Showing 87001 words to 90000 words out of 109227 words
Chapter 30 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
zabga hira tamkar ba kusan a tare suka yiniba, Amatallah Na rik'eda
muneerah wada tad'an fara woyo masha ALLAH.
Sund'an dad'e tsaye kafin su sami abin hawa, kasancewar yau juma'a anata hada-hadar
masallaci.
Bankwana sukayi dasu goodness kafin kowacce tashiga napep tanufi gidanta.
***********
Kusan atare suka iso da yara wad'anda aka d'akko daga makaranta, duk suka rungumeta
suna mata oyoyo, itama cikin farinciki ta rungumesun kafin ta tasasu gaba su shiga cikin gidan.
Babu kowa a falon, gidan shiru kamar babu mutane, watak'il matan gidan barci sukeyi
kowasu uziri acikin d'akunansu.
Yaran kowa yashige 6angaren Uwarsa, Amatallah ma jakka da takardun hannunta kawai ta
ajiye ta cire hijjab tashiga kichin Dan Neman abincin rana.
Tana tsaka da girki Fateema tashigo kitchen d'in, gaisheta Amatallah tayi kafin tace, "ina
mah-mah?".
" mah-mah tana barci aunty yara, ya makaranta?".
"Wlhy Alhmadllh".
Ruwa Fateema ta d'auka tafita, a bad'ini kuma bawai d'aukar ruwanne yakawotaba,
tazagayone taga mi Amatallah ke girkawane, Dan tasan yau maigidan zai dawo hannunta,
agida kuma zaiyi lunch saboda inya dawo sallar juma'a baya sake fita kuma. fita tayi tana d'an
ta6e baki, caraf kuma suka had'a ido da Aneesa da fitowarta kenan daga 6angarenta, itama da
alamar gulmarce ta fiddota, (hakan yazame musu tamkar al'adar gidan, ranar girkinki sauran
matan idonsu nakanki, kowa sotake taga yanda kikayi idan mijin yadawo nata tamasa
mafiyinsa).
Kauda ido Fateema tayi tashige 6angarenta batareda ta tankama Aneesar ba, itama saitaja
guntun tsaki tanemi kujera ta zauna a falon.
Amatallah kanta Fateema na fita tarakata da harara dafad'in magulmata anfara ma mutane
lek'en asirinne, aiko k'afafunku sagaji babu maiganin mizanyi saiyaje kula.
Hohoho matan Muhammad Ahmad Labbo! Kuna shagalinku wlhy♀♀.
Har Amatallah tagama girkinta babu wadda tasake lekota, hakan kuwa yamata dad'i, tana
tsaka da gyaran kitchen d'in tajiyo horn d'in boss, bata fitaba Dan tasan bama zai shigo da
motar cikiba tunda zai sake fitane.
Bata kuma jiyo horn d'in nasaba kuwa sai takun tahowarsa, ta ajiye moper d'in hannunta ta
d'auraye hannun dad'an goge fuskarta tagyara zaman d'ankwalinta sannan tafito, a falo suka
had'u harya shigo, har yanzu Aneesa Na zaune afalon. Ko kallo bata ishi Amatallah ba tanufi
mijinta suna sakarma juna murmushi. Ta kashe masa ido d'aya yayinda sukazo gab da juna, murmushin yakuma mata, tawani
kashe murya can k'asa yanda komin kusancinka dasu bazakaji mitaceba, tace, "barka da
dawowa my jaan!".
Kad'an ya rankwafo ya sumbaci la66anta, kafin yace, "yauwa my heartbeat!".
Harga ALLAH Uncle baiga Aneesa ba, Amma Amatallah tanakan Sani, itama hannunsa
takami ta sumbaci tsakkiyar tafin hannun.
Ya wani narke mata yana fad'in my best karki kaini k'asa a falonnan fa".
Jakar hannunsa ta kar6a tana wata shu'umar dariya, tai wani far da ido tajuya tana taku
d'ai-d'ai, bayanta yabi da kallo kafin yafara takawa shima.
