ganinta suka saka mata albarka da addu'oi sannan aka maidota da
alkairi mai yawa daga garesu.

Alhmdllh taro yatashi lafiya, (Fan's barkanku da gajiyafa, lallai kunyima Uncle kara, irin wannan
tururuwa haka, harfa gaza lissafoku nayi saboda yawa, to ALLAH yabar zuminci sai, kowa tasha
kanwa saboda ciye-ciye damukayi, kar atashi da 2go da safe�, dansu o e naga har guzurin
extra akayi a viva leda�. Ba ruwana ban dad'i sunaba dai.�‍♀‍♀‍♀‍♀.

To gida yayi lafiya, daga masu gidan sai Nazeefa da zaliha, sai anty maijidda da Anty badiyya
yayar fateema itama Dan ba'a nan Kano take aureba, a jigawa, (yau tazo da safe, sikuma zuwa
jibi ta koma. saikuma Anty Sadiya da Anty Furera da Asiya 'yan jos, saikuma inna Nafe.
Kowa yayi laushi, da k'yar suka tak'ark'ara sukad'an share falo akayi morphing,
wanke-wanke kan ko kallon arzik'i bai samuba, a babban kitchen suka killace kwanukan kawai,
Yarama dakansu sukai wanka, suka kwanta, Dan suma sunyi laushin.
Da k'yar Amatallah ta tak'ark'ara tadafama Uncle cus-cus, Dan bazata ita bashi sauran

jagwalgwalon mutaneba.
Dama su Anty Sadiya suna 6angaren Aneesa, tace annan zasu kwana, Anty maijiddah kuma
da Anty badiyya zasu kwana 6angaren Fateema sai inna Nafi.
Nazeefa Asiya zaliha suna 6angaren Amatallah.
Abincin ta kinkima takai falonsa, da k'yar take taka step d'in saboda jikinta yak'ara tsami,
harwani zazza6i takeji, ga bakinta d'aci yake mata, Uncle baikai ga shigowaba, Dan ba'a dad'e
dayinma isha'iba, sukansu gajiyace tasaka kowa Neman makwanci bayan yayi salla. Duk
abinda yake buk'ata ta ajiye masa danufin shikenan bazata dawoba, a 6angarenta zata kwana
wajensu Nazeefa.
Takuma tako step d'in dak'yar tadawo, wanka tashiga tayi da ruwa mai zafi sosai, tagasa
jikinta da k'yau kozataji sassauci.
Su Nazeefa duk suna baje a gado, Asiya Na waya da saurayinta, Zaliha da Nazeefa kuma
charting sukeyi.
Bawani dogon shiri tayiba, komai bata shafaba tasaka wando da Riga masu kauri, tad'an
saka tirare. gadon tanufo tana fad'in "hajiyoyi a matsamin".
Da mamaki Nazeefa da Zaliha suka kalleta, zaliha tace, " Anty Ama....ina kenan (dukda
zasuyi sa'anni da zaliha Anty take cema Amatallah).
"Nan mana..."
Amatallah ta nuna gadon.
Cikin zaro ido zaliha takuma fad'in ''yayanfa?".
Hararta Amatallah tayi, "ni malama Ku matsa Na kwanta, ALLAH barci nakeji".
" hhhh aikuwa badai a gadonnanba".
Cewar Nazeefa tana k'ara bajewa sosai yanda Amatallah bazata samu wajeba.
Asiya data katse wayar saboda mahawarar tasu itama tace, "lallaima Amatallah, ke in ance
ki kwanta anan saiki kwanta? Shikuma bawan ALLAH fa......"
Har Amatallah zatayi magana wayarta dake saman madubi tashiga 'Yar tsuwwa alamar kira.
Juyawa tayi ta d'auka, ganin Uncle ne ta tunzuro baki gaba.
Hakanne yasakasu Nazeefa kwashewa da dariya.
"sai'a tattara atafi kiran boss".
Cewar Asiya.
Hararta Amatallah tayi kafin tad'aga kiran tasaka a kunne.
" wai ba'asan nadawo bane? Kokuwa ba'a yayinane?". Uncle yay maganar cikin
sassanyar muryarsa wadda taratsa 6argo da jinin Amatallah".
Bubbuga k'afa Amatallah tashigayi ak'asa, cikin shagwa6a tace, "kai Uncle da bak'ifa".
"ayaaa kina nufin saboda bak'i bazakizo ki tarairayeniba? Nifa bazan iya barci nikad'aiba
my best, a tausayama bawan ALLAH mana".
Yanda yay maganar a mariraice saiya bata dariya, ta to she baki tanayi k'asa-k'asa.
"Oh dariyama kikemin ko?".
Da sauri tace, " ALLAH uncle a'a, ammafa su anty furare fa........
"Karkimin k'arya, nasan suna 6angaren Aneesa, aina lek'o d'akin naji nagasu Nazeefa ne
kwance akan gado, Dan haka nabaki 10minute's, kokizo da arzik'i konazo dakaina wlhy
agabansu Na cicci6eki babu ruwana".... d'iff ya kashe wayar.
Tamkar Amatallah ta FASA ihu haka taji.

