Showing 33001 words to 36000 words out of 109227 words

Chapter 12 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE BOOK By A'isha Galadima .pdf

Advertisement

Hannunsa kawai taji akan kumatunta yana goge mata hawayen, muryarsa can k'asan
mak'oshi yafara lallashinta.
"Kiyi hak'uri Khadija, mu kar6i jarabawar mu da hannu biyu, ni kaina ina cikin rud'ani wlhy,
bansan yanda zuciyata zata d'aukeki a matsayin matata ba, bayan kuma matsayin d'iya mafi
soyuwa kike dashi agareni, banida wata mafitane akan hakan, saboda alk'awarin rik'eki naima
Brother yayinda Numfashinsa yarage k'iris ya k'are daga gangar jikinsa." "Kullum cikin tunanin mafita nake, amma nakasa samowa, ni kaina inajin tamkar mun cutar
dake, gashi kuma bakin alk'alami yarigada ya bushe, dan banida damar ruguje alk'awarin
danaima brother bayan k'asa ta rufe idonsa. kiyi hak'uri, insha ALLAH komai zai zama labari,
lokaci na zuwa dazamu fara kallon kammu ni da ke amatsayin miji da mata kinji". Kai kawai ta iya d'aga masa.
Waya mai k'yau ya bata a kwalinta, " ga wannan ki rik'e, nasaka miki Number ta, duk
abinda kike buk'ata kobai mikiba ki kirani ki sanar mini, da nayi tunanin kicigaba da zama wajen
Innani harna dawo. to sai kuma baba yace hakan bai daceba, gara kawai a kaiki gidan, k'ila
kafin na dawo kin saki jikinki, ga ν ΌνΏ§ d'ina nan duk sanda kike buk'atar kud'i saikiyi amfani dashi,
Nazeefa zata dawo gidan itama harna dawo, karki yarda wani Abu ya had'aki da Aunty's naki
kinji, (duk da ma dai bayan tafiyata d'aya a cikinsu zata Bini) kibasu girmansu kamar yanda na
sanki, kuma kicigaba da hak'uri akan duk abinda za'a miki bai mikiba, (duk da dama nasan
ked'in mai hak'urice), duk Wanda yamiki wani Abu a cikinsu ki kirani ki sanarmin kinji."
Nanma kanta kawai ta jinjina masa.
"Yawwa my best D.. , ALLAH yay miki albarka, d'inkunanki nacan Nazeefa takai da duk
abinda kike buk'ata, banda wasa da karatu, banda tarkacen k'awaye, ki maida hankali sosai,
kuma dan ALLAH kirage yawan damuwarnan kinji ko".
Yanzuma kanta ta jinjina.
Yace, " kimin magana please naji mana".
Yanda yay maganarne yasakata murmushi, ta share ragowar guntun hawayenta, "ngd sosai
Uncle, ALLAH ya biyaka da mafificin alkairi, Yakuma Baka nasara akan abinda zaka nema".
" amin my best D..., ngd da addu'arki, yanzu miza'a bani dazan ringa tunawa".
"Uncle mikake so?".
" komai nasamu inaso my best D.."
Shiru tayi alamar tunani, zuwa can ta kalleshi, "Uncle kafad'a, ni narasa mizan Baka ai".

