Showing 6001 words to 9000 words out of 109227 words
Chapter 3 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
Ringing da wayarsa tafara. batareda ya d'aukaba ya kai
dubansa kan screen d'in wayar.
My wife tee..
Yagani 6aro-6aro yana yawo a fuskar wayar, ya d'an furzo iska kad'an daga bakinsa. d'aukar
wayar yayi yana k'ok'arin kiranta sai kuma takuma kira.
Koda ya d'aga saiya saka Hans free, muryarsa mai matuk'ar sanyi da nutsuwa yace, "
Assalamu allaiki Ummu Abul-khair".
"Wa'alaikassalam Nurrina, lafiya kuwa har yanzu baka shigoba? ko ka manta kana azumi ne?".
Murmushin sa ya saki mai k'ayatarwa, ya kai hannu yana shafa gemunsa daya k'awatu da
bak'in gashi dakuma fari d'ai-d'ai (furfura). "Ban manta ba My tee.., wlhy go slow ne ya rik'eni,
gashi har an shiga sallah".
Ya karashe maganar cikin 6acin rai.
A san yaye tace, " sorry Nurri, ALLAH ya kawoka lafiya to".
"Amin nagode, su Abul-khair fa? Kundai turasu masallaci ko?".
" eh sun tafi shida Sahib".
"Saifuddin fa?".
" bayajin dad'i,
koma islamiyya bai jeba".
"Amma shine bata fad'a min ba?".
Har zata bashi amsa saiya katseta, " kinga ina zuwa, naga motocin sun ragu". 'Bai jira
cewartaba ya yanke wayar'. Motar yay ma key yay gaba, saboda hanya data bud'e, dama dai
wani abunne ya haddasa go slow d'in.
Cikin mintunan dabasufi 30 ba ya k'araso gida, a k'ofar gida yay parking, yafito yay alwala a
nan massalacin k'ofar gidansa, hankalinsa duk yana kan sallar magriba data wucesa, a
gaggauce ya gaisa da mutanene dake k'ofar massalacin zaune suna jiran kiran sallar isha'i, ya
shige yay sallar magriba, ya idar babu dad'ewa akayi isha'i. Bayan an idar ya tsaya gaisuwa da jama'a makwafta sannan yakoma mota, horn yayi sau
biyu.
Kusan mintuna 5, aka bud'e gate d'in. bayan ya shige ta maida gate d'in ta rufe. Sannan ta
k'araso wajen motar tasa.
Yana zaune har yanzu a ciki, wayoyinsa yake k'ok'arin sakawa a aljihu, ta bud'e motar tana
fad'in ''sannu da zuwa".
"Yauwa Uwargida na, ya gidan?".
"Lafiya lau yake". K'o k'arin fitowar dayake yasata matsawa baya, ya fito idonsa akanta,
kwalliyar tata tamasa k'yau, haka kullum matan nasa suke cikin kwalliya, kowa burinta tazama
gwana awajensa.
Murmushi yamata yana kashe ido d'aya, cikin sassanyar muryarsa yace, " kinyi k'yau my
tee...".
Itama murmushin tamasa, kafin tace, "thanks you Nurrina".
Kansa ya jinjina mata, "da akwai kaya a backseat ki d'ebo su".
"Okey".
Yara ukune suka fito da gudunsu suna fad'in "oyoyo abbunmu!!".
Murmushi yasaki, har fararen hakwaransa Na bayyana, idonsa akan yaran nasa, ya bud'e
masu hannayen sa, hakanne yabama babbar rigarsa ta blue black d'in shadda bud'ewa. gaba
d'ayansu suka shige ciki, ya had'asu ya rungume shima yana fad'in " oyoyo my children's, I Miss
you all". Matarsa data gama kwaso ledojin dake kujerar baya tatsaya tana kallonsu fuskarta d'auke
da murmushi.
Tace, "oya to a sakeshi ko yagaji, kumuje ciki".
