Showing 57001 words to 60000 words out of 109227 words

Chapter 20 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

kuma.


____________________
*_Number 22_*
____________________


Kamar yanda yasaba da asubahi yabisu duk ya tada kowacce dantayi salla, yatasa yaransa
gaba suka tafi masallaci.
Koda suka dawo saiya haye samansa yay kwanciyarsa.
Aneesa ma da barcin ta koma abinta, komi tagani kuma saita tashi tafita kitchen had'a
break fast. tafara babu dad'ewa Amatallah ta shigo kitchen d'in itama, kallon juna sukayi,
Amatallah tace, "ina kwana Anty".
Cikeda yanga Aneesa ta amsa mata.
Amatallah bataji komai a rantaba, dan har zuwa yanzun bata gama Sanin ma'anar kishinba,
tarayu gidansu Amminta ita kad'aice, shiyyasa bata ta6ajin zafi ko haushin wani Abu da
Aneesar keyiba, tanama d'aukar hakan kawai a tunanin halin Aneesar ne.
Kauda tunaninta tayi gefe, tai murmushi da matsawa kusada Aneesa tana fad'in " Anty mizan
tayaki dashine?".
Yanzunma a d'age Aneesa tad'an kalli Amatallah, saikuma tacigaba da abinda takeyi, "no
kije abinki, sonake yau na had'ama my Dear special breakfast da kaina, kodan na nuna masa
godiyata na dad'in daya jiyar dani jiya, ai ba ayi mai miji da banba mai girki daban kingani ".
Dukda Amatallah taji duk maganar Aneesa tsaf, sai dai bata iya fassara magana ko d'aya
ba a ciki, amma ta fahimci maganace cikin magana tamata. d'an murmushi kawai tamata tace, "
OK bara naje to nayi shirin school, dama inada lectures d'in safe". bata jira amsar Aneesa ba
tafice abinta. Aneesa taraka bayan Amatallah da harara tana ta6e baki.


Nidai nace, " hummmm".


*********
A 6angaren Fateema tunda maigidan ya tadasu da asuba taga Saifuddin a d'akinta saitaji
wani haushi, wato ita Dan an raina mata hankali shine aka d'akko yaro aka kawo mata dansu su
samu su warwasa yanda sukeso. To aii idanma gaskiyane yau d'akin Amatallah yakamata ya
kwana ko, kenan Aneesa tayi wani makircin?, ai ko sai tayi mata abinda zata bak'anta ranta yau
d'innan basai gobeba.

Tayi wata 'Yar dariyar mugunta.


Tofa Uwargida ran gida, mikike k'ullama Aneesar kuma?.�


**********

Tunda Amatallah tabar kitchen d'in takasa manta maganganun Aneesa, datayi k'ok'arin
mantawa sai maganar tadawo mata a rai, sai takejin wani gefen zuciyarta yanajin kamar d'acin
maganar, haka tagama shiryawa sukuku.
Tayi k'yau cikin zani da riga Na shadda oxblood color, zani Rafa sket, saiya fita tamkar sket
d'in, hakama rigar Tamata d'as, batawani yi kwalliyaba, fauda kawai ta shafa da kwalli sai
lipstick data saka, d'an kwalinma normal d'auri tayi, tana tsaka da kimtsa abinda zata buk'ata a
handbag yay sallama. Amsawa tayi a sanyaye, sannan ta rissina ta gaidashi.
Tsura mata idanu yayi ganin yanda takeyi komai a sanyaye, tamkar mai tunanin wani abu.
"Khadeeja!".
Yakira sunanta yana zama kan stool d'in madubinta datayi shafa.
Kanta a k'asa tace, "Na'am Uncle".
" bakida lafiyane?".
Yanzunkam sai da ta kallesa, idonta yad'an Tara kwalla, saboda haka kawai maganar
Aneesa har yanzu cin zuciyarta takeyi, tanason tasan ma'anar maganar, Dan yanayin da
Aneesa Tamata maganar kawai ya tabbatar mata bamai dad'i baceba.........
"Khadeeja!". Yakuma kiranta dad'an k'arfi Dan ganin tatafi wani tunanin, hakan kuma ya
tabbatar masa akwai abinda ke damunta d'in.
Da Sauri tace, " na'am Uncle, INA jinka".
"Kina jina ko kina tunani dai my best, kinga please fad'amin damuwarki, karki 6oyemin
khadeeja, yanzu nine Brother, nine Ammi, nine Uncle, kuma nine Miji, duk abinda yadameki
nizaki tunkara Na share hawayenki kona kare mutuncinki nakuma kwato miki hak'k'inki kinaji
ko". Kanta ta jinjina masa tana had'iye kukan dayazo mata.
"Yauwa my Best! to fad'amin kinji, ki d'auka yanzu Nid'in Ammice, nasan dai bazaki iya
6oyemata damuwar kiba ko?".
Muryarta Na rawa tace, " ALLAH babu komai Uncle".
"Khadeeja ban yardaba, Bahaka muka rabuba jiya da daddare". yayi maganar yana
tasowa zuwa gareta.
Handout d'in hannunta da bag d'in ya amsa ya ajiye akan gadon, ya d'ora hannayensa duk
biyu a kafad'arta, idonsa Na kallon fuskarta.
Ita kuma ta duk'ar da idonta tana kallon k'afarsa.
Cikin sassanyar muryarsa wadda takuma komawa slowly yace, " waye ya 6ata miki rai a
gidanan? Fateema!".
Ta girgiza kanta.