Murmushi yayi yana kamo hannun damarta.
Kallo tabishi dashi dantaga mizaiyi da hannun.
Bud'e yatsunta yayi sosai sannan yakai bakinsa tsakkiyar tafin hannunta ya sumbata.
Wani yarrr taji ajikinta, harda 'yar girgiza da runtse ido.
Ya d'ago yana kallon fuskarta da murmushi.
Saurin kama k'ofar motar tayi zata gudu. Yay saurin rik'o hannunta yana fad'in " yazaki gudu
baki baniba?".
Wata matsananciyar kunya da mamakin sane ya cika Amatallah, a zuciyarta tace dama
haka Uncle yake? naga ta kaina.
Ba yanda baiyiba amma tak'i juyowa ta kalleshi, ganin bazata juyo d'inba saiya zame
gyalen kanta tareda d'an kwalin.
Idanu Amatallah ta zaro waje dan mamaki wannan aiki na Uncle.....
Kafin takai k'arshen mamakinta taji ya zare pink d'in Ribbon d'in data d'aure tsaka tsakin
gashinta daba wani tsawone dashiba.
Yana zarewa tasamu ta fice, da gudu tashige gidan kakanninta da yayan Ammi da k'aninsa
ke ciki yanzu.
tabar Uncle da dariya.
Ribbon d'in ya saka a hannunsa sannan ya d'auki d'ankwalin atanfarta data bari ya d'ora a
cinyarsa, ya tada motar kawai yatafi, yanamai jin wani nishad'i dashi kansa baisan
ma'anarsaba...........✍🏻



�👎🏻







*_ALLAH ka gafartama Mahaifanmu�🙏🏻_*
[1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💑
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉

_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ceν Ύν΄™ν ΌνΏ»_*


____________________
*_Number 13_*
____________________

Da sallama ya shiga d'akin.
Amatallah dake zaune a bakin katifar Nazeefa tana canja rigar filo da sauri ta juyo tana
amsa sallamar cikin rawar murya. jikinta har rawa yakeyi.
Shiru yay yana kallonta. Sai yaji babu dad'i ganin yanda yanzu kamar tsoronsa takeji, saima
yazo gidan sau uku bata bari sun had'uba, yau ma yasan k'ila batasan yazo ba.
Murmushi gefen baki yayi, ya d'an kauda kwayar idonsa daga kanta saboda zanine kawai
da vest a jikinta.
''My best D......", sai kuma yakasa k'arasawa, yace, " kintashi lafiya?".
Da sauri tace, "Uncle sorry ina kwana".
Yanzun ma murmushin gefen baki yayi, kafin ya amsa, ya kuma kallonta kad'an, "bak'ya jin
sanyine? Kika zauna haka?".
Gaban tane yafad'i, tama manta da kayan dake jikinta, hijjab tajawo da sauri ta saka, wata
matsanan ciyar kunya takuma lullu6eta, saita koma ta zauna bakin katifar ta kifa kanta a cinya.
Zama yayi bisa wani stool dake d'akin, cikin sanyin muryarsa yace, " yanzu yaya kikejin
jikinki?".
Bata d'agoba, ta amsa da "naji sauk'i, sai dai yawan ciwon kai".
" tunanifa kenan my best?".
Kanta ta d'ago, idanunta cikeda kwallah ta girgiza masa kai batareda tayi maganaba.
Shima kan ya girgiza mata alamar kartayi kuka.
Ta saka hannu ta share hawayen dasuka fara bin kumatunta.
Mik'ewa yayi tsaye dan bayaso ta karya masa zuciya, yace, ''inaga zuwa Monday zan nema
miki school d'in dazaki koma, anfara Reghestiretion d'in SSCE, koba k'yason ki zana a wanan
year d'in sai next year?".
Share hawayenta ta shigayi tana murmushi, "a'a Uncle inaso zanyi".
Murmushi yayi saboda ganin tana kuka tana dariya, ya matso kusada ita Yakuma k'asa da
muryarsa kamar mai tsoron kar a jisu, yace, "kimin alk'awari to".
Yanda yay maganar sai bugun zuciyar Amatallah ya k'aru, ta d'ago manyan idanunta
dasuka yi d'an ja ta kalleshi.
Ya jinjina kai alamar ta amince.
" uncle alk'awari kuma?".
"Yes my best".
" uhm Uncle nami to?".