Sakinsa sukayi su duka, yakama hannun Sahib da Ummita, Abul-khair mai d'an wayon ya
kar6i wasu daga cikin ledojin hannun mamansa, suka nufi hanyar k'ofar babban falon gidan.
Sahib da Ummita kam sai zabga masa labarin school sukeyi, murmushi kawai yakeyi.
Da sallama suka shigo falon, nanma wata matar nagani tsaye a falon, hannunta rik'eda
yarinya dake kunshe cikin kayan sanyi.
Wannan ya tabbatar min cewa matansa biyu.
Fuskarta d'auke da murmushi ta k'araso inda suke tana masa sannu da zuwa.
Amsawa yayi shima yana murmushin da k'arema amaryar tasa kallo cikin jin dad'i, dan itama
cikin kwalliyar take mai d'aukar hankali. (A raina nace, ''wannan ai sai a gaza gane mai
girki").
Hannu ya mik'a mata alamun tabasa babyn hannunta.
Ta saka masa babyn dabazata wuce 3month ba a hannun nasa.
"O, my Siddiqa barci kikeyi?". Yay maganar a hankali yana sumbatar goshin yarinyar.
Sannan ya mik'a mata ita, " bara naje Na d'an watsa ruwa Neesa!".
Cikin salon kissa tace, "okey Dear".
Harya fara tafiya saiya tsaya, ya juyo yana kallonta, " Saifudden fa?".
"Jimm tayi alamar tsoro, ta kauda idonta daga kansa tace, " yana barci".
"Barci? A wannan time d'in? Halan lafiya?".
Yanzunma a cikin jimamin tace, " bashida lafiya".
"Shine kika kasa kirana ki sanar min?". bai jira amsarta ba yafara hawa matattakalar benen
dake tsakkiyar falon, dama tuni yaran mamansu tajasu sunyi 6angaren ta.
Kamar zata fasa kuka tabishi da kallo, tasan haushi yaji, Dan mijin nasu bai had'a matsalar
'ya'yansa data kowaba, yanason yaransa sosai, kodan yadad'e bai samu haihuwarba ne? Oho.
Jiki a sanyaye tashige nata 6angaren itama.
Tun daga falon k'amshi mai dad'i yabugi hancinsa, ya shak'a ya lumshe idanunsa, babbar
rigarsa yafara k'ok'arin cirewa, ta k'araso da sauri ta taimaka masa suka cire tare.
Cikin kashe murya tace, " da kanka Nurrina? ".
Murmushi kawai yay yana shigewa bedroom d'insa. da sauri ta d'auki babbar rigar tabi
bayansa domin taimaka masa yayi wanka...............✍
*_ya rabbi ka gafartama mahaifanmu _*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce_*
____________________
*_Number 6_*
____________________
Baban Ama.. ne ya kalli uncle M.A dake zaune gefenshi bayan sun kalla cin abinci,
hankalinsa ya maida gaba d'aya agareshi. "Brother ina saurarenka".
Uncle M.A ya d'an gyara zamansa, kafin yay gyaran murya kad'an.
"hugm!, brother kasan mi nake tunani kuwa? Akwai wani Abu kusan 1year data shige daya
d'aga hankalina, dawo da maganar bashida wata ma'ana, amma yanda rikicin ya kasancene
yata6a zuciyata. matasan k'asarnan sunada buk'atar mai jagorancin tunaninsu, saboda duk
wani Abu da zaije yadawo akansu yake k'arewa, dasu ake amfanin wajen haddasa duk wani
rikicin SIYASA KO K'ABILANCI da ADDINI a k'asar nan, sannan kuma sune akafi kashewa, su
akafi lalatama rayuwa. (kuma kullum sune cikin k'orafin gwamnati batayi dasu). Al'halin sune
suka maida darajarsu can k'asa har kowacce gwamnati idan tazo take tunin k'ask'antar dasu, ni
aganina matasanmu sunada hanya mafi sauk'i dazasu jagoranci k'asarnan brother, amma bata
hanyar rikicin siyasa ko k'abilanci ko 6angaranci ko fad'an addiniba.......".
