Showing 48001 words to 51000 words out of 109227 words
Chapter 17 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
k'iba sosai, Dan zaima iya ninkashi biyu.....
Maganarsace ta katse mata tunani, ta kalleshi da Sauri saikuma ta kauda kanta, zama tayi
kujerar dayake nuna mata. bayan zamanta ta gaidashi a ladabce. Shikuma ya amsa cikin fara'a.
Sun tattauna da Jabeer, aka bata wasu takardu tasaka hannu sannan suka masa sallama
suka fito.
Har department d'insu Jabeer ya rakata, ya d'an mata bayani sannan yamata sallama yatafi
bayan yabata 1k, yace bayan sun gama takirashi.
Kanta ta jinjina masa tayi godiya.
Tafiyar Jabeer babu dad'ewa wayarta tafara wringing, Jakarta tabud'e ta lalubo phone d'in,
ganin sunan Uncle saida gabanta yafad'i, d'an wawwaigawa tayi Dan Neman inda zata zauna. A
dakalin barandar wajen taje ta zauna, dan taga wajen yanada tsafta, ta d'aga wayar tasa a
kunne.
Sassanyar muryarsace tamata sallama.
Itama a sanyayen tace, "wa'alaikassalam, Uncle ina kwana".
" lafiya lau my best, amma mu munshiga yini nan, ya Ku isa makarantar?".
"Eh Uncle, harma Yaya Jabeer yatafi".
"okay, to babu wata dai matsala ko?".
" eh Uncle, komai normal".
"To Alhmdllh, saikuma a dage, banda wasa da k'awayen banza please my best! Kinji,
banda biyema samari dan ke matar aurece kin sani".
Idontane yacika da kwalla, itafa kokad'an batason atuna mata wai tanada wani aure,
aurenma Na Uncle d'inta.........
" kuka kikeyi ko my best!? ".
Da sauri ta share hawayenta, tace, " a'a Uncle ina jinka".
''Imyiim, bagashi naji muryarki Na rawaba".
"Uncle murace kawai keson kamani".
" kokuma Uncle akeson yima wayo ba, anyway koma dai Yaya kiringa tuna alk'awarin da
kikamin na kin daina kuka".
Kuma share hawayen tayi, sannan tace "to Uncle, insha ALLAH bazaka sake jiba".
" haka kullum kike fad'amin ai, amma kin kasa cika alk'awari".
"To kayi hak'uri Uncle, zan kiyaye yanzu. yasu Anty da siddiqa?".
" suna gida lfy lau, ni ina school ne".
"Uncle inka koma ka gaida minsu".
" zasuji insha ALLAHU, yanzu ki samu wata a wajen saiki tambayeta inkunada Lecture by this
time kinji".
"To Uncle sai anjima".
''Ok bey bey my heartbeat".
Da sauri tace, " Uncle!".
''Yace uyim, yayane? kobaki yarda ke heartbeat d'ina bace?". A wani salo yay maganar.
Da sauri ta yanke wayar, shikuma ya tuntsure da dariya daga can.
Nima dai Na tayaka Uncleí ¾í´£, nasan Fans ma zasu tayamuí ½í±Ží ¼í¿».
Amatallah tana yanke wayar ta rik'e ha6a tana fad'in "o ni Khadija, dama haka Uncle yake?".
Amatallah kad'anma kika gani indai Uncle ne.
Mik'ewa tayi tana cigaba da juya lamarin Uncle d'inta a zuciya, harta k'arasa wajen wata
dake zaune can gefe itama cikin shiga ta kamala, aganinta ita kad'ai ta dace tama tambayar da
Uncle yace tayi, dan tun tana waya taga wucewarta har zamanta awajen.................âœí ¼í¿»
í ½í±Ží ¼í¿»
One Luv my sweet Fan'sí ¾íµ°
*_ALLAH yajik'an iyayenmu._*í ½í¹í ¼í¿»
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typingâœí ¼í¿»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*í ½í²¡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* â‰
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceí ¾í´™í ¼í¿»_*
_masoyanmu Amanna afuwa dajin *YAR SARKI CE* shiru, wasu 'yan dalilaine suka kawo
hakan, amma insha ALLAH zata cigabaí ¾íµ°í ¾íµ°._
____________________
*_Number 20_*
____________________
Wani Saloon Ya Jabeer yakai su Amatallah, a can suka iske Anty maijiddah, itadai
Amatallah sai mamaki take a k'asan ranta.
Babu 6ata lokaci wata farar mata tajata wata k'ofa, Ashe cikin gidane, koda suka shiga saita
kaita wani d'aki, zani tabata tace tacire kayanta tana zuwa.
