Showing 78001 words to 81000 words out of 109227 words

Chapter 27 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

Murmushi yak'arayi ya hawo gadon sosai ya kwanto a bayanta da d'ora kansa bisa dokin
wuyanta, cikin kunnenta yace, "shikenan bara to a maimaita irin na jiya tunda babu wani Uncle
kikace......"
Ai bata bari yakai k'arsheba ta tureshi ta diro daga gadon, wuff tafad'a toilet d'insa.
Dariya sosai yakeyi, (daka gansa kasan yana cikin tsantsar farinciki) nishad'in dake kwance
saman fuskarsama kawai ya isheka amsa. Sakkowa yayi yafita Dan tada jama'ar gidan.
Babu maganar shiga 6angaren kowaccensu, Dan duk da bak'i, knocking kawai yayi musu,
yana tsaye har suka tattashi, yacema Aneesa ta tado masa su Abulkhairi, dan a 6angarenta
suka kwana.
"Kashigo mana, mufa kad'aine sai Nazeefa da Zaliha, kuma suna d'akina su". murya ad'an
cinkushe take magar, Dan haka kawai haushi yake bata tunjiya dataga Amatallah zata
6angarensa.
Bai damu da yanda tai maganaba yashige, a zatonsa ko mura keson kamata�, harma
tabar falon takoma d'akinta.
d'ayan d'akin yashiga yatadasu, sukayi alwala sannan yatasasu gaba suka tafi massalaci,
ana idar da sallah aka rad'a sunan baby Ameenatu (sai muce ALLAH ya raya Uwargida).

Suna dawowa yashiga d'akin Amatallah, ALLAH yaso Anty maijidda takwashe kayan jiya,
ko ina tsaf saidl mayataccen k'amshinta daya rigaya ya mannewa 6angaren. Waldrop yabud'e
ya d'akko mata wani less mai k'yau da d'aukar ido, yahad'o da mayafi kalar filawoyin less d'in,
ya d'auki takalma flat suma dai kalar gyalen, sannan ya d'ibi kayan kwalliyar saman mirror d'inta
da turarruruka, dukda wasuma baisan amfanin suba shidai duk ya had'a mata yafito.

A falo suka had'u da Aneesa tafito d'aukarma siddiqa ruwa, kallonsa take shida ledar
hannunsa, dakuma kallon 6angaren Amatallah daya fito. yad'anji kunya, Dan haka cikin
basarwa ya kalli ledar da d'an d'agata sama sannan ya kalli Aneesar yana murmushi.
Harararsa tayi tara6a ta gefensa zata shige kitchen abinta.
Da sauri yasha gabanta, "my Nessa ba gaisuwa?".
Dukda taji kunya saita dake, batace komaiba ta kauda fuska gefe.
Ya marairaice murya tareda d'an langa6e kansa gefe ''haba Neesa ninefa Muhammad d'inki,
miyayi zafi ake fushi dani?".
Dariya yabata sosai, Dan haka ta murmusa, rissinawa tayi ta gaidashi da tanbayar ya
angwanci.
Yad'an zaro ido waje ''my Nessa! angwanci kuma?".
Haushi yakamata, aranta tace, " Namiji munafuki.." (Bani nafad'aba Neesa ce🤭).
Gaba tayi abinta tashige kitchen d'in.
Yabi bayanta da kallo yana murmushi har hakwaransa Na bayyana, gwalo yayma bayanta
yanufi 6angarensa yana fad'in "baki k'aryaba Nessa, yaukam ni angone mai lasisi".

(Hoooo Uncle d'inmu, kana aljannah muna binka da addu'ar fatan alkairi�).

Aneesa kam saida tayi hawaye a kitchen (duk dama batasan koya angwance d'in da
gaskeba) tana son Muhammad harma batasan iyakaba, shiyyasa take kishinsa, itafa ko'a
makaranta kishin kar afita yasata kasancewa mai k'ok'arin tsiya, bare kuma Muhammad d'inta,
duniyarta, farin cikinta, tanamasa so irin Wanda batama San adadinsaba, ta wanke fuskarta
sannan tafito.