"Hakane brother, amma tayaya kai kake ganin zasu fahimci manufarmu, kafa tuna cewa
matasan namu, ba kowan nensu ke maida hankali akan karatu ba, idanma sunyi sai domin aiki,
ta wacce hanya kake ganin yakamata su fahimci sune k'asar?".
Murmushi uncle M.A yayi, "yauwa brother anzo wajen, wannan tambayar nakeso kamin
dama".
" bara kaji brother, tunfa farko mu SIYASA bata kar6i Africa ba gaba d'aya, wlhy sanadin
SIYASA komai namu ya LALACE, da bamusan k'abilanciba, saboda kowa yana a 6angarensa,
idan kaga d'an wancan k'abila cikin waccan to harkar kasuwancice ta kaisa. amma tundaga
lokacin da Turawa sukace ga SIYASA komai namu ya canja salonsa, tundaga lokacinda
turawan mulkin mallaka suka bama wasu 'yan k'asarnan shugabancin wasu yankunan kasarnan
komai yafara dagulewa, domin hakanne yazama ummul aba'isin haifar mana da rikice-rikicen
ADDINI DA K'ABILANCI a sassa daban-daban na k'asar nan, sannan sukazo suka kuma
fasaltamu a yankuna kashi uku, yankin HAUSA FULANI, YORUBA, IGBO, wannanma ya taka
rawar gani wajen raba kawunanmu. wannan suna d'aya daga tushen matsalolinmu a NIGERIA,
Dan sune suke jagorancin duk wani rikicin siyasa ko K'abilanci har yanzun a k'asarmu wlhy,
wad'anda suka fara suntafi sunbar baya da k'ura, har kuma yanzun mun rasa samun
nagartattun dazasu kawoma k'asar gyara, saima komai dayake k'ara ta6ar6arewa da lalacewa a
kullum, daga talakawan har masu mulkin kowa yana buk'atar gyara Kansa da ahalinsa ma
farko, to amma baikamata mu maidasu hujjar farko dazata hallakamuba ai. Abubuwa dayawa
sun faru a k'asar nan, Wanda maimatasu bashida wani amfani, dan kamar k'ara dagula
komaine, a yanzu hanyar gyara kawai yakamata mu fuskanta, shine zai zama NEXT LEVEL
namu."
Sai baba, ammafa inji bilyn Abdul.
Dariya sukayi suduka, wadda nikaina bansan dalilin taba.
Baban Ama yace, "to minene shirinka a next level brother?".
" kafa *KUNGIYAR MATASA* domin nusar dasu illar rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI,
FA'DAN 6ANGARANCI KO ADDINI*, yakamata mu fiddo hanya ta wayarma matasanmu kai
dansu san k'alubalen dake tare dasu, sannan suma sufito adama dasu a k'asarsu, kamar yanda
sauran k'ashen duniya keyi, duba tsarin CHINA, abin birgewa, mafi yawa matasan sune akan
madafun iko, akwai k'asashe daban-daban dasuke cikin wannan tsarin, Amma mufa Africa son
mulki yahana mu bama matasan dama, sukuma matasanma idan zakayi dubi tawani 6angaren
saika gane basu cancanci madafun ikonba, saboda rashin nutsuwarsu da sanin muhimmancin
Kansu. to amatsayinmu Na matasa tayaya zamu kawo CANGI a wannan tafiyar? yanda za'a
fuskanci mumafa 'yan k'asane NAGARTATTATU kuma ababen ALFAHARIN al'ummar k'asarmu
da yankunanmu, kaga dolene saimun sami had'inkan matasanmu Na KUDANCI DA AREWACI
kenan". sai dai inda gizo ke sak'ar tayaya zamu samu hakan ta kasance?, matasan su
fahimcemu sukuma k'aunaci Kansu, dan maganar gaskiya SIYASA DA K'ABILANCI tuni sun
rarraba kanmu a k'asarnan dama Africa baki d'aya".
Baban Ama yasaki ajiyar zuciya kafin yace, "hanya d'ayace brother nake gani".