Yace, "Aneesa!".
Shiru tayi.
Hakanne yasashi fahimtar Aneesa Ce.
Iskar bakinsa ya furzar sannan yakuma cewa ''Aneesa Ce ko? mita miki?".
Hawayen datake mak'alewa ne suka zubo a kumatunta, murya Na rawa tace "babu abinda
fa tamin Uncle, kawai naje tayata girkine tace nabarsa zatayi, shine naji babu dad'i, gani nake
ko wani Abu namatane, tunda kaga da bakanan kullum tare mukeyi da Anty Nazeefa , wani
lokacin kuma da ita Anty Aneesar, shiyyasa yanzu datace Na barsa sainakejin babu dad'i kamar
wani laifi namata".
Iska Yakuma furzowa a bakinsa, kafin yamatso da ita jikinsa ya rungumeta yana shafa
bayanta alamar lallashi. Sunkai kusan Minti 3 a haka sannan ya d'agota, hannunsa yasa ya
goge mata hawayen kafin yakai bakinsa ya sumbaci goshinta. " ki daina damun kanji Indai akan
hakanne kinji my heartbeat, badan kin mata laifi bane, kawai inaga Dan taga zakije school ne,
amma zan mata magana, daga yau karki kuma zubarmin da hawayennan masu tsada akan
wata a gidannan, kema matar gidace kamar kowaccensu, zankuma tabbatar musu da hakan
kinji ko?".
Kanta ta d'aga masa alamar to.
Yace, ''yauwa my babyna, yimin murmushi mana konaji sanyi". 'Yay maganar yanajan
kumatunta'.
Hakanne yasata sakin murmushi mai k'ayatarwa.
Sumbatar goshinta da kumatunta yakumayi yana fad'in "yauwa kokefa my best".
Kunya dukta kama Amatallah itadai.
" kinada lectures d'in safene?".
"Eh Uncle".
" Okay, to k'arasa shirin ki sameni a falo mutafi, idan Na ajiye yara a School saina k'arasa
dake".
Kanta ta d'aga masa alamar to. shikuma ya juya yafita.
Afalo ya iske yara angama shiryasu, zama yayi duk suka zauna kusada shi suna gaidashi,
ya amsa yana sumbatarsu d'ai-d'ai a kumatu.
Babu dad'ewa Fateema tafito cikin kwalliya, (a raina nace Uwargida kina fama da kankinma
bazaki hutaba).
Tunda ta fito idon Alhaji Muhammad Na a kanta, sai murmushi suke sakarma juna, mik'ewa
yayi ya taimaka mata ta zauna, yanason yad'an sumbaceta amma ga yara, Dan haka yamata
magana rad'a-rad'a, "sorry my tee.. My children's na kallonmu".
Murmushi tamasa, Dan tasan miyake nufi, yanason sumbatarta ga yara, tasan bazai iyaba.
Gaidashi tayi da tsokanarsa ango kasha k'amshi, duk angwancinne yasa aka manta
damune?".
Wata 'yar dariya yayi, yakuma k'asa da murya Dan kar yara su jisu, " my tee... Nazama abin
tsokana kuma? ai na shiga kina wanka, su Abulkhairi basu sanar miki bane?".
Itama dariyar tayi, tace, "wasa nakeni Nurrina, ya gajiyar hanya".
"Alhmdllh my tee.., ammafa akwai, gashi yau dolene nad'anyi wasu yawo wlhy a cikin gari".
" amma dai daka hak'ura kad'an huta yinin yau a gida, zuwa gobe saikayi duk abinda
kakeso".

