Showing 12001 words to 15000 words out of 109227 words

Chapter 5 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

tun kafin su shigo k'amshin turarensa yayo gaba, Amatallah ta shak'a tareda kuma matse
idanunta, still zuciyarta nacigaba da bugawa da sauri-sauri. Addu'a tafara karantowa, dan
batasan dalilin wannan gudun da zuciyarta keyiba?, kuma tun ganinta Na farko da *_Uncle
M.A_* a wancan zuwan hakance tafaru, harya tafi wancan time d'in idan suna waje d'aya koya
shigo sai heartbeat d'inta taringayi kamar zata fito, kuma itakam a shekarun baya tana yarinya
batajin hakan akansa, komiyasa yanzu kuma?...........

Sansanyar muryarsa ce ta katse tunaninta. bayan sun gama gaisawa da Ammi yamatso gaban
gadon saitin face d'inta.
Yace, "My best daughter! barci kikeyine?".
Ya sallam!, tafad'a a zuciyarta. batasan ya zata musalta yanda cool voice d'in uncle M.A ke
razana zuciyarta da dukkan magudanar jininta ba, jitake kaf duniya yafi kowa dad'in murya.
Babantane ya ta6a k'afarta tareda d'an bubbugawa.
Ta bud'e ido ahankali tamkar mai barcin gaskiya, da uncle M.A tafara tozali, yana tsaye
agaban gadon kusada fuskarta, sanye yeke cikin Cyan color d'in tattausan boyal, Wanda yasha
d'inkin babbar riga, ya kafa hular zanna bukar black akansa da ratsin cyan kad'an, sai bak'in
agogo da bak'in takalmi heir cover. Waro ido tayi cikin acting like tana mamaki ganinsa. Tattausan murmushi ya sakar mata.
Ta yunk'ura a hankali tatashi zaune tana "lah Uncle yaushe kazo".
Still murmushin yakuma yi, kafin yace, " my best daughter yanzunnan nazo kina barci, ya
jikin naki?".
"Da sauk'i uncle, ya hanya? Yasu Saifudden da jikin baba?".
"Everything Alhmdllh my best D..., amma gaskiyafa kin rame sosai, anya kinacin abinci my
best?".
K'asa tayi da kanta tana murmushi, saikuma tad'an jinjina kai, tamkar wata k'adan garuwa.

Tana fad'in ''inaci uncle, katanbayi baba da Ammi ma".
Murmushi yayi, sannan ya maida kansa ga babanta, " brother wai miya faru da my Daughter
hakane?".
"Humm ai Brother inaga muje gida, sai muyi maganar a can, dan yinta anana zai iya zama
danger gaskiya".
"okey, amma anbata sallamane?".
"No basu sallamemuba, inga dai k'ilan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan kaganta
yanzudai normal, sai dare yayi jikin ya rikice, taita firgita, kullum akanta muke kwana babu barci
wlhy".
" ya salam, abin yayi tsamari haka Dama?".
"Brother Amatallah dama haka take da rik'e Abu, shiyyasa kullum nake cikin fargabar irin
mijin da ALLAH zai iya had'ata dashi, ba kowane zai iya d'aukar wannan rayuwan tataba
gaskiya, so ina tausaya mata".
" karkace haka brother, muyi mata addu'a kawai, insha ALLAHU ALLAH zai bata miji
nagari ma".
"To ALLAH yasa brother".
dahaka suka k'arasa motar sa.
Har sun shiga motar Baban Ama... Ya hango Ammi Na tahowa da sauri.
Kallon Uncle M.A yayi dake k'ok'arin jan motar yace, ''d'an dakata ga Ammin tanan, inaga
munyi mantuwar keys d'in gid......
Bai k'arasaba Ammi tak'araso, keys d'in tamik'a masa kuwa tana fad'in "kun manta keys d'in
ai. abinci nannan a seatroom Na shirya".
Murmushi Baban Ama... Yayi yana fad'in " jazakallahu khairan uwargidana".
Hararan wasa tamasa tace, "kuma amarya ba".
Duk su biyun dariya sukayi shida uncle M.A, Baban Ama... Yace, " ai nima aure zan k'ara,
bakiga brother ma 2 Star ne ba? kilama yana shirin zama 3 ban saniba, gara nadage nayi nima
Amatallah tasamu abokan shawara itama".
Juyawa Ammi tayi tana fad'in " wace zata auri tsoho?".
Dariya suka kumayi, sai da suka fita daga asibitin Uncle M.A yace, "brother mata basa
girma akan kishi, wani lokacin har mamakinsu nake, komin k'ank'antar Abu sai yazama Na kishi
a wajensu fa".
Baban Ama... Yace, ''ai kishi a jinin mata yake brother, babu mai iya rabasu dashi sai dai
ALLAH kawai, kana daiji mi Saliha kefad'a yanzun, wai wazata auri tsoho? alhalin zan iyama
d'aukar budurwa sa'ar Amatallah". Yak'are maganar da dariya.
Uncle M.A ma dariyar yakeyi, " kai brother, yanzu in ance ga budurwa sa'ar my daughter
saika aura kuma?".
"Ah da guduma kuwa, kana ganin tamin kad'anne?".
" hhh kamata yawa dai brother, mumafa balaifi munja kwana a duniyarnan, kusan 47years
fa".
"Ai brother rayuwa nabani tsoro wlhy, ALLAH dai ya gafarta mana, yau kake gobe sai
labarinka, yanzu nan su kawu da mamana Khadija harsunyi 12years da rasuwafa kenan?".
" ajiyar zuciya uncle M.A ya sauke, yad'an shafa fuskarsa yayinda k'asan zuciyarsa yay
rauni saboda Baban Ama... yata6o masa wani sashen rayuwarsa, cikin sanyin muryarsa yace,

