Showing 99001 words to 102000 words out of 109227 words
Chapter 34 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
saboda yaran gaba d'aya sun d'auke hankalinta.
Suna zuwa gida mai napep d'in dake kai yara school yana isowa, ya d'akkosu daga
islamiyya.
Tare suka shiga cikin gidan.
Da daddare bayan sun gama cin abinci da 'Yar hira yace yaran suje suyi shirin barci su
kwanta.
Kafin yashige yaje yayma Aneesa saida safe yayma su saifufden addu'a kamar yanda
yasaba yafito, itama Fateema yashiga yayma yaran addu'a.
Amatallah tagama tsaftace jikinta da baje ko wanne lungu da sak'o na jikinta da k'amshi, duk
a sanyaye takeyin komai, dan rashin haihuwarnan tata na damunta, musamman yau dataga
babyn Nazeefa ma. A sanyaye tashigo bedroom d'in nashi, haryama kwanta danya gaji da
jiranta. Hannu yamik'a mata alamar tazo gareshi ganin ta tsaya a bakin k'ofar.
Idonta harya cika da kwalla ta taka a hankali zuwa gaban gadon, shiya kamo hannunta
yajawota tafad'o jikinsa.
Rungumeta yayi sosai, a cikin kunanenta yace, "my heartbest waya ta6amin kene?".
Ai tamkar yazugata saita rushe masa da kuka kawai.
Dama yasan za'a rina dan tund'azu batada walwala koda ana hirama.
Bai hanataba ya barta tayi kukan sosai yana shafa bayanta a hankali, alamar lallashi, saida
tayi sosai sannan yad'ago kanta ya manne bakinsa kan nata kawai, yafara mata lalashin
dazatafi gamsuwa dashi.
Saida hankalinsu yadawo jikinsu sannan yashiga mata kalamai masu sanyi da ratsa 6argo.
" haba my best fad'amin matsalarki please, nine Uncle nine baba nine Ammi nine miji kuma
kinji?".
Kanta ta d'aga masa, murya a raunane tace, "uncle maganar haihuwarnan bata
damunkane?".
Shiru yay danya rasa mima zaice mata, zuwa can yace ''ki kwantar da hankalinki khadeeja,
insha ALLAH baki tare da kowacce matsala, Amma ranar Monday ki shirya saimuga doctor
mana".
" Uncle inajin tsoro wlhy, inajin tsoron kar ace bazan ta6a haihuwaba........."
Da sauri yarufe bakinta, ''insha ALLAH zaki haihu, sainaga jinin brother d'ina da nawa
cakud'e a waje d'aya da izinin ALLAH my best, ki d'auka komai akwai lokacinsa, watarana sai
labari, kikama sani ko nayi ajiya wannan watan". yay maganar cikin tsokana yana shafa
shafaffen cikinta. Kanta takuma cusawa a k'irjinsa tana 'Yar dariya.
Yayi dariyar shima yana sumbatar Sumarta da fad'in kokefa, amma da anatamin rowar
fara'arnan dake yalwata farincikina da annashuwata nima.
Kuma k'ank'amesa tayi tana fad'in kai Uncle".
"ALLAH kuwa my Dee....."
***** ******* *****
Ranar Asabar d'in week d'in Abulkhairi yashiga layin yara masu zana jarabawar fita daga
primary, shima zai wuce secondary insha ALLAH A wannan year d'in, yaron yagirma,
kamanninsa da Uncle suna kuma fitowa sosai, hakama Sahib shima yaron yayi girma, dan
dakad'anma Abulkhairi zai fishi tsawo, yamafi Abulkhairi wayo.
A ranar Monday d'in kuwa Amatallah ta zabgama Uncle wayo dankar suje asibiti, dan itafa
tsoro takeji taje ace akwai matsala.
Dukda yaganota haka ya k'yaleta, dama shimad'in bayason aje asibitin.
