Showing 36001 words to 39000 words out of 109227 words

Chapter 13 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

wad'annan matsaloli dai."


Nace, "amin Nazeefa�.



____________________________

Tunda yafita sai Aneesa tafad'a gadonsa ta hau rusa kuka, tabbas sunada aiki agabansu,
yarinyarnan bama ganinta yakeba a shekarun baya yasuka k'are, kullum zancenta na bakinsa,
inaga yanzu ta dawo kusa dashi, tana amsa sunan matarsa kuma.
Tunda k'addara ta dawo da Amatallah Kano basu sake samun kan mijin suba, motsi kad'an
yana gidansu, dasunyi magana saiyace yaje duba jikin babane, insunyi k'orafi akan Amatallah
yace basuda tausayi.
Tasan yarinyar nabata tausayi, amma gaskiya tana matuk'ar kishin mijinta, taso ace daga ita
sai shi da 'ya'yansu zasu rayu, amma tunkamma tazo gidan saita taras wata tarigata shiga,
maimakon abarta taji da zafi d'aya, gashi kuma rana tsaka ankuma aura masa wata, k'aramar
yarinya ma, sa'ar k'anwarta ta biyu. Dolene ta d'auki mataki wajen ninka soyayya da kulawar datakema mijinta fiyema data
dacan, dan tafison yasota fiye da kowacce acikinsu. jibafa tunda tayi sallar asubahi taketa kaida
kawo wajen ganin tahad'a masa break fast mai rai da lafiya, saboda ganin kwana biyu bayacin
abinci sosai saboda damuwar dayake aciki tarashin amininsa. (Duk da dama shi bamai yawan
cin abinci baneba) Amma dan wulak'anci shine yafice wai sauri yakeyi, yanzu haka kuma
yanacan wajen bak'ar yarinyar can.
saita kuma rushewa da kuka kuma.


Nace, ''bantan uba, Aneesa kinada aiki wlhy, zan bama Xoxo kwangilarki�".


Ita kanta Fateema abin yabata mamaki, ganin yafita cikin fushi ko d'akinta bai kallaba, bayan
kuma k'a idarsane duk Safiya zai shiga d'akin wadda ba itace da girkiba su gaisa, hakama idan
yadawo aiki zai shigo miki, yaji ya lafiyarki keda yara, da darema kafin a kwanta zai shigo yamiki
sai da safe yama yaransa addu'ar barci. Amma yau ko yaran bai sauraraba, saima k'arar bud'e
gate da rufewa sukaji.
Cikin damuwa tagama musu shirin makaranta ta turasu wajen Aneesa suyi break fast, amma
sai suka dawo suna sanar mata momyn batanan, kuma ko Saifudden ma ba'ama shirin school
ba.
Tashi tayi tafito, ta lek'a 6angaren Aneesa batanan, har bedroom sai Siddiqa dake barci a
kan gado, tad'anyi knocking k'ofar toilet amma shiru, saifudden ne kawai kwance afalo lullu6e
da towel, da alama wanka aka masa ba'akai ga shiryashiba ma, dan ga uniform d'insa nan a

gefensa da manshafawa da turare.
Kallon Sahib tayi tace, "Sahib jeka saman Abbu kagani kotanacan tana sharane".
" to Umma". Sahib yafad'a yana fita da gudu.
Babu dad'ewa ya dawo yafad'a mata tana d'akin Abbu tana barci.
"Barci kuma? lafiya kuwa?".
fita tayi tana fad'in " Abulkhairi tada Saifudden ka shiryashi ina zuwa".

Sai da tayi sallama kusan sau uku sannan Aneesa ta amsa.
Fateema tashigo d'akin idonta akan Aneesar.
"Momyn yara lafiya kuwa?".
Tashi Aneesa tayi zaune, tayi kwafa sannan tafad'ama Fateema abinda yafaru, dan aganinta
wannan matsalace dazasu raba tare sukuma d'auki mataki akanta.
Fateema tace, " Humm momyn yara kenan, nimafa haka yaymin ranar da yarinyarnan ta
farfad'o, gaya mikine kawai banyiba".
Aneesa takuma yin kwafa, tace,
"Wana mataki kike ganin zamu d'auka? inba hakaba yarinyarnan saitama kiremu daga kan
'yayanmu wataran, dan naga rawar jikin dayake akanta tayi yawa tunkanma tashigo gidan, raina
mana hankali kawai akayi, za'ace wani babanta yarok'eshi ya aureta, wlhy dama can son
yarinyarnan yakeyi, shima Baban nata ya gane hakanne shiyyasa ya k'ak'aba masa. nifa har
mamakin yanda babanku yayarda yama Muhammad wakilcin auren nakeyi, bayan kuma yasan
keza'ama kishiya".
Duk da maganar Aneesa ta k'arshe ta 6atama Fateema rai haka ta danne saboda kishi na
cinta itama, tace, "miye shawararki to akai? Nasan dai Muhammad bazai ta6a sakin Amatallah
ba, kodan k'aunar mahaifinta dayakeyi".
''Yo idan shi bazai iya sakintaba, ai ita saimu sata masa bore tace bata sonsa, ai dole dai ya
barta ko".
" hakane, amma tayaya zamuyi hakan?".
''Muyi tunani na kwana uku, abinda kowa ya yanke saimu tattauna yiwuwarsa mugani
kawai, koya kikace?".
"Hakan yayi d'in, yara sun shirya, ke suke jira karsu makara".
Mik'ewa Aneesa tayi suka sakko k'asa tare, a gaggauce suka bama yara break fast dan mai
keke napep d'in dake kaisu makaranta yazo................✍