"hakane brother sunkai".
Yanda baba yaji muryar uncle M.A ta canja saiya canja hirar shima, ya d'akko hirar abinda
yay sanadin kwanciyar Amatallah a asibiti.
Ahaka suka k'arasa gida, mamaki dukya cika Uncle M.A, cikin damuwa yace, " brother
gaskiya ina wata shawara da zuciyata tun kusan 1year data wuce, akan wani rikici dayafaru,
danake kallo a labarai sainaga duk matasane a wajen, sannan duksu akafi kashewa, hakan
yatada hankalina wlhy, tun lokacin nake juya maganar araina, amma narasa dawa zan
tattaunata, kasancewar nasan akwai fuskantar k'alubalen masu dafamin mu tallafi tafiyar.
Murmushi baban Ama... Yayi, kafin su zauna a kujerun seatroom d'in, uncle M.A yacire
babbar rigarsa shima ya zauna, ruwanda Baban Ama...yazuba a cup yamik'o masa, kar6a yay
yasha.
"Brother mikake rik'e a zuciya har kusan 1year? In dai ka yarda dani kafad'amin, insha
ALLAH ina tare dakai 100%".
"Haba brother mikake tunani? ai duk duniya inka cire baba da innani babu Wanda yasanni
sama dakai, kama fisu sanin wasu abubuwan akaina, dansu bakomai zan iya yi agabansuba
kona fad'a musu, kaikam a sirrin rayuwata miye baka saniba brother?".
" tom naji, nayi kuskure, amin afuwa, yanzu fad'amin mike ranka to? Insha ALLAH ina tare
dakai".
"Alhmdllh brother".......
Katseshi Baban Ama... yayi, bayan yagama zuba musu abincin, yace, "mufara cika
tunbinmu, sai maganar tafi shiga to".
Dariya suka tuntsure dashi suduka, sannan Uncle M.A ya sakko.


______________________________

" Oga akwai fa matsala gaskiya".
Wani yaron zike ne ke magana cikin muryar maye.
Zike dake zaune kan dakalin sokawe Na toilet d'in primary school yana busa taba yad'ago
jajayen idanunsa yana kallonsa, "matsalar mi manu!?".
" oga! Gagis fa bai wullaba wlhy, ance yana general hospital kwance, kaima kasan yana
mik'ewa yak'ine kawai zai tashi, ALLAH wlhy".
Wata 'yar zabura zike yayi, yacire tabar dayake busawa daga bakinsa, kallon sauran
yaransa yayi daduk suke a cake, wasuma kwance suke a k'asa, wasu kuma suna busa wiwi,
wasu kuma rik'e suke da roban faro suna shan wani far in abu, ya maida kallonsa kan manu,
''kai waye yafad'a maka?". "Oga ba d'azun ka aikeni gidan Oga Pam ba? natarar wannan shegen d'an koran nasa
zasuje wai dubashi a asibiti, harda mai k'aton kannan da ido gulu-gulu kamar Na kasa jan goro
a faranti".
Dariya duk suka bushe da ita, amma banda zike da hankalinsa ke a tashe, yasan wanene
gagis sarai, tashinsa kuma bazai zama sauk'iba a garesu su dukansu, kallonsu yayi, duk suka
tsaya da dariyar dasukeyi.
Yace, ''kai guys, dolenefa yau d'innan lahira tayi bak'on bawa, am telling you idan gagis

yatashi sai kowa yabar jos, kuma kunsani".
Manu yamik'e yana tangad'i, " Oga shiyyasa nafad'a maka ai, yanzu hakafa yaransa
nemanmu sukeyi, danma Oga Pam yayi gargad'in kar Wanda yayi wani abune, ammafa
dayanzu anfara Caskale a garinnan, ALLAH wlhy". yay taga-taga zai fad'i, saikuma yarik'e
bango. "Yau Operation biyu garemu, dolane mu k'addamarma tsohon yarinyar can daya had'amu
da kwalawa wlhy, sannan Na yayyaga uwarta a gabanta, itama haka, kafin Na wullasu gidan
daba'a dawowa".
Dariya suka kuma bushewa da ita, yanzu kam harda zike.
Yacigaba da fad'in saikuma wancan sauran gawan gagis, har yaransa saina k'are musu
tanadi,, yanzu kutashi muje lik'a posters d'in Oga, koba'aso dolene ayisa kokuma lahira tai bak'i
wallayi".