Agurguje please
Rayuwar tacigaba da tafiya ahaka, yau fari gobe tsumma, yau dad'i gobe hak'uri, ansha sunan
yaron Nazeefa, (Sulaiman). su Amatullah kam anata karatu, dukda tanada damuwa azuciyarta
bata bar hakan yazama silar raunanar karatunta ba, kullum Fa'iza da Aysha cikin kwantar mata
da hankali suke da nuna mata muhimmancin hak'uri da yarda da k'addara. Hakama 6angaren danginta su kawu hafizu, koda yaushe sukayi waya yakan k'ara kwantar
mata da hankali.
Shikansa Uncle d'in duk abinda zai kwantar da hankalinta da kauda mata damuwar
rashin haihuwar yanayi. ganin yanda duk suka damu sai itakuma tafara rage nuna tata
damuwar, tama d'auke tunaninta daga wajen gaba d'aya, ta duk'ufa gayama ALLAH kukanta
dayawan azumi, sadaka dadai sauransu.
To Ama..... ALLAH dai yasa mudaceí ½í¸¢í ½í¹í ¼í¿».
****** ****** ******
"Wai lafiyarki kuwa Ama......?"
"K'alau Fa'iza, mikika ganine?".
" kawai tun jiya nifa wani sukuku nake ganinki, tamkar wata mara lafiya".
Kanta ta kwantar jikin kafad'ar Aysha tana jan k'aramin tsaki, "kibari kawai, nifa jikin
nawane ma duk babu wani dad'i, kuma babu inda yakemin ciwo wlhy".
Da sauri Fa'iza tace, " tin yaushe kika faraji?".
"Yanaga kin wani tsorata? bafa wani abu bane".
Cikin dariya Aysha tace, " aimu fatanmu yazama wani abun, nifa wani k'yauma naga kinayi
kwanan nan hajiyata, miye sirrin?".
Duka Ama... takai mata, Aysha ta goce da sauri tana dariya.
"To miye na dukanta? ba gaskiya tafad'aba? baby ALLAH yasa abinda muke fatane dai,
amma koni wlhy naga kin k'ara k'yau, maganace dai kawai banyiba".
" uhm kuma daina wahal da kanku, ni banida komai, kawai inaga malaria keson kamani
dai".
Dariya suka mata, akadai bar maganar ahaka, kowa kuma ak'asan ransa yana addu'ar
ALLAH yasa abinda suke fatane.
Kwana biyu dayin wannan maganar Ama.... ta tashi da zazza6i mai zafi, gashi ranarma Uncle
ba d'akinta yakeba, yana wajen Aneesa.
Har zasu fara break fast babu Ama...., dayake weekend ne.
Uncle ya kallesu yana fad'in wai Khadija fa?".
Aneesa tace, "Wlhy nibanga tafitoba tun d'azun, Siddiqa ma tashiga tafito tace barci takeyi,
tona d'auka ko gajiyace tahanata tashi da wuri".
Fateema ma tace, " ni wlhy kwana biyunnan ma sainaga kamar Auntyn yara batajin dad'i
sosai".
"Nima nad'an zargi hakan, harma Na tambayeta amma tacemin babu abinda ke damunta,
bara dai Na dubata kawai".
Sukace to.............
Manage please
One luví ½í¸»í ½í¸»í ½í¸»
[1/25, 12:25 PM] Aysha Galadima: *_Typingâœí ¼í¿»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*í ½í²¡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* â‰
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceí ¾í´™í ¼í¿»_*
____________________
*_Number 39/40_*
____________________
Tundaga falo jikinsa yafara sanyi, dan babu alamar tayi gyara, da sallama yashiga
bedroom d'in, babu amsa, ya kalli gadonta, tana k'udundune a bargo tarufe har kanta, da sauri
ya k'arasa ya yaye bargon.
"Khadija lafiya kuwa? da uban zafinnan kika lullu6........"
Maganarsa ta tsaya a mak'oshi saboda yanayin daya ganta, ga jikinta zafi zauu, har wani
huci ke fitowa.
