Showing 21001 words to 24000 words out of 109227 words
Chapter 8 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
yawan
gaske a kasuwancin mahaifin nasa, kasancewar shi d'an zamanine kuma mai ilimi.
Shikam Isma'il yana jos babu abinda yakeyi, lokaci-lokaci dai yakanzo kano, yayi kwanaki ya
koma abinsa.
A wannan tsakanin auren Isma'il yatashi, ALLAH bai cika musu burinsu nayin aure rana
d'ayaba, dan Isma'il ne yafara angwancewa. batun yanda shagali ya kasance 6ata lokacine ma
aii.
Bayan auren Isma'il Muhammad yakawo musu shawarar sukoma suyi masters nasu,
(degree na biyu), 100% Isma'il ya aminta da batun. dan haka suka fara nema a University of
Lagos (Lagoon), nanma sunyi nasarar samu kuwa, dan haka suka fara karatunsu cikin nasara.
A lokacin Saliha matar Isma'il nada ciki. Rashin auren Muhammad yafara damun Isma'il, dan haka yafara takura masa akan maganar
Khadija.
Amsar daya saba bashice yakuma maimaita masa, akan yana jiran Khadija ne kamar yanda
iyayenta sukace saita kammala karatu ta.
"Haba brother, kaikuma saika zauna saita kammala d'in?".
Dariya Muhammad yayi, yadafa kafad'ar Isma'il yana fad'in " cool dawn mana my brother,
duka kwana nawane yarage? Insha ALLAH baifi watanni 7 bafa kaima kasani".
"Haka kullum kake fad'a, amma har yau ni banga wata bakwai d'in zata k'areba, kuma
mizai hana kaima baba magana a tsaida rana tun yanzu, bayan ta kammala sai musha biki
kawai".
Shiru Muhammad yayi yana nazarin maganarsa, zuwa can kuma yace, " gaskiyarka fa
brother, kaima kazo da shawara".
Babu 6ata lokaci sukayi amfani da shawarar Isma'il aka kai kud'i aka tsaida rana, sai ta
kammala karatunta.
Watanni bakwai na cika kuwa akasha biki, lokacin Saliha ta haihu d'an baizo da raiba.
Wattani shida tsakani saliha yakuma samun wani cikin, amma Khadija dai babu labari.
Watanni tara cif Saliha ta haifi d'iyarta mace k'yak'yk'yawa.
Muhammad yayi matuk'ar farin ciki, tamkar shi aka haifamawa, komai kuwa Na hidimar
sunan baby Muhammad ne yayishi, hatta da suna ma shine yarad'a mata Khadija, sunan
mahaifiyar Isma'il, kuma matarsa.
Tun daga wannan lokacin Muhammad yad'auki son duniya ya azama Khadija dasuke kirada
(Amatallah), komai yagani Na yara saiya siya matashi, kullun firarsa akan best daughter d'in
sace.
A haka suka kammala degree d'insu Na biyu daga lagos suka dawo gida, Isma'il jos,
Muhammad kano.
Muhammad yacigaba da kulada kasuwancin baba, kuma har zuwa lokacin ko 6atan wata
Khadija batayiba, duk k'arshen wata Isma'il kan d'akko iyalansa suzo kano, kokuma shi
Muhammad yaje danasa iyalan.................✍
Kubini bashi a page 11 please
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce_*
*_Ku gargad'i mai gina ramin mugunta!! _*
Wannan gaskiyane
*Doctor Alhaji mamman (shata)*
ALLAH ya gafarta maka
____________________
*_Number 9_*
____________________
A k'ofar gida yay parking motar sa, sannan ya kama k'ofar zai bud'e, a rufe take.
Shiru yayi yana kallon k'ofar, yasan tunda baya nan bazasu ringa barin k'ofar a bud'eba. Mota
ya koma ya d'akko wayarsa. Aneesa yakira.
A yangance tamasa sallama.