Amatallah dai mamaki dukya kasheta, amma duk abinda aka sakata babu musu takeyi,
tasan Anty maijidda dai bazata cutar da ita ba.
Tana gama cirewa babu dad'ewa matar tadawo da kwa6a66en Abu a boket k'arami.
Mik'a mata boket d'in tayi, tace, "dan ALLAH karki cutar da kanki, ki tabbatar ko ina Na jikinki
yasamu, bayan kin gama murje jikinki saiki shafa wannan shikad'ai a fuskarki wannan kuma
bayan kin gama zanzo nasaka miki a gashi. daganan kishiga nan cikin, ta nuna mata wani
k'aton bambu da aka saka wani Leda. Kai Amatallah ta jinjina mata.
Duk yanda matar nan tasakata haka tayi, abun sai wani masifar k'amshi yakeyi, haka dai
tagama murje ko ina najikinta tashiga banbun kamar yanda matar tace, kusan mintuna biyar da
kammalawarta matar tayi Knocking k'ofa da tambayarta ta kammala.
Amatallah ta amsa mata da eh.
Shigowa tayi, taga Amatallah tayi yanda duk tace, taji dad'i, dan haka tafara shafa mata
d'ayan abun a gashinta, tana gamawa tasaka bak'ar Leda ta d'aure mata kan, tafice ta barta.
Sai da Amatallah tayi kusan awa biyu sannan matar ta shigo tahad'a mata ruwan d'umi da
k'amshi, sai wani sabulu tabata tace tayi wanka.
Indai tak'aice muku sosai Amatallah tasha gyara a d'akinnan, kusan awa 3 sannan suka
dawo ainahin wajen saloon d'in, su Anaty maijidda sai yaba k'yan da tayi sukeyi, Nazeefa harda
tatta6ata.
Itadai Amatallah murmushi taitayi, ita kanta tanajin canji Na musamman a jikinta.
An kuma wanke mata kai aka gyara matashi, sanan aka mata kunshin Jan lallale da bak'i.
Dole ka ganta kasan Amaryace, tahad'u sosai abin harma ba'a magana, ga wani sirrin
k'amshi Na musamman.
Basubar saloon d'inanba saida aka yima Amatallah simple makeup mai burgewa, ba'a
cikashi d'inanba yanda zai canja mata kamanni, amma tayi k'yau masha ALLAH.
bayan matar nan ta had'ama Amatallah wasu kayan gyaran jikin dazata ringayi a gida suka
tafi.
Anty maijidda gidansu ta wuce, Jabeer kuma ya maida Amatallah da Nazeefa gida.
Kusan k'arfe 3:26pm lokacin, kuma ALLAH yasosu Aneesa bata dawoba.
Dawowarsu babu dad'ewa sukaji dawowar Aneesa, itama gyaran jiki taje, takumayi k'yau
sosai wlhy, sai shek'i da walk'iya takeyi kamar amaryar itama.
Batawani 6ata lokaciba tashiga ketchin, dama kafin ta fita ta tanaji komanta, had'awa kawai
zatayi.
Nazeefa Ce tafito ta tayata komai, danta hana Amatallah fitowa. Tace baza'a ganta ba a waje
sai su Uncle sun shigo gidan.
Rashin ganin Amatallah yasa Aneesa d'aukar koma bata gidan, bakuma ta tambayi Nazeefa
ba.
K'arfe hud'u suka gama komai, suka kuma gyara gidan da bazama kowanne lungu da sak'o
k'amshi mai dad'in gaske.
Aneesa ta shigo 6angarenta dan tsara kwalliyar tarbar mai gida.
Amatallah tana idarda sallar la'asar saiga Nazeefa ta shigo, itace ta zaunar da ita ta gyara
mata kwalliyarta datayi alwala wasu guraren suka d'an 6aci.
Wani material pink colour da akaima d'inkin sket da Riga Nazeefa tabata,
d'inkin yayi 'yau over, gashi yafitar da ainahin Shep d'inta, sannan colour d'in ya haska bak'ar
fatarta. Nazeefa tamata d'auri mai k'yau, itadai Amatallah kallon ta kawai takeyi cikeda mamaki,
amma takasa cewa komai, ita damuwartama yanda zata had'u da Uncle d'in nata, dan
kunyarshi takeji sosai, musamman ma idan ta tuna da yanda yake mata a waya yanzun. Bayan Nazeefa ta gama mata komai hardasu sark'a da abin hannu, ta fesheta da turarurruka
masu k'amshin tsiya da shiga zuciyar mai shak'arsu.
Hummm, masu karatu, yaufa Amatallah d'inku ba'a magana, ni tsorona ma karta haukatar
mana da Uncle faí ½í¹†í ¼í¿».