"Ya salam my best!" yafad'a yana zama gefen gadon, hannu yakuma kaiwa a wuyanta ya
ta6a, tarik'e hannun da sauri tana rawar sanyi, "Uncle please bar ta6ani, hannunka sanyi".
"dama bakida lafiya amma baki fad'aba Khadija? kuma har tadaki nazo nayi da asuba".
" Uncle sannan zazz6in ya saukane, banyi zaton zai dawoba da safe".
"Dashi kika kwanama kenan?".
Kanta tad'aga masa tana wani lumshe idanu dakuma dunk'ulewa waje d'aya saboda bargon
daya cire mata.
Tashi yay yashiga bayinta, yahad'a ruwa maid'an zafi sannan yadawo, ya taimaka mata
tasakko tanata rawar sanyi da fad'in "Uncle please kabarni Na kwanta, ina ganin jirine".
" Sorry my best! Bara namiki wanka kiji d'an k'arfi saimuje Asibiti".
Tirjewa tayi tana tura baki gaba, "nidai Uncle basai munje asibitiba, danasha parasitemol
zan warke".
" to naji shagwa6a66iya, muje dai ayi wankan first ".
Da kansa yamata wankan, ya taimaka mata suka fito, a bakin gado ta zauna, ya d'akko
Vaseline ya shafa mata, tanata langa6e masa itafa jiri take gani, hakadai ya lalla6ata yasaka
mata doguwar riga bak'a.
Fita yayi itakuma takoma ta kwanta harda jan bargo takuma lullu6a, taji dad'in wankan, dan
ciwon jikin saitaji yaragu harma da zafin.
Yana fitowa suka hau tambayar miya faru da Ama.... d'in?.
"Batada lafiya Ashe, zazzabi takeyi, Aneesa had'a mata break fast d'inta".
Sun nuna jimamainsu akai, Aneesa ta had'a break fast d'in ta d'auka da kanta domin kai
mata, Fateema da Uncle sukabi bayanta.
Da k'yar tatashi tasha kunun bayan su Fateema sunmata yaya jiki, ta amsa dak'yar tana
tambayar ya yara suka kwana.
Uncle yayi yayi tatashi suje koda camix ne tunda yau babu aiki amma tak'i, itadai yabata
perasetimol tasha kawai.
" nifa bazan baki maganiba kai tsaye, nasani ko ALLAH ya share kukanmu ne, kokuwa
salon nama kaina ganganci".
Baki ta turo masa tana matso hawaye, "amma Uncle kofa masu tsohon ciki sunasha, kuma
babu abinda yake musu, tunda a asibiti muna badawa aii".
Shiru kawai yayi yana kallonta, yama rasa mizai cemata, daga k'arshe dai saishi ya hak'uran,
yabata tasha takoma ta kwanta.
Zazza6i dai yak'i sauka, saidai jikin ya huce yakuma dawo, ba Uncle ba hatta su Aneesa
duksun damu, dan tasaba ranar weekend sunta shagalinsu da yaran agida kafin su tafi
islamiyya, su Kansu yaran duk sunyi sukuki.
Da daddare dai abinda batason dole akayi, Uncle yakira doctor Shu'aibu yadubata, gudun
karya bata Magani suyi 6arna yace tayi gwajin tsinke.
gwajin farko ya nuna mumsami babyí ½í²ƒí ¼í¿».
Murna wajen Uncle ba'a magana, babu kunya ya rungumeta a gaban Doctor Shu:aibu,
Ama..... kam hawaye kawai takeyi, dukda tad'an dad'e tana zargin cikine dama, soboda
aikintane, (dan kunsan doctor Ce fannin mata insha ALLAH anan gaba kad'an zata zama
kwararriyaí ½í²ƒí ¼í¿»). Su Fateema Kansu dai murna sukeyi, kodan k'aunarda Ama....kema 'ya'yansu dolene su
tayata farincikin samun NATA itama, kuma ko kad'an basuji kishin farin cikin da mijinsu ke
nunawa akan cikinba.
Doctor Shu'aibu yace, "dama nasan itama tasan tanada, kawai dai ta 6oye mukune".