Komawa yayi inda yatashi zaune yasake zama kan stool d'in, "my best inason kimin
alk'awari zaki rage yawan damuwa, rashin kwanciyar hankalinki nawane, kukanki yana ta6amin
zuciya ainun Khadija, ki daure wajen kar6ar wannan jarabawar tamu, duk sanda kikaji zuciyarki
cikin k'unci ki d'auki alkur'ani ki karanta, su brother addu'armu suke buk'ata kawai a yanzu kinji". Kanta ta d'aga masa tana share hawaye, " uncle insha ALLAHU duk zanyi".
''Yauwa my dear, ALLAH yay miki albarka". 'Yay maganar yana mik'ewa'.
Amatallah tace, "amin".
Agogon hannunsa ya kalla yana fad'in " bara naje to, idan na dawo saimuyi magana ki za6i
school d'in da kikeso ko?".
"To Uncle, amma ko wacce kaza6amin tamayi".
"Shikenan, amma baradai Na dawo d'in".
Kanta ta jinjina masa, sannan tamasa addu'ar dawowa lafiya.
Yana murmushi ya amsa sannan ya fice.
A tsakar gida yatarar da Nazeefa.
"Lah Yaya dama kana gidannan?".
Murmushi yayi yana kallonta gaidashi tayi, ya amsa yana tambayarta babu dai wata Matsala
akan Amatallah ko?.
" eh wlhy Yaya tarege yawan kukan bakamar da ba, kuma danaga zata fara tunani sainayita
janta da hira danta saki jikinta, amma nakula kamar bata isashen barci".
"Nima nalura da haka kam Nazeefa, Dan tama min complain akan kanta yana ciwo".
" rashin barcine da tunani Yaya".
"Babu damuwa, insha ALLAH zan d'auki mataki, kedai kicigaba da k'ok'ari wajen rage mata
yawan tunani da damuwar, a satin nan zan nema mata school dazata zana SSCE d'inta, maybe
hakan yad'an d'auke hankalinta".
" yawwa yaya, hakan ma yayi sosai".
"Yawwa bara na wuce time Na tafiya, yau bazakije school bane?".
" eh Yaya. Yau bamuda exam......

Fitowar Shehu daga d'akinsa yana mik'a da hamma, babu zancen rufe baki a tsarinsa, dagashi
sai gajeren wando da vest.
kallonsa sukayi suduka.
Uncle M.A ya had'e fuska yana kallonsa, cikin daka tsawa wadda bata hana muryarsa fita da
sanyiba yace, "kai! Shehu!, wane irin iskancine wannan? zaka fitoma mutane tsakar gida da
boxer? kamar kai kad'aine a gidan?".
Shehu ya yad'an Sosa k'eyarsa yana duk'ar da kansa, " kayi hak'uri Yaya, ni bansan kana
gidanba ai".
"Lallai kam, wato sai ina gidanne zakayi shigar mutunci? Nazeefa da Amatallah ba
k'annenka baneba? kai bakajin kunyar su ganka a haka? to ni abindama nakeson na sani, sai
yanzu katashine kokuwa?".
Nazeefa tayi saurin " fad'in ALLAH Yaya sai yanzunne yatashi, da asuba babu irin bugun da
ya Jabeer bai masaba amma yak'i bud'ewa, hakama innani".
Harararta Shehu yayi, amma baice komaiba.
Cikin matuk'ar 6acin rai Uncle M.A yace, "wai Shehu mikakeso kazamane kaikuwa?