"Ai fitar tanada muhimmanci my tee..., Alhaji Sabi'u a matse yake dason ganina, nima
kuma dai hankalina na kansa, za6e yakuma gabatomu gab, dolene muyi wani motsi da
gaggawa kinga".
Kallonsa take cikeda so da k'auna, jin mijinsu take harcan k'asan ranta saboda
k'yawawan halayensa...
Ahaka Aneesa tafito daga 6angarenta cikin kwalliya ta samesu. ganin yanda suke kallon
junansu sai kishi ya kamata, harara ta balla musu.
Sarai Fateema ta ganta, amma shi bai gantaba saboda yabata baya kad'an.
Dariya Fateema tayi a ranta, da fad'in bakiga komaiba 'yan mata, saima anjima ma kin shiga
tarkon dazan d'ana miki.
Fitowar Amatallah yasaka Fateema janye idonta daga kansa, ta maida kan Amatallah tana
murmushi, " Amatallah kin tashi?". tafad'a cikeda fara'a.
Itama Amatallah d'in murmushin tayi, kafin tabata amsa yaran duka sukayo kanta suna
fad'in "Antynmu ina kwana!". Kowa na 'Yar rige-rigen fad'a da shigewa jikinta.
Duk had'asu tayi ta rungume, ta amsa musu da tambayar sun tashi lafiya?.
A tare sukace " lafiya lau antynmu".
Daga Uncle har Fateema kallonsu suke suna murmushi, zuciyoyinsu najin dad'in yanda
Amatallah keson 'ya'yansu, (masu iya magana kance mai d'a wawa) wannan yasaka Fateema
kanji sassaucin kishin Amatallah tunkan ta tafi Dubai,, dan duk wada yaga yanda Amatallah
kema yaran yasan har zuciyartane. Guntun tsaki Aneesa tayi tashige kitchen. tana jiyo yanda Amatallah ke gaida Fateema cikin
girmamawa, itakuma Fateeman tana amsawa tamkar da biyu. jitai duk tak'ara tsanarsu suduka.
Uncle kam dad'ine sosai yakuma kamashi, Dan ganin yanda Fateema take bama Amatallah
kulawa, sai yaji takuma girma da kima a idonsa.
Yarane kawai sukayi break fast d'in, Amatallah ma tea kawai tasha, danji tayi bazata iya
cim ko lauma d'aya daga abinda Aneesa ta girkaba, saitaji ma'anar maganganunta sannan.
Uncle baice mata komaiba, danya fahimci haushin Aneesa takeji, kuma tabbas ta 6oye
masa ainahin abinda Aneesar ta mata.
Aikam ganin shine zaikai Amatallah school ko rakkiya Aneesa bata masaba, baibi ta
kantaba shima ya fice abinsa, amma yanason saiya san ainahin abinda taima Amatallah d'in.
Amota ma Amatallah tayi shiru, sai shine keta hira da yaransa dake bashi labarin abuwan
da akayi bayanan.
Wani yayi magana wani kuma yayi murmushi kawai, ahaka har sukaje school d'in yaran.
Yaran duk suka fita, shikuma yajuyo yana kallon Amatallah, "my best d'an bani 5minutes
naga headmaster d'insu, ai bazaki makaraba ko?".
Kanta ta d'aga masa. da fad'in " eh Uncle".
Fita yayi yana murmushin miskilancin Amatallah, yadad'e da sanin dama Amatallah
miskilace ta bugawa a jarida.
Kusan mintuna bakwai saigashi ya dawo suka tafi. motar tayi shiru, shi yana tuk'i yana
kallon jama'ar gari da nazarin wasu abubuwa gameda yanayin matasan daketa kaikawo, ko
zaiga wani canji dasuka samu a 11month's d'in d'aya d'auka baya k'ar, sai dai baiga wani canjin
ba koda k'aramine. Amatallah kuma tayi shirune tana kallon mutane dakuma cigaba da juya maganganun

Aneesa, (kusan dai Amatallah wajen rik'e Abu arai).
Har gaban department d'insu ya kaita, amma yace bazai fitaba, Dan bada shirin shigowa
yazoba.
Har zata fita yarik'o hannunta.
Juyowa tai ta kallesa, yawani langa6e kai "my best! dama haka ake sallama da miji?".
K'asa tayi da kanta tana murmushi. ya murza hannunta. dag'owa tayi tad'an kallesa,
shikuma ya d'aga mata gira.
da sauri ta juyar da fuska tana fad'in ''kai Uncle". a shagwa6e tayi maganar.
"Lallai yarinya, ashe zamu kwana a motarnan kenan? dan yau babu wani Uncle anan".
Juyowa tayi tace, " uncle kwanafa!?".
"Sa wasa kiga aiki kuwa yau".
" wayyo Uncle, ALLAH munkusa shiga lecture, kagama su Goodness can da alama nisuke
jira".
''Laifin waye to?".