" Uncle ya kalli Ama..... yace, "wai haka my best!?".
Kanta ta 6oye cikin bargo tana murmushi.
Duk sai sukayi dariya, Uncle yaraka Doctor sannan yadawo suka cigaba da farimcikinsu.
Ranar dai dole Aneesa tayi sadaukarwa na kwananta ga Ama....., Uncle yakwana a wajenta
saboda jikinta. (Anee kin biyamu kwannamu).
Hummm kafin kacemi maganar cikin Ama....Yazagaye dangi makusantansu, har 'yan jos an
gwargwad'a musu, murna dai ba'a magana, 'yan dubiya su Anty maijidda dasu Asiya su
Nazeefa mai jego, ita Ama... Kunyarsuma takeji, duk kuma d'okin son samun cikin saiya 6uya
yanzu da'aka samu d'in. Babama yayi murna, hakama innani, dukda bata fito ta nuna a filiba, amma takanas shehu
yakawota tazo ta duba Ama.....
Amatullah nashan wahalar cikinnan, dan laulayi takeyi sosai, dolene kaganta Tabaka
tausayi, dukta rame sai uban haske data k'ara, dukda kasancewarta bak'a.
Girki dai su Fateema sun sauke mata, saidai ta kwana da miji, wataranma idan abin yay
tsanani hakura suke da kwanan Nasu ya kwana a d'akinta, tanashan k'arin ruwa kam tamkar
wata galloní ¾í´, kullun cikin zirara mata akeyi.
To Ama...ALLAH yaraba lafiya.
***********
Kwanci tashi babu wahala wajen Ubangiji, ga Ama.... cikinta yashiga wata na 7, yafito d'as
kuma yamata k'yau, tanata karatunta hankali kwance, dan Alhmdllh tunda cikin yashiga wata na
5 tasamu sauk'in laulayin, saidai abinda ba'a rasaba, harma taje jos tayo sati biyu acikin d'an
hutun dasuka samu, tazaga dangi sosai dukda ba wannane zuwanta Na farkoba, har
anguwarsu taje ta gaida makwafta dasuke mutunci dasu kafin rasuwar su baba, dukda ma
wasunsu sun rasa rayukansu a lokacin wancan rikicin, wasu kuma sunbar garin gaba d'aya, har
kuka tayi dataga kufan gidansu, Dan tuni Uncle yanemi shawarrata akan ayi masallaci ko
islamiyya awajen, domin ladan yadinga kaiwa ga iyayenta, takuwa amince, yasa akayima wajen
gyara bayan an rushe, masallaci akayi k'arami da islamiyya mai aji hud'u k'anane amam, sai
Bohol da akayi mutanen anguwar NATA d'ibar ruwa, dama basudashi. Wani son Uncle Yakuma
ratsa ruhinta saboda wannan hidima dayay ga mahaifanta, (kowa yasan anason sadaka mai
gudana ga mamaci). a zuwanne takejin labarin d'aure Ramzaki da akayi, saboda kashe wani da
Mr Pam yasa sukayi, kuma aka kamasu, koda sukace shine yasakasu aka kirashi saiyace
shibaima ta6a ganinsuba ballantana ya sansu, k'arya suke masa, hakanne yasa aka kaisu
Court, hukuncin shekaru 25 aka yanke musu a prison. Amatullah dai jitayima INA itace alk'alin ,
da ratayesu zata sakama ayi take anna, amma hakanma tayi farinciki koba komai zai d'and'ani
azabobi kafin yaje waken ALLAH kuma. Satinta biyu tadawo Kano ta koma school aka cigaba
da bugawa.
Rayuwar gidansu nanan yanda take, saidai 'yan canje-canje daba'a rasaba, amma sunan
akan tattalin mijinsu da kishinsa, kuma hakan bai hanasu k'yautatama junaba.
Haka shima mijinsu mai gajiya da basu soyayya mai tsaftaba, kowacce gwargwadon iko yana
nuna mata tattali da soyayya, yana k'ok'arin adalci a tsakaninsu, wadda yafi so kuma yabarma
zuciyarsa.