Shikuma ya amsa murya na rawa.
Gabantane yafad'i, tacire wayar daga kunnenta ta kuma kallon screen d'in domin tabbatarwar
shine kokuwa?. ganin shid'inne yasata maidawa a kunnen.
"My dear! Lafiya kuwa?".
Ajiyar zuciya ya sauke, a raunane yace, " kizo ina k'ofar gida......
Bata jira yakai k'arsheba tafito da sauri. K'aramar k'ofar gate d'in ta bud'e ta lek'a.
A tsaye ta gansa ya jingina da jikin gate, gabanta yakuma fad'uwa, hakan ya kuma tabbatar
mata babu lafiya.
Takowa yayi ahankali yashiga gidan, ta kalleshi tana fad'in "dear motarfa".
Kansa ya girgiza mata yace, " fita zan kumayi". yana maganar yana tafiya.
Wannan yasata binsa da sauri itama. babu kowa a falon k'asa, dan haka ya haye samansa,
Aneesa na binsa abaya.
A kan gadonsa ya zube yana sauke numfashi, Aneesa ta zauna kusadashi tana
tambayarsa miyafaru cikin damuwa.
Bai bata amsaba, sai dai cewa yayi ''had'amin ruwan wanka".
Jiki a sanyaye tamik'e zuwa bathroom d'insa, ruwa mai d'an zafi ta had'a masa, tana niyyar
fitowa shikuma yashigo, matsawa tayi yashiga sannan ta fita.
Yana wanka yana hawaye, lallai duniya abar tsoroce, jiya iyanzu yana tareda amininsa,
amma yanzu gashi awani hali mai rikitarwa, ALLAH sarki Saliha, ALLAH ya gafarta miki.
Aneesa kam da sauri ta sauka k'asa zuwa 6angaren uwargidanta.
A falo ta iskesu itada yara suna homeworks d'in makaranta.
Yanda tashigo a rikice yasaka Umman abulkhair saurin kallonta, "lafiya kuwa momyn yara?".
" inafa lafiya ummansu.........nanda ta sanar mata abinda ta Sani gameda canjawar mai
gidan nasu, da dawowar babu zato babu tsammani da yay musu, alhalin gobene yakamata
yadawo.
Atare suka fito zuwa d'akinsa.
Bai fitoba, dan haka suka zauna zaman jiransa. Babu dad'ewa yafito, sannu da zuwa
Fateema tamasa.
Batareda ya kallesuba ya amsa yana k'ok'arin shinfid'a abin sallah. Sallar magriba ya
gabatar, sannan yay isha'i, duk suna zaune suna kallonsa.
Yay addu'a yana share kwallar dake bin kumatunsa.
Sosai jikin matan nasa yakuma yin sanyi k'alau, sun k'agara ya idar suji mike damunsa.
Ganin yanda suka damu matuk'a yaga baidace yabarsu a duhuba, cikin dauriyar danne
hawayensa yaymusu bayani.
Daga Aneesa har Fateema kuka suke sosai.
Mukullin mota da wayarsa kawai ya d'auka yafita zuwa asibitin, yabarsu Aneesa nacigaba
da kukansu.
A motama yana driven yana hawaya, yakasa jarumtar danna kukansa, tausayin Amatallah
da abokinsa kawai ke nuk'urk'usar ruhinsa. a haka ya Isa asibitin.
Jabeer da kawunsu Malam Yakubu ya tarar suna jiran isowarsa.
Gaida kawu Yakubu yayi, ya amsa tareda masa ta'aziyya sannan suka k'arasa ciki.
Inda aka kwantar da baba sukaje, suduka kallo d'aya suka masa suka fara hawaye. Ba k'aramar
k'una baba yasamuba gaskiya, abin ko dad'in kallo babu. barci yakeyi saboda sunmasa allurar
barci kozai samu sauk'in rad'ad'in dayakeji.