Nace, " humm, wai Fateema da Aneesa ne yau a inuwa d'aya�, lallai Amatallah da k'arfinta
tashigo.





Rashin comments d'inku kesani wannan laziness d'in, buk'atar typing d'ina kullum yana
hannunku☹✋, inkun gyaran nima zakuga sauyi a gareni‍♀�.

‍♀





*_ALLAH ya jik'an iyayenmu�_*
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce_*


____________________
*_Number 16_*
____________________

Da gudu ta wuce Furera matar kawunta yayan Ammi dake tsakar gida tana wanke-wanke.
"Ke Amatallah lafiya kuwa?". Anty Furera tafad'a a tsorace tana zare hannunta daga
ruwan wanke-wanken, ganin tawuce d'aki itama tatashi da gudu ta shige inda Amatallah tashiga
harda rufe k'ofar.
Ganin haka da Sadiya tayi matar k'anin Ammi itama saita afka d'akinta ta banke k'ofa harda
sakata.
Sufa duk zatonsu wasune suka biyo Amatallah d'in, gashi mazan gidan duk basanan sun fita.

Tashi Amatallah tayi daga kwanciyar datayi a gadon Anty Furera danjin tarufe k'ofa.
''Lah Anty Furera lafiya kuwa kika rufe k'ofar?".
" keza'a tambaya Amatallahi, miyafaru kika shigo gida da gudu haka?".
Sai yanzu Amatallah tatuna da yanda tashigo, dariya tashiga tuntsurama Anty Furera, dan
ganin jikinta har rawa yake saboda tsoro.
Sai da Anty Furera tamata magana sanan ta tsagaita da dariyar datakeyi, "Anty Furera babu

komaifa, wai da kina zaton minene?".
Ajiyar zuciya Anty Furera tasauke, " kai Amatallahi kin d'auki hak'ina wlhy, kinsan garinan
ba lafiya yacikaba, har yanzu a d'ar-d'ar kowa yake, waya biyoki haka to?".
Guntuwar Dariya Amatallah tayi, ''kai Anty Furera haka kike da tsoro ashe?, babu komai
wlhy, bud'e kiga wayarda Uncle ya siyamin".
Amatallah tayi maganar donson kauda tanbayar da Anty Furera kemata.
Bud'e d'akin tayi, sai lokacin itama Anty Sadiya tabud'e nata.
Fitowa tayi tana tambayarsu ko lafiya taga sun shiga d'aki?".
Labari Anty Furera tabata, Amatallah bata bari zancen yayi tsawoba tabasu kwalin wayar
suka shiga kallo da yaba k'yanta.


***********

Uncle M.A kam haka yabar jos cikin farin ciki da kewar brother d'insa, dan baibar garinba sai
da yabiya ta gidan su.
Komai ya k'one, da Alama ma ankuma sakama gidan wutane, dan randa abun yafaru
gobarar bako ina ta cinye hakaba, amma yanzu harda gidajen makwaftansa, bayan kuma
waccan ranar wutar bata ta6a kowanne gidaba, anguwarma gaba d'aya tayi kaca-kaca.
Mota yakoma yatafi kawai, wani 6angare na zuciyarsa na tuno masa abinda yafaru
tsakaninsa da Amatallah, sai yakanyi murmushi, lokaci-lokaci kuma yakan kama d'an kwalinta
dake kan cinyarsa ya shak'i k'amshin.
Haryaje Kano ribbon d'inta na a tsintsiyar hannunsa. sai da zai shiga gida yacire d'ankwalin
yasaka ribbon d'in ciki ya nannad'e ya tura a aljihu.
Yau girkin Fateema ne, dan haka ita tabud'e masa gate. yauma kamar kullum a cikin kwalliya
take, hakama yaransa suna gida saboda Alhamis ce babu islamiyya kuma ana hutun boko,
itama Aneesa cikin kwalliyar tafito tamasa sannu da zuwa, suduka basusan ma inda yajeba.�
Da taimakon Fateema yay wanka, sanan ta shirya masa abinci, bai ciba sai da suka dawo
sallar Magrib shida yaransa.
Suna kammala cin abinci suka fita sallar isha'i, daga can gidan su yawuce da yaran gaba
d'aya, suka gaida kakanninsu.
Sun dad'e agidan suna hira shida Jabeer da Shehu da Nazeefa, Rabin hirar duk akan
tafiyarsace dakuma Amatallah, innani dai bata saka musu Baki sosai, amma tana saurarensu,
baba kam tunima yayi barci, dan babu laifi jikinsa da sauk'i.
Basu koma gidaba sai da yaga plashing d'in Fateema, dole yatafi shi kad'ai yabar yaran
nan, dan dare yayi, kuma duk sunyi barci, gashi a Napep sukazo ba motaba, shima mashin d'in
Jabeer ya kar6a yatafi a kai.