(Neesa sai dai hak'uri, duk sonsa dakike k'addararki kenan zama da kishiyoyi🤭�. Sai hak'uri
dai. Nina Inason my Abdull d'ina, kuma k'ila saiyamin kishiya�😢).

Ya tarar Amatallah na shirin fitowa, taja baya yashigo, kanta a k'asa ta rissina ta gaidashi.
Murmushi yayi kafin ya amsa yana fad'in " ya gajiyarki babyna?".
Bata iya amsashiba, saima k'asa data kumayi da kanta. Bai damuba danshi kunyarta kuma
tsundumashi a kogin k'aunarta yakeyi.
Yakama hannunta suka koma ciki yana tambayar INA zataje?.
A marairaice tamkar zatayi kuka tace, "Uncle please kabarni Na sauka, kaga akwai ayyuka
da za'ayi, ga breakfast ga......."
Baima bari Takai k'arsheba yajawota saman gadon sosai "yo karsuci breakfast d'in Indai
saikin sauka kinyi musu, ai idan wani ya ganki a k'asa saidai nanda 12 Na rana", ya rungumeta
a jikinsa " kinga muyi barcinmu ma".
"Uncle!" tafad'a tamkar zatayi kuka.
Hannu yasaka kan la66anta yay mata Alamar zipí ¾í´.
Shiru kuwa tayi Dan dolenta, wani salo yafara mata, ahankali tafara lumshe idanu Dan
sak'on Na shigarta, jin yana neman canja hanya sai hankalinta yatashi (karfa Uncle yace zai
k'arayine nashiga uku ni Khadija), shiru tayi tahau barcin k'arya, dukda zuciyarta Na bugawa da
sauri-sauri saboda tsoro, a sannu dai har barcin gaskiya ya kwasheta, dama barcin takeji

dauriyace kawai yasata son saukar dakuma kunyar aganta da safe tafito daga 6angarensa.
Jin shiru da saukar numfashinta ahankali bisa k'irjinsa yasashi lek'a face d'inta, goshinta ya
sumbata Yakuma rungumeta da k'yau yana murmushi da jero mata wasu addu'oin fatan alkairi
zuciyarsa, shima babu jimawa barcin yay gaba dashi.

Babu wanda ya nemeta acikinsu Anty maijidda, saima hidimar d'aura breakfast dasukeyi
abinsu.
Garama Aneesa tasoyin magana saikuma tayi shiru.
Dasuka kammala breakfast d'inma Anty maijidda tace Nazeefa ta d'auka takai sama.
Har Nazeefa tashiga ta ajiye bataji koda motsinsuba, hasalima k'ofar bedroom d'in arufe
take. 'Yar dariyar mugunta tayi kafin tafara gyaran falon nashi, a zuciyarta kuma tana addu'ar
ALLAH yasa an gamune, sai zabga murmushi takeyi harta kammala, ta saka turaren wuta
sannan taja musu k'ofar tafice abinta. A k'asama ta iske su Anty maijidda sunata gyaran gidan, an kora yaran duka waje,
6angaren Amatallah tashiga, tayi mamakin yanda taga mirror d'in a hargitse, batace dai komai
tagyara mata ko'ina, ta saka turaren wuta sannan tarufo tafito.
Bayan sunyi breakfast kuma suka shiga kujiba-kujibar d'aura girkin suna da duk abinda za'a
buk'ata, zuwa lokacin kuma su Anty Mariya yayyen maijego sun dawo, Dan da daddarennan
duk suka tafi gida, yanzn kuma suka dawo Dan kama girki.