(Duk cikin harshen turanci suke magana, Dan k'alilanne ma acikinsu kejin hausar, manu nema
kad'ai bahaushe, saurankam kowanne dayarensa, kusandai yanda jos ta tara yarurruka iri-iri,
wannan yasa aka cakud'e waje d'aya, baka isa cewa wannan yarene tsageraba a jihar, saboda
matasansu a cakud'e suke, musamman ma irinsu zike marasa jin magana).
Duk mik'ewa sukayi, kowannensu a buge yake, dan sunyi mank'as da kayan mayen da Oga
Pam ya basu, wani buhu dake gefe suka d'auka, zike yabud'e yad'ebo posters yana raba musu,
saida kowa yasamu sannan suka tafi, kowa yana rik'eda posters da gam na ruwa a hannu. Sai
ihu suke suna kirari wa Oga Pam. Jikin pols da bangon gidaje suke lik'a posters d'in, daduk inda yay musu, babu mai hanasu
Dan ansan halin tsagerancinsu sarai. ihu suketa zabgawa.
"Wuyyyyyiiii huhuuuuuuuu!!!!!, sai Oga Pam ko jiki yay tsami, a za6esa dole ko wlhy uwar
gayu tahaifi wani, wuuuuyii huhuuuuuu!!!!!!!.
Abinda suketa fad'a kenan, ba yaraba hatta manya gefe suka koma suna kallonsu. duk
poster d'in da suka gani cireta sukeyi, inhar bata Mr Pam baceba.
Kad'an yarage fad'a ya kaure tsakaninsu da wasu matasan anguwar, wad'anda suka lik'a
wasu posters da suke cirewa. amma wani dattijo yamusu magana. ALLAH yasa wad'ancan
masu fahimtane, akwai sauran hankali a jikin, saisuka k'yalesu akan zasu had'une koba yauba.
Su zike kam filin nasune, haka sukaita bin anguwanni suna lik'e-lik'en fostar Mr Pam.☹
Wata anguwar a tanka musu, wani wajen kuma ayi kamarma ba'a gansuba. Saida suka gama
tas sannan suka koma bayan Government primary school inda suka maida dan-dalin
shaye-shayensu suka zauna maida numfashi, da hirar tsiyatakun dasukayi a yau d'in, wani suyi
dariya. Wani suyi surutu da zage-zage.

_____________________________

Tunda suka fita Amattalah ta sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarta tayi tana tunanin rashin
zuwan Sadeeq saurayinta dubata.
Kobaiji batada lfy bane? Kokuma yazo tana barci halan?.

Gashin wayartama tana gida balle ta kirashi, kuma tanajin kunyar tambayar Ammi
koyazo...........✍



*yawan comments, yawan kwazona fa�.*


One luv my fans





*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*�
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce_*


____________________
*_Number 7_*
____________________

*_WASHE GARI_*
��

Abin mamaki washe gari da safe sai ga labarin kisan gagis yafito, anje har cikin asibiti da
daddare anmasa yankan rago.
Kai tsaye kowa su zike aka zarga, musamman da akasan tushen abinda ya kwantar da gagis

asibitin.
Humm, amma abin tsoro da ALLAH wadai sai aka nemi su zike aka rasa a cikin jos, Ashe
suna gidan Mr Pam yabasu mafaka, bayan sungama tsara masa k'arya da gaskiya akan su
gagis sunason 6ata siyasarsane shiyyasa suka kasheshi.
Sosai Mr Pam ke hura hanci da banbamin masifa akan k'are Duk wani dayace zai kawoma
siyasarsa togaciya dolene a 6addashi, koda kuwa abokan takararsane.
A daren ranar yadank'ama su zike makamai masu had'ari sosai, wai surik'e domin kare
kansu. sunyi farin ciki sosai da wannan k'yauta, dan aganinsu k'arin k'arfin guwwane agaresu.