Jiki a sanyaye sukabar d'akin, inda Amatallah take sukaje, tana kwance kamar yanda ya
barta. matuk'ar tausayinta ya mamaye zukatansu, Uncle M.A ya kauda kansa daga kallonta
saboda hawayen dasuka cika idonsa, d'an yatsa d'aya yasa ya goge sannan yanemi gefe ya
zauna.
______________________________
Uncle M.A da Jabeer a asibitin suka kwana.
Wajen k'arfe 7:am suna shirin tafiya da gawar Ammi gida dan amata sutura Amatallah ta
farfad'o.
Da sunan iyayenta ta farka a baki, tana kuka tana kiran Ammi da baba ta. da sauri wata
Nurse taje ta sanarma doctor shu'aibu Amatallah ta farka.
Dagashi har Uncle M.A a hanzarce suka k'araso.
Tana ganin Uncle M.A tamik'e da sauri tana fad'in Uncle ina Ammina da babana!, suna ina
dan ALLAH Uncle? ".
Rasa mizai fad'a mata yayi, yay tsaye kawai yana kallonta, idonsa taf da hawaye. Doctor
shu'aibu ne kawai ke lallashinta. da k'yar yasamu ta tsagaita da kukan.
Doctor yamatso kusada Uncle M.A, ahankali yace, " Alhaji Muhammad yakamata mubarta
taga gawar mahaifiyarta........
Bai k'arasaba Jabeer yashigo yana hakki, ''yaya! Yaya! Kuzo yaya Isma'il ne, gashi can.......
Suduka basuji k'arshen maganarba suka fice da gudu, harda Amatallah dake binsu cikin
layin rashin k'arfin jiki.
'Dakin da Baban Ama ke kwance suka shiga.
Hannunsa dabai k'oneba sosai yake mik'oma Uncle M.A, yana kiran brother a ahankali. ga
numfashin sa Na fita da k'yar.
Uncle M.A ya k'arasa da hanzari gareshi, shima hannun ya mik'a masa yana hawaye da
fad'in sannu brother.......
Dai-dai nan Amatallah tashigo tana tangad'i, kawu yakubu da wasu mutane hud'u suma suka
shigo d'akin.
K'ara Amatallah ta kwala tazube awajen saboda tozali datayi da babanta.
Dukansu kanta sukayi har Uncle M.A daya zare hannunsa daga na babanta.
Baisan ya cacumotaba yana kiran Khadija! Ke Khadija!! Please karkimin haka kema dan
ALLAH Khadija. Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, ya ALLAH gareka nake, a gareka kuma nake
neman taimako......yak'arashe maganar yana fashewa da matsanancin kuka.
Shima Jabeer kukan yafara ganin yanda yayansa ke kuka sai kace ba babban mutum ba.
Baban Ama ma hawaye yake yana murmushi da kallon abokinsa da d'iyarsa.
Da k'yar doctor shu'aibu yasamu ya janye Amatallah daga jikin Uncle M.A.
kai jama'a, ALLAH ka gafarta mana.
Kusan mintuna 16 aka samu komai ya lafa, amma Amatallah tana a halin doguwar suma.
Uncle M.A ya koma inda Baban Ama yake, saboda kiran sunansa kawai yake.
Yanzuma hannunsa yarik'e, ahankali yake iya magana, amma duk suna jinsa sabida shiru da
d'akin yayi.