Wannan wace irin rayuwace kaza6ama kanka? gwargwadon iko kowa k'ok'ari yake dakai
agidannan kan kazama mutumin kirki, amma gakanan tamkar wanda bakin iyaye ke d'auniya
dashi? yanzufa ka kalli agogo kusan 7:30 amma bakayi sallar asubahiba, amatsayinka na
matashi mai lafiya, ko baba dake kwance yana jiyya kullum saiyabi jam'i a gida, kaje kayi tayi
wlhy, rayuwarkace, idan ka gyara kaine zaka anfana, idan kabari ta lalace asararkace, shekarar
k'arshe kake a makaranta amma yanzu haka yau kunada exam, kana kwance kana barci
k'ilama ko karatu bakayiba?".
" Yaya nafayi, dad'ewama danayi ina karatunne yajamin makara.....
"Rufema mutane baki kafin na sa6a maka kammanni wlhy, ina k'ofar gidan su Rabi'u kazo ka
wuce kaida abokanka kunata warin sigari, nasan baka ganniba ai, kuma koda na dawo gida
kwance na iskeka kana barci zakace wani karatu kayi. walhy Yaya idan yaronan bai tsallakeba
wannan karon karka kuma 6ata kud'inka akansa, banza kawai Mara amfani wa kansa bare
waninsa".
Jabeer ne mai maganar cikin k'unar rai da bak'incikin halin d'an uwan nasu daya biyema
abokan banza suna shashanci.
"Abinda dama na yanke kenan Jabeer, ka duba shekarun da yaronnan ya d'auka a
makaranta, tunfa Nazeefa na ss2 a secondary, gashi harzata kammala degree d'inta tareda
dashi, k'ilama takuma barinsa....
''Dan ALLAH Yaya karkace haka, insha ALLAHU zan dage nabar jami'a wannan year d'in,
kodan naga kunyi farinciki, kuyi hak'uri Dan ALLAH, kucigaba damin addu'a".
ALLAH sarki, d'an uwa rabin jiki, sai kuma tausayinsa ya kamasu, a raunane Nazeefa tace,
" please ya Shehu ka canja mana, kodan k'ok'ari da Yaya Muhammad keyi a kanmu kullum
shida ya Jabeer, ga halin da baba yake ciki, ALLAH abinda kakeyin nan yana k'ara saka
damuwa a ciwon baba, kai abin baya damunka ne?".
''Ya za ayi ya damesa Nazeefa? tunda duniya da abokan banza na kaimasa yanda yake
buk'ata, ALLAH ya shiryeka Shehu, kawuce kaje kai Salla rana na kumayi, ni bara na wuce
kasuwa".
"Yaya nagama karin kumallo fa, kazauna kaci dan naga yanda kafito da safen nan dawuya
idan kayi a gida".
"No auta, karki damu, ina saurine yau kayanmu suka iso, gashi zanje office yau, inada
meeting da lecturers".
Bai jira cewartaba yabama Jabeer hannu sukayi musabaha ya fice.
Dariya Jabeer yayi yace, " auta kema kinsan Yaya da abinci aii, nidai bani nawa na d'ora
natai aiki".
Itama dariyar tayi kawai tanufi ketchin.
Abincin kowa ta zuba takaikai musu, sannan ta d'auki nasu itada Amatallah.

Baba da innani duk sunajin abinda ke faruwa a tsakanin 'ya'yan nasu. hakama Amatallah
tana jiyosu, sai hakan yasata kewar families d'inta, dajin sha'awar inama tanada k'anne ko
yayye itama, ko babu komai ai zasu tattauna akan matsalolinsu suji sanyi, wannan tunanin ne
yasata kuka sosai. motsin shigowar Nazeefa yasata saurin share hawayen tacigaba da shinfid'a
bedsheet a kan katifar.

