Showing 18001 words to 21000 words out of 109227 words

Chapter 7 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

yakema doctor.

Babu 6ata lokaci komai yagama kammala, aka kai su Ammi cikin Ambulance, dukda itad'in ta
rasu, amma doctor Joshua yakasa fad'ama Uncle M.A d'in.

Amatallah kan a motar Uncle M.A aka sakata, haka sukatafi zuciyar uncle cikeda rauni,
lokaci-lokaci yakan juya ya kalli Amatallah dake kwance a baya tamkar gawa....



*************

Tafiyar Awa 3½ ce ta kaisu garin Kano, kai tsaye asibitin Aminu Kano suka wuce.
A cikin gaggawa kuwa aka kar6esu, saboda ansan da zuwansu, tunkan subaro jos Uncle M.A
yakira doctor Shu'aibu ya sanar masa zuwansu. Wannan yasaka suka Tatar da komai a ready,
su kad'ai ake jira.
Amatallah ma anbata gado, Dan har zuwa yanzun batasan ina kanta yakeba.
Sai da Uncle M.A yaga komai ya dai-daita sannan yatafi gidansu danya sanarma iyayensa.
Yana shirin shiga mota doctor shu'aibu yafito da sauri yana nemansa. hangosa dayayi yana
shirin shiga mota yasashi fara kwala masa kira.
"Alhaji Muhammad! Alhaji Muhammad!!".
Harya saka k'afarsa d'aya ya fito, ganin doctor shu'aibu Na tunkaroshi da sauri sai gabansa
yashiga fad'uwa.
Doctor shu'aibu yak'araso, "sorry Alhaji Muhammad Labbo! na tsaidaka, so dama.......
Sai kuma yay shiru.
"Ina jinka doctor, mike faruwane?".
Tsayuwa doctor ya gyara, sannan cikin damuwa yace, " sorry Alhaji Muhammad, ko kasan
macen tarasu?, kamarma tun kusan a wanni 22 dasuka wuce".
A sanyaye Uncle M.A ke kallon doctor shu'aibu, ya dafe kansa dayaji yafara sara masa.
Hak'uri doctor yafara bashi, tareda lallashi da masa Nasiha.
Uncle M.A baice komaiba yashiga motar, kansa ya kifa a sitiyarin motar yafara hawaye.
Kusan mintuna 7 sannan yad'ago, motar ya tada yabar asibitin.

______________________________

Tunda yashigo gidan Innani dake tsakar gida tana alwalar magriba kebinsa da kallo.
Jingina yayi da bango, batareda ya saniba hawaye suka fara bin kumatunsa.
Da sauri Innani ta k'arasa alwalar, "kai lafiyarka kuwa? Da girmanka kake kuka? Miya faru,
yaushe kadawo ma?".
Yanda Ammi ta jero masa tambayoyin saiya samu kansa dakuma fashewa da kukan.
Shiru Ammi tayi tana kallonsa, jikinta sai rawa yakeyi.
Cikin d'an daka tsawa tace, " wai baka jinane?".
Share hawensa yayi, sannan yashiga bata labari.
Innalillahi ...... Kawai Innani ke iya ambata.
Baba na daga d'aki duk yanajinsu, saidai baya iya fitowa sai an fiddoshi, maganar Uncle M.A
bak'aramin girgizashi tayiba kuwa.
Ana cikin haka saiga Jabeer yashigo shima, nan suka had'u sunata jimamin abin, jabeer
ma harda kukansa rurus.

Bayan Uncle M.A yashiga sun gaisa da baba, shima yak'ara masa bayani sannan yatafi
gidansa danya d'an kimtsa sannan yakoma kar Amatallah ta farfad'o babu kowa a
kusa............✍




_Dan ALLAH ina rok'onku Ku ringa turama masu cigiya, saboda ALLAH banida time d'in turama
kowa ta PC, amin afuwa saboda uzurina, hakanne zaisa nasan kuna k'aunata�._




One luv my fans





*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu�_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce_*