_"d'an uwana kaga yanda k'addara tayi damu, tsakanin jiya kawai zuwa yau, mungodema
ALLAH brother, danshine mafi hikimar masu hikima akan hakan, mutuwa tabbatacen abune
akan kowanne bawa, saidai kowa akwai sanadin tafiyarsa brother, wannan mu shine namu
sanadin d'an uwana, duk duniya banida kamarka, dukda inada dangi amma kafisu matsayi
agareni, sun kashemin Saliha ta hanyar soka mata wuk'a, awannan halin na isketa bayan
dawowata sallar magriba, nikuma sun kunnamin wuta, tabbas nasan yaran da Khadija taganine
sukai wannan aikin, brother! Na d'auki hakan a matsayin K'ADDARARMU, ga Khadija nan
nabaka halak malak, ita kad'aice tarage mini, babu kuma mai iya rik'emin ita tamkar ni sai kai
d'an uwana Muhammad, ba ruk'on Amatallah kawai nakeso kayi nawani d'an lokaciba, sonake
ta kasance a gareka har k'arshen rayuwarka. brother inaso yanzunan a d'auramaka aure da
Khadija..."_
Wata muguwar zabura Uncle M.A yayi, jikinsa da muryarsa na rawa yace, ''brother mikake
fad'ane haka?, haba brother khadija fa d'iyatace, inajinta tamkar su Saifudden ne a zuciyata,
karkayi haka dan ALLAH brother, gara kace na aurama j........
_Da sauri Baban Ama ya katseshi cikin hawaye, "a'a brother karkace komai dan ALLAH, inhar
nid'in d'an uwankane da gaske, bakuma k'yamar had'a zuri'a kakeyi daniba ka amince da auren
Khadija tunda ALLAH bai haramta makaba, karkayi dubi da d'iyatace, kasancewarta a wajen
kane kawai zaisaka ruhina nutsuwa a cikin kabarina, inada tabbacin har Abadan bazaka ta6a
barinta tayi kukan rashina ni da mahaifiyarta ba, duk Wanda zaisan muhimmancin Khadija ko
kulawa da ita bayankane, dan ALLAH ka amince, danni lokuta k'alilanne suka rage a cikin
dak'ik'un rayuwata, brother nima mutuwa zanyi, insha ALLAHU tare zaku bunne gawata data
matata, bazan rayuba brother, Nika d'ai nasan minakeji, please ka amince dan girman ALLAH
da k'aunar dake a tsakaninmu._
Kowa a d'akin kuka yakeyi saboda tausayi.
Uncle M.A yana kuka yace, " indai hakan zai sakaka farinciki na AMINCE brother, na
amince da auren Khadija dukda ina kallonta a matsayin d'iyata, insha ALLAHU zaka tashi
brother, cuta ba mutuwa baceba..........
Kasa k'arasawa yayi saboda kuka daya sark'esa.
Baban Ama ya k'ara k'ank'ame hannun Uncle M.A yana fad'in "ngd da amincewarka brother,
kasani farinciki, zanbar duniya cikin shauk'in farincikin ganin auren Khadija da ALLAH yabani ita
d'aya tilo a duniya, ALLAH yasaka farinciki da kwanciyar hankali a rayuwarku, ALLAH ya hana
duk wani azzalumi tasiri akan wannan aure, ina rok'on alfarmar a d'aura yanzunan brother kafin
numfashina ya k'are.
Kai kawai Uncle M.A ke d'aga masa yana zubda kwallah
*****
Kawu yakubu da sauran mutane hud'u, sai doctor shu'aibu da abokan aikinsa doctors
kusan 10+, sai Jabeer dawasu mutane k'alilan masu jiyya suka shaida d'aurin auren *_Alhaji
Muhammad Ahmad labbo da Khadija Isma'il uba (Amatallah)_* akan sadaki naira dubu 30 da
kawu yakubu yabada, bayan Jabeer yayi saurin zuwa ATM ya fidda, kawu yakubu ne wakilin
ango, yayinda Baban Ama da kansa yay waliccin auren d'iyarsa tilo Khadija (Amatallah).
Ana gudanar da d'aurin aure cikin dariya da tsantsar farinciki, amma nasu Amatallah acikin
kuka da tsantsar k'unar rai aka d'aurashi, babantane kawai keyin kuka da murmushi lokaci
d'aya.
Cikin farin ciki ya k'ank'ame hannun Uncle M.A yana masa godiya, tareda k'ara jaddada
masa Amanar Amatallah.