___________________________

Gobene takama tafiyar Uncle, duk abinda yakamata ya kimtsa yayisa, abinda ya danganci
gidansa dana mahaifansa duk yamik'ashi hannun Jabeer, hakama lamarin kasuwa, dukda

akwai yara masu kulada shagunan, amma dole sai da mai kulawa lokaci-lokaci.
Abu d'ayane ke damunsa arai dabai samu koda kafa harsashin saba, yarasa wazai fara
tunkara da batun? Dan bakowa baneba yakeda zuciyar irin wannan jihadin, musamman ma
daya kasance abune da sai an ta6a aljihu.
Zuciyarsace tashiga bashi shawarar kiran Sabi'u m Ali. Wayarsa ya d'auka sai dai zuciyarsa
na fad'a masa yakira ko karya kira, danya kai tsawon wata 10 rabosa da waya dashi, dama can
yafisu k'ok'arin kira a waya dama zumincin dagashi har marigayi.
Shawara ya canja, yafara masa test massage. kusan mintuna 15 saiga kira yashigo. Wayar
ya d'auka yana k'aramar dariya, Dan ganin Alhaji Sabi'u ne. Sai da ta tsinke sannan shi ya kira.
Alhaji Sabi'u na d'agawa Uncle M.A yafara bashi hak'uri kawai.
Dariya Sabi'u yayi daga can yace, "ya zanyi daku, kai da Isma'il ko kad'an bakwason zuminci
dani na lura".
" a'a wlhy, ba haka baneba, amma amana afuwa kanmu bisa wuya".
"Hhh shikenan ya wuce aii, ya gida ya iyali?".
" duk lafiya lau muke".
''To Alhmdllh".
Gyaran murya Uncle M.A yayi, sannan yace, "wlhy maganace a bakina, gashi kuma ban saniba
ko kana kano?".
" eh ina Kano, ai munma dawo gaba d'aya, zirga-zirgan ta isheni ne".
"A lallai na yarda munada laifi sosai a wajenka, yanzu nan har kadawo da iyalinka Kano
amma babu labari balle a k'ulla zuminci?".
" to nima nayi laifi amin hak'uri, bama su dad'eba, 3month's kenan da dawowar, kaina bisa
wuya".
Still dariya Uncle M.A yayi, yace, "shikenan to, indai ban takuraka ba zuwa 4:pm insha
ALLAH zan shigo, Dan gobe zan bar k'asar ne".
" mutumina ina kuma zaka fad'a haka? Halan kaida Isma'il ne?".
"A'a, nasan namaka laifi gaskiya, amma Isma'il ALLAH yamasa rasuwa kusan 6month's
ago". yak'are maganar hawaye na cika idonsa.
A can kuwa Sabi'u ya masifar rikicewa, sai sallalami yakeyi, dole Uncle M.A ya yanke wayar,
dan k'ara karya zuciyarsa yakeyi. kusan mintuna goma sannan Sabi'u yasake kira, yamasa
ta'aziyya sosai sannan yace babu damuwa yazo su had'u a gida, zai turo masa address d'in
inda suke yanzun. Uncle M.A yamasa godiya sukayi salama. Jin gina yayi da kujera ya furzar da huci, a hankali
ya furta ALLAH yajik'anku brother, I miss you so Much wlhy.