Aneesa da zuciyarta keneman fitowa ta danne da k'yar tace sannu da zuwa dear?".
Da sauri yakalli sashen da akayi maganar, cikin d'an kame-kame yace, " my Nessa dama
kina falonnan?".
Wani murmushin takaici tayi tace, "a'a yanzu nazo". tana gama fad'a ta harari Amatallah
tabar wajen.
Amatallah ma Harar tata tayi batareda tabari Uncle yaganiba balle Aneesar, suna had'a ido
dashi kuma tasaki murmushi, " Uncle kafayima Anty Aneesa laifi".
Yad'an yamutse fuska yana kallon Ama...., "laifinmi my best?".
Step d'in tafara takawa tana murmushin mugunta dafad'in " saika shigo".
Binta yayi da kallo kawai, a zuciyarsa yace zaki kasheni da salonki khadeeja, ked'in
tadabance......
Fitowar yaran yasashi maida hankali garesu, harsunyi wanka anmusu shirin masallaci, duk
suka gaidashi ya amsa cikeda so da k'aunarsu. ''Yauwa my sweet children's ku zauna kar
Wanda ya6ata jikinsa naje nima nayi wanka karmu makara salla, ina Ummah?".
Sahib yace, ''Abbu tana wanka".
"OK, to nima bara naje nayi ko".
A tare sukace to " Abbu ".
Tunda yashigo falon mayataccen k'amshin turaren da Amatallah ke saka masa yabugi
hancinsa, shak'a yayi ya lumshe idanu kafin yak'arasa bedroom d'in. A toilet yajiyo motsinta,
dan haka yafara cire babbar rigarsa.
Yana ajiyewa tafito itama, k'arasowa tayi inda yake, kowanne idonsa akan d'an uwansa, yana
k'aunar yarinyarnan harma baisan iyakaba, sometimes idan tana Abu saita ringa d'ebe masa
kewar Brother d'insa...
K'ok'arin cire masa bottles d'in rigarsa datakeyine yasashi dawowa hankalinsa, tamkar wani
yaro haka ya koma mata, itace tamasa komai hatta da wankan da shirin masallacin cikin milk
color d'in shadda, ta fesheshi da turare, shidai kallonta kawai yakeyi, 'Yar k'arama da ita sai
wayon tsiya, abaya yana ganin kamar Amatallah zatana cutuwa agidan saboda k'ank'artatrta da
k'arancin wayo, amma a yanzu yakula koda za'a cuceta saidai tawani fannin amma bawajen
kulawa da mijiba, ta kowanne fage tagama kwarewa, har yana mamakin tamkar wadda ake
koyamawa, dukda har yanzu salonta Na nuna kunyarsa tana nan tanayin kayanta, (wadda
kunyar tata nakuma sakashi a shauk'in k'aunarta) dan idan 'yan kunyar nakanta takan masa
Abu tamkar ranar suka fara had'uwa amatsayin miji da mata, shikansa saiyanjin kamar ranar
aka kawo masa ita........
Yanata zancen zuci har tagama kimtsashi tsaf.
"Kayi k'yau my Uncle". tafad'a tana shafa fuskarsa.
Hannun yarik'e ya sumbata, kafin yajawota jikinsa ya rungume tana shak'ar dadd'an
k'amshinsa.
Cikin sassanyar muryarsa yace, " ALLAH yamiki albarka khadeeja, yajik'ansu brother kinji".
Tana murmushi ta jinjina masa kanta, kafin tad'ago tana kallon fuskarsa, "my lollipop bara
nabaka ko fura kad'ansha mana? banason kafita da yunwa".
Yanda ta narke masa haka shima ya narke mata, " no my heartbeat karmu makara fa, idan
nadawo naci abinci kawai....."
Bata bari ya k'arasaba ta tashi daga jikinsa tana tura baki gaba. Saurin rik'o hannunta yayi ya
maidota baya yana fad'in sorry my beat karki fushi, haba Amintacciya 'ya daga ALLAH, banito
nasha ko kad'anne".