*****


Koda Amatallah da Uncle basukai 12 ba kamar yanda Uncle yay fata sun kai dai 10 suna barci
abinsu, Amatallah ce tafara farkawa,bayan tayi addu'ar tashi barci ta kalli yanda ta kanannad'e
jikin Uncle, kai kace zata komane jikin nashi, ta tsurama fuskarsa ido tana kallo, Uncle yanada
k'yau dai-dai misali, kuma yanada haske babu laifi, amma bak'ine, gemumsa da zagayayyen
gashin bakinsa sune suka k'ara masa kwarjini da cikar haiba, hannu takai a hankali ta shafa
gemunda tadad'e tana kwad'ayin ta6ashi saboda burgeta dayakeyi, masha ALLAH tafad'a a
zuciyarta, saboda wani laushi da santsi ga k'amshi da gemun keyi, (ba dole yayi laushiba, kud'in
da gemunnan ke lashewa aiba Na wasa bane).
Tunda tafara ta6a gemunsa ya farka, kokad'an bashida nauyin barci, amma bai nuna mata
yatashiba, danya kula tanajin dad'in shafa gemun nasa.
Ringing d'in wayarsa yasaka ta janye hannunta da sauri, tayi k'ok'arin janye jikinta amma
yak'i bata damar hakan, kallonta takai ga agogon d'akin kafin tadawo da kallonta kansa tana
zare idon tsorata da mamakin yanda lokaci yatafi, amma takasa magana bare ta tadashi.
Aka kuma kiran wayar, batareda ya bud'e idoba, baikuma saketaba yamik'a hannunsa d'aya
ya d'auka, kad'an ya kalli screen d'in wayar kafin yad'aga yasa a kunne yana fad'in "Assalamu
alaika".
Daga can Alhaji Sabi'u yace, " Alahji Muhammad lafiya naji muryarka haka?".
Murmushi Uncle yayi sannan yace, "a barci ka tadani".
" barcifa kace? wasa ko gaske?".
"Da gaske" yay maganar yana kuma k'ank'ame Amatallah kamar za'a kwaceta🤭.

"Lallaikam, kaiko wane aiki ya hanaka barcin dare? Saikace dakai ake abincin sunan".
'Yar dariya Uncle yayi, kafin yace, " mutumina bazaka ganeba ne kawai, yanzudai miya
faru?".
"Uhhm nakirake dama naji kokana kasuwa, amma badamuwa, idan kafito kakirani inason
mu had'une".
"OK, saina fitod'in".
"An rad'a suna ko? Gashi ko 'Yar walima bamu had'aba".
"hhh Alhajina kainane yad'au zafi, shiyyasama ko maganar walimar banyiba, mata kawai
suyi nasu, mu munyi namu da asuba ai, baby taci sunan Aminatu".
" Masha ALLAH, ALLAH ya raya manasu akan sunna, ya albarkaci rayuwarsu, yasa masu
mana addu'ane bayan k'asa ta rufe idonmu".
"Amin ya rabbi. Insha ALLAH zuwa 12 zan sameka a office kawai".
"okay babu damuwa saina ganka".