" wace hanyace brother? ". cewar uncle M.A.
" masu taimakonmu brother, bawai 'yan yima dukiyar k'asa babakere da handamaba, nidai
nabaka goyon baya 100%, saimu fara Neman wad'anda tafiyarmu zatai dai-dai da tsarinsu,
kamar mutum 8 ni da kai cikon Na goma, daganan komaima saiya biyo baya".
Uncle M.A yarasama mizaiyi saboda Nuna jin dad'in goyon bayan abokin nasa, sai kawai
ya rungumeshi yana jero adu'oin fatan alkairi agaresa, shima Baban Ama addu'ar yake masa.
Acewarsa shiyadace da wannan addu'ar, tunda shiya k'irk'iro cigaban, Wanda duk da yasan
zasu fuskanci k'alubale iri-iri, saboda aikine bamai sauk'iba, musamman idan akayi dubi da
yanda k'asar tagama lalacewa ta 6angarori daban-daban Na Siyasa da k'abilanci da Addini,
dukda yana hango nasara wataran insha ALLAH.
haka sukaita tattauna batun, har aka kira sallar magriba, alwala sukayi suka fita massalaci.
_______________________________
"Wai oga wuk'armi kaketa faman wasawane haka kuma tun d'azun?".
Jajayen idanunsa yad'ago yana kallonsa, yasa bayan hannunsa ya shafi gefen hancinsa,
fuskarsa ata6e tamkar yaga mala'ikin mutuwa akansa, d'auke idonsa yayi yamaida kan
madai-daiciyar wuk'arsa maikamada *fad'ama jini nawuce* saboda tsabar d'aukar ido datakeyi
Na kaifi, amma dukda haka kaifin baimasaba yake sake wasata. K show bai daddaraba yakuma maimaita tambayar ga Zike.
Wani banzan kallo yamasa, sannan ya tofar da yawu, da yare yace, "aikin daka 6ata zaka
koma ka gyara, inba hakaba hummm....". Yay shiru batareda ya k'arasaba.
K show ya hura hanci gaba, amma baice komaiba.
Su manu duk suna tsaye ake wannan dramar, amma basuji mi zike yafad'ama k show ba,
saboda da yare yay maganar, k show da zike kuma yarensu d'ayane.
Ramzaki dake zaune gefe yana busa taba yajuyo yana kallonsu, cikin harshen turanci yace,
Oga sir dangin waccan babynfa? Inason abani kwangilarsu, dama nadad'e inajin haushin old
man d'inta, dan nata6a zuwa k'ofar gidan wajen babynnan amma ya koreni, wai shi ba
mahaukaci bane dazai had'a jini dani, kasanfa hausawannan akwai shegen k'abilanci da nuna
addininsu yafi Na kowa......
Da Sauri manu ya tsaidashi, " kai! Kai Ramzaki, please kama kankafa, karda tabarka
tagayamaka hauka ka rainamin yare, kai k'abilar taka basama mutane k'abilanci ne? 'yan kad'an
daku sai shegen gadara, wama yasan da k'abilar takune? Iyakarta jos fa, wlhy yanzu zamu
kwashi 'yan kallo a wajenan........ Shima katseshin yayi, tareda mik'ewa da sauri yaje yadaki kafad'ar manu, "to kozaka
gwadane?". Yay maganar yana hankad'a manu baya.
Shima manu duka ya kai masa.
Kafin kace me fad'a ya hark'ume, da k'yar sauran matasan suka rabasu.
Zike Na zaune yana jinsu, ko kallo basu isheshiba, wuk'arsa yake wasawa har yanzun.
K'ala baice dasuba kuma yamik'e ya tura wuk'ar gefen cikinsa, ya gyara rigarsa yay gaba
abinsa yabarsu.
Da sauri wasunsu suka bi bayansa, akabar manu da ramzaki a wajen, harar juna sukayi kafin
subi bayansu sunajan tsaki was juna, kowanne na zage-zage da yarensa.
(Nidai bilyn ku nace, " ALLAH ya k'yauta to".)