Tad'an kalleshi tana turo baki gaba, a shagwa6e tace, "really?".
Gira ya d'aga mata kawai danya kasa magana.
hannunsa takamo suka fito galo, ta zaunar dashi a kujera sannan tad'iba furar a frighte d'insa
tasaka suga kad'an ta motsa, kusadashi tadawo, (hummm) mai makon ta zauna gefensa saita
zauna a cinyarsa tana kashe masa ido d'aya.
Wani lalataccen murmushi ya sakar mata, ya sak'alo hannunsa a k'ugunta, " my beat karfa
kimin Squeezing da kaya nida zanje masallaci".
Kofin furar tasaka masa abaki tana 'Yar dariya. amma batace komaiba.
Haka taita basa furar saida ya shanye bai saniba, ta ajiye kofin a Center table tana fad'in
Uncle kafa shanye tas".
Bakinta ya sumbata, "yazanyi tunda 'Yar shagwa6a ta turkeni".
" wato Uncle turkekama nayi ko? Shikenan munyima fad'a karka kumamin magana harka
dawo masallaci ehe.
Da sauri yakamota yana dariya, ya manne bakinsa kan nata. (Hummm dagananfa.....babu
ruwana).
Da k'yar tasamu ya saketa yafice yana kashe mata ido d'aya da d'aga mata yatsun
hannunsa biyu alamar bye bye.
Gira ta d'aga masa itama tamasa alamar I love you da hannunta.
Tsayawa yay cak yana kallonta, harya d'an juyo zai dawo takoma bedroom d'insa da gudu
tarufo k'ofar, tasan inhar ya kamata bakinta saiyaci k'aniyarsa, gashi time d'in masallaci nakuma
k'urewa.
Sauka yay yana murmushi, dakumajin k'aunar Amatallah dake Shiga jininsa da 6argo. har
yanzu yaran Na falo inda yabarsu, Shiga yay 6angaren Fateema suka gaisa, sannan yashiga
wajen Aneesa itama, dukda tanata shamasa k'amshi bai damuba danyasan laifinsa.
Yana masallaci amma dukkan tunaninsa naga Amatallah, burinsa kawai a idar Yakoma
gareta............✍
_Ama.... kina zamani, walla banga laifinkiba, murd'a kanbunki dak'yau karki saka
wasa♀♀._
One Luv my sweet fan's
*_ALLAH ka gafartama iyayenmj_*
[1/19, 10:20 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce_*
____________________
*_Number 35_*
____________________
Kafin su Uncle su dawo masallaci Amatallah tagama had'a abinci a falon k'asa data kuma
gyarawa ta kunna turaren wuta. wanka taje tayi, tsaf ta d'auki gayu cikin wata light popul d'in
atanfa da ratsin pink sai bak'i kad'an ajiki, yauma dai kwalliyar bawata mai yawa bace, amma
tayi d'as da ita, tasha d'aurinta mai k'yau, ga k'amshinta mai rikita Uncle dasu Aneesa yana
tashi ajikinta.
Zamanta tayi a falonta ta kira matan kawunta hafizu da kawu hamza Anty furera da anty
sadiya sukasha hira abinsu, saikuma ta kira Asiya, suna tsaka da hirane tajiyo horn!. tashi tayi
da sauri tana fad'in "ke 'yammata shugana yadawo sai munyi waya next time". bata saurari
dariyar da Asiya ke tuntsura mataba ta yanke wayar, d'aukar k'aramin gyalenta tayi tasaka
sannan tasaka takalminta flat kalar gyalen, saika rantse budurwace zata fita (lol).
Gate d'in tabud'e yashigo sannan tarufe, motar tasa tanufo cikin takunta Na nutsuwa da
sanyi, yara harsun fito, shikam yana zaune yana kallonta ta madubi yakasa ko kwakwkwaran
motsi saida ta bud'e masa k'ofar, murmushi suka sakarma juna, ahankali ta furta "welcome sir!".
kasa amsata yayi, saiwani mayen kallo dayake binta dashi, badan yaransaba da babu abinda
zai hanashi rungumeta a wajen, yakan rasa tantance watafi wata iya ado acikin matan nasa?