Amatallah tace nashiga tara, wai Uncle ya manta matsayinsa ne agareni. a zuciyarta tayi
maganar.

Kamar yasan mitake fad'a kuwa yakuma ruk'o hannunta da k'yau, "my best kifa rage kunyarnan,
lokaci yayi dazaki fara d'aukar Uncle d'inki a matsayin miji ba Uncle kawaiba, koda yake
niyakamata na canja wannan matsayin nawa a gareki". yak'are maganar da sumbatar
hannunta. Idonta ta rimtse a zuciyarta tace ya salam.
Yana sakinta ta fice da sauri.
Dariya kawai yayi yana girgiza kai, ya tada motar ya tafi yanamai jin farincikin yanda
Amatallah tafara sakin jiki dashi, yana ganin zuwa yanzu lokaci kad'an zai k'ara mata komai ya
dai-daita, ayanda yake gani itama takamu da sonsa kamar yanda ya koyar da ita.

Tunda ta fito a motar wasu daga d'aliban suka saka mata idanu, hardasu Fa'iza.
K'arasowarta yasaka Rita fad'in "baby ke da waye yau? muntafi tarbanki mukaga ba ya
Jabeer bane".
Da sauri Amatallah tace, " uncle d'inane".
Fa'iza dake zaune da tsohon cikinta tayi dariya, danta kuma gaskata Amatallah nada aure
yanzun..... Kafin tayi magana Goodness tace, "Amatallah anya Uncle d'inan ba mijinki
baneba?".
Harararta Amatallah tayi batareda tace komaiba.
Aiko suka saka mata dariya, Fa'iza ta yunk'ura ta tashi dagyar tana kallon Amatallah, " to
'yammata ai yanzu munsan komai, sai a daina raina mana wayo, aini wlhy tundaga yanda kike
amsa masa waya nasan yawuce Uncle kawai, yaukuma munga zahiri, dan yanda yarik'e
hannunki yana miki wani kallo kad'ai yabamu ams........" Amatallah bata bari ta k'arasaba tarufe mata baki. Rita da goodness suka shek'e da dariya.
Sai kawai Amatallah ta fashe musu da kuka, dama ga abinda Aneesa ta mata yanata
caccakar ranta. shiru sukayi, saikuma jikinsu yayi sanyi, nan suka shiga lallashinta, suna bata

hak'uri.
Share hawayenta tayi tace, "kubar bani hak'uri, nifa bakune kuka sakani kukaba, kawai dai
yanda auren namu ya kasance da Uncle na tuna.
Tabasu tausayi sosai. ganin time d'in lecture d'insu yayai tace Subari su fito zata basu labari.
A sanyaye suka jinjina mata kansu, sanan suka nufi lecture................✍






One luv my sweet Fan's







*_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*�
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce_*


_Na gaisheku Aminan arzik'i, *Miss Xoxo and Ayusher Muh'd* kud'in na da banne a zuciyar
Bilyn Abdull_
_i love you so much masoyan kwarai�_

____________________
*_Number 26_*
____________________


Dariya ce takusan kufcema Amatallah amma tayi k'ok'arin dannewa, dariyar tata tazone
kam saboda ganin yanda Aneesa take sakkowa daga benen tamkar wadda aka biyo. tayi
k'ok'arin kauda kanta gefe tana cigaba da jere kulolin abincin bisa tiren data d'akko.
Sai da Aneesa taimata wani kallo sannan ta shige 6angarenta tana murmushin muguntar
data shiryama Amatallah itama.
Sarai Amatallah taga mugun kallon da Aneesa tamata, amma bai dametaba, tadai nemi
tsarin ALLAH daga sharrinta a zuciya, Dan tasan tabbas wannan kallon bazai zamto Na alkairi
bane.
gyara mayafinta tayi sannan ta d'auki tiren abincin tayi sama, komai cikeda dauriya
takeyinsa, amma k'asan ranta ita kad'ai tasan a fargabar datake. Sallama tayi a k'ofar falon
batareda ta shigaba.
Uncle dake kishingid'e har yanzun inda suka barsa ya amsa yana kallon k'ofar, "shigo mana".
Yafad'a yana maida kallonsa ga TV.
Sai da tad'a sauke ajiyar zuciya kafin ta tura labulen da tiren tashigo.
Batareda ya kalletaba yace, " lafiya naga kin dad'e?".
Kanta ta kad'a masa kawai tana ajiye tiren bisa santa table d'in dake tsakkiyar falon.
Hakanne yasakashi juyowa ya kalleta, dai-dai itama ta d'ago zata cemasa ga abincin suka
had'a ido. Da sauri ta sauke nata. shima janye nasa yayi yatashi zaune yana murmushi, k'arar
TV ya rage

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login