Kuka kawai Uncle M.A keyi yana fad'in "brother bazaka mutuba, kabar fad'a domin ALLAH,
cuta ba mutuwa baceba brother....
Murmushi mai ciwo Baban Ama yayi, " brother sai dai hak'uri, mutuwa kam tazama tilas, ka
tabbatarma Khadija na yafe mata, ALLAH ya albarkaci rayuwarta, yasaka mata hak'uri da juriyar
danganar rashinmu, tayi hak'uri da k'addarar data shigowa rayuwarta, watarana sai labari,
badan ALLAH baya sonta bane ya d'aukemu, watak'il hakan shine mafi alkairi a rayuwarta,
ngdma ubangiji dayabamu damar rayuwa da ita na tsawon shekaru 18, har zuwa yau danaga
aurenta, ALLAH yayi mata al ....bar.... ka.......
Baban Ama ya k'arasa maganar a rarrabe, ahankali kuma yafara kalmar shahada.
Lamarin daya rikita Uncle M.A kenan ya rungume Baban Ama yana kuka mai ciwo da k'unar
zuciya......
Jin jikin Baban Ama ya saki yasaka Uncle M.A d'agowa yana girgizashi da kiran Isma'il!
Isma'il!!!! Please karka tafi kabarni dan ALLAH, brother karka tafi please.........
Yanda Uncle M.A ke kuka da sambatu sai da kowa ya koka awajen, da k'yar aka iya
janyeshi akan gawar Baban Ama, aka lullu6eshi da farin bedsheet d'in dake kan gadon.
ya ALLAH ka gafarta mana.
Mutuwa kenan 'yan uwa, bata kwankwasa k'ofar kowa, babu d'an sak'on isowarta, babu
alama ko yanayin alamomin kusantuwarta.
Saika gama shagala da duniyar kawai saikajita, babu shamaki tsakanin mutuwa da d'an
Adam, koka shirya, kobaka shiryaba saita d'auka, komai girman mulkinka ko dukiyarka ko
talauci, komin yawan mak'iyanka ko masoya saika tafi, karki manta, karka manta, karna manta,
, ni da kai da ke da su duk zata iya d'aukarmu yanzunnan, wlhy duk sai mun
mutu muma.
Suda suka tafi basuyi sauriba, muda muka rage bamuyi jinkiriba narantse
muku..............✍
*_Yau kam inason naga comments ruwa-ruwa akan auren Amatallah da Uncle M.A, a kowanne
groups, inba hakaba ALLAH bazan cigaba da typing ba sai sabuwar shekara idan ALLAH ya
kaimu. Yawan comments d'inku yawan kwarin gwiwwarku gareni, inhar banji k'yashin typing ba,
baikama kuji k'yashin comments dabai wuce layi biyu zuwa uku ba gaskiya. Idan kunason
naciga, nagani a k'asa♀. Dan yanzune labari zai fara_*
*_YA ALLAH ka gafartama banana._*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce_*
____________________
*_Number 11_*
____________________
Rayuwa tacigaba da tafiya musu a cikin nasarori, Isma'il yafara aiki anan jos, amma
Muhammad yacigaba da kasuwanci, babu ma maganar Neman aiki a tsarinsa.
Kwanaki sunyi saurin zama shekaru, harga Amatallah da shekaru bakwai a duniya, duk
hutun duniya kuma a kano takeyinsa, tattali da kulawa mai ban mamamki take samu daga
khadija da muhammad, bazaka ta6a cewa ba d'iyarsu baceba, tayi masifar sabo dasu sosai.
itama dai mamanta tundaga ita babu wani labari, haihuwar taimusu cak ta tsaya. kamar yanda
matar Muhammad itakuma sai a lokacinne ALLAH yabata ciki, fad'a muku murna da farincikin
dasukayima 6ata lomacine, amma kam lamarin ba'a magana kam.