Dan kowa gwanace a dressing. ganin yana k'ok'arin fitowa tamatsa baya kad'an, wayoyinsa
yamik'o mata sannan yafito, yara suka kwashi ledojin fruits da chocolates d'in da aka siyo musu
sukai ciki.
Ganin yaran sun shige yakai hannu zai kamota ta zille tana dariya, shima dole yadara yana
fad'in " my best! rowar kanki kikemin? babu damuwa zan rama ai".
Dariyarta tacigaba dayi tai gaba abinta, shima sai yabi bayanta yana murmushi.
A faloma wasu taurarin yaci karo dasu, Dan tuni Fateema da Aneesa ma sunfito, kowacce
cikin kwalliyar d'aukar hankali da birgewa, atare suka masa sannu da zuwa, ya amsa cikeda
shauk'in ganinsu cikin ado, kowacce saida yakashe mata ido d'aya tareda mata alamar jinjina.
duk sukayi murmushi kowacce najin kanta on top da tunanin itace zinariyar gida. Kallonsu yayi yace, "bara nad'an rage kayannan ko?". yay maganar yana k'yaftama
Amatallah idon. Murmushi tayi dantasan miyake nufi.
Saida yafara hawa steps d'in sannan tabi bayansa, suna shiga falo ya rungumeta, Dan
yakasa hak'uri.
" humm Uncle kai d'innan ko! ALLAH bakada dama".
Yay guntuwar dariya da jawo hannunta suka zauna a kujera, tana saman cinyarsa "my best
minayi kuma?".
" humm babu komai, ai abin bana fad'a baneba. mika rok'omin a masallacin?".
Kansa yad'aga sama alamar tunani, saiya kaleta yana k'ayataccen murmushi, "k'anwa na
rok'o miki, naga gidannan kowa yanada k'anwa bandake, sainaga ba girmanki bane hakan,
gara nayo amarya ta hud'u kema kisami 'Yar k'anwa ko? dama wata yarinya tanata bina a
bayar...". 6ata fuska tayi kafinma ya k'arasa, ta yunk'ura zata tashi daga jikinsa..
Rik'eta yayi da sauri yana dariya, " ooh my best! Inakuma zakije? aiban gama fad'aba, Dan
harda twins Na rok'o mana masu kama da brother".
Murmushin takaici ta sakar masa, cikin dakewa tace, "Su Aunty's fa suna jiranmu da yara".
Kuma fashewa yayi da dariya tareda k'ank'ameta ajikinsa yana fad'in oh god, my best!
Kishinki mai ajinefa, kina burgeni over wlhy".
Mintsininsa tayi a hannu tana fad'in "waya gaya maka kishi nakeyi?".
ya saketa da sauri yana fad'in "Uchh!, my best wannan muguntarfa?".
Yanda yayi da fusaka saiya saka Amatallah fashewa da dariya tana mik'ewa a jikinsa tace,
" saika taho ".
Yana kiranta amma ko waiwayensa batayiba tafice abinta.
Kansa ya jingina da kujera yana murmushi, da shafa Inda ta mintsinesan, dan yaji zafifa,
ahankali ya furta "oh my Khadee ked'in Special ce acikin mata".
Can kuma Amatallah data fita dariya takusa kasheta, ganin idon Fateema da Aneesa duk
yana hanyar saman, murmushi tayi ta k'arasa cikin falon, " Sorry my Aunty's mun shanyaku,
wlhy Uncle".
Fateema dai murmushi takaici tayi, Aneesa kuwa saitaja siririn tsaki tana kauda kanta gefe.
Murmushi Amatallah ta kuma yi tafara had'a abincin a babban fleet, Dan yau tare takeson
suci abinci su duka har yaran.
Daga Aneesa har Fateema kallon mamaki suke mata, mizatayi da wannan abincin?.....
Shikansa Uncle dake sakkowa kallonta yakeyi, ya canja kayansa zuwa dogon wando Na
jeans da blue d'in T-shirt.