Nidai nace, "hummm".☹



____________________________

Tunda sassafe Baban Ama yay shirin tahowa asibitin, danya kar6i Ammi taje tai musu
girki.
Alhmdllh yatadda jikin Amatallah da sauk'i, jiya kuma firgitar kad'an tayi, sai dai zazza6i mai
zafi data kwana dashi, dukda Magani da akabata bai saukaba, haka taita sambatu da kiran
sunan Ammi da babanta.
Lokacin da babanta yake fitowa saiya ci karo da uncle M.A, babu irin rok'onsa dabaiyiba akan
yay kwanciyarsa yak'ara hutawa zuwa anjima amma yak'i, yace suje tare kawai asibitin su kar6i
Ammi.
Haka suka taho badan baban Ama yasoba.
Sun iso Amatallah Na barci, saboda batayi barcin dareba, bayan sun gaisa da Ammi tawuce
gida sukuma suka zauna hira.

Kusan 9:30 Ammi takirasu akan sutaho tagama.
Har lokacin Amatallah Na barci.
Ammi tataho sukuma suka tafi,
Suna kammala cin abinci suka tafi k'auyen da zasu kar6o maganin baba.
Basu dawoba sai misalin 2:38pm. kai tsaye asibitin suka nufo.
Amattalah na zaune a kan gadon datake jiyya, abinci takeci tana hawaye, ga likita tsaye
agefenta yana kallonta yana murmushi shida wata Nurse, Ammi kuma Na a bakin gadon zaune
tahad'e fuska tana fuskantar Amatallah, da Alama itace ta tsareta takeci abincin.
Cikin gur6atacciyar hausar likitan yace, "Ametala please mana, stop crying, baka sen kai
babba baniba? amma kinama common injection kuka? randa zakaje labour room kuma fa
iye?......"
Banza Amatallah tamasa, jitake kamarma ta bugeshi dan haushi, shigowar su baba yasaka
doctor da Ammi kallonsu, duk suka amsa sallamarsu.
Uncle M.A yak'araso da d'an sauri yana tambayar lafiya? Amatallah ke kuka?".
Doctor ne yamasa bayani akan sunason mata allurane saboda zazza6i yak'i sakinta, to gashi

bataci komaiba kuma, shine yace tad'anci abinci kafin sumata. tace tak'oshi, Ammi ta tsareta
saitaci, wannan ne dalilin kukan nata.
Babantama dariya abin yabashi, dan haka yay dariya kad'an, can k'asan ransa kuma
yanamai jin tausayin d'iyar tasa tilo, sai dai bai San daliliba, tunda safe dasukazo ya kalleta yaji
kwalla sun cika idonsa, haka kawai yau yawayi gari da k'ulafucin tunaninta da tausayi.....
Ajiyar zuciya yasaki, yayinda ya tsinkayo muryar uncle M.A Na lallashinta.
Bai ce komaiba, saima gefen Ammi daya koma ya zauna yana kallonsu cikin wani yanayi,
ita kanta Ammi kallonsu takeyi a wani iri.
Da lalashin uncle M.A akasamu Amatallah taci abinci aka mata allura. tun tana hawaye har
barci ya d'auketa, suduka ajiyar zuciya suka saki, kafin su tashi su fita zuwa gida cin abinci,
sukabar Ammi Na gadinta, lokaci-lokaci masu dubiya k'awayen Amattalah da makwafta da 'yan
uwan Ammi Na zuwa.

____________________________

Gab da magriba Baban Ama yakira Ammi akan tazo gida tabashi wasu takardu daya bata ajiya.
Tayi d'an Jimm kafin tace, "to Baban Ama wazai zauna da ita? gani nake bai dace nabarta ita
kad'aiba anan.
Ajiyar zuciya Baban Ama ya dauke, kawai saiyaji idonsa yacika da k'walla, zuciyarsa tayi
rauni, a sanyaye yace, " karki damu, ga Brother nan yataho wajenta, idan kika d'akkomin saimu
koma asibitin tare ni da ke".
Kanta ta jinjina tamkar tana a gabansa, tace, "to ganina zuwa".
Amatallah na kwance tanajin Ammin ta, jitayi bata k'aunar tafiyar Ammin, bayan Ammi ta
yanke wayar Amatallah ta kalleta, hawaye taf da idonta tace, " Ammi ki kwatantama baba inda
takardun suke saiya d'auka basai kinjeba". tak'are maganar da zubda kwalla.
Kallonta Ammi tayi, tana mamakin miye abin kuka anan? daga dai zuwa d'akko takardu
tadawo.
Matsowa tayi jikin gadon, ta dafa kan Amatallah tana murmushi, "haba Khadija miye abin
kuka to? yanzufa zanje na d'auka masa mudawo, kiringa hak'uri da rayuwa Khadija, wannan
k'ulafucin namu dakikeyi ki ragesa, karfa ki manta akwai mutuwa, kuma ke d'iya mace ce,
wataran aure zakiyi kibarmu dole, kizama mai hak'uri kinji, komi kike tunani, koya cutar dake,
koya sakaki rud'ani, to kisaka *HAK'URI* agabansa, insha ALLAH zaki zama mai riba a
duniyarki da lahira..........
Sallamar Uncle M.A ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login