Kallonta yayi bayan ya kashe wayar, ta lumshe idanunta dan bataso su had'a ido.
Murmushi yayi yashiga zagaya yatsansa kan la66anta, murya k'asa-k'asa yace " 'yammatana
da guduwa zakiyi ki barni kenan?".
Wayyo ALLAH, tafad'a a zuciyarta.
Jin bata amsa mishiba ya yunk'ura yatashi da ita a jikinsa, "shikenan tunda bazakiyi
maganaba, tashi muje namiki wanka kar 'yan suna sufara jajenki".
Babu shiri ta ware manyan idanunta kansa.
Ido d'aya ya kashe mata�, tai azamar janyewa.
Sauka yayi itama yakamo hannunta zai saukar da ita ta tirje tana langa6e kai, " please
Uncle zanyi da kaina Dan ALLAH".
"ban yardabafa my best, dolene nakuma gasaki karkije kina tafiya agane yau......"
Hannu tasa ta rufe masa baki tana cewa "kai Uncle".
Hannun ya janye yana dariya, " to naji bazan fad'aba, muje Na had'a miki ruwan kawai".
Batak'iba wannan tabishi, yahad'a mata dad'an zafi yace "ki daure karki cuci kanki, kisan yau
taron jama'ane agidan kinji".
Ta d'aga masa kai idonta a k'asa.
Kumatunta ya sumbata yafice.
Bakuwa ta cuci kan nataba tagasa ko ina yanda yakamata, dan bawani zafi sosai takejiba dai
mai cutarwa, tundama Uncle yamata gashi Na musamman da daddaren, amma tanajin jikinta
ko'ina yana ciwo, gakuma wani canji Na musamman dukdai ba yanda tasaba jiba.
Tadad'e tsaye tana kunyar fitowa da guntun towel d'insa dake bathroom d'in, amma babu
yanda zatayi ganin time nakuma tafiya a banza tafito a takure.
Babu kowama a d'akin, hakanne yasata sakin ajiyar zuciya, kayanta tagani a saman gado,
tayi mamaki sosai, amma haka ta d'auka a gaggauce ta shafa mai da body spry, sannan
tashirya tsaf, sosai kayan suka mata d'as ajiki.
Bawata kwalliya tatsaya yiba, tana cikin shafa fauda yashigo da sallama, da alama shima
wankan yayo a d'ayan d'akin dake 6angarensa inda Nazeefa ta zauna sanda yana Dubai.
" hummm my Heartbeat Ashe nasan kala nima, kinyi k'yau kamar Na zauna naita kallonki
abuna".

Murmushi tayi tace "ngd Uncle".
Shima murmushin yayi yahau shirinsa, ko sau d'aya Amatallah bata kalli inda yakeba.
" my best zoki za6amin kaya ko".
Tad'an kallesa kafin tace "Uncle nikuma?".
Gira ya d'aga mata kawai.
Mik'ewa tayi tanufeshi, danta tuna (maganar Anty furera). Yana tsaye gaban Waldrop d'in,
hakanne yasa yad'an matsa tashigo gaba, kallon kayan ta tsayayi, tsarin komai ya birgeta.
Jitai ya sak'alo hannunsa kan cikinta ya rungumeta tareda d'ora kansa akan kafad'arta, itako
yazatayi da wannan lamari Na Uncle....
Maganarsa ta katse mata zancen zucin datakeyi.
" kifa za6amin kalar naki ehe".
Murmushi tayi ta jawo wata sky blue d'in shadda d'anya, tad'an juyo ta kalleshi da nuna masa
kayan. Wuyanta ya sumbata yana fad'in ke tadabance my best! kamar yanda komanki yake
nadaban".
Taji fad'in kalaminsa sosai, Dan haka ta danne kunya ta taimaka masa ya shirya, cikin janfa
da wando Na kayan, rigar tawuce gwiwarsa da kad'an, amma sunmasa k'yau ainun, saikace
wani d'an 30+ (�...lol).
Tana saka masa ma6allin gaban rigar suna murmushi, tagama tafesa masa turarensa.
Yace "saura hula my best".
Murmushi tayi ta za6o masa derk blue acikin hulinan data gani birjit. A mamakinsa saiyaga
tana karin hular..... (Abinda nakasa iyawa🤭 Ama... Zanzo ki koyamin narigama boss d'ina
nima�) tsayawa yayi kallonta cikeda birgewa. Bayan tagama tamatso kusadashi, yafita tsawo,
danhaka yad'an duk'o ta saka masa, tareda dai-daitata da k'yau. Kallon kansa yayi a madubi yana murmushi, " my best ina kika iya Karin hula haka?".
"Uncle wajen baba mana, tun ina masa yanacewa baiyiba harna dage Na iya kala-kala".
"Masha ALLAH my best!" Yafad'a yana kuma kallonsu a madubin, tabbas yasha ganin karin
hularnan akan brother d'insa, ringumeta yayi yashiga bata masu zafi....(😘 kundai gane).
Saida tasha dad'ad'an kalamai sannan suka fito falo, dakansa yabata brekfast d'in dasuka
gani a falon.
Bayan sun kammala kuwa babu yanda baiyiba su fita tare tak'i, yamata kisses yafice tana
masa addu'a.