Yana gama sakkowa tana gama zubawa, ta sakama kiwa cokali sannan ta kallesu, ''to
bismillanku, Sahib, Saifudden Abulkhairi kutaho ina Ummita?".
"Anty taje fitsari". Cewar Saifudden.
Abulkhairi yace, " lah Anty, yau harda Abbu dasu momy zamuci abinci?".
Kanta tad'aga masa tana murmushi.
"Yau kuma tare family zamuci abinci kenan?". Uncle yay maganar yana zama.
Amatallah tad'aga kanta alamar eh, kafin tace " wai musami albarkacin juna Uncle, suma
yara suyi farinciki sunci abinci da iyayensu, kumama cin abincin tare yana k'ara dank'on k'aunar
juna da zuminci mai k'arfi".
"Gaskiyane my best! ALLAH yayi miki albarka".
" Amin Uncle".
Fateema da Aneesa dai sai sukaji gingirin, Dan sudai basu ta6a wannan tunaninba. duk suka
danne kishinsu suka nuna goyen bayansu akan abinda Amatallah d'in tayi.
Uncle yaji dad'in goyon bayan Nasu kuwa, shima duk yasaka musu albarka. yanajin dad'in
idan wata acikinsu takawo shawara mai k'yau kowani Abu yaga sun taru sun bata had'inkai,
bawai kishi yasasu gwaletaba.
Abin sha'awa da birgewa sukaci abinci tareda 'ya'yansu a nuse kamar yanda suka horar
dasu, family ya had'u abin zaakk'yau.
Bayan sun kammala Amatallah ta gyara wajen, daga nankuma sukayi zaman hira, yaran
sunata wasansu sukuma suna hira su hud'u. dolene kagansu su burgeka, gasu cikin kwalliya,
kuma kowa a nutse take hirar babu hantarar juna ko habaici wa juna irinnan kishiyoyi, dukda
kuma kowacce kishin nacinta a zuciya, amma duk suka danne suke hira cikin son faranta ran
mijinsu, shima kuwa cikin kulawa da soyayya yake amsawa kowaccensu, babu nuna wata tafi
wata, nunawa yake duk matsayinsu d'ayane a zuciyarsa.
*_(Wlhy Ma'aurata munada matuk'ar gyararraki a gidajen aurenmu, wani fannin saikaga laifin
maigidane wajen tarwatsewar zaman lafiyar gidansa, saboda rashin adalci namiji agaban
abokiyar zamanki saiya dizgaki da nuna tafiki matsayi a gunsa, hakan ba daidai baneba, inhar
maza zasu gyara zaman takewar gidajensu suyi adalci wlhy sai ansami raguwar zafin kishi Na
mata, Dan wani abun mazanne ke haddasashi ga zamantakewar matan, zakiga wata
Uwargidan tanada sauk'in kai, to amma mijin yagama 6atata ga amaryar tunkan ta shigo gidan
saboda son zuciyarsa, kunga koda ta shigo bazataga darajar uwargidanba, to mijin yanuna
uwargidan tagazane shiyyasa ita yakawota, kokuma ita amaryar yadinga munafuncinta ga
uwargidan Dan kawai yanason uwargidansa Dason faranta mata, saiya fara gulmar iyayen
amarya akan kayan d'akin ko gararta ko kud'in daya kashe a aurenta kokuma yace iyayenta
suka manna masa ita Dan anga yanada hali Kodai yayta 6ata amaryar itama ta hanyoyi
dadama, koya zama MUNAFUKIN MATA a tsakaninsu hakan ba daidaibane, wlhy maza kusani
akwai hisabi, kuma duk Wanda ya gagara adalci a tsakanin matansa aranr lahira zai tashi 6arin
jikinsa shanyayye, kuma babu makawa sai an antayashi a wutar jahannama, idan kuma bak'in
cikinka yasaka mace bin malamai da bokaye wlhy kaima Kanna da wani tsagi Na zunubi aciki,
bawai inabin bayan mata su aikata bane, amma mafi yawan mata sukanbi