Showing 45001 words to 48000 words out of 109227 words
Chapter 16 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf
tare da sati d'aya zata fara school d'inta.
Tun kuma daga wannan lokacin ko Uncle ya kira Amatallah a waya bata d'agawa, daga
k'arshrma saita kashe wayar baki d'aya. a ganin inta d'aga bazata iya masa maganaba, dan sai
a yanzune batun Auren nasu ke matuk'ar damunta, dan ta tabbatar da gaskefa akeyi Uncle
yazama mijinta. Abin ya damu Uncle M.A matuk'a, da rashin d'aga wayarsa da Amatallah keyi yana cin
zuciyarsa, daga k'arshe ma saiyabar samuntaba kwata-kwata
___________________________
Aneesa na zaune kusada Alhaji Muhammad dake shan fruits salad data had'a masa na bud'a
baki, (dan duk litinin da alhamis d'in duniya sai yayi azumi), tsaf take cikin kwalliyar d'aukar
hankali, Siddiqa na gefe zaune (danta fara zama) an barbaje mata kayan wasa.
Lokaci-lokaci yakan d'ago ya kalleta suma juna murmushi, haka Aneesa keso, takasance
daga ita sai Muhammad d'inta, shiyyasa wannan damar data samu take tattalinsa tamkar kwai a
cokali, a 6angaren kula da miji daga Aneesa har Fateema kowa kwararrene.
Kiran wayarsa da akayine yasaka Siddiqa tsorata harta fashe da kuka.
Su duka dariya sukayi, Aneesa ta d'auketa tare da d'akko masa wayarsa ta mik'a masa,
dama tana hannun Siddiqa ne tana wasa da ita cikin kayan wasanta, wayar ta fad'a jikintane
babu zato kuma aka kira, sai ringing d'in ya tsoratar da ita shine ta razana.
Hakanne yabama iyayenta dariya.
Har wayar ta tsinke Alhaji Muhammad bai d'agaba saboda dariyar da Siddiqa ta basu, sai da
ta tsinke sannan shi ya kira, dama Jabeer ne ya kirashi.
Bayan sun gaisa ya tambayi jikin baba da sauran abubuwa.
Jabeer yace komai Alhamdllhi.
"To masha ALLAH, akwai matsalane?".
" eh to Yaya matsalarnan kam Alhmdllhi babu ita, sai sai kawu Hafizu ne ya kirani, wai akan
punches d'in Amatallah ne, yace na tura masa Account Number d'ina zai turo kud'in daza'a saya
mata anan Kano basai ansha wahalar saye daga can jos ba. shine nace masa to yad'an bani
lokaci ina office amma zan kirashi. to shine nakiraka na sanar maka". "ALLAH sarki Hafizu, to in banda abunsa ko dai Isma'il nada rai ai inaga nine maima
Khadija kayan d'aki ko, wannan maganarma a barta kawai, dama nayi niyyar maka magana
akan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu kuje kai da maijidda Ku za6o mata duk wani abinda ake
buk'ata". " OK Yaya babu damuwa, shi yazan cemasa yanzun kenan?".
"Ka barni dashi zan kirasa kawai".
" hakan yayi to Yaya".
"Yauwa, waifa jiya saina manta na sanar maka inason nafara turo kaya daga nan, muga
kuma abinda ALLAH zaiyi".
" kai Yaya wlhy nayi farin ciki, dama inata tunani akan kaje garin Business amma banji kana
maganar d'ebo mana hajaba, ashe abin na ranka".
Dariya Alhaji Muhammad yayi yace, "tom zan turo maka wasu kaya ta WhatsApp ka gani,
idan sunyi saina turosu k'arshen watannan mugani koza'a fad'a".
" to ALLAH ya tabbatar mana da alkairi Yaya".
"Amin Jabeer, ya Shehu fa? yana zuwa kasuwan kuwa?".
" da dai yafara wasa kam, amma tunda innani tamasa magana saiya maida hankali da
zuwa sosai, kuma Alhamdllh zuwan nasa yana d'auke hankalinsa dan naga kamar
shaye-shayen ma yarage".
"Alhmdllhi, ALLAH ya shirya manasu baki d'aya".
" amin Yaya, a gaidamun Siddiqa da Anty Aneesa".
"Ok, zasuji, inka koma gida zan kiraka muyi magana da baba da innani".
" shike nan saina koma d'in".
Daga nana suka yanke wayar.
Duk wayar nan da yakeyi babu Aneesa a wajen, tatashi tunda yafara wayar saboda kukan
Siddiqa, har kuma yagama bata dawoba saboda tsayawa lalla6a Siddiqa tayi barci datayi.
Har ya kammala shan fruits salad d'in bata dawoba, yashiga toilet d'in falon yay alwala yafita
sallar Isha'i a masallaci..............✍
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce_*
____________________
*_Number 18_*
____________________
Rashin samun Amatallah a waya yana k'ara damun Uncle M.A, sai yake ganin kamar tana
cikin k'unci da damuwane.
Yarasa wazai kira yahad'asu.
Duk da yakira kawu Hafizu akan pinches d'in Amatallah d'in, yakuma nuna masa koda da ran
Isma'il shine ya cancanci yama Amatallah kayan d'aki aii, bare kuma yanzu ma amatsayin
matarsa take.
Da k'yar kawu Hafizu ya amince, amma dukda haka yace zasu mata kayan ketchin, dole
Uncle M.A ya amince da hakan.
Duk da bawani gagarumin biki za'ayiba dai sunyi shiri bakin gwargwado.
Su Anty Sadiya nata bama Amatallah magunguna, amma saita faki idonsu ta zubar batasha,
duk basusan ta6argazar datakeyiba.
Ahaka dai yarage saura kwana biyu kacal.
Sosai Amatallah ta birkice musu, sai lallashinta kowa keyi daban baki, hardai ranar kaita
kam batama da lafiya. Zazza6i sosai da ciwon kai sun addaba mata, harma k'ara narkewa
takeyi wai koza'a d'aga.
Amma saitagama sai kuma shiryawa sukeyi. Ranar daza'a kaita gida yacika da dangi da
makwafta, akad'anyi shagali na mata kawai a cikin gida.
Da k'yar Anty Furera tasaka Amatallah tayi wanka, babu zancen kwalliya dantak'i amincewa,
farar hodama dak'yar tayarda ta shafa.
Kusan k'arfe 11am saiga mutanen Kano sunzo d'aukar amarya, sai dai gayyar duk abokan
Jabeer ne, kaikace shine angon, saikuma samarin family d'insu da mata kad'an su Anty
Maijiddah da Nazeefa da Gwaggo Rakiya, saikuma wasu dangin baba na sokoto, dan sunzo
suma. Amatallah tasha nasiha wajen iyayenta, kuka kam ai ba'a magana, dan kowa saida ya
tayata ranar, kodan tuna iyayenta.
Ahaka aka d'akko Amarya Amatallah sai Kano, (gashi ango baya kusa bare yay lalashi).
Kai tsaye gidan Uncle M.A aka wuce da ita, sun iske gida cike taf da dangi na Sokoto dana
nan Kano, makwafta da abokan arzik'i, (dan biki sosai sukayi abinsu dukda babu ango), nanfa
gida ya rud'e da tarbar amarya 'yar k'amshi, aka rakata har d'akinta.
Masha ALLAH na fad'a, dan ganin yanda aka tsara 6angaren nata, lallai Amatallah 'yar gatan
Uncle d'inta, komai Pink colour ne da milk kad'an, (Uncle yadad'e da sanin Amatallah nason
pink sosai, shiyyasa yace komai Jabeer ya d'auki pink). Aikam Kodai mak'iyi yagani dolene ya
yaba, dan komai yayi acan-acan a talauce ba'a sarauce ba. Sunci sunsha Alhmdllhi, duk kuma sun yaba da karamcin da akai musu, musamman ma na
Fateema, dan tanata rawar gani gaskiya.
Amatallah kam tak'i yarda taci komai sai kuka take. Sai da k'yar Nazeefa da Asiya suka
lalla6ata tasha fura da Nazeefa tasayo mata.
Da daddare koda Uncle yakira yace Nazeefa tabama Amatallah wayar.
Nazeefa batace mata komaiba tasaka mata wayar a kunne kawai, dansu ukune a d'akin,
'yan rakiyarta duk suna d'aya d'akin 6angarentan, Asiya kuma tayi barci saboda gajiyar tafiya..
Saukar Muryarshi kawai taji acikin kunnenta.
A zabure tatashi, jikinta har wani rawa yake, azatontama koyana a d'akinne, ganin Nazeefa
zaune kusada ita da waya a hannun saita saki ajiyar zuciya.
Nazeefa kam dariyama tabata, amma saita gumtse batayiba, tasake mik'a mata wayar, dan
Uncle nakan layi bai kasheba, "kar6a mana Amatallah, yanafa jiranki".
Kunyar Nazeefa takeji, shiyyasa ta amshi wayar tasaka a kunne. Nazeefa kuma yashiga
toilet d'in d'akin.
Sallama yasake mata.
Dak'yar ta iya amsawa, muryarta na rawa, hawaye harsun fara zirara a kumatunta.
Jikinsane yay sanyi, yatashi daga kwancen dayake yafito corridor d'in falon, Aneesa da
fitowarta kenan daga ketchin ta had'o masa shayi tabishi da kallon, rantane ya 6aci, ita tamayi
zaton Fateema Ce, dan batasan yau Amatallah zata tareba.
A kujerar dake corridor d'in ya zauna, muryarsa a matuk'ar sanyaye yace, " My best! kuka
kikeyi dan kindawo gidana da zama?".
Kanta ta girgiza masa tamkar tana gabansa batareda tace komaiba.
Jin bata amsaba, saidai shashshekar kukanta yake jiyowa yace ''kinason nima namiki
kukan?".
Da sauri tace, "A'a Uncle na daina".
" haba Khadija! Bak'yason zama dani?".
"A'a inaso Uncle". tayi maganar da fashewa da kuka.
" to Amma miyasa kike kuka Khadija!? ".
" ba komai Uncle, ina tuna su babane".
Ajiyar zuciya yayi, Yakuma raunana muryarsa sosai, "kiyi hak'uri Khadija kinji, badan ALLAH
baya sonki bane ya d'aukesu, Kimusu addu'a ba kukaba, su tasuma tayi k'yau, dan koba komai
mutuwar shahada sukayi, wannan kad'ai ya Isa muyima su brother murna ba kukaba kinji ko?".
" to Uncle zan daina insha ALLAHU".
''Yauwa my best, yanzu ki share hawayenki kinji ko".
"To" ta amsa tana share hawayen tamkar yana ganinta.
"Yauwa babyna kokefa, yanzu dai fad'amin kobak'yason zama Kano nasa Jabeer yamiki
visa ki dawo nan Inda nake?".
Da Sauri tace, " A'a Uncle, inason nan, ba makaranta zanjeba?".
"Makaranta zakije my best, amma sainake ganin kamar bazaki iya karatunba, saboda
damuwar dakike ciki".
''Wlhy Uncle zan iya, inason karatu, indai kukane na daina bazan sakeba".
" promise".
"Promise Uncle".
" tom ngd, yanzu kinci abinci ko?".
"Eh nasha fura".
" fura aiba abinci bace my best, nasan tunda aka sake tarewarnan bak'yacin abinci ko?".
"Inaci Uncle".
" kai ban yardaba".
"ALLAH kuwa".
" to shikenan, yanzu mikike sha'awar ci nasa a kawo miki?".
"Babu komai Uncle na k'oshi, furan ya isheni".
" kin tabbata".
"Eh Uncle, ALLAH kuwa".
" shikenan, karna kumajin kinyi kuka, yanzu kitashi kiyi wanka, saikiyi alwala kiyi nafilfili da
karatun alku'ani, insha ALLAH zakiji zuciyarki tayi sanyi da salama, kima su brother addu'a,
ALLAH yay miki albarka kinji".
"Amin Uncle, ngd zanyi to".
''Yauwa my best D.., saida safe ko, zan sake kira bayan kin kammala naji kinbar kuka ko an
karya alk'awarin Uncle bawan ALLAH".
hannun tasaka tarufe fuskarta kamar tana gabansa, ta saki wayar a kan gadon, dariya yayi
ya kashe wayar, dan yanajiyo mutsu-mutsunta kasancewar sabuwar katifa ko ledar ba'a cireba
aka shinfid'a bedsheets d'in.
Nazeefa ma dake tsaye a bakin toilet dariyar tayi, aranta tana jin sha'awar wannan soyayya
ta uncle da d'iyarsa, a ranta tace ALLAH ya daidaita komai cikin sauk'i Amatallah. K'arasowa
tayi ta d'auki wayarta, saitaga yakashe, ta kalli Amatallah dake shirin sauka a gadon tayi
murmushi. Batace mata komaiba tafice d'akinta.
Duk yanda Uncle yace haka Amatallah tayi, ai kam Alhmdllhi tasamu nutsuwa, saigata
suna 'Yar hira da Asiya data farka har barci ya kwashesu.
Washe gari akayi walima 'yan jos suka koma da yamma, bayan sunje gidansu Uncle sun
gaida baba da jiki.
Shatara ta arzik'i Uncle yasa Jabeer ya had'a musu, sun tafi sunbar Amatallah Na kuka
tamkar ranta zai fita Anty Maijidda da Nazeefa sai lallashinta sukeyi, daga k'arshe dai saida aka
kira Uncle yay lallashi da tuna mata alk'awarin datayi Na ta daina kuka sannan tayi shiru, amma
sai zazza6i mai zafi ya rufeta, dole jabeer ya nemo mata Magani tasha.
____________________________
Tunda Aneesa ta fuskanci Amatallah Ce ta tare saita hau zum6u-zum6ure wa Alhaji
Muhammad.
Shareta yayi, yay tamkar baisan mitakema fushinba, saima ya maida hankalinsa wajen yima
Siddiqa wasa, da daddare kuma yakira Fateema tabama yaran sukasha hirarsu. yakira Nazeefa
tabama Amatallah tace tayi barci, saboda maganin datasha da yamma, da k'yarma tayi salloli
takoma ta kwanta. sallama yamata ya yanke wayar.
_____________________________
Rayuwa tacigaba da tafiya cikin Nasarori da jarabawa, yau kwanakin Amatallah hud'u agidan
Uncle d'inta.
Kullum da safe takanje har d'aki ta gaida Fateema, ta taya Nazeefa aikin gidan tana k'ara
nuna mata komai yanda zatayi, Dan Fateema bata iya aikin saboda laulayin datake fama dashi,
dama ita haka take fama a farkon kowanne ciki.
Ita Nazeefa ma hakan dad'i yamata, Dan koba komai Amatallah zata kuma koyon abubuwan
dasuka dace sosai takuma kware da wahalaryi kafin mijin nasu ya dawo.
Yaran kuwa sun maida 6angaren Amatallah nanne wajen zamansu, itakam jansu takeyi
ajikinta sosai, Dan tana kallonsu tamkar k'annenta, kuma hakan Na sakata Nishad'i sosai,
saboda ta tashi ita kad'ai kwallin kwal a gidansu, babu Yaya babu k'ani, su Ammine komai nata,
shiyyasa shak'uwa tashiga tsakaninsu sosai wadda taketa wahal da ita har yanzun. Uncle kam yana kira a wayar Nazeefa yace abata, wani lokacin dataga Nazeefa da wayar
saita shige toilet d'in k'arya, har sai yagaji ya kashe, sai idan Nazeefa ta rutsatane sanan take
amsar wayar.
Ganin kamar yana takura mata saiya rage kiran, koya kira Nazeefa baya cewa abata.
Aneesa kam bayan tagama fushinta ta sakko Dan kanta batareda ya kula da lamarintaba,
danshi tausayi da dariya take bashi..
*_one Week ago_*
Sati d'aya cif da tarewar Amatallah tafara zuwa school, Jabeer dakansa yakaita a motar
Uncle.
Sanye take cikin shigar mutunci, dantasha gargad'i wajen Uncle sosai. Atanface siket da riga
porpul mai haske da ratsin pink kad'an da bak'i, saita saka pink d'in hijjabi mai hannu iya gwiwa,
ta saka d'an abubuwan dabaza'a rasaba a cikin pink d'in lady's bag, takalman tama flat pink,
duk da bawata kwalliya tayiba tayi k'yau sosai, sai k'amshin turarenta marar k'arfi dake fita
k'ad'an, inba ma kusada ita kakeba bazakajiba kam.
Gaba ta bud'e zata shiga Jabeer yace, "a'a shiga baya abinki Amatallah".
Kunyace ta kamata, ta duk'ar dakai tana murmushi, a hankali tace, " a'a Yaya Jabeer, kabari
Na zauna a gaban kawai, kaiba driver d'ina bane".
Murmushi kawai yayi shima, yabud'e mata murfin motar tashiga gaban sanan yatada motar
suka fice daga gidan.
Motar tayi tsit, babu mai magana acikinsu, Jabeer yamaida hankalinsa ga tuk'i, itakam
Amatallah kalle-kalle kawai takeyi tana sauraren redio daya kunna har suka shiga cikin BUK.
Tunda suka shigo take addu'oin Neman nasara a rayuwar wannan makaranta dazatayi.
Guri Jabeer yasamu yay parking, har Amatallah zata fita yace, "ki kunna wayarki Ya
Muhammad yace zai kiraki".
Kanta ta jinjina masa batareda ta juyoba.
Atare suka fito, Amatallah nata kallon mutane dake kai kawo, wasu 'yan mata da samari
wasu kuma samari zalla, wasu 'yan mata zallah, kowa dai da abinda yakeyi. wasu kuma daga
cikinsu duksun zuboma su Amatallah idanu, hakanne yasaka Amatallah duk'ar dakai, Dan ita
irin mutanen nanne da basu cika son taron jama'a ba. Jabeer ya kalleta yace, " muje".
gaba yay tabishi abaya har zuwa wani Office. sai da yayi Knocking aka bashi izinin shiga
sannan yashiga Amatallah Na binsa abaya.
Mutumin dake zaune a office d'in wanda da alama shine mamallakin office d'in koda ba'a
fad'aba, ya fad'ad'a murmushinsa da fad'in "Jabeer kun iso?".
Jabeer ya amsashi da " eh yaya Lawan".
Ta gefen ido Amatallah ta kalleshi, shima dai zai iya kaiwa sa'an Uncle d'inta. sai dai yafi
Uncle