Murmushi tayi tareda shafa fuskarta tana fad'in my Uncle I love you so much, lallai ka
cancanci kowacce mace ta haukace a kishinka, hummm wani sirrin saidai *RUHI* kawai".
Dahaka ta koma bedroom d'in ta gyara, ta tartare kayanta a ledar ta ajiye gefe. Saidaifa wlhy
bazata iya fitaba, to dawane idon zata kalli jama'a?.
Nazeefa takira wai Dan ALLAH tazo.
"Nazo namiki mi? yarinya kima sakko idan zaki sakko, ai gidan babu mutane sosai".
" please Anty Nazeefa, ALLAH bazan iyaba inajin kunya".
"Meyasa baki biyo mijinkiba, kinga shi gashina yanata gaisawa da dangi, kuma mai hotoma
ya Jabeer ya kawo, gakuma 'yan jos nan su Anty Sadiya sun iso yanzunan".
" da gaske Dan ALLAH Anty Nazeefa su Anaty furerane?".
"ALLAH kuwa, gasuma Suna gaisawa da Yaya a falonki........."

Ai tuni Ama....ta manta dawata kunya bare abinda yafaru da ita, dukda tanad'anjin zafi hakan
bai hanata sauka dad'an guduntaba, wannan yasa duk kallon k'urillarka bazaka gane mitake
cikiba. Ta wuce su anty maijidda Afalo.
Duk dariya suka saka mata, har Aneesa kasa daurewa tayi ta dara, (a ranta tana kuma jinjina
tsantsar k'uruciyar Amatallah).
Anty maijidda tace "k'uruci kenan dangin hauka".
Nanma dariyar dai akayi, kishiyar Anty maijidda tace nikam tana birgeni, ko kad'an batada
damuwa Amatallah wlhy".
Aneesa tayi murmushi tace, " gaskiya tanada hak'uri, tunda babu mai cewa tamasa wani
Abu Mara k'yau a gidannan wlhy, ALLAH dai yacigaba dabamu zaman lfy".
Gaba d'aya akace amin.
Kowa yasan Aneesa tanada kishi, amma macece mai fad'ar gaskiya da mutunci idan taso,
gashi bata iya wulak'anta dangin mijiba, ita kowa natane, duk sharrinka wlhy bazakace kazo
gidan ta wulak'antaba, ko Fateema datake 'Yar uwarsu jininsu iyaka dai kenan, (kishine dai kam
ba'a cewa komai a wajen Aneesa�). amma kam tanada fada sosai wajen dangin mijinta dana
kishiyarta, (zatayi kishi kam dake, amma danginki komai a mutumce)................âœí ¼í¿»








�👎🏻

One luv my sweet Fan's







*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*�í ½í¹í ¼í¿»
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typingâœí ¼í¿»_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_

*_SIYASA KO K'ABILANCI_* â‰
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 32_*
____________________


Amatallah Na shiga ta cikukuye Anty Sadiya dake kujerar farko, "fad'i take oyoyo anutys
d'ina, saikuma tasaki Sadiya takoma kan Anty furera da Asiya.
Uncle dai murmushi kawai yake zubawa, yaji dad'in ganin Amatallah a farinciki, kullum haka
yake fatan ganinta, bayason ta yawaita kukan maraici.......
Maganar Anty furera ta katse masa tunani.
" uch Amatallah, wai yaushe zakisan kin girmane?".
"Babu rana Anty furera". Amatallah tafad'a tana dariya, suka had'a ido da Uncle, gira yad'an
d'aga mata.
Ta kauda idonta tana murmushin itama.


Humm yau Amatallah fa ba'a magana, tana nanik'e da Aunty's d'inta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login