Tana zin6ure-zin6ure tasaka hijjabi yatafi, su Nazeefa suna mata dariyar wai dole a amsa
kiran boss ko jiki yay tsami.
Fita tayi tana balla musu Harara, tabugo musu k'ofar da k'arfi.
Aiko suka kwashe da dariya, har tafara taka step tana jiyosu sunayi.

Nimafa bara nayi kad'an Ama....., fans kuma kuyi 'Yar kad'an� Dan kar musa Ama..... Ta
fashe, naga tacika fam��)................✍














*_ALLAH kajik'an iyayenmu_*�
[1/19, 8:33 AM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce_*


____________________
*_Number 33_*
____________________

Da sallama ciki-ciki tashigo falon nasa, baya nanma, tasan yana bedroom maybe.
Zamanta tayi afalon tana tura baki gaba, kusan 2minutes bai fitoba tayi kwanciyarta a
doguwar kujerar, agajiye take over, dan haka barci yad'an fara figarta.
K'amshin turarensa daya cika mata hanci yasata bud'e idanun kad'an ta sauke akan
fuskarsa, bud'e idon tayi sosai tana kallonsa.
Ya sakar mata murmushi yana zama gefen kujerar datake kwance, "anya kuwa amaryarnan
tawa ba raguwa baceba?". yay maganar yana shafa fuskarta da hannunsa na dama, na haggun
kuma yad'orashi akan hannayenta dake saman cikinta.
Tad'an lumshe idanun takuma bud'esu a kansa tana turo baki.
" shagwa6a namiki k'yau my best. yanzu dai ya kikejin jikinki?".
"Kwalkwal tayi da ido tana niyyar masa kuka, " ALLAH Uncle duk babu dad'i, bakinama d'aci
yakemin".
"Ayya sorry my best duk na girmane, inji yaya d'acin bakin yake". Yay maganar yana manne
bakimsa kan nata. (Humm, Uncle wayo kenan�).
Kusan mintuna 3 yana k..... nata, tuntana d'an dojewa hardai ta barsa yayi yanda yakeso,
yad'ago yana kallonta da murmushi, " nimafa naji d'acin bakinnan my best, kodai muje muga
doctor Shu'aibu? Amma bara nakumaji kad'an". Yamatso zaikuma had'e bakin nasu.
da sauri ta yunk'ura ta tashi "Uncle wannanfa wayone wlhy".
Ya tuntsure da dariya yana sakkowa k'asa kan carpet, itama murmushi takeyi tana zuba
masa abinci.
" my best! My best!! Wato kin gane wayo nake miki kenan?".
"ALLAH kuwa Uncle ai na ganoka". ta tura masa abincin gabansa.
" shikenan my best tunda kin ganoni, matso muci abincin".
"No Uncle Na k'oshi, barci nakeji wlhy, nagaji".
Yanda tayi maganar saita sakashi narkewa, ya jinjina mata kai kawai danya kasa magana.
Tace, " Uncle naje Na kwanta?".
Kai ya d'aga mata yanamai lumshe idanunsa da shafa gemunsa.
Mik'ewa tayi tana neman k'ofar fita, da sauri yace, "my Best wai ina kike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login