Maganar K'UNGIYARSU kam saimuce Alhmdllh, yanzu haka suna k'ok'arin had'a wani
gagarumin taro na k'asa, domin wayarma matasa dakai a kan za6en dake tunkaro k'asar,
Wanda bai wuce saura kwanaki k'alilanba a gudanar dashi.
Sai dai kuma a wannan tsakaninne wani Abu Mara dad'i yafaruí ½í¸¢, shine Rasuwar baba,
adaren juma'a ranar alhamis kenan jikinsa yay tsanani, hankali tashe Innani takira Uncle kusan
1pm, harma ya kwanta, dan ranar a d'akin Amatallah yake, suna tsaka da barci tana kwance a
jikinsa, yayinda hannunsa ke rungume da cikinta, da k'yar ya iya lalubar wayar a k'ark'ashin filo,
batareda yaga mai kiranba yad'aga dafad'in "please wanene?".
Muryar data daki kunnensa tasashi wartsakewa babu shiri, innani yajiyo tana fad'in "
maza kazo gida Muhammadu jikin babanku ya rikice".
A firgice ya wuntsilo daga gadon, haryana bigema Ama.... cikinta, Wanda zafinne yasata
farkawar dole tana fad'in "wayyo ALLAHNA".
ina Uncle bai sauraretaba, sorry kawai yace mata yafice da sauri.
Dukda azabar da Ama... keji haka ta tashi zaune da k'yar, mamaki yacikata, tabbas babu
lafiya, dan ko juyi zatayi cikin barci saiya farka, kuma zai taimaka mata ta juya cikin lalla6awa,
amma yanzu ji yanda ya maujeta bai kulaba, sakkowa tayi tafito tana d'an cije baki, dan har
yanzu inda ya bigeta bai daina zafiba, yaran cikinta sai motsawa yakeyi alamar shima yaji zafin
maybe (lol).
Tana fitowa falon yana fita shikuma a rikice, ya canja kayan barcinsa zuwa farar jallabiya,
hakan yakuma rud'ar da Ama... ta tada su Fateema duk ta sanar musu.
Jigum-jigum sukayi, kowa yana sak'e-sak'e da tunanin mike faruwa? dukda wani 6angaren
tunaninsu yana kan babane k'ila, saboda jiya jikin nasa yad'an motsa har sukaje suma suka
gaidashi.
Kasancewar titi babu motoci sai tsilli-tsilli yabama Uncle damar zabga gudu, lokacin dayaje
gidan lamari ya 6aci kam, danba baba ba hattada Innani tafita hayyacinta, Aysha sai kuka
takeyi, hakama gwaggo Rakiya.
Dole adaren suka tafi asibiti, sai daifa babu tsumi babu dabara, kafin asubahi rai yayi
halinsa, ALLAH ya d'auke kayansa.
Mutuwar data zamema Uncle ta uku dabazai ta6a mantawa da itaba, duk yanda yaso ya
daure ya rarrashi su Innani yakasa, shima kansa yakifa akan gawar yafashe da kuka.
hakanne nima yasani kukan, danna tuna da rasuwar nawa mahaifin, ALLAH ka gafarta
musu, ka yafe musu, muda suka bari ALLAH ka d'auki ranmu muna a masu imani da tsonka ya
rabbi, ya ALLAH ka k'ara mana soyayyar manzon ka tsaftatacciya a rihinmu.
Marayu ALLAH yabamu hak'uri kunji, inayinku a duk inda kuke.í ¾í´í ¼í¿».
To anyita ta k'are, baba yatafi ya barsu Uncle, yanzu shine babban wa, shine kuma Uba.
Washe gari misalin 10am akayi jana'izarsa wadda ta tara d'unbin Al'umma, kodan d'ansa
yatara, dan matasa dama dattijan sunta tururuwar halattar wannan jana'iza domin nuna hallaci
ga Alhaji Muhammad Ahmad Labbo.