*_Duk naga comments naku, kuma sun k'ayatar dani gaskiga.sai dai wani Abu yasakani
dariya matuk'a, kunsan minene?. Masu cewa Uncle M.A yama Amatallah tsufa�._*
*_Wai miyasa abinda zai iya kasancewa gaske Reader's ba kuson ganinshi a Novel's?
Abinda na sani kuka sanine, ko a zahiri mai shekarun uncle M.A ba tsoho baneba, kisamu wani

a anguwarku mai d'iyar dazata iya kaiwa 18years, tazam kuma itace d'iyarsa ta Fari ki k'iyasta
dashi, ko Wanda yakai shekara 60 yana auren budurwa ai, balle 47years, kuma ko a cikinmu a
kwai wad'anda mazajensu suka kai wad'an nan shekarun, my Abdull ma shekarunsa
kenan�._* _mu rubuta abinda azahiri zai iya zama gaske kuce bai daceba, muyi Wanda mu da Ku
kunsan bazai yiwuba Ku zagemu kuce muncika k'arya ko._
_koma Yaya dai ALLAH yabar zuminci, Dan mu daku duk munacin amfanin junane, inba mai
karatu babu abinda zaisa Marubuci 6ata lokacinsa, hakama inba Marubuci mai karatu bazai
samuba littafinba, mun gode sosai, irin Trillion's d'innan._




____________________
*_Number 10_*
____________________

An gudanar da zana'idar iyayen Amatallah a gidan mahaifan Uncle M.A, Innani tasha kuka
lokacinda taga gawar Isma'il da matarsa a shinfid'e, lallai duniya batada tabbas ko kad'an.�
Wandama ya d'aura d'ammara da ita saiya kwance.
Babama yashiga rud'ani sosai, dan sai da ciwonsa yayi tamkar zai motsa, sai allurar barci
akai masa.
Har aka binne su Uncle M.A na kuka, koda suka dawo daga mak'abarta d'akin Jabeer
yashige ya kwanta, kuka yake tamkar ransa zai fita.
Dolene ka gansa kaji tausayinsa. shima dai daga k'arshe dole allurar barcin Jabeer yasaka
akai masa.


*_Two days later_*

Alhmdllh yau kwanakinsu Baban Ama biyu a k'asa, amma Ammi kwananta uku da
rasuwa.
Duk da 'Yar Nutsuwa tazoma su Uncle M.A hakan bai hanashi warewa gefe yasha kukaba
wani lokacin, musamman inyaje asibiti duba Amatallah da Nazeefa ke zaune da ita, dawata
k'anwar Innani, gwaggo Rakiya.
Har yanzu Amatallah bata farfad'iba, dan doguwar suma tayi, amma tana samun kulawa
daga likitoci sosai.


_______________________________

*_Jos_*

A jos kam lamari yayi k'amari, k'ank'anin Abu yajawo mutuwar d'aruruwan al'umma da
asarar dukiyoyi, abinda yafaru akan SIYASA dalilin wasu marasa jin magana ya rikid'e yazama
fad'an k'abilanci da addini.
'Yan jaridu da kafafan yad'a labarai na social media sai baza rahotannin k'arya sukeyi,
anrasa jin jinar magana akan dalilin wannan rikici na *SIYASA KO K'ABILANCI!?*.
A dalilin hakan kuma wasu gur6atattun matasa masu ruguza zaman lafiya suka kuma tada
rikici a KADUNA, ik'irari sukeyi wai ankashe 'yan uwansu dake jihar Jos, dolene suma su d'auki
fansa.
Ba'awani ja danisaba Kano ta d'auka, babu gaira babu sabar nanma wasu bara gurbin
matasan suka haikema wasu k'abilu dake killace awata anguwa da ik'irarin d'aukar fansar
abinda akaima 'ya uwansu a Kaduna da jos.
Abinda yafaru a kano yabama k'abilun kudancin k'asar suma tada tasu husumar, suka fara
kisan 'yan arewacin k'asar a nufin d'aukar fansa‍♀.