Har Fateema tashigo ta shirya masa abincin Karin kumallo a k'asan carpet bai saniba, ya
Lula sosai a duniyar tuna rayuwarsa da Brother d'insa.
Ganin shirun yayi yawa Fateema ta k'arasa kusadashi ta zauna. Sai da ta ta6a kafad'arsar
sannan ya juyo yad'an kalleta.
" haba Nurri tunanin mikake hakane?".
"Kansa kawai ya girgiza mata baice komaiba".
Shuru tai tana Kallonsa kawai, amma fuskarta ta nuna alamun shiga damuwa.
Hannunta yakamo yana murzawa a hankali, cikin sassanyar muryarsa yace, " my Tee... ina

tuna brother ne".
Tausayi yabata sosai, tasan har Abadan mijinsu bazai ta6a manta Baban Ama ba, Dan
ubangijine kad'ai yasan irin k'aunar dasukema junansu. hannu tasa tad'an shafi k'asumbarsa
zuwa gemu, sorry Nurrina, kacigaba damasa addu'a, muma duk ita muke jira, ALLAH ya gafarta
musu sukuma". "Amin ya rabbi".
" please abinci to, karya huce".
'Dan murmushi yayi ya sauka yana fad'in "wayo dai za'amin. yara fa?".
" taf ai wad'an nan tuni suka karya tun kana barci".
"Tofa lallai, yau kuma ba'a jira Abbu ba?".
" hhh aiko dai basu jirakaba, harma mai lesson d'insu yazo".
"OK, bara nima kiga na karya, fita zanyi naje nadawo da wuri, sonake yau na yini a gida ina
kallonku kawai".
" kai Nurri, saikace wad'anda zasu mutu?".
"Mutuwarma ai bamuda tabbas d'in rashin zuwanta my tee".
"hakane kuma Nurrina".


Bayan ya kammala break fast yay wanka, gayu sosai yaci cikin shadda galila brown color mai
duhu, yayi k'yau sosai, ya d'ora hular zanna bukar itama brown. Fateema dake fesa masa turare
sai k'od'a k'yan dayayi take.
Murmushi yayi yana kashe mata ido d'aya, " my tee fesamin turarennan sosai, wata k'ilma
nasamo ta hud'u".
Daina fosa turaren tayi, ta wani had'e fuska ta juya masa baya.
Dariya sosai yayi, har hakwaransa na bayyana, ya rungumeta ta baya yana mata magana a
kunne, "my tee... bakwason ta hud'un ne?".
Juyawa tayi suna kallon juna, ta d'ora d'an yatsanta saitin zuciyarsa, idonta akan face
d'insa, shima kallonta yakeyi yana murmushi, " Nurrina indai ina cikin nan ❤ ban damuba, kayi
in dai amaryace, ai kowa da halinsa zai zauna."
Rungumeta yayi yana murmushi, "my tee... Karyi kokwanto kinji, kinacan k'asan-k'asan
zuciyar Muhammad, babu kuma wata mace dazata iya tureki ko wacece ita kin gane".
Dad'ine sosai yakama Fateema, takuma rungumeshi tsam ajikinta tanaji kamar tashige
kawai ciki, a hankali tace, " I love you more my Nurri".
Shima a hankalin kamar mai tsoron ajisu yashiga jero mata kalamai masu kwantar da
hankali, kai kace itaka d'aice matarsa babu wasu.
Hakan da Alhaji Muhammad kema matansa yakesa kowacce d'aukar kanta itace mowa, Dan
duk matar data kasance tana tare dashi, yakan nuna mata soyayya tamkar ita kad'ai gareshi,
shiyyasa suke masifar kishi da juna, kowacce d'auka take anfi sonta da k'aunarta.
Shikam yanayin hakane danya saka kwanciyar hankali da farinciki a tsakaninsu, kuma
Alhmdllh yaci nasara da salonsa�.

Tare suka sakko falon k'asa, ya shiga 6angaren Aneesa.
A falo ya isketa tanama Siddiqa kwalliya, idonta a k'ofa harya shigo dan tunkan ya shigo

k'amshinsa yayo gaba, ba k'aramin d'aukar hankalinta kwalliyarsa tayiba.
Ta sakar masa murmushi, shima ya maida mata murtani yana zama kusada ita.
"Dear irin wannan d'aukar wanka haka? ina zuwa?".
" zanje Jos ne wajen amarya".
Baki tad'an ta6e badai tace komaiba.
"Ko bak'yason najene?". 'yay maganar yana d'aukar Siddiqa dake cinyarta'.
"ni a suwa dazan hanaka zuwa wajen matarka?".
Kusada ita yamatsa sosai, yasa hannu d'aya ya sak'alo k'ugunta dashi tareda kuma
mannata da jikinsa, "ke a matata wadda nake tsananin so mana my Neesa".
Kallonsa tayi tana wata dariya ban yardaba.
Goshinta da la6annta ya sumbata yana kuma mannata jikinsa da fad'in " kobaki yardaba ne
my Neesa?".
"Humm dear kenan, zaka wajen wata kuma kanamin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login