Aneesa ma tanacan tana tsara nata gayun, itamafa babu sauk'i, dan wanka iya wanka tayi, ta
bulbule lungu da sak'o Na jikinta da k'amshi, dama harda Siddiqa aka tafi gidansu innani.
A can kuwa 4:30 nayi su Anty maijidda da yara suka tafi tarbo su Uncle a airport.
5:8pm jirgimsu ya sauka.
Uhhm nafad'a lokacinda naga Fateema Na sakkowa jirgi da k'yar, cikinta ya tsufa, tak'ara
k'yau da haske ga k'iba, Alhaji Muhammad Na bayanta shimafa ba'a magana, ya murje dakuma
kwarjini, sajennan da gemunsa sunkuma yin bak'i sid'ik, sai furfura d'ai-d'ai data k'awata gemun
nasa, wadda bazamuce ta tsufa bace sai dai baiwarta da ALLAH yamasa. Da gudu yara sukaje suka tarosu suna ihun Kiran Abbunsu da Ummansu.
Alhaji Muhammad duk yahad'asu ya rungume harda yaran Anty maijidda guda uku, bayason
su Ce zasu rungume Fateema dantayi nauyi.
Tsaye tayima tana kallinsu da murmushi jin dad'in ganinsu.
Anty maijidda ta k'araso tana mata sannu da zuwa da tsokanarta uwar biyu.
Duk dariya sukayi, aka shiga gaishe-gaishe kafin su k'arasa mota, dole saida suka had'a da
taxi dan motar tamusu kad'an.
Duk hayaniyar da akeyi a gidan Amatallah Na jiyowa daga d'aki, gabanta sai kuma fad'uwa
yake, heartbeat d'inta nak'ara k'arfi, amma takasa fitowa Dan kunya takeji.
Uncle kam tunda Aneesa tafito idonshi akanta, bak'aramin k'yau kwalliyarta tamasaba,
gadan-gadan shi ta nufa zata rungume amma saiya doje ya d'auki Siddiqa da Umminta, Dan
bazai iya abin kunyarnan gaban k'annensa da yaransaba.
Lamarin yabama Fateema dariya sosai, danta lura tsaf da nufin Aneesar dakuma abinda
mijin Nasu yayi Na gujema manufarta.
Nazeefa ma ta lura, ta juya fuska tana dariya.
Duk da abinda yamata ya 6ata mata rai, amma saita danne, ta k'araso daf dashi tana masa
sannu da zuwa, cikeda fara'a ya amsa mata da kanne mata ido d'aya. ta sakar masa da wani
sihirtaccen murmushi kuwa da d'age masa gira.
Kallo d'aya tama Fateema tace sannunki.
Ran Fateema ya 6aci da rainin wagon Aneesar, ya gida kawai tace itama tayi gaba abinta.
Har suka k'arasa ciki yana baza idon son ganin Amatallah amma babu ko k'urarta. Anty
Maijidda Na lura dashi, sai kawai tayi murmushi, a zuciyarta tace ya Muhammad Amatallah
tawuce arhar ka ganta kai tsaye, saika bita har d'akinta.
Dukda daular abincin da Aneesa ta had'a musu bata d'auke hankalin Uncle ba, gaba d'aya
hankalinsa nakan son ganin Amatallah, soyake kawai yaga halin datake ciki.
Suna cikin cin abinci Fateema ta kalli Nazeefa tana fad'in "Nazeefa wai Amatallah fa?".
Da hannu Nazeefa ta nuna 6angaren Amatallah d'in.
Uncle datun da suka fara maganar ya d'ago ido yana kallonsu yace, " lafiya dai ko bata
fitoba?".
Nazeefa tace, "Yaya ban saniba nima, tundai d'azun tana ciki"..
Ajiye spoon d'in hannunsa yayi ya mik'e yana fad'in "bara Na dubata to".
duk binsa da kallo sukayi, wani haushi yakama Aneesa. Fateema kuma tayi murmushin
mugunta, dama danta rama abinda Aneesa tamata ta tambayi Amatallah d'in, Dan tasan dole
mijinsu yayi wani Abu akai.
Anty Maijidda kam da Nazeefa sai dariya sukeyi a zukatansu.
Amatallah da har suka shigo cikin falon tana jiyosu, tana kwance a doguwar kujerar falonta
tana game a waya, dukda zuciyarta sai harbawa take da fargaba. game d'in kawai takeyi, amma
bawai yana mata dad'i baneba, Rabin hankalinta nakan su Uncle d'in.
A hankali yaturo k'ofar falon ya shigo.
Ko kad'an Amatallah bataji shigowar saba, sai k'amshin turarensa saboda ta juyama k'ofa
baya, kuma a la66ansa yayi sallama yanda bazai yuwu tajiba.