_hum wane irin tunanine da matasan k'asarmune? Mike shiga kanmune? Muke za6ama kammu
da k'asarmu irin wannan rayuwar? Wace riba mukeci ko nasara idan mun girmama irin wannan
rikice-rikicen dabumuma San tushensuba, karfa Ku manta idan ta rikice da kai da ni duk
bazamu shaba, ahalinka da nawa babu Wanda zai tsira, dukiyar k'asarmu zata ruguje,
karatunka danawa Dana 'ya'yanmu duk zai zama labari, watak'ilma kaida kazama jagoran
fad'ad'a tashin hankalin kaine zaka fara mutuwa ko ahalinka, Ku kalli gagis, zike, k show, dasu
aka fara, an tarwatsa ahalinsu da basujiba basu ganiba, Amatallah dabatasan tushen rikicinba
an rabata da iyayenta, an tarwatsa mata family saboda son zuciya irinna gur6atattun
matasanmu, wad'anda mugun tunaninsu bayasa mu d'aukesu a jerin masu amfani da amfanar
da k'asarmu, basuda buri saina haddasa rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI!?* Saboda son
zuciyarsu, kullum zuciyarsu na karanta musu AMUTU KO AYI RAI ba damuwarsu baceba, da
ance an kad'a tambarin SIYASA saikaga jikkunan matasan k'asarmu na rawar Mazarin
shirye-shiryen duk yanda takama, basuda zuciyar k'yak'yk'awan fata wa k'asarsu ko nagartar
ginata ta hanyar zarran mazatankar samartaka na k'uruciya da ALLAH yabasu. miye ribarka
idan an siyeka dawasu 'yan kud'ad'e dankayi jagoranci wajen hallaka ahalinka da k'asarka?
Wadda bakada kamarta, bakada Inda yafita, duk Inda zakaje saikazama abin tsangwama da
gudu , watak'ilma akiraka d'an ta'adda mai lasisi, bakada damar shan ruwan wata k'asa cikin
salama tunda ba k'asarka baceba._
Yanzu haka wad'anda suka baka kud'in duk 'ya'yensu basa k'asarma, sannan su sunada
tsaronda babu wani mahalukin daya Isa ya tunkari gefen anguwanninsu ballema yasamu ganin
su, amma kai anbaka kud'in siyen ahalinka batareda kayi dogon tunaninaba, basuda Matsala da
watsewa ko tarwatsewar k'asar, dan sunada isassun kud'ad'e a ciki da wajen k'asar, sunada
lasisin zuwa kowacce k'asa su warwasa batareda an tsangwamesu ba kamarkai daza'a kafama
tantin d'akunan tamfol ko buhu ko katako a filin ALLAH ana kiranku da suma *'YAN GUDUN
HIJIRA*�.
Abincinma dazakaci ko ruwa saiya gagareka, ballantana maganar lafiyarka ko akasinta.
Haba matasanmu, kudawo cikin hankalinkufa, kubar yadda da 'yan jari hujja masu amfani
daku wajen amfanuwarsu suna haddasa fad'ace-fad'acen addini ko SIYASA da K'ABILANCI ta

sanadinku, ni da ku damuke a arewaci da kudanci duk munada ikon canja mummuna zuwa
k'yak'yk'yawa, duk Wanda kagani Asama mune muka kaishi, kuma munada ikon ingizoshi k'asa
ayayinda muka fuskanci d'an wawasone akan abinda yake mallakinmu, da wahalhalinmu suke
tak'ama da baza riguna da cin zarafinmu suna zare idanu, to muma saimu gyara domun gyaro
abinda ke cin dunduniyarmu, mukiyayi saidai RAYUWARMU akan rikicin SIYASA KO
K'ABILANCI da wasu tsiraru ke jagorancin haddasa mana domin cimma wani burinsu akanmu,
sai matasanmu sunyi gyaran halayensu sannan madafun iko da ragamar k'asarmu zata iya
dawowa hannunsu.
Wannan k'alubalen nakune matasanmu.
Amma ta sanadin zaman lafiya a k'asarmu da muhimmin sanin darajar kawunanku, kuyi fatali
da duk wani banbancin addini ko k'abila kuzo mu rungumi juna domin kawo sauyi wajen
tankad'e da rairayar duk wasu masu rusamu ta k'ark'ashin k'asa, karike na rike ki rike mu rike
hannun juna domin maida matasanmu jagorori akan madafun ikonmu�. Ta hanyar
zaman lafiya da k'aunar junanmu cikin zarrar amsa suna 'yan *NIGERIA* k'asa d'aya, uwa d'aya
uba d'aya.
Karmu bari mu ruguje daga ansa sunanmu na 'yan k'asa d'aya dalilin *SIYASA KO
K'ABILANCI*
Ko shed'ancin wasu jagorori masu nemawa Kansu mutunci kawai.