♀da sauri nabi bayansu Dan ganema idona ina zasuje kuma?.
______________________________
Zaune take akan abin salla, tunda ta idar da sallar isha'i bata tashiba, Ammi Na zaune
akan d'aya daga kujerun plastic namasu jiyyasa. tunkan su shigo k'amshin turarensa yayo gaba.
K'irjintane yafara bugawa da sauri-sauri kamar yanda yakeyi koyaushe, hannu tasa ta dafe
tana mamakin wannan lamari, aranta tace, miye ma'anar hakan ni Khadija?.....
Sassanyar muryarsace ta tadaki kunnenta. Ammi ta amsa sallamarsa tana mik'ewa, tareda
musu sannu da zuwa.
Shikad'ai ya amsa, Dan Baban Ama waya yakeyi.
Ta gefen ido Amatallah ta ke satar kallonsa, ya canja kaya zuwa fara tas d'in jallabiya mai
dogon hannu, sai bak'in wando daya lek'o kad'an da silifas d'in babanta a k'afarsa.
Kujerar da Ammi ta tashi ta tura masa, ya ajiye ledojin hannunsa kafin ya zauna yana fad'in
"sorry madam mun barku Ku kad'ai ko?".
" lah babu komai wlhy, kaida kasha hanya ma, kamata yay kayi kwanciyarka ka huta basai
kadawoba".
Kafin yabata amsa Baban Ama yagama wayar. matsowa yayi inda suke yana dariya, kibari
kawai, babu yanda banyi dashiba ya zauna yak'i, wai saiyaga mamana". Yay maganar yana
kallon direction d'in da Amatallah ke zaune.
duk tana jinsu, saita k'irk'iri addu'ar k'arya, bayan kuma tadad'e da idar da salla. shafawa tayi
sannan tataso, kanta a k'asa ta rissina tana gaishesu.
Atare suka amsa da tambayarta ya k'arfin jiki?.
tace, "Alhmdllh".
Uncle M.A yace, ''My best daughter kinci abinci kuwa?".
Da sauri ta d'aga masa kai alamar eh taci.
Hararta Ammi tayi, " k'arya dai babu k'yau Amatallah, yaushe kikaci abincin?".
Kanta tad'ago ta kalli Ammi, idonta taf da kwalla tace, "kai Ammi".
" kai Ammin uwar mi?, tashimin anan kafin na bigeki ak'ara miki kwanaki a asibitinnan".
Da sauri Amatallah ta haye gadon datake jiyya.
Uncle M.A yace, "madam inafa jin kunyarki, naga kin tasomin d'iya a gaba".
" haka kullum takeyi wlhy brother, nafad'a mata rashin cin abinci halittane, harma ina mata
misali dakai, amma bata d'agama mamana k'afa ko kad'an.
Uncle M.A ya kalli Ammi yana murmushi, sorry madam, rashin cin abinci halittace, haka
kusan koda yaushe innani kemin, sai dai in baba Na kusa ya kareni ko Maijidda, yanzu haka
matsalar kenan nidasu Fateema, kowacce da irin tunaninta, nifa har asibiti innani takaini ina
yaro ban mantawa wlhy, wai likita ya dubani banacin abinci, kowani ciwone dani?. Dariya sukayi gaba d'aya, harda Amatallah datayi murmushi tana satar kallon uncle M.A d'in.
sun d'an ta6a hira, harya kira Fateema da Aneesa suka gaisa da Amatallah da Amminta,
amma kowacce badan ranta yasoba, musamman Aneesa dakejin zafin Amatallah sosai, (koda
yake halintane, tanada zafin kishi, akan Alhaji Muhammad d'in, saboda auren soyayya
sukayi). Sai wajen tara suka tafi da k'yar, akabar Ammi da Amatallah.
dukda baba Ama Na fargabar barinsu su kad'ai, saboda halin da Amatallah ke kwana
aciki, gefe kuma yanajin kunyar barin abokinsa ya kwana shika d'ai, haka dai suka tafi yana
addu'ar ALLAH