Shiru tayi tana hasashe, a zatonta ko tun daga waje k'amshin ke shigo mata.
Uncle kam al'ajabine ya kamashi, shiyyasa yakasa motsawa, tunda yake bai ta6a ganin
Amatallah da kwalliyaba sai yau.
Jin kamar mutum tsaye akanta yasata juyowa cikeda fargaba. da Sauri ta mik'e tana fad'in
"Uncle sannu da zuwa, ALLAH banasan ka shi..go..ba ne".
Murmushi yayi, ganin yanda jikinta har rawa yake, kai kace taga wani ojuju ne, takawa
yayi a hankali har inda take batareda yace komaiba, daga zaune Amatallah tad'an matsa baya
kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, a kujerar ya zauna shima kusada ita, ai saitaji
kamar tatashi ta tsilla a guje. Hannunsa ya d'ora kan yatsun hannunta datake wasa dasu, yanda Jan lallen yay rad'am ne
ya burgesa, murza yatsun yayi, hakanne yasaka Amatallah d'agowa tad'an kallesa.
Komi ya tuna kuma saiya saki hannun, cikin sassanyar muryarsa yace, " haba my best! Babu
fad'a miya kawo gabane? Laifin mi mukayi aka k'i fitowa tarbarmune, ko ba'a murna da
dawowarmu mu koma Inda muka fito?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta dantaji kunya sosai tace, "Sorry Uncle, ALLAH ba haka bane
fa, kawai dai".
Murmushi yayi mai k'ayatarwa, yasa yatsun hannunsa biyu ya d'ago ha6arta tareda saka
d'ayan hannun ya janye hannayenta data rufe fuska, saita rumtse idanunta.
"bud'e idon to, kifad'amin kawai dai me? kokuma nayi wani Abu".
Tace, "ALLAH uncle inajin kunya".
" my best! to miye najin kunyar?, nifa Uncle d'inkine, ko yanzun an daina Uncle d'in dani sai
mij......"
Bai kai k'arsheba ta waro manyan idanunta a kansa.
Shima saiya waro nasa kamar yanda tayi yana murmushi har hakwaransa Na bayyana a fili.
Yunk'urawa tayi zata tashi danta gudu ya rik'e hannunta yana fad'in kinga wasa nakeyi,
muje kici abinci, kowa ya hallara babu ke, har Fateema Na tambayarki taga bakizo mata sannu
da zuwaba".
"Uncle azumi nakeyi ai".
" azumin me my best? Yaufa Saturday?".
Rasa mizata cemasa tayi, dankuwa k'arya ta mullik'a babu wani azumi, tana dai jin kunyar
fitane saboda kwalliyarta.
Hakanne yasa yagane k'arya take.
Mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita tsaye.
Ta marairaice masa fuska kamar zatayi kuka, "wayyo Uncle da gaskefa nakeyi".
Baima San tanayiba, dan kallonta yake daga sama har k'asa, bak'aramin zama kayan
sukayi a jikintaba.....
Ganin hankalinsa bama kanta yakeba ta girgiza hannunsa dake rik'eda nasa.
Kallonta yayi da sauri, yace, " mikikace my best!?".
A shagwa6e tace, "kai Uncle kana nufin baka jiniba ma?".
Kasa amsata yayi, yaja hannunta dan yakula inhar suka kai wani lokacin a falonnan zai iya
kauce hanya ya aikata abin kunya....
''Uncle please zanje da kaina, ALLAH zanma ci abinci". Amatallah tayi maganar da sauri
dan ganin da gaske soyake ya kaita har falon yana rik'eda hannunta.
Baice mata komaiba ya saki hannunta, fitowa sukayi yana gaba tana bayansa, dan haka ta
6oye sosai a bayansa.
Fitowarsa yasaka Fateema da Aneesa d'agowa suna kallonsa, kowa da dalilinta na kallonsa
da son suga Amatallah d'in.
Anty Maijidda tace, " a'a Yaya lafiya dai ko? ina Amatallah d'in to?".
Juyawa yay a zatonsa bata biyoshiba, sai ya ganta a bayansa, tana famar 6uya, matsawa
yayi gefe yanda zasu ganta yana fad'in ''k'alau take, kunyarku takeji saboda tayi.....". Sai kuma
yay shiru ya k'are maganar da 'Yar dariya yana zama a kujerar daya tashi wadda Aneesa da
Fateema suka sakashi tsakkiya. Amatallah jitai tamkar ta nurse k'asa dan kunya, Fateema da Aneesa duk sukad'an waro
idanu kanta cikin mamaki da ganin k'yan