"Anty Nazeefa kin ganni har yau ban gama gyaran d'akinba".
Dariya Nazeefa tayi tana ajiye tiren hannunta, "inafa za'a gama mana gyaran d'aki, kunyi
bulum keda Yaya a d'aki kamar bakwa gidan kunata shan soyayya".
Cikin zaro ido waje Amatallah tace, " kai Anty Nazeefa, soyayya kuma? Uncle nefa". 'tak'are
maganar kamar zatayi kuka'.
Sosai Nazeefa take dariya, "yo Amatallah ai yanzun yatashi daga Uncle, yakoma miji, ba
laifi bane idan anyi soyayyar. Kinsan kuwa bala'in dacewar da kukayi keda ya Muhammad?
wlhy karki bari damarnan ta ku6ce miki, ya Muhammad garas yake tamkar wani d'an 30years,
yandama yakeda k'aramin jikinnan wasu d'auka suke ma Anty maijidda ce babba, kofa ya
Jabeer yafishi jiki. wama zaice ya Muhammad yanada mata biyu, koda yake uku fa yanzun". ta
d'agama Amatallah gira.
Baki Amatallah ta tura gaba, " Anty Nazeefa kibari Dan ALLAH, nifa ALLAH Uncle d'inane"
ta matso hawen dasuka taru mata a ido tunda Nazeefa tafara maganar.
Kusada ita Nazeefa ta zauna, ta dafa kafad'arta, "kiyi hak'uri Amatallah, nasan anan gaba
kad'an zakiso ya Muhammad amatsayin miji ba Uncle kad'aiba. na tabbata saiya nuna miki
soyayya maiban mamaki, dan soyayyar dayakema Yaya Isma'il duk zai tattara yahad'a da
wadda yake miki, ya Muhammad yanama ya Isma'il k'auna maiban mamaki, to yakike zaton
kuma kasancewarki matarsa jinin masoyinsa ya Isma'il?, gakuma ke kanki dama yanda yake
sonki sosai tamkar 'ya'yansa. lokaci kawai muke jira na ganin hankalinku ya kwanta dagake
harshi, dan har yanzu duk kuna cikin rud'anine na abubuwan dasuka faru, amma nabaku
shekara d'aya zuwa biyu kacal, insha ALLAH sai kunzama abin kwatance a duniyar masoya. Ke
dai kawai ki koyi yanda zaki zauna da matansa, dan gidan ya Muhammad zama akeyi namasu
ilimi da kissa, kowacce jitake da kanta akan tayi karatu mai zurfi, saiki dage sosai akan
karatunki, tunda inada tabbacin yaya bazai barkiba kema, zai maidaki makaranta, fatana dai
kirage wannan sanyin naki, dan zama dasu Anty Aneesa sai jaruma, kuma mai wayo. Zan
cigaba da baki haske a zaman mu, yanda kema zaki kwaci 'yancinki a hannun mijinki, harma
kizama tauraruwa fiyeda kowa a zuciyarsa kinji".
Kai kawai Amatallah ta jinjina mata, tasaka hannunta biyu ta share hawayenta, sai dai
k'asan zuciyarta tana tunanin yanda za'ayi ta zauna da Uncle d'in nata a matsayin miji, bayan
zuciyarta tana girmamashi tamkar mahaifinta, tabbas maganar Anty Nazeefa gaskiyace, babu
wanda zai kalli Uncle yace yakai shekarunsa, saboda k'aramin jiki da ALLAH yabasa, baza'a
kirashi siririba, hakama bashida k'iba, sannan yana tsaka tsaki a tsawo, ba dogoba ba gajereba
kuma........
Girgiza tan da Nazeefa tayi ne yasata sakin ajiyar zuciya.
Nazeefa tace, "kinga bar aikin mu karya tukunna ko".
" to".
Kawai Amatallah tace tamik'e, MacLean da brosh ta d'auka tafita.
Nazeefa tabita da kallo a sanyaye, tausayinta na kuma ratsata, a fili tace, "insha ALLAH
zakiyi farin ciki a rayuwarki Khadija, nasan ya Muhammad zai kawo sauyi a duniyarki, ALLAH
dai yak'ara baki hak'urin jurewa wannan jarabawa tarashin iyaye lokaci d'aya, kuma yakawo
mana sauk'in rikice-rikicen dasuke sanadin wargaza farin cikinmu a k'asarnan. ALLAH ma yay
miki gata ke, tunda yabarki da Ya Muhammad, a kwai yara irinki masu yawa dasuka shiga halin
k'uncin rashin families d'insu ta sanadin irin wannan rikice-rikicen *SIYASA KO K'ABILANCIN*,

amma rashin gata damasu tallafa rayuwar tasu yasasu shiga k'angin wahala da tarwatsewar
rayuwar tasu suma, ALLAH ka kawomana iyakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login