a wannan ga6ar dolene masu karatu susojin dangan takar dake tsakanin Alhaji Isma'il Uba da
Alhaji Muhammad.�
Kubiyo bilyn Abdul domin jin tushen labarin.�


____________________________

Alhaji Muhammad Ahmad Labbo, shine cikakken sunan Uncle M.A.
'Dane na farko daga Alhaji Ahmad Labbo.
Alhaji Ahmad Labbo cikakken basakwace ne d'an kasuwa, kasuwancine yakawoshi garin
Kano, a da yakanzo ya sari atanfofi yakoma sokoto, sai dai daga lokacin da tafiya tafara nisa
saiya dawo garin na Kano baki d'aya, yasamu shago a kasuwar kwari.
A nan Kano ALLAH yahad'ashi da matar aure Zainab (innani).
Shekararsu 1 da aure ALLAH ya albarkacesu da haihuwar d'a namiji, Wanda yaci sunan
Muhammad (Uncle M.A kenan). bayan Muhammad innani tasake Maijiddah, sai Barirah, (amma
ALLAH yay mata rasuwa), sai Jabeer,, Shehu, Nazeefa auta.
Gwargwadon iko 'ya'yansu sunsami tarbiyya, sannan sun tsaya tsayin daka domin ganin
sun sami ilimin addini dana zamani.

Muhammad yarone dayataso k'ark'ashin kulawar mahaifi, dan innani tana kawaici sosai
alamarinsa irinna 'ya'yan Fari, bata fad'ar sunansa, sannan kuma bakomaine take sakashi
acikiba
Amma a k'asan zuciyarta tana matuk'ar k'aunarsa fiyema da sauran 'ya'yanta.

Bayan kammala primary d'in Muhammad yadage akan boarding yakeson zuwa, babu
yanda iyayensa suka iya suka shiga cuku-cukun kaishi Government secondary school Bichi.
A canne ALLAH ya had'ashi da Isma'il Uba Salisu, Wanda rana d'aya aka kaisu makarantar,
shi an kawoshine daga Kusada local government dake jihar Katsina. tun daga wannan ranar
suka k'ulla alak'ar abota mai k'arfi, suna kiran junansu brothers.
Kowa a makarantar ya d'auka 'yan uwan junane makusanta saboda k'auna da tattali dasuke
nunama juna.
Ko kad'an Muhammad baya k'aunar yaga anta6a Isma'il, haka shima Isma'il d'in, idan aka
kama d'aya da laifi, akazo hukuntasa sai d'ayan yay tsale yace shine, dan bayaso ata6a lafiyar
d'an uwansa. idan kuwa d'aya bashida lafiya ai saika d'auka dukansune suke jiya. gaskiya
akwai k'auna mai k'arfi a tsakaninsu mai kuma ban mamaki. Kafin kace mi duk families nasu sunsan da wannan k'auna tasu. har yazam Isma'il kanzo
Kano Hutu gidansu Muhammad, haka shima Muhammad kanje jos ko kusada hutu........


Isma'il Uba salisu shine cikakken sunan Baban Ama, d'an asalin jihar jos ne, Dan anan
yataso yaga iyayensa,
Su biyu iyayensu suka Haifa, Amina itace babba, sai Isma'il. tun suna k'ananu mahaifiyarsu
ta rasu, babansu wanda suke kira da kawu yak'ara auren wata makirar mace mai suna
Huzaiyya, takan nuna k'aunarta a garesu agaban mahaifinsu, amma dazarar bayanan tashiga
gallaza musu kenan, makircinta yahana kawu fahimtar komai akansu. ana haka ALLAH ya
fiddoma da Amina miji, amma fatauci yake zuwa jos shi d'an katsina ne a kusada L.G. wannan
yasa koda akai aurenta sai aka kaita Kusada.
Tunda Amina tayi aure sai Isma'il yakuma shiga uk'ubar huzayya, wannan yasakashi tada
hankalinsa akan shi akaisa wajen 'yar uwarsa Amina. Mahaifinsu bai fahimci komaiba, shi duk
tunaninsa Isma'il na kewar Amina ne. Haka ya d'akko Isma'il da kansa yakawoma Amina
danufin yayi hutu. Sai dai koda hutun Isma'il ya k'are saiya dage akan bazai komaba, kawu yay
lalla6ar duniya Isma'il yace bai komawa. haka dole kawu yabar Isma'il awajen Amina.
Mijin Amina ne ya nemawa Isma'il makarantar boarding ta Bichi danya cigaba da karatunsa,
tunda yagama primary a jos.
Daga wannan lokacinne kuma suka had'u da Muhammad labbo, Wanda yazame masa d'an
uwa kuma aboki.
Idan anyi Hutu Isma'il yakan fara zuwa kusada ne yay kwana biyu sannan ya wuce jos. Wani
lokacin kuma a kano yakeyi gidansu Muhammad, a wani karon kuma su wuce jos shida
muhammad d'in suyi acan bayan sunje kano, kokuma kowa yatafi gida, sai bayan kwanki kamar
uku zuwa hud'u saiya tafi gidansu d'an uwansa hutun. har lokacin kuma Amina bata haihuba.
Ahaka suka kammala karatunsu Na secondary, sun rabu cikin damuwa sosai alokacin, Dan
kokad'an basuyi murna da graduate d'in nasuba.
Kwanaki bakwai kacal dayin candy d'insu Muhammad yakasa hak'uri yashirya sai jos, sosai
Isma'il yay farin cikin ganinsa, hakama kawu.
Har zuwa yanzu huzayya tananan da makircinta, amma zuwa yanzu Isma'il baya d'aukar
raininta.

Haka suka maida Kansu kulum cikin yawo daga Kano zuwa jos, har results d'insu ya fito,
suduka sunsami abinda suke buk'ata, wannane yasakasu farinciki.
Babu 6ata lokaci kuma aka shiga nema musu makaranta, cikin amincin ALLAH kawu
mahaifin Isma'il yay nasarar sama musu a University ta jos.
Wannan ne dalilin dawowar Muhammad jos da zama, sai lokaci-lokaci yakanje Kano.
Sun fara University babu dad'ewa ALLAH yayma Amina yayar Isma'il rasuwa, sosai rasuwar
ta girgiza Isma'il da kawu, hakama Muhammad danya santa sosai.

Rayuwar samartakar Isma'il da Muhammad abin sha'awace, dan zaratan samarine masu
kulada addini da kare Kansu wajen rud'in zamani da samarinmu ke jefa Kansu. Sun maida
hankali sosai akan karatunsu, kuma suna samun nasara sosai.
Suna a level two ALLAH yahad'asu da Khadija, yarinya nutsatstsiya itama, tunda Isma'il yaga
Khadija yafara k'aunarta, sai dai ya 6oye abin a zuciyarsa da burin saisun kammala karatunsu
ya furta mata.
Sai dai kash Ashe shima Muhammad ya kamu batareda sanin Isma'il ba, shikam yakasa rik'e
hakan a ransa ya furtama amininsa Isma'il.
Hankalin Isma'il yatashi sosai, saboda k'aunar Khadija yakeyi sosai, amma haka yayta
jarumtar dannewa, yabama brother d'insa kwarin gwiwwa da goyon baya 100%, shinema da
kansa ya sanarma Khadija soyayyar da brother d'insa kemata. batawani basu wahalaba ta
amince, dandanan soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Muhammad da Khadija. Isma'il kuma
yanata yak'in cireta a ransa, dan har k'asan zuciyarsa yagama aminta yabarma d'an uwansa
Muhammad ita.
Kullum Muhammad kan takura Isma'il akan yakamata shima yayi budurwa, yanda dasun
kammala karatu sai ayi bikinsu tare.
Dariya kawai Isma'il keyi yace katayani nema brother, nifa har yanzu ban k'yalloba.

Suna gab da kammala karatunsu saiga Saliha shima ALLAH yabashi.
Muhammad yayi murna sosai, yakuma k'arfafa d'an uwansa.
Alk'awalin ALLAH ya cika, su Muhammad sun kammala karatunsu, nanma ansha tata 6urza
akan komawar Muhammad kano.
Koda Muhammad yakoma gida sai mahaifinsa yajawosa suka cigaba da zuwa kasuwa,
ahankali Muhammad ya dilmiya a harkar, ya kware sosai tareda